Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 20

Sponsored Links

Page 2️⃣0️⃣

 

 

Duk zuba ido sukayi suna karewa dakin kallo kamar daga sama suka farajin busan sarewa hade da kakaki me shegen dadi,wani farin hayaki ne yake ta bulbulowa adakin Yana fitar da kamshi me dadin shaka , ga sanyi me ratsa jiki da zuciya Yana ratsa su , hayakin yanakan cigaba da fitowa tako wace bangare, lungu da sakoh seda yazamana basa kallon komai tsaban yanda hayaki ya maimaye cikin dakin sunfi minti 10 kafin nan yatsaqaita , jakadiya abashiyya nahango tsaye cikin shiga na alfarma dakuma nuna itadin tafito daga masarauta ne , dogon riga take sanye dashi me matukar girma farine tass badigon wani kala ajikinshi se gold,duk jikin rigan anmishi kwalliya da duwatson zinari,
Saman rigan Dede cikinta andaureshi da belt fari da gold stone ajiki hannun rigan nada girma gabadaya rigan an mata kwalliya ne da gold , hannunta Da wuyanta da kunnen ta sunsha kayan ado duk zinarine , fara ce Sosai fari bana wasa ba, Babbar mata ce kyakyawa idonta manyane sosai sannan ba irin namu bane cikin kwayar idon fari ne sal eyeballs dinta yakasance Shiba fari ba shi ba ruwan toka ba se shekin dayakeyi , gashin kanta kuwa tsaban tsawonshi yawuce guiwanta yakusa karasa kafanta Dake sanye da tumsa me matukar kyau kallo Daya zaka mata kagane ita din badaga jinsin bil adama take ba. Suman tsaye su ya al ameen sukayi sunkasa motsa Koda hannunsu ganin aljana agabansu , murmushi me qayatarwane dauke afuskan abashiyya sunkuyar dakai baba da mama sukayi alamar girmamawa sude su suhaima idonsu qyam akanta matsowa tayi daff da inda suke ” barka da wannan lokaci yakai Muhammad, uba agun sarauniya wacce takansan shugaba agunmu ,jaruma Kuma sarauniyar nasminaya ” tagama fadin hakan tana kallon mama da ita kwata_kwata bataji dadin hada hanya dasu ba tayi bakin cikin hakan matuka aduk sanda suka ambaci fanan amatsayin sarauniyarsu bakaramin Kuna zuciyarta takeyi ba Amma yazatayi kaddara tariga fata haka Allah ya rubuta Kuma shikadai yasan dalilin hakan domin kuwa kowani Dan Adam tun kafin yazo duniya kaddararsa arubuce take da abinda zesameshi , farin ciki ko akasin hakan , wannan ne kadai inta tuna hankalinta yake dan kwanciya tasan komin qaqa yarta bazata taba barinta ba tunda ita ta tsuguna tahaifeta tasha wahalarta . Duk abinda take tunani abashiyya nasane da hakan tausayin mama ne yaka mata domin babu uwar dazataso rabuwa da yarta Koda kuwa babu shakuwa atare dasu Amma babu yanda zasuyi fanan tariga da tazama wani bari na rayuwansu tundaga ranan da takai wata biyar 5 acikin mahaifiyarta. Murmushi tayiwa mama , mayar mata da murmushin mama tayi duk da nata yakasance na yake baba ne yajuya yakalli su ya Usman dasuka daskare guri Daya yace ” kukam Baku iya gaisuwa bane !?” Firgit sukayi suna kallon baba da alaman tambaya afuskansu ya al ameen ne yayi karfin halin fadin ” wa!waye din zamu gaisar!?” Tsuke fuska baba yayi bakuga munyi bakuwa bane ” kallon su suka maiyar kan abashiyya da itama sudin take kallo tana murmushi cikin inda_inda kamar wayanda suka hada Baki wajen fadin ” Ina kwanaaaaaaa” fuskanta asake ta amsa musu da “lafiya Lau yarana ” sude Basu Kara cewa uffan ba ganin lamarin sukeyi kamar almara wai yau aljanace agidansu sannan baba harcewa yakeyi su gaisheta tabbas akwai abinda ake boye musu. Tafiya takeyi ahankali harta karaso bakin gadon fanan Dan ta tasheta daga baccin datakeyi saboda ta gabatar da sallah, tana kokarin tabatane khairatyyy tabayyana a dakin innalillahi suhaima kam guduwa take kokarinyi ya al Ameen yariketa gam yaki sakinta duk da suma sundan tsorata Amma suka danne yarinyace kyakyawa itama tana sanye da irin kayan da jakadiya abashiyya take sanye Amma nata bekai na abashiyya ado ba itakam khairatyyy gashinta har ja yakeyi da kasa, cikin girmamawa tace ” shugaba nayi yanda kika umarceni da inyi sannan yafadamin babu abinda sarauniya tamasa kawai son zuciyane yasashi sha mata jini shine aka yanke mishi hukunci” “Masha Allah khairatyyy Allah yamiki albarka ” cikin jindadin anya beta tace “Ameen yake shugaba” maimaita sunan kawai ya Usman yakeyi khairatyyy….? Wow suna me dadi tunda tabayyana yaji ta tafi da imanin shi dukda yadan tsorata , kallonta kawai yakeyi komai nata burgesa yakeyi nan take zuciyarsa takamu da santa ( tofa ana wata ga wata kaikuma Usman meya maka zafi haka daga ganin yar kyakyawar yarinyar aljanu harka fola to nide baruwana nayi nan )
Shafa fuskan fanan abashiyya tayi nan take tamike da salati abakinta ita bataga kowa ba se su mama da su baba dasauran Yan gidan kallonsu takeyi da mamaki ganin su kaff adakinsu abinda be taba faruwa ba tunda tasan tayi wayo baba Sau biyu yataba shigowa dakinta nan ma lokacin bata da lafiyane suka shigo shida ya Usman dubata mamace de take shigowa se auta , zura kafafunta kasa tayi tamike tsaye zubewa akasa abashiyya da khairatyyy dakuma sauran dogarawan fanan dabaa ganinsu sukayi akan guiwowinsu kansu akasa . Rike hannun mama fanan tayi tana fadin ” mama meyake faruwa na ganku anan wani abun yafaru ne!?” Ya al ameen ne yayi saurin cewa ” wai fa suhaima ce tana tashi daga bacci taga kadangare adakin ku shine tafasa ihu mu mundaukama wani Abu ne yafaru Ashe wai kadangare takewa wannan ihun Kai suhaima Allah yashiryeki ” kallon cikin idonta yayi ganin ko karyan dayamata yakarbu se gani yayi tajuya tana kallon suhaima tana dariya kasa kasa ” wallahi suhaima Allah yashiryeki yanzu kadangare kikewa ihu haka ” itade suhaima Jin irin karyan da yayanta ya zambada ne yasata taketa murmushin yake dan haryanzu taki sakin jikinta, ” fanan jekiyi sallah kizo kishirya kitafi aikinki Kinga zakiyi letting kinji !? Cewar mama dake ficewa adakin, toilet tashiga zatayi alwala fita suka farayi one by one Amma Banda ya Usman da haryanzu yanata kallon babynshi , ya al ameen magana yake mishi Jin shuru ne yasashi kallon direction din da yake kallo yayi sauka idonshi yayi akan khairatyyy da haryanzu suke zube akan guiwowinsu basu ko dago ba, kama baki Al ameen yayi Yana ganin iKon Allah meyake shirin faruwa meye dalilin da zesa Usman yakafe khairatyyy da ido haka Allah yasa ba abinda yake tunani bane Tabb inde hakane usman yadauko wa kansa dala ba gammo . Jan hannunsa yayi sukabar dakin, suhaima zama tayi abakin gado kasa_kasa take kallonsu dede lokacin da khairatyyy tadago idonta sukayi 4 eyes dasauri suhaima takawar da kanta gefe dariya abin yabawa khairat Dan tagane suhaima tsoronta takeji kasancewar ita idonta yafi na jakadiya girma, fitowa fanan tayi daga toilet din tayi wanka tare da alwala hijab tasaka ta tada sallah bayan ta idar ne tana zaune tana azkar ta tuna abinda yafaru adaren jiya Amma setake ganinshi amafarki share lamarin tayi tashi tayi tana cewa ” suhaima iyayen tsoro Dan mikomin kaya acikin wardrobe Dina mana ” cike da masifa suhaima tace ” Nina san kalan kayan dazaki sakane ” kumshe dariyan dayazo mata fanan tayi Dan tasan suhaima tashaqa bata Kara bin takan taba taje tabude wardrobe din tadauki abaya Baki me kwalliyar blue …

 

 

Zaune take adakinta ta buleshi da hayaki tana Shan shisha kayan jikinta dasu da babu duk dayane hannunta na rike da tiyo din shisan tana zuqa gaba daya abuge take idonta harwani rufewa yakeyi ringing din wayartane yasa tawaro idonta dasukayi jaa picking tayi tasa akunne tana ” hello mommy ” adaya abangaren aka amsa da ” aneesa meyasa duk abinda zangaya miki bakya jine ban hanaki shaye_shayen nan bane ahakan ne kike cewa kinason Azaad inya San kina shaye_shaye zeyarda ya aure kine ansamu Abubuwa sunfara tafiya smoothly and now you’re trying to ruin everything right!? rai abaci mommy take magana, wastsakewa aneesa tayi ta kashe choal din katse Kiran mommyn tayi cikin hanzari tamike tanufi toilet dinta tana tafiya tana tangal_tangal kamar zata fadi shower tasakarwa kanta tafi 20mint kafin taji tafara dawowa Dede dakin tadawo tana sanye da towel dialing din number mommy tayi bayan tadagane take cewa ” am sorry mommy nayi kwana biyu bansha komai bane yau kuma natashi Ina matukar missing dinsu shisa nasha but it won’t happen again” ajiyar zuciya mommy tasauke tace ” better yanzu abinda nakeso dake duk wani abinda kikeyi kibari kihado kayanki kidawo gidan nan dazama idan Kuma bahaka ba karki yarda kiyi kuka da kowa” cikin rashin fahimta aneesa tace ” mommy meyasa zandawo gidan dazama isn’t necessary? impact why would I come over to your house and stay gaskiya bazeyuba azaad ze takuramin baze taba barina inyi abinda nakeso ba” cikin tsawa mommy tace ” am doing this for your own good aneesa tunda ke bakisan ciwon kanki ba to ki tsaya kallon ruwa kwado yamiki kafa yar alhaji badamasi me ruwa yarsa nusaiba datake mutuwar son azaad yanzu haka flight dinsu yatashi tana hanyar zuwa gombe yanzu shawara yaragewa meshiga rijiya ” katse wayarta tayi ranta a matukar bace taurin kan aneesa Yana bata mata Rai.

Abangaren aneesa kuwa bakaramin tashin hankali tashiga ba Jin datayi wai nusaiba nahanya batayi wata_wata ba ta mike trolley dinta tadauko duk abinda tasan zatayi amfani dashi tasaka aciki , wando jeans fari tasa da Tshirt orange color tasa Sannan tadauki wata karamar gyale fari tadan Yana akanta number masu aikin gidan takira shigowa dakin wani security yayi nuna mishi trolley dinta tayi yafitar dashi waje yasa mata a boot sannan tafito afalo tasamu hajiya Zainab ( mahaifiyarta) ko kallonta batayi ba tawuce abunta girgiza Kai hajiya tayi tace “Ubangiji Allah yashiryamin ke yasa kigane hanya”

Horn sukayi wangale musu gate din akayi driver yashigo yaje yayi packing fitowa nusaiba tayi tana bin gidan da kallo setaga komai yacanza ko dan tadan dade batazo bane shiga ciki tayi driver nabinta abaya da akwatin kayanta,suna shiga falo tahango ummi dagudu tafada jikinta tarungumeta ” wayyo ummina nayi missing dinki wallahi ” shafa kanta ummi tayi “nima haka nusyy ya mutanen gidan ” kowa klau ummi kallon zeenat tayi wacce tayi kicin_kicin da rai kamar batasan da zuwanta ba tabe baki nusaiba tayi ummi ce tace ” tom tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci Koh!?” Tom ummi haurawa upstairs tayi tashiga dakin datake sauka Dan kwata_kwata basa shiri da zeenat jininsu bezo dayaba balle suzauna daki Daya.

Fitowa fanan tayi cikin shirinta tsaf na tafiya afalo tasamesu suna kokarin fara karyawa “baba nizan wuce”

Jiya danayi posting kukata magana short page ne bashida yawa Gsky page din yayi guntu , to abinda yasa banasamun comment yanda nakeso ne kamar jiya mutane kalilan ne sukayi comment , nibazance bazanyi posting ba Amma kam zakuta ganin guntun page inde bazaku dingayi comment ba . Ballema in bakuyi comment ba wlh ba lallai inyi posting gobe ba

 

 

SE mun hadu gobe ko jibi inda Rai da lfy

 

 

 

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story Written by ( MRS ISHAM )

 

 

Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

 

 

Free book

 

 

____________________________________________

Back to top button