Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 16

Sponsored Links

Page 1⃣6⃣

Sultana Bilkisu ko da takoma gida cike da farin ciki tasamu Sultan Ahmad take bayyana masa yadda sukayi da iyayen zarah, shima farin cikinsa yanuna a fili yace gaskiya naji dad’i ammah kuma ba’a nan takeba,

murmushi sultana tayi tace nasan kana tunanin matsalar da zamu fuskantane wajensu memartaba da yarima?

Sultan Ahmad shima murmushi yayi yace tabbas hakane ammah Insha Alkahu komai zaizo da sauk’i kibani lokaci nima inyi tunanin yadda zamu 6ulloma lamarin domin maganar nan tana buk’atar tunani mai zurfi a cikinta.

Sultana Bilkisu Cike da damuwa tajinjina kai tace hakane nima zanje inyi tunani domin musamo mafita.

Sultan Ahmad tausayin matarsa yakamasa domin yasan yadda take son d’an nata, yace kidaina damuwa indai Allah ya k’addara akwai aure tsakaninsu toh za’ayi inkuma babu toh hak’uri zamuyi domin wani baya auren matar wani fatanmu dai Allah yashige mana gaba.

Sultana Bilkisu cike da gamsuwa da maganar mijin nata tace Ameen.

 

 

Gimbiya sumayya duk yadda taso tadaure kar tabada kanta ga yarima ammah kasawa tayi a daddafe tayi kwana biyu.

bayan sallar la’asar shiryawa tayi sosai tafito tanufi 6angaren yarima tana shirin shiga sai gashi ya fito da alamu fita zaiyi, kallo d’aya yayi mata yad’auke kai yana shirin ra6awa ta gefenta yawuce dasauri Gimbiya Sumayya tasha gabansa tace haba yarima wajenka fa nazo.

fuskar yarima babu alamun fara’a yace me zanyi miki?

Gimbiya kallonta takai ga dogarawansa da guards d’insa da duk kansu yake sunkuye suna jiran ogan nasu, ga kuyanginta da suke bayanta tsaye, kallonta tamaida ga yarima tace am daman, nan tafara kame-kame tace ko dai zamu shiga…… Yarima hannu yad’aga mata yace whatever ma dai you should meet me later, bai jira jin abinda zataceba yawuce dogarawan da guards d’insa suka take masa baya.

Gimbiya sumayya takaici duk yacikata ganin yadda yarima yadisgata gaban guards d’insa hararar kuyanginta tayi da kansu yake sadde a k’asa tacemunafukai kun zuba min na mujiya duk sai nad’au mataki a kanku.

dasauri duk suka zube k’asa suna cewa Allah yahuci zuciyar gimbiya, Allah yaja da ran gimbiya.

wucewa tayi fuu dasauri suka tashi suka take mata baya sunayi mata kirari.

ko da takoma part d’inta saman gadonta tafad’a tare da dafe kanta tsaki taja tace wannan mutumin bansan irinsaba anya yarima bai fara bin mataba? ya za’ayi yad’auki tsawon wannan lokacin batare da maceba? gabantane yashiga fad’uwa cikin d’aga murya tace No! i dont think yarimana akwai macen da zai iya kulawa wlh ba halinsa bane, chan takaima katifa bugu da hannunta tace inma akwai zan bincika domin nasan yarima baya iya kai tsawon wannan lokacin without ya yi making sex da niba ko da ace bana so, inma har naga akwai wadda yake tare da ita toh wlh ba zan bartaba sai na kasheta!!!

wayarta tajawo takira zinat bugu biyu tad’auka, muryar sumayya tana rawa tace wai ke zinat yaushe zaki dawo k’asarnan?

dariya zinat tayi tace kinyi missing d’ina ko?
tsaki sumayya tayi tace ke ni tambayarki nake.

zinat murmushi tayi tace Allah yahuci ran gimbiyar yarima very soon zan dawo nima ai nayi missing d’in k’asata.

Sumayya tace hmm Allah yasa dagaske kike, nidai in kindawo kifara biyowa ta wajena.

‘yar dariya zinat tayi tace sai kin ganni, sumayya dai badan ta yadda da maganar zinat ba takashe wayanta tare da komawa takwanta tana sak’e-sak’e cikin ranta.

 

Da daddare ganin ta kasa bacci yasa tamik’e tajawo alk’yabbarta tad’aura saman kayan baccinta tafito batare da ta nemi rakiyar kowaba tanufi 6angaren yarima addu’a take Allah yasa kar yadisgata domin ita tasan yau duk wulak’ancin da zaiyi mata ba zata damuba Indai zai biya mata buk’atarta inyaso daga baya sai tarama.

lokacin da tashiga ganin yarima baya parlour yasa direct tanufi bedroom d’insa, tsakiyan gadon tahangosa kwance idanuwansa a lumshe, cikin ranta tace lallai ma bacci yake

ahankali tataka tanufi gadon tahau takwanta a saman jikin yarima, muryarsa taji yace me kike buk’ata?

dasauri tad’ago kai takalli fuskarsa har a lokacin idanuwansa a lumshe suke ita tayi azan bacci yake, komawa tayi takwanta tace zuwa nayi intayaka bacci.

yarima dakyar yabud’e idonsa yasafkesu akan fuskarta yace sumayya kitafi kawai daman ai bake ketayani baccin ba saidai idan akwai abinda kike buk’ata.

Sumayya tallabo fuskar yarima tayi tace dear ni bacci kawai nazo muyi.

yarima janyeta yayi daga jikinsa yace ohk muyi baccin.

takaici yakama sumayya ganin yadda yake faujewa kamar bai fahimci abinda take nufiba, komawa tayi jikinsa tace wai yarima meyasa kakemin haka?

yarima kallonta yayi yace me nayi miki?

Shagwa6e fuska tayi tace naga yanzu kamar ka daina buk’atata, ka ma fita harkata, baka kula da ni bakasan yadda nake kwana nake tashiba baka tsoron hak’in aure?

yarima wata muguwar harara yawurga mata yace sumayya ashe kinsan hak’in aure? murmushin takaici yayi yace ammah ni kike tauyemin hak’ina.

sumayya haushine yakamata ganin yadda yarima yake neman wulak’antata cikin ranta tace kayi kagama ba zan damuba tunda ni nakawo kaina.

shafa sajensa tayi tace sweetheart yanzu dai shikenan na amshi laifina, yanzu kafad’i abinda kakeso zanyi maka.

yarima shuru yayi yakyaleta, marairaicewa sumayya tayi tace kayi magana mana.

Yarima murmushi yayi yace da zaki taimaka kibarni inyi bacci da nafi buk’atar hakan.

haushine yakama sumayya domin bata d’auka haka zaice mataba, ganin yadda tayi kicinkicin da fuska abun yaso yabashi dariya ammah yadake yace ya dai?

Sumayya d’auke kai tayi daga kallonsa tace suhail yanzu naga kamar ka daina buk’atata ko kasamu watane?

murmushi yarima yayi domin ya gano inda gimbiya tanufa yace Sumayya akanme zanta bibiyarki aini yanzu jikinki bai dameniba please kikyaleni ina buk’atar hutawa yanzu kinsan bana son yawan magana.

Sumayya fashewa tayi da kuka tace Suhail kaji tsoron Allah hak’ina fa? idan kai baka buk’atata nifa?

yarima d’aure fuska yayi yace ai banga alamun kina buk’ataba ni hak’ina nawa kika tauye?

gimbiya cikin kuka tace toh wlh ba zan yaddaba nidai nace kayi hak’uri.

Yarima cike da rashin damuwa yace shikenan naji zan taimaka miki, idan kin shirya toh bismillah.

 

Sumayya dai haka tabiyema yarima wulak’anci iri-iri yayi mata ammah lalla6asa tayi itadai burinta ya yabiya mata buk’atarta.

 

bayan komai ya lafa yarima tashi yayi yaje yayi wanka yazo yakwanta Sumayya mirginawa tayi jikinsa zata kwanta dasauri yarima yatureta yace kar kisaki kira6eni batare da kin tsarkake jikinkiba.

takaici yakama sumayya takoma gefe takwanta domin ita batayi shirin wanka yanzuba sai da asuba, cikin ranta tace yanzu ko zan fara rama wulak’ancin da kayi min.

da asuba saida yayo alwallah sannan yatadata dakyar tatashi saida yaga ta mik’e sannan yawuce masallaci.

 

tun daga ranar da sumayya taga tasamu biyan buk’atarta sai tadaina zuwa wajen yarima shi abunma dariya yake basa ganin sai tana buk’atar wani abu take zuwa wajensa, yarima bai wani damuba yace shi hakan ya fiyemasa da tazo tadameshi da surutu da haukanta.

 

*BAYAN KWANA BIYU*

yarima suhail ne a gidan gona tare da shaheed cikin wani k’ayataccen lambu, suna zaune bisa wani lallausan carpet da aka shimfid’a musu suna shan iska, daga chan nesa da su kad’an k’osassun guards d’insane tsaye, hannun yarima suhail rik’e yake da cup mai d’auke da ruwan inibi ammah ba sha yakeba, shaheed da yake zaune yana cin tufa kallonsa yakai ga wata ‘yar tsuntsuwa da tad’auke hankalin yarima.

murmushi shaheed yayi cike da zaulaya yace ranka yadad’e tsuntsuwannan ta burgekane asa guards d’inka sukamo maka ita?

yarima suhail shima murmushi yayi tare da kai cup d’in bakinsa yad’an sha ruwan inibin batare da ya kalli shaheed ba yace kawai ina kallonta ne ammah…

shaheed jira yayi yaji abinda yarima zai ce ammah yayi shuru, ganin haka yasa yace ammah ta burgeka ko?

yarima suhail aje cup d’in hannunsa yayi tare da juyowa yad’an kalli shaheed sannan yamaida kallonsa ga tsuntsuwar yace eh kusan haka.

shaheed ma kallonsa yamaida ga tsuntsuwar yana shirin yin magana nan wayan yarima suhail tafara ringing dasauri d’aya daga cikin guards d’insa yazo yad’auko tare da russunawa yamik’a masa.

Suhail kar6a yayi ganin Daddynsane yasa cikin sauri yayi picking tare da yin sallama.

daga chan 6angaren daddy amsa masa yayi tare da tambayarsa yana ina?

yarima cike da ladabi yace daddy ina gidan gona.

daddy yace toh kazo gida kasameni domin akwai maganar da nakeso muyi me muhimmanci.

Suhail baikawo komai a ransaba yace toh daddy ganinan zuwa.

 

bayan ya gama waya da daddy kallon shaheed yayi yace muje gida daddy nason ganina.

 

 

ko da yadawo direct turakar iyayensa yaje a parlour yasamu daddy da ummi zaune da alama jiransa suke, dasallama yashigo tare da samun waje k’asa gefen daddy yazauna nan yak’ara gaishe da iyayen nasa suka amsa masa.

daddy ne yayi gyaran murya yace suhail wani taimako ne mukeso kayi mana ammah bamu san ko zaka iyaba.

yarima suhail d’ago kansa yayi yakalli daddy yace daddy kunfi kar6in haka a wajena ni mai cika umurninku ne.

daddy jinjina kai yayi yace nasan haka, sannan yace suhail aure mukeson muk’ara maka.

A firgice yarima suhail yad’ago kai yakalli iyayen nasa yace aure kuma daddy? Ina fa da aure.

ummi tace munsan haka wannan ma za6inmu ce mukeso ka aura, halinta da tarbiyarta sunyi mana, sumayya ‘yar uwarkace kasan muna sonta, kawai alkhairine muka hango a tattare da k’arin aurenka, wannan alfarma ce muka nema a wajenka.

yarima suhail cike da tashin hankali yace kugafarce ni ummi ba wai nak’i bane kuduba kuga sumayya had’ani akayi da ita ba za6ina bace za6in memartaba ce, kuma a yanzu kuna neman kuhad’ani da wata, indai auren kukeso inyi toh na amince zanyi ammah kubari insamo za6in zuciyata.

Sultan Ahmad da ummi kallon juna sukayi sai chan sultan yace yarima ba wai munk’i ta takaba wannan auren za6inmu ne kaima kana da ikon auren za6inka a nan gaba ammah mudai muna buk’atar ka amince ma za6inmu insha Allahu akwai alkhairi a cikinsa.

 

Yarima shuru yayi na d’an lokaci yana tunani cikin ransa ko haushi yakamasa ammah baya ji zai iyayi ma iyayensa musu sai da yayi kusan minti biyu a haka sannan yad’ago kai yakalli iyayen nasa da suka zuba masa ido suna sauraren jin amsar da zai basu ahankali yabud’e baki yace daddy na amince zan aureta.

ummi da daddy farin ciki yakamasu kasa 6oye murnarsu sukayi sukace gaskiya munji dad’i sosai suhail yadda kafaranta mana kaima Allah yafaranta maka insha Allahu ba zakayi da nasaniba a cikin auren da zakayi.

yarima suhail murmushi kawai yayi batare da yace komai ba domin shi kad’ai yasan abinda yakeji a ransa na bakin ciki.

Daddy ne yanisa yace saidai wani hanzari ba guduba wannan auren bamusan kowa yasan mu muka had’asa munaso kanuna kaine kakeson yin auren, matsalar ma yanzu bamusan yadda yakamata a tunkari su memartaba da maganar ba.

 

gyad’a kai yarima yayi yace shikenan daddy ni zanje insamesa nasan abinda zance masa.

ummi tace a’a suhail kabari dai musamo mafita domin amincewarsu a lokaci guda kamar zatayi wahala.

 

d’an guntun murmushi yayi yace kar kidamu ummi kubarmin komai a hannuna.

ummi tace to yaushe zakaje kagano matar taka? na tabbata kaima zaka sota

 

haushi yak’ara kama yarima jin wai ummi ta ce zaiso wata, girgiza kai yayi yace no ummi ba sai najeba.
nan yayi musu sallama yataso yafito ransa duk a 6ace duk gaisuwar da mutane suke duk’ewa suna k’wasa bai amsama ko mutum d’ayaba yawuce yakoma part d’insu yana shiga 6angarensa guards d’insa yayi ma warning kar subari kowa yashigo ko da kuwa gimbiya sumayya ce.

 

koda yashiga saman gadonsa yazauna tare da dafe kansa yana jin wani iri a ransa ganin duk an watse masa budget domin kwata-kwata bai shirya k’ara aure yanzuba yafiso sai yasamu macen da yakeso sai ya aureta, tsaki yaja tare da kaima katifa naushi cikin d’aga murya yace wacece wannan wadda iyayena sukeson had’ani da ita me ke gareta da har tarud’esu taja duk wani plan d’ina ya watse tashi yayi yashige toilet tare da sakarma kansa shower.

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Wannan page d’in nakune my *Blood Sis Aufana nd Mummy Sainah Ummun Meenal* hak’ik’a kunfi k’arfin page a wajena, fatana Allah yabarmu tare ‘yan uwa nagari_

Back to top button