Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 26

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*26*

Da safe Hajjo ta tashi fuska a kumbure saboda tasha kuka a boye bayan ta gama Jin tarihin rayuwar inna da Kuma abunda take Shirin aikatawa , inna ta Gane lagonta Amma tayi banza kamar batasan meke faruwa bayan sun gama breakfast wayar inna tayi Kara masoyin nata ta dauka ta shige daki hajjo ta tabe Baki tana kallonta suka hada Ido da maman Nana ta sauke numfashi tace ” kiyi hakuri Hajjo nasan baza kiji dad’in wannan lamarin ba Amma Ina son ki taya malama da adua Allah ya zaba mata Mafi alheri Kuma ni banga laifin Hakan ba a kalla dai tayi kokari ta share shekaru tana fama da gwagwarmaya Kinga Allah ya kawo mata mafita dole ta karba da hannu biyu biyu ” tabe Baki ta sake Yi ta ba tare da tace komai ba, maman Nana ganin haka taja bakinta tayi shiru. Haka rayuwa ta cigaba da gudana Hajjo ta zama so silent tana yawan tunanin mahaifinta yanzu girma yazo hankali ya fara shiga tasan ciwon kanta ita dai Bata son wannan auren da inna ke Shirin Yi saboda yanzu shiri inna take Babu Wani boye boye har ta fara wasu Yan siyayya irin namu na mata, gaba d’aya zaman gidan ya daina mata dad’i gashi Babu kayan kallo bare ya Debe mata kewa sai wayar maman Nana da take game dashi, ita ba kawaye ba Kuma Bata zuwa ko’ina kullum tana gida sai bitar karatun addini da inna ke musu duk dare tare dasu maman Nana. A kwana a tashi wata biyu ya kare anfara komawa school ana registration na zuwa Ss1 a wannan lokacin su Aman ke rubuta final exams nasu a jami’a, inna ta tattara kudaden hannunta da Wanda ya Yusuf ya Bata ta shirya zuwa registration a skul dinsu hajjo tana zuwa Mrs Juliet ta shaida mata anriga an biya komai har kudin WAEC da NECO Bude Baki inna tayi cike da mamaki tace waye haka, murmushi Mrs Juliet tayi tace ” wannan dan uwan naku kyakkyawa” murmushi inna tayi daga haka ta nemi list din abubuwan da Ake bukata ta koma gida tana zuwa ta labartawa maman Nana tace ” ni bansan dame zan sakawa yaron nan ba mmn nana, ya gama min komai na rayuwa Allah ya saka masa da alheri Kuma Kinga ko gayamin Baiyi ba ” Anya malama ba son Hajjo yake ba wannan kyautatawan tayi yawa ” hmm..kin manta saboda Dan uwansa yake wannan karamcin ” toh Allah ya saka masa da alheri ” Amin ya rabbi yanzu zan kirasa kuwa a waya ” nan ta fito da wayar ta fara Neman layin Ayman yayi ringing Bai d’aga ba har ya katse. ta ajiye ta nemi abinci ta zauna taci hajjo na kwance a daki tun bayan ta fito ta mata sannu da zuwa ta koma Bata sake fitowa ba, suna dan taba hira da maman Nana har aka kira magariba suka tashi suka gabatar da sallah suna zaune a tsakar gida sallama yayi suka amsa take gidan ya cika da qamshin turarensa na kamfanin Avon . Murmushi inna tayi tace ” d’an gidan inna ashe kana nan tafe” karasowa yayi inda aka shimfida masa dardumar sallah ya zauna nan ya gaida inna sannan maman Nana, bayan sun gaisa ne inna ta kawo masa kunun aya da jallof din taliya da sukayi , kunun kadai yasha yace ya koshi . “Kai dai baka gajiya da dawainiya Ayman wato sai da kaje ka biya kudin makarantar yarinyar nan bansani ba, Allah ya Bada Lada yayi albarka Allah ya Kara arziki” Ameen ya Allah inna akoda yaushe aduar ki nake bukata, Ina so ki kara adua yau na kammala karatu Alhamdulillah saura jiran results a sakamu a adua ” ” Masha Allah congratulations Ina tayaka murna Allah yayi albarka ya albarkaci abunda aka karanta ” Ameen ya rabbi nagode inna ” ya Dade suna hira kafin ya tafi . Washegari inna suka tafi kasuwa da hajjo sukayi shopping din abubuwan da take bukata murna agun hajjo baa cewa komai dama tagaji da zaman gidan , har bayan azahar suka koma gida nan ta karasa sauran shirye shiryen komawa. ranar da zata tafi ta dauka da motar kasuwa zasu tafi domin mashin sukahau da kayanta zuwa under bridge din maraba suna nan tsaye inna tana waige waige can bayan mintuna goma sai ga wata prada jeep tayi parking kusa da inna aka sauke glass ” magirah ” nan suka hada Ido dashi ya sakar mata Wani murmushi inna tana sanye da doguwar hijab har kasa ruwan Hoda ya matukar fito da kyaunta , hajjo ta kura masa Ido nan driver ya fito ya Bude booth ya shigar da kayan nasu sannan ya Bude mata back seat inna ta juya tace ” taho muje” Babu gardama hajjo ta shiga kusa da inna ta zauna driver yaja suka kama hanya, cikin sanyin murya hajjo ta gaida uncle Yusuf ya amsa cike da fara’a Yana mata Yan tambayoyi tana bshi amsa . Basu zarce koina ba sai H-medix dake wuse sukayi parking nan yace su fito inna tace ” Yaya mungama siyayya fah Babu abunda ya rage ” kingama naki ki barni nayi nawa , this the first time we met ” Bata Kara cewa komai ba tasan halinsa baya son gardama nan suka shiga ya fara lodawa hajjo Wani sabon shopping na kayan bukatu da kayan makulashe ya gama ya biya driver ya fito dasu daga nan suka wuce school din nasu Kai tsaye.
Sun b’ata lokaci a makarantar saboda dalibai Dake dawowa anyi checking angama komai daga nan suka mata sallama suka tafi bayan inna ta Kara mata nasiha da Jan kunne, maimakon su Kama hanyar gida sai Kuma suka shiga gari inna tace ” Yaya sai Kuma Ina?”
Murmushi yayi Ya juya ya dan kalleta yace ” gidanki zan kaiki ki gani ” Bata ce komai ba sukadau hanyar Apo , bayan dogon tafiya suka iso tangamemen estate din Wanda aka rubuta da manyan haruffa *Amina court Apo* inna tana kallon tsarin unguwar nan ta lumshe Ido tana tasbihi ga ubangiji lallai idan kayi hakuri a rayuwa bayan wuya sai dad’i nan ta tuna gidan Sulei inda tayi rayuwa a can baya da Kuma Aso unguwar makafi, numfashi ta sauke tana Kara Mika godiya ga ubangiji komai na duniya Mai karewa ne wataran sai labari a dai dai nan akayi parking yace ta fito , da Kansa ya Bude mata mota ta fito suka jera yasa keys ya Bude gidan nan ta fara kallon gidan samane Hawa biyu falo 3 wato kowane floor akwai falo da dakuna , a second floor ne kitchen yake da dinning area da babban falon da yafi sauran girma Kuma kowanne an shirya tsaf da kujeru da kayan alatu. Inna dai kasa magana tayi tasan dai gidansu babban gidane na sarauta Basu rasa komai ba na rayuwa Amma wannan gidan ta cire ran zama cikin irinsa a rayuwarta gaba d’aya bayan aurenta da Sulei, ” gimbiyata gidan yayi ko a nemi Wani?” Muryarsa ne ya katse ta nan tayi murmushi tace ” Yaya ka Faye zolaya, ai wannan gidan tubarakallah Masha Allah Babu abunda ya rasa ” akwai babban abunda ya rasa kuwa gimbiya ” toh menene shi Yaya?” Ke! kece gidan yake bukata kafin ya zama complete, magirah kullum Ina cikin zulumin ganin na mallakeki wannna shine babban burina a rayuwa” ” haba Yaya kwana nawa ya rage idan Muna raye ”
“U won’t understand magirah, Gani nake tamkar zan iya rasaki cikin wannan 1 month din da ya rage ” karka damu insha Allah wannan karon ni din taka ce Yaya nah mijina ” murmushi ta sakar masa me Sace zuciya ya lumshe Ido cikin zuciyarsa Yana yawan fargaba kar Sulei ya sake shiga tsakaninsu, haka suka gama zagaye gidan ya Hadu over daga karshe suka fito nan suka sauketa har kofar gida kafin sukayi sallama ya tausaya mata da Yaga irin gidan da take rayuwa cki donhaka ya shirya Sanya farin ckin da ta rasa a baya cikin rayuwarta Yana tausayin maraicinta Kuma yayi alkawarin Maida ita gida cikin dangi da iyayensu.

___________

Ammi ce zaune da yaran nata suna hira cike da farin ciki murna kamar ta zuba ruwa a kasa tasha auta Aman da Ayman sun kammala degree ga Kuma lokacin aurensa na matsowa da son ra’ayinsa ne sai ya gama service Amma Ammi tace sam ,gashi Kuma Yaya babba yazo Hutu da familynsa Yaya sultan kyakkyawa ne Yana kama da Aman wajen hasken fata Amma fuskar dad dinsu ya dauka Yana da fara’a da saukin Kai. Ayman ya danne danne a wayarsa baby ta shigo da sallama da zauna kusa dashi tayi kasa da murya ” ya Ayman please let’s go shopping” kallo d’aya ya mata ya dauke Kai ” please mana Yaya…” ta karasa maganar a shagwabe Ammi ta kalleta tace ” ke Kuma lafiya kike Bata fuska haka ” Ammi so nake mu fita shopping da ya Ayman ne yaki kulani ” haba dai Yaya ka tashi kuje man kaifa babban Yaya ne ” ya tashi tsaye yace” am not feeling fine Ammi ta bari zuwa gobe ” daga haka ya juya ya shige part dinsu dama a falon Ammin suke, anty sofy tace ” wai Ammi wanene shi naga baison hayaniya tunda muka zo naga Bai cika magana ba gashi kyakkyawa” ya sultan ya harareta yace ” ko kin kyasa ne ” murmushi tayi tace ” haba dear kasan u r my everything kawai tambaya ce ” cousin bro dinmu ne , he is a prince kinsan jinin sarauta ” wallahi nidai da zai yarda sai na bashi ummita dinmu ya aura Yana da hankali ” dariya Ammi tayi tare da cewa ” kwantar da hankalinki ga nan matarsa tana jinki ” baby ta tabe Baki batace komai ba, anty sofy tace ” au haba.. sorry bansani bane karkiji haushi nah” Faty yayar Aman ce wacce take zama tare da ya sultan a can Italy tare sukazo Hutu. ta fito kenan d’aga daki Aman Dake faman chatting a waya ya kalleta yace ” kasa uwar bacci sai yanzu ” hararinsa tayi tace” ba laifinka bane dan rainin wayo auren da Ake Shirin Maka ne yasa kanka ke rawa ” dariya yayi yace ” toh ni na Hana Wani yayi auren ne ” wallahi karka min rashin kunya ko agaban matar taka zan iya jibgar ka wallahi ” Tabb…jibga, are you serious ” gaba d’aya suka kwashe da dariya , Ammi ta kalleta tace ” uban wa yahana kiyi auren ba kin tsaya ke uwar Boko ba ” Ammi let’s not start this please” toh ki kyalemin yaro ” tabe Baki tayi ta nemi waje ta zauna . Ayman kuwa yana shiga d’aki ya kira Fauzan a waya yace ya musu booking flight gobe su wuce Sudan bayason ciwon kai ya tabbata idan ya cigaba da zama kusa da wannan yarinyar zata cigaba da takurawa rayuwarsa ne shi Kuma baya bukatan Hakan a yanzu donhaka ne yasa yayi deciding akan cewa a Lagos zaiyi service bazai zauna Abujan ba bare a like masa wata har a bijiro da zancen aure, hajjo ce ta fado masa a rai ya lumshe idanu Yana tuna kyakkyawar fuskarta haka ya cigaba da juye juye bisa gado.

Back to top button