Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 31

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na talatin da ɗaya_

_____________

*_ZAFAFAN DAI_*

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤‍❤‍❤‍

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

______________

……A hankali take buɗe idonta jin kamar ana ja mata yatsan ƙafa. Sunanta da ya sake ambata kamar mai raɗa ya sata buɗe idanun da ƙyau. Shine kuwa tsaye cikin tattausan jallabiya sai ƙamshi yake kamar ba asuba ba. Sake faɗin, “Tashi asubahi yayi kiyi alwala” da yay ya sata jin jina masa kanta cike da kunya. Sai dai ta gagara motsawa dan ji take bazata iya hakan a gabansa ba. Fahimtar hakan da yay ne ya sashi juyawa yana ce mata, “Na wuce massalaci ni”. Bata iya sake cewa komai ba harya fice. Cikin sauri ta sakko a gadon dan Alhamdullah bata jin komai yanzu zazzaɓin ya tafi. Harta nufi ƙofa sai kuma ta koma. Gadon ta shiga gyarawa a gaggauce ta gama tsaf tamkar ba’a shine suka kwanta ba. Gani komai ya mata yanda yake so ta fita. Sashen gaba ɗaya ta bari dan jiya da Noor ta mata jagora duk da kanta a rufe yake tana gane hanya. Da sanɗa ta shiga sashenta. Motsin ƴan rakiyarta da taji a ɗakuna biyun dake a sashen nata yasa ta saurin shigewa na can ciki da aka kaita. Tana maida ƙofar ta juyo da jingina jikinta idonta a rumtse tana sauke ajiyar zuciya. Buɗe idon da zatayi suka haɗa ido da aunty Firdausi, sai aunty Luba dake salla. Daburcewa tai, amma ganin Aunty Firdausin ta ɗauke kanta cike da basarwa itama saita wuce toilet da sassarfa kamar zata faɗi. Kai kawai aunty Firdausi ta girgiza tana sakin murmushi. Ta jima kafin ta fito a bayin, dan bayan tai alwalar sai tai tsaye tana shawarwarin fitowa da tunanin kallon da su Aunty Firdausin zasu mata. Jin massalatai har sun fara idar da salla ya sata fitowa a sanyaye, sai dai ta tsuke fuska ta yanda karma su mata wata tambaya. Tama samu basu idar da sallar ba, dan haka itama ta saka hijjab ta kabbara tata a bayansu.
Koda suka idar da sallar babu wanda yace mata komai. Sai ma bayan gaisuwar datai musu suka koma hirar irin karamcin da akai musu a gidan da yanda wasan jiya yay matuƙar ƙayatar da su. Khadijah dai na saurarensu bata saka baki ba, a haka ma barci ya saceta sai da aunty Luba tace ta tashi ta koma gado sannan ta miƙe… Kallon juna sukai suka saki murmushin shaƙiyanci kawai. Sai dai babu wanda yace komai…

Misalin takwas da rabi Gwaggo Safina ta shigo ta tada Khadijah wai taje tai wanka haka nan su kaita ta gaida surukarta. Suma zasuyi shiri ne zuwa goma zasu wuce in sha ALLAHU. Jiki a sanyaye tabi umarnin Gwaggo. Tsaff tai wankanta Aunty Nabela tai mata kwalliya kaɗan ta shirya cikin atamfa datai mata matuƙar ƙyau da amsar jikinta golden, sai ƙyalli take da ɗaukar ido ga kwalliyar stones tasha mai sheƙi. Ga wani uban ƙamshi na tashi a jikinta kamar fadar miss xoxo ta haɗa turate. (Mai son YERWA INCENSE AND MORE ya nemi wannan no ɗin 08095215215. Kayan ƙamshi ƴan gaske na maidugiri guys karku bari ayi babu ku) An kawo mata abincin karin da aka kawo musu mai rai da lafiya. Dan farfesune har kala biyu da kayan shayi da soyayyen doya da masa. Shayin kawai ta ɗan sha kaɗan tace ta ƙoshi, duk yanda su Aunty Luba ke mata faɗan ta dinga cin abinci bata iya tacin ba sai kuka da take neman yi musu, dole suka ƙyaleta.
Su Gwaggo sun kaita ta gaisa da Mamy, anko karramasu sosai dan suma sun ji daɗin girmamawar da dangin Khadijah suke musu. Khadijah dai yau ma kanta a ƙasa ta kasa kallon kowa. Sai ma Noor ce tazo ta leƙata a mayafin tana dariya. Mamy dakema Noor daƙuwa ta tambayeta yaya jikinta. A kunyace ta amsa da cewar alhmdllh taji sauƙi. Murmushi kawai Mamy tayi dan ta fahimci surukar tata badai kunya ba. Basu wani jimaba sukai musu sallama aka dawo da ita. Zaman sake mata faɗa akayi, yayinda iyaye ke haɗa kayan garar da sukazo da shi dana rabo domin miƙawa sashen Mamy. Dai-dai nan Noor ta shigo da sallama, amsa mata sukai da fara’a, cike da girmamawa ta sanar musu Hammanta zai shigo ya gaidasu ne gashi a ƙofa. Da sauri suka shiga gyarawa dan kusan duk iyayene a wajen babu mai son suruki ya shigo ya gansa a mummunar kama. Amsa mata sukai daya shigo, dan haka ta koma wajen ta sanar masa. Ita ta fara sake shigowa kafin wata sassanyar murya tai sallama a ƙofar falon. Kasancewar ba wani surutu sukeyi sosai ba yasa suka jisa, dan duk isu-isu mayanne a falon wanda ke a cikin ɗakunan ƙalilanne irin su Khadijah da auntys nata ke can sun saka tsakkiya da nasiha da sake koya mata dabarun riƙe miji suna kuma sake banka mata abubuwa.
Kamar ko yaushe ƙamshinsa ne ya fara shigowa kafin shi. Kansa a ƙasa cike da girmamawa ya kai duƙe yana gaishesu. Suma dai kawunan nasu a ƙasa suke. Sai masu ƙarfin halin satar kallonsa ƙasa-ƙasa suna gulma da zukatansu da tsarkake sunan UBANGIJI dan kuwa Abaan cikakken bafilatani ne zirryan babu gauraye ƙyaƙyƙyawan gaske. Ya jera musu godiya sosai da addu’a kafin ya miƙe. Inna Zulai da bata san Khadijah a ɗakinsa ta kwana ba, dan su duk tunaninsu bayan Doctor ya dubata nan ta sake dawowa. Cikin dattako da hange irin na manya ta ce, “Ka shiga suna ciki ai su Khadijahn tare da sauran ƴan uwanta”.
Kasa yimata musu yay, dan haka ya kalli Noor data masa rakkiya ƙasa-ƙasa, da ido yay mata alamar tayi gaba. Dariyar dake taso mata ta haɗiye, dan tasan wanene Hammanta akan kunya. Yanzu ma da ƙyar Mamy ta kaɗoshi zuwa gaisuwar nan. Anan ɗin ma sai da Noor ta shiga ta sanar da zuwansa sannan ya shiga. Tuni su Aunty Luba sun kimtsa suna ma tsatstsaye ne. Khadijah kuma na zaune a bakin gado yarinyar Aunty Saddiqa na hannunta tana ɗaura mata ƙananun band a kai, sai mutsu-mutsu yarinyar keyi alamar bata so. Itako ta dage saita mata dan yarinyar akwai gashi masha ALLAH. Kafin ma ya gaishesu su tuni sun fara gaidashi saboda yanda kwarjininsa ya wani cika musu ido. Shiko kansa a ƙasa tun kallo ɗaya da yayma Khadijah bai sake ɗago kansa ba. Da ɗaɗɗaya suka dinga fita, hakan ya sashi miƙewa da ga ɗan ɗofanar da yay a hannun sofar dake ɗakin ya koma gaban mirror dake facing Khadijah da sam taƙi yarda ta kalla inda yake. Aikin ma Baby Zeenat kitso kawai takeyi duk da tunda ya shigo gabanta ke faɗi ta daure bata kallesa ba. Ga kunya dan abinda ya faru jiya yana yin sallama komai ya shiga dawo mata dalla-dalla.
“Boddo kin tashi lafiya?”.
Ya faɗa cikin muryarsa mai fita da nutsuwa da sanyi. Jitai kunya ta sake lulluɓeta dan tasan fassarar Baddo ɗaya kirata. Kamar aɗan daburce ta ce, “Ina kwana” batare data yarda ta kallesa ba.
“Uhhm dama haka ake gaida miji?”.
Kamar zata fasa ihu taji, dan wlhy kunyarsa take ji sosai. Amma taga shi ko’a jikinsa kai tsaye yake mata magana kamar sun wani saba. Ƙoƙarin gyara baby Zeenat dake zamewa take, sai son matse yarinyar take itako taƙi yarda shima take miƙama hannu alamar son ya ɗauketa. Murmushi yayi da tasowa daga jinginar da yay a mirrorn ya ɗauka yarinyar. Hakan ya bama hannayensu damar haɗuwa waje ɗaya. Da sauri ta janye nata kamar wadda lantarki ya taɓa. Duk da shima yaji shock cikin dakewa ya fuske abinsa yana komawa jikin mirror da ɗan ɗaga yarinyar sama yana mata wasa. Itako sai faman wangale masa baki take.
Mamakin yanda ya shagala da yima yarinyar wasa yasa Khadijah zuba masa ido batare data sani ba. Karaf kuwa suka haɗa idon, da sauri ta janye nata cike da kunyar kamata tana kallonsa. Cikin son ƙara bata kunyar ya furta, “Ina matuƙar son yara da yawa. Ina fatan kin shirya bani nan da wata tara Boddo!”.
Sosai kuwa ta rikice ta daburce da kalaman nasa. Har yanda tayi ɗin yaso bashi dariya. Dan dama ya faɗa ɗinne dan yaga yaya zatayin. Aiko ya gani fiyema da yanda yay tsammani. Dan har sai da ya ce, “Uhhm ayi haƙuri to wasa nake. Yaya jikin naki? Babu zazzaɓin dai ko?”. Ya faɗa cikin son kauda waccan maganar. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke da jinjina masa akai alamar eh babu. “Alhamdullah ALLAH ya ƙara afuwa. Bara naje Awwal na jirana dan ina da baƙin da zan gani nanda awa ɗaya. Ina dai fatan babu wata matsala ko?”.
Nanma kanta ta jinjina masa, sai kuma a hankali ta ce, “Babu komai”.
Ya ce, “Masha ALLAH. Mamy tace min yanzu baƙinmu zasu wuce. Naso su bari sai zuwa gobe su sake hutawa amma sunƙi yarda da hakan.”
A take idanun Khadijah suka ciko da ƙwalla, muryarta a karye ta ce, “Dan ALLAH ka sake roƙonsu, bana son su tafi nima”.
Cike da tsokana ya ce, “Idan kin yarda zaki sake kwana ɗakina yau ɗin ma mizai hana na roƙesu sumayi mana sati”.
Da sauri ta maida kanta ƙasa kunya kamar ta nutse a ƙasa take ji. Ƙaramar dariya yayi da dire mata Zeenat kan cinya. A wata bazatar taji saukar sumba a gefen kuncinta. Kaɗan ya rage ta saki Baby Zeenat ƙasa. Shiko ya nufi hanyar fita yana murmushi da faɗin, “Ki kula da kanki sai na dawo. Banda kuka, banda tunani”.
Kasa amsa masa tayi dan ya riga ya gama kaita ƙarshe a kunya…..

__________★

Kamar yanda Dafeeq ya buƙata Kainaat ta amsa da hannu biyu kam, dan akwanikan nan da suka gabata suna zaune lafiya sai dai ta ciki na ciki. Yanda yay alƙawari ya dawo mata da duka takardunta, hakan ya sakata jin matukar farin ciki har wani sashen zuciyarya na mata kokwanton anya kuwa bada gaske Dafeeq keyi ya zubar da makamansa ba? Sai dai wani sashe na kwaɓarta da hakan kuma. Dan haka ta cigaba da saka masa ido kamar yanda ta shirya masa, tare da fara aiwatar da plan ɗinta itama.
Idan ka gansu a yanzu zaka ɗauka wasu masoyan arziƙi ne. Dan kowa na ƙoƙarin ɓoye mummunar manufarsa akan ɗan uwansa. A zukata kam da wahala a haɗu ba’a zagi juna ba. Kullum tare suke zuwa aiki su dawo. A gidan ma suna manne da juna ko yaushe. Kamar yanda ya saba zuwa gida Kano duk ƙarshen wata wannan watan ma yay shirin hakan. Harda yima Kainaat tayin ko zataje. Kamar tace a’a sai kuma ta canja shawara tace da shi zataje. Sun gama shiri tsaff tun a daren jiya yau da safe ta wayi gari da ciwon ciki mai tsanani. Hankali a tashe tun asuba suka nufi asibiti, tako samu kulawar gaggawa kasancewar likitan nada alaƙa da Abaan, dan kusan ma shine silar saninshi da tayi. Bayan sun rabu kuma bata daina zuwa wajensa ba, shi kuma bai taɓa tunanin bama sa tare da Abaan ɗin ba tunda alaƙar likita da maralafiya ce kawai ta haɗasu. Ko aure da yasamu labarin yayi a kwana uku da ya wuce wani abokinsa ne ke faɗa masa, shine ma ɗazu yay kiransa ya tayasa murna. Ganin Kainaat kuma a yanzu ta sashi tunanin toko suna ma a Adamawa ne anan akai bikin? Sai dai yayi mamakin ganin wanda ya kawota dan shi Awwal kawai ya sani makusancin Abaan dakan iya kawo matarsa ko ƙanwarsa ko Mamansa asibiti. Amma dai sai baice komai ba ya shiga bata kulawa yanda ya kamata. Har kusan azhar sannan ya sami nutsuwar zama, result ɗin gwaje-gwajen daya bada amata aka kawo masa. Cike da farin ciki da zumuɗin ganin abinda sakamakon ya bada ya shiga laluben neman Abaan a waya batare da yayi tunanin fara magana da wanda ya kawota ba. A kiran farko ba’a ɗaga ba, sai baiyi tunanin komai ba tunda yasan Abaan da sabgogi. Kusan mintuna goma tsakani sai ko ga kiran Abaan ɗin ya shigo masa. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗauka tare da rangaɗa sallama ta girmamawa…….✍️

_Kai dai wannan likita sam baka da man kai gaskiya_

Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846

Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria

Ummu khalifa 01017018846

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button