Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 16

Sponsored Links

Page 1️⃣6️⃣

 

 

Duka suna zaune cirko cirko sunyi shuru sunrasa abinyi ahaka har aka kira mangrib mazan duka masallaci suka tafi dakyar suka iya tashin FANAN da bacci yadauketa taimaka mata sukayi tamike tana rike da kanta dakin zeenat sukaje adaddafe tayi sallah tadawo tazauna shuru kanta akasa can Kuma kamar wacce aka mintsina ta tuna gida dawo Dede tayi aidasauri tafito dakin duk sundawo daga masallaci suna zaune afalo tafito gudu_gudu mikewa sukayi suma sun dauka wani abun ne yafaru ummi ce tariketa tana fadin” FANAN lafiya” arude tace ” wayyo ummi yau nashiga uku Dama mangrib yayi innalillahi wainna ilaijiraji unnn yanzu mezan fada agida anhanani Kai dare awaje “takarasa magana idonta nazubo da hawaye yaseer ne yace “karki damu kizo sena kaiki inwa Yan gidanku bayani” kallonshi tayi tana girgiza Kai “ya yaseer bazaka gane bane daga zarran 5:40 yayi duk inda nake ana San ran dawowana wlh yau nasan mama da baba zasuyi matukar fushi Dani ” tafashe da kuka dukkansu tabasu tausayi rungumeta anty Amina tayi tana rarrashinta, azaad da gaba Daya kukanta yadameshi tacika mishi kunne jiyake kamar zeyi hauka saboda ya tsani kukan mace kamar yarufeta da duka haka yakeji ummi tace” azaad daughter (anty Amina kasancewar itace yar farinta bata Kiran sunanta) yaseer Dani da zeenat zamuje gidansu fanan mukaita gida semu bawa iyayenta hakuri duka sunyarda da shawaranta .

 

Matukar tashin hankali da firgicine yabayyana akan fuskokin mama da baba gaba Dayansu babu Wanda yake cikin hayyacinsa duk sunfito compound din gidan suna jiran dawowar FANAN mama kam takasa jurewa inbanda hawaye ba abinda takeyi damin kuwa sukadai sukasan mezeje yadawo har inde tabiyo Daren nan tafito suhaima ce take rarrashin mama baba ne yace ” nasan yata da gangan bazata tabayin abinda ze batamin rai ba da dawowarta awannan dare gwara ta Kwana aduk inda take domin nasan tana hannu nagari fitowarta awannan dare barazana ce ya Allah ka kawo mana sauki ” ya al ameen,ya Usman, suhaima duk da hankalinsu atashe Amma kansu adaure yake meyene suke gudun faruwansa domin sun sasu aduhu shuru sukayi suka zubawa sarautar Allah ido.

 

Bayan sun idar da sallah isha ne suka fito da motoci Dan sukai FANAN gida itakam tsabar tsoron abinda zata tarar agida yahanata magana fitowa sukayi daga falon shiga cikin motar sukayi ummi da azaad da FANAN suna motor Daya SE anty Amina da yaseer SE zeenat motar yaseer ce tafarayin gaba, me gadi yawangale musu gate suna fita na azaad yabi bayanshi guguwane yatashi lokaci Daya Wanda yasa seda suka Dan tsaya domin jiran tsaqaitawansa yafi 10mint kafin yatsaya .

 

 

 

Hhhhhhhhhhhhhhhhhhh TAFITOOOOOO! TAFITOOOOOO SARAUNIYAR tafitoooooo tabayyana burinmu yakusa cika shugabansu ne yake magana Yana kallon madubin Dake gabansa mutum ne zaune akan kujera ta sarauta kansa da kaho Daya Baki Daya ja, katone Wanda zaa iya kiransa da basamude halittarsa rabi mutum rabi daba Yana sanye da jan Riga juyawa yayi ga mutanen sa dasuke irinsa sede dukkansu babu Wanda yakaishi girma daga musu hannu yayi kafin yace abinda muke Jira tsawon shekaru 18 yau yagabato garemu ihu suka farayi mara dadinji suna kururuwa shagali sukeyi bana wasa ba.

 

 

TANZARZAR nahango Yana zaune akan kujeran mulkinsa tare da Yan kungiyarsa dagaba Dayansu suke sanye da bakaken kaya jikinsu duk gashi Kai bakyaun gani kansu akasa idonsu arufe hannunsu ne dayake dauke da zuku zukun yatsu suka daga sama suna wani irin jujjuyashi suna lankwasashi kamar wasu masuyin rawa gaba Daya wajan yaturnuke da hayaki SE wani irin dariya sukeyi Wanda idan bil adama nawajan baze iya jurewa ba. Cikin wata irin murya me ban tsoro tanzarzar yace” tafito dole mune zamu mallaketa domin tana kunshe da dukan wata irin karfi da jaaazana atare da ita duk wani bayanai Yana dauke da ita tundaga lokacin datake ciki har izuwa yanzu abun da muke Jira yazo garemu hhhhhhhhhhhhhh.

 

 

 

Wani irin gurine Daya kasance komai fari kamshine me dadin gaske ke tashi bana tunanin nan duniyar mutane ne kowa tafiya yakeyi akan iska masu firewa ma sunayi furanni ne tako Ina masu gwanin burgewa Wanda bazakaso ace inde kana wajan nan kabar gunba hango tarin mutane nayi atare Wanda a iya hasashena sunfi karfin dubun nai karasowa nayi sanye suke da fararen kaya komai nasu fari bantaba kallon masu kyau da kyawun halitta irin suba mazansu da matan su , wani irin kujera nagani Wanda yake na zinari yasha ado da gwala gwale wani irin sheki yakeyi wani tsohone yataso me matukar kyau yatsaya agabansu Yana fuskantar gaba Dayansu kafin yafara dacewa ” Ni Abdul_shakur Ina me sanar daku yaune ranar da SARAUNIYAR mu ta taka mataki nafarko arayuwarta Wanda ze kusantota damu sannan ze kusantota da wayancan azzaluman makiyanmu nasan yanzu zasu fara kokarin Kaimata farmaki saboda yanzu ne suke da iKon yimata abinda zasuyi dukda ita haryanzu bata gama sannin wacece itaba Kuma menene take dauke dashi ba batasan ma yazata fara amfani da karfinta ba Amma baze dau lokaci ba jaaazana ze bayyana agareta dolene mukareta da iyayinmu ” kammala magana yayi fuskanshi dauke da murmushi dakuma damuwa (iKon Allah wannan aisede aljani Taya lokaci Daya Abu biyu zasu bayyana afuskan mutum Tabb nide nayi nan)‍♀️‍♀️‍♀️.

 

 

Tafiya suketasha akan titi kwatance gidansu tayiwa azaad har suka iso kofar gidansu fitowa sukayi daga motar yaseer ne yayi knocking gate din FANAN buya tayi abayan ummi ya Usman ne yabude sukayi musabaha “dama Baki kukayi Muna tare da FANAN ” cewar yaseer ya Usman yanajin an ambaci FANAN yace “Bismillah kushigo ” dasauri yakoma yafada musu sunyi Baki shigowa sukayi da sallama abakinsu falo suka shigo ummi ce tashigo akarshe FANAN Dake bayanta ne tayi sallama ahankali gaggaisawa sukayi ganin yanda FANAN ta takurene yasa mama tamata alama datazo mikewa tayi taje gun mama ta rungumta cikin muryan kuka tace ” Dan Allah kuyafemin nasan nayi muku laifi nakarya dokan dakuka gindaya min ” shafa bayanta mama takeyi ” kedin yace me biyayya munsan bazaki tabayin abinda ze bata mana ba kedin ta musamman ce yata” zuba musu ido mutanen falon sukayi suna jinjina irin soyayyan Dake tsakanin uwa da yarta gyaran murya ummi tayi cike da Kamala tafara Basu labarin abinda yafaru daga spark din da TV yayi harzuwa suman datayi har izuwansu gidan nan bakaramin tashin hankali suka shigaba abinda suke gudu yafaru baba ne yamike yafara safa da marwa Yana nanata Kalmar innalillahi wainna ilaijiraji unnn gumine yawanke mishi fuska kafin yakalli mama yace” mamansu abinda muke gudu yafaru abinda muke tsoron tsawon shekaru 18 yafaru ya Ubangiji Allah katarwatsa mumunar kudirinsu akan wannan baiwar taka dabataji ba bata gani ba ka tsareta da tsarewarka ” amsawa sukayi da Ameen ya hayyu ya qayyum duk da yasasu aduhu komawa yayi yazauna fanan ce ta rarrafo gabanshi tarike hannayensa” baba Dan Allah kutaimakamin ku fadamin gaskiyar abinda yake faruwa” shafa fuskanta yayi karki damu lokaci yariga da yazo Amma sekin Jira kadan duka mutanen falon jikinsu yayi sanyi duk da Basu San meyake faruwa ba Amma alamu yanuna wannan ahalin suna cikin hard time.

Azaad cikin cool voice yafara magana” idan badamuwa zamu iya sanin abinda yake faruwa” girgiza Kai mama tayi tace” bazeyu muyi muku bayani ba domin yin hakan zezama bayyanar FANAN ne cikin sauri da karfi” kamarya bayyanar FANAN bayan gata nan abayyane agabamu Muna kallonta zeenat takarasa maganar tana binsu da kallo duk da basa cikin yanayi me dadi Amma hakan be hanasu murmusawa ba ummi ce tamata signal da ido akan tayi shuru mama ce tamike takira FANAN da suhaima biyota sukayi kitchen drinks tabasu dasu fruit a trays suka kawo falo Bismillah suka musu Dan tabawa sukayi kadan kafin ummi tace” yakamata mu gabatar muka da kanmu sunana Aysha Muhammad azaad mainasara sannan tanuna anty Amina itace first born Dina sannan tanuna azaad Shima danane shine nabiyu Wanda FANAN take kulawa dashi se wannan tanuna zeenat itace auta ta akwai yayyunta maza guda biyu a gida SE wannan Shima Dana ne Dan kawata ne Kuma abokin azaad tun suna yara ” Masha Allah, Ubangiji Allah yaraya miki zuriyarki yakara hada kanku babane yake musu adduah duka falon suka amsa da Ameen. Ganin dare nayi ne yasa suka ce zasu tafi sallama sukayi mazan suka rakasu har bakin motar su suka tafi.

Bayan sun dawo ne baba yake ma FANAN Yan tambayoyi “mekikeji ajikinki yanzu karki boyemin” kallonshi tayi cikin nutsuwa tace ” banajin komai baba ” ajiyar zuciya suka sauke atare shida mama sude sunzuba musu ido kawai tunda sunki fada musu komai, to shikenan kowa yaje yakwanta dare yayi seda safe sukayi suka shige daki FANAN da suhaima hira sukayi kafin suka kwanta tare dayin adduah bacci……..

 

 

 

 

Meye FANAN take dauke dashi ? Menene jaaazana dasuke son karba daga gareta? Suwaye wayanda suke shirya farmakan FANAN??? Shin wasu irin kungiyoyi ne wannan??? Meye abinda Tanzarzar yake bukata atare da ita?????? Taya akayi fanan takasance sarauniya ????????

 

Kubiyoni domin kuji amsoshin tambayarku senajiku a comment section

 

 

 

 

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by (MRS ISHAM )

 

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci

 

 

 

____________________________________________

 

Back to top button