Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 48

Sponsored Links

Zeenat ce ta fara farfadowa tana wani irin amai me dauke da jini da nama_nama seda ta amayar daduk wani abinda ke cikinta tsaban yanda aman yaci karfinta seda kaff kuzarinta yakare riketa sosai anty amina tayi tana kiran abu tazo ta gyara wajan daki takai zeenat ta kwanta bacci , fanan na kwance akan kujera har time din bata farfado ba kusan an hour shuru , tun suna san ran tashin fanan nan kusa har tsoro yafara kamasu jinta shuru duk wani abinda zasuyi danta tashi sunyi amma fa shuru , da karfin gaske Mr azaad ke jijjigata duk da haka bata tashi ba lamarin yabasu tsoro seyanzu suka kara danasanin barin zeenat tasha mata jini gashi yanzu taki farfadowa daukanta Mr azaad yayi yakaita bedroom dinshi yakwantar da ita akan bed sannan yarufeta da blanket.zama yayi agefenta hannunsu rike dana juna . ba abinda yake matsar dashi daga gefenta fa ce sallah gudun karta farfado ba kowa akanta har dare fanan shuru ba labari, haka ya gyara musu kwanciya suka kwanta.

Asuba ta gari.

tashi tayi ta zauna tana murza idonta kallonta tayi a dakin Mr azaad kuma babu shi aciki tuna abinda yafaru tayi danna wayarshi da ta gani a kasan pillow tayi karfe 5:40am ta gani batayi mamakin ganin haka ba tashi tayi tashiga toilet tayi wanka da alwala dressing room dinshi ta shiga bangaren jallabiya taje ta dau arche color tasaka yawa yamata ganin hijab dinta tayi akan kujera dauka tayi, tayi sallah tana zaune tana azkar ya shigo ya zauna akan kujera yazuba mata ido harta idar, juyawa tayi ta kalleshi kafin tace ” Ina kwana Mr azaad” batayi tsammanin ze amsa ba taji yace ” lafiya ! tashi kizo” tashi tayi taje ta tsaya a jikin kujeran da yake zaune , ” malama ki zauna mana kin tsaya min akai” zama tayi dan tasan halinshi yanzu se ya fara , bayan ta zauna ne yake tambayarta ” ko zan iya sanin fa’idan shan jininki da kika bar zeenat tayi?” bashi amsa tayi da ” Mr azaad ka rigada kasan nidin wacece , dakuma abinda nake dauke dashi ina da ya kinin shan jinina da tayi ze iya fitar da maitar ajikinta” cike da gamsuwa da maganarta hadi da kaunarta yace ” Allah yasa ” ta amsa mishi da ” ameen ” satan kallonshi tayi suka hada ido itama ita yake kallo gyara zama yayi yace” to miye na kallon kuma ” girgiza kai tayi . Kwantar da kanta tayi a kafadarshi ta lumshe ido kamar tana bacci tana shakar daddadar kamshin turarenshi , ” fanannnn!” batare da ta Bude ido ko ta tashi ba tace ” naam” shafa kumatunta yayi ya dan jashi kadan runtse ido tayi saboda yamata zafi ,” fanannnn meyasa kike boyemin abinda ke ranki ?” cewar Mr azaad da har lokacin yana shafa mata kumatu , tashi tayi daga jikinshi ta zauna suna kallon juna tace ” Mr azaad miye nake boyewa din ?” kwantar da kanshi yayi a jikin kujeran be sake ce mata komai ba ganin haka yasa fanan mikewa zata tafi bedroom dinta rike hannunta yayi yace ” karki tafi please” kaman wani bako haka take kallonshi wai yau Mr azaad ne yake ce mata please anya ba mafarki takeyi ba kuwa, janyo hannunta yayi tafado jikinshi sunfi 5mint kafin ya sauke ajiyar zuciya yace ” fanannnn am sorry for all mistakes nasan na miki Abubuwa da dama kiyi hakuri na miki alkawari hakan baze sake faruwa ba ” sosai idonta ke fitar da ruwan hawaye tun tana hawaye harta fara shesheka azuciyarta tana godewa Allah da yasa Mr azaad ya gane abinda yake mata ba dede bane dukda bata taba rikeshi arai ba son da take mishi yasa bata ganin laifinshi . rungumota yayi ajikinshi yana rarrashinta dede kunnenta yakawo pink libs dinshi wura mata iska yayi acikin kunne da yasa taji tsigan jikinta ya tashi kafin ahankali cikin rada yace ” baby be with me for the rest of my life! I love you ” cak duk wata ma gudanar jinin jikinta seda yatsaya yadena aiki na wasu lokuta jin abinda ko da amafarkin wasa bata taba tsammanin ji ba hawayen farin ciki ne yafara saukowa daga idonta runtse idon tayi sosai tana rokon Allah yasa koda a mafarki nake Allah karkasa in tashi , haka ya dinga fada mata daddan kalamai dashi kanshi besan ya akayi ya iya su ba kawai abinda yasani duk abinda yafada mata daga cikin zuciyarshi yafito, rungumeshi tayi gam muryanta na shake tana kuka hade da dariya tace ” I love you too Mr azaad inasanka sosai” raba jikinsu yayi ya manna mata kiss a goshi tare da fadin ” Allah ya miki albarka my wifey” kallon cikin idon juna sukeyi babu ko kyaftawa hawaye me zafine ya gangaro kuncinta hannu yasa ya share matashi yana girgiza mata kai sannan yace” hawaye bashida gurbi a cikin rayuwarki har inde ina tare dake ! adah nabari kinyi amma banda yanzu domin kuwa inya sake saukowa zan hukuntashi ” dariya tayi tana kwanciya ajikinshi tayi lamo .

______ bacci suka koma se 11 suka tashi komawa bedroom dinta tayi sakeyin wanka tayi ta shirya cikin atampa super Holland me purple color se touch din maroon da fari, dinkin doguwar rigace pencil gown me dogon hannu kasan hannun an mishi play wuyan rigar kuma adan bude yake batayi kwalliya sosai ba kawai powder tashafa se kwalli da libstick , dankunne da sarka tasa na gold tayi dauri me v feshe jikinta tayi da turarurruka masu dadi dakuma sanyayyar kamshi hills tasaka a kafarta maroon sak tafito a amarya tayi kyau sosai kamar wacce zataje gasar kyau gashi kayan sun matseta nafitan hankali duk wani shape dinta seda yafito fili . yau fess takejin ranta ji takeyi babu wanda yakaita farin ciki a irin wannar rana saboda wanda take matukar so shima yana santa, kallon kanta tayi a mirror ta kashe ido daya tare da fadin ” excellent” knocking tayi yabata izinin shigowa, samunshi tayi yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya three quarter dark blue yasa da kuma riga armless baka waya yakeyi da yaseer dake tambayar shi jikin zeenat kamshin turarenta ne ya sanar dashi isowarta kallonta yayi da narkakkun idonshi kasa magana yayi kawai yayi hanging din kiran murmushi dauke a fuskanta, tafiya takeyi ahankali kamar wata me tausayin kasan, har izuwa lokacin be kawar da idonshi akanta ba cike da kissa ta zauna agefenshi ta shagwabe fuska tace ” Mr azaad wannan kallon fah?” cize libs dinshi yayi kafin yace ” to laifine dan na kalli matata?” rufe fuskanta tayi ajikinshi tana dariya dagota yayi yatsurawa libs dinta ido dayasha man baki matso da fuskanshi yayi daff danata ahankali ta lumshe manyan idanunta,hade bakinsu yayi waje daya yasakar mata hot kiss sannan yadago yana kallonta yace ” baby kinyi kyau sosai” dadi ne taji yarufeta jin yabon daya mata tana kokarin yin magana sukaji anyi knocking tare da fadin ” sir your food is ready” beyi magana ba sukaji alamar wanda yakawo abinci ya fita tashi sukayi sukaje falon sukayi breakfast.

Haka suka kasance cikin farin ciki a wannan rana har dare suna part dinsu suna soyewa ( ohhhhh su Mr azaad an fada tarkon love) wanka tafito tana daure da towel daya tsaya mata a cinya zama tayi agaban mirror shi , lotion dinshi me dadi tashafa tare da perfumes dinshi yana kwance akan bed ya zuba mata ido duk wani motsinta akan idonshi yana binta da mayun idonshi duk inda tayi idonsa na kanta surar jikinta yana matukar daukan hankalinshi, tashi tayi ta nufi hanyar barin bedroom din kasa_kasa yace ” ina zakije ” waigowa tayi tana murmushi tace ” Mr azaad zansa kayane sannan in hada mana dinner” gyada Kai kawai yayi ta fita a dakin , sleeping dress tasa rigar doguwa ce har kasa white color silky gown , hula tasa akanta dan bako yaushe takeson farin gashinta awaje ba ( matan aure da yan mata kudena barin kanku abude saboda shedanu kuma haramun ne inma bazaki iya daura dankwali ba ga hula nan sekisaka akanki barin kai abude bashida kyau ko kadan wasu kam ma ahakan suke shiga bandaki batare da hula ba to ku kiyaye Allah yakyauta) kitchen tashiga tama rasa me zata musu fast food fridge tabude gashashiya ta dauka tayi musu peppe chicken se ta soya chips data gama ta jerasu akan tray da su drinks , knocking tayi ” come in” kawai yace mata , ajiye tray din tayi akan center table tayi saving dinsu batare da ta kalleshi ba tace ” Mr azaad food is ready” tasowa yayi yazauna, cin abincin takeyi cikin nutsuwa ji tayi kamar ana kallonta yasa tajuya suka hada ido kayittaciyar murmushi ya sakar mata mayar mishi da murmushin itama tayi sannan tace ” Mr azaad meyasa bakacin abincin ?” kallon abinci yayi ya kalleta kafin yace ” to ki gama ci sekiyi feeding dina” dariya yaso bata yanda yayi kamar dan karamin yaro ajiye spoon din tayi tadawo gabanshi tazauna sa hannu tayi acikin plate din kazan ta gutsura takai mishi baki,karba yayi tare da hadawa da yatsanta daya ” wayyo Mr azaad zaka cinye min hannu” murmushi kawai yayi bece mata komai ba,haka tadinga bashi abaki yana hadawa da hannunta har ya koshi yasha drinks itakuma ta tattara komai takai kitchen bata dawo ba seda ta wanke komai tukun ta maidasu wajan zamansu , bedroom taje tadau dogon hijab kasancewar kayan bacci ne ajikinta tasa slippers tashiga bedroom dinshi ganinta da hijab ne yasa Shima ya mike dukda besan ina zata ba riko hannunta yayi suka bar part dinsu, part din ummi suka shiga bakowa direct bedroom din zeenat suka shiga .
_____ a can kuryan gadon suka sameta ta dukunkune awaje daya ta hada kanta da guiwa waje daya tayi shuru hawa gadon fanan tayi ta dafata a firgice ta dago tana kallonta rungumeta tayi tana kuka ” nagode sosai anty fanan Allah ya biyaki da gidan aljanna kimin abinda bazan taba mantawa dake ba ” shafa bayanta fanan takeyi tana fada mata kalaman da suke kwantar mata da hankali raba jikinsu tayi tazauna suna kallon juna fara magana fanan tayi ” zeenat ki saki jikinki kinji kidena boye kanki yanzu fadamin yaushe kika tashi ?sannan kuma kinajin akwai alamar wani abu ajikinki?” girgiza mata kai zeenat tayi tace ” yanzu ina jina kamar wata yantattiyar baiwa da aka yanta,banajin komai atare dani yanzu ! dazun natashi daga bacci yanzu kusan awa 3 kenan” shafa fuskanta fanan tayi tace ” in sha Allah kin rabu dasu kenan da izinin Allah” Mr azaad tunda suka shigo yazauna akan kujera yake binsu da ido bece musu komai ba se godiya yakewa Allah aransa da yasa be rabu da fanan ba itadin seyanzu yagane ita din mahadin rayuwarsa ce tundaga lokacin da tafara haduwa dashi taimakon shi da family dinshi takeyi tabbas su masu saa ne da suka samu yar baiwa atare dasu kuma me daraja wacce tasan daraja , bashi da bakin da ze mata godiya shisa a kowani awa, a ko wani minti , a kowani dakika santa kara karuwa yakeyi azuciyarshi ,san rayuwa da ita na har abada yakeyi sede kuma kash hakan ba me faruwa bane.
zeenat da batasan tare suka shigo da Mr azaad ba cikin yar zolaya tace ” anty fanan ina heartbeat dinki kika baroshi kikazo nan?” hannu fanan tasa tana nuna mata inda Mr azaad yake ware ido tayi tana ” yaya yaushe kashigo?” yar dariya yayi dan yanda ta zare idon kamar wacce taga abin tsoro be bata amsar data tambayeshi ba yace ” yanzu kam babu abinda kikeji ko?” gyada Kai tayi watsa mata harara yayi nan take ta bashi amsa da ” eh ya azaad babu abinda nakeji” ” good “.

 

Se munhadu Monday inda rai da lafiya.

Masuyin comment na gode Sosai wayanda Kuma sukeyin comment da yanzu haka kurum suka dena ko sun karanta bame cewa kala bayan Kuma da suna comment Kuma sannunku da kokari kunji nace sannunku yanzu kunzama daya da wayanda basayi.

 

Haka yau fanan ta wuni wata sukuku da ita saboda lamarin zeenat ya tsaya mata arai dan tasan karya kawai zeenat tayi mata dan ta kaucewa zarginta , har tara Mr azaad be dawo daga gidansu yaseer ba abincinta taci tayi wanka tasa sleeping dress dinta ta kwanta.

Packing din motarshi yayi a packing lot tafiya yakeyi kawai yaga kamar gilmawar mutum wul ta gabanshi dakatawa yayi da tafiyar yana kallon the whole house, masu gadine kawai suke zaune suna jin radio sekuma securities da suma hiransu sukeyi , cigaba yayi da tafiyar harya shigo part dinshi har ze shiga bedroom dinshi se yajuya zuwa nata bedroom din wutan dakin a kashe flashlight din wayarshi ya kunna ya haskata akwance take tana bacci takawa yayi har izuwa bed dinta shafa cutie face dinta yayi daga bisani kuma ya manna mata kiss a forehead (goshi) komawa bedroom dinshi yayi shima wanka yayi ya kwanta. Sanyayyar murmushi fanan tasake lokacin da ya manna mata kiss tun shigowarshi ta tashi adduah takeyi aranta Allah yasa Mr azaad yafara sonta kamar yanda itama take sonshi.

To fa wato akace in zaka tona ramin mugunta ka tona dede kai yanzu de tsakanin mommy da zeenat nide narasa wazan kira mugu acikinsu.

Mommy tasamu lafiya sumul da ita tashirya fita dan taje itama tasamo yara 8 da suka rage zaayi sacrifice dinsu, itakuma zeenat tashiga part mommy har bedroom din Mansoor domin aiwatar da abinda a kasata ga shi dan banzan yunwa takeji tana bukatar jini ko nama kwance tasamu Mansoor yayi dai dai akan gado yana bacci bayan yagama shaye shayenshi dalewa kan gadon tayi tasa dogayen yatsunta tafara tsaga cikinshi , shuri daya Mansoor yayi rai yayi halinsa tass zeenat ta cinye namanshi da jininshi
Tana gamawa kuwa ta bace ta tafi dakinta tayi kwanciyarta cikinta a cike.

Karfe 3 mommy ta dawo gidan ta kashe yara biyar 5 takai kungiya, tana shigowa part dinta tafara jin karnin jini mamaki ne yakamata bin direction din inda karnin jinin ke tashi tayi tafiya takeyi har dakin Mansoor dake kwance babu rai ajikinshi babu koda tsokan nama sede kashi uwar ihu da kururuwa tayi wanda yacika gidan yayi sanadiyar tashin kowa daga bacci har rige_rige sukeyi suka fito kaff dinsu afalon ummi suka hadu suna tambayar junansu meyafaru tsaban rudewa dukkansu da kayan bacci suka fito buga kofar falon akeyi kamar zaa ballata babu ko tsoro Mr azaad yaje ya bude bangaje shi mommy tayi ta nufi abba ta rikeshi kam tana kuka kamar ranta zefita, duk ta daburtar dasu sun rasa gane abinda yake faruwa jijigata abba yayi saboda ta dawo cikin nutsuwarta cikin tashin hankali tace ” muhammad sun kasheshi sun kashe Mansoor sun kashemin dana Mansoor” innalillahi wainna ilaijiraji unnn zufa ne yafara yanko musu jin kalamanta saketa abba yayi yawuce part dinta yau ne rana ta farko da yasanya kafa a part dinta tun bayan shekara 12 saboda ya dade da sanin wacece mommy har dakin mansoor din yashiga runtse ido yayi lokacin da yayi arba da gawar mansoor ko kuma in ce gwarangwal din mansoor bakyaun gani, shigowa su ummi sukayi suma duk kallo daya sukawa gawar suka kauda kai, yau kam sun shiga matsanancinyar tashin hankali , babu abinda kirjin fanan yakeyi fa ce bugawa da karfi_karfi tsoronta daya shine kar zargin da takeyi yazama gaskiya akan zeenat saboda yanzu tasake samun hujja ganin dan kunnenta yashe akasan gadon sa kafa tayi ta bigeshi yashige can kasan gadon batare da kowa ya gani ba. bedsheet Mr azaad yasa ya rufe mansoor dashi duk karfin zuciyarshi da taurin zuciya seda yaji tsigan jikinshi yatashi barinma da yaga fuskan mansoor kaf an kwakule komai harta ido an cire , fita sukayi daga dakin zuciyarsu a karye sosai tausayin mommy yakamasu .
haka suka kwana a part din mommy batare da sun runtsu ba yanda sukaga dare haka suka ga rana .
Sallah suka tafi a masallaci Abba yafadawa liman akwai jana’iza agidanshi dan shi ya rasu , liman yayi sanarwa a masallaci mutane suka tayi musu taaziya.
haka akayi jana’izar mansoor aka kaishi gidanshi na gaskiya kowa na binshi da adduah Allah yaji kanshi , mommy kam yar karamar hauka ne kawai batayi saboda duk duniyar nan babu dan adam din da takeso sama da danta mansoor saboda halinsu yazo daya duk wani mugun nufinta bata taba tunkarar shi ba , ko magana bata iya yi balle ta karbi gaisuwar , su anty shayida da anty zainab da anty amina duk sunzo , me martaba da duk jamaar masarauta sunzo, haka su mama suma sunzo sun musu taaziya sun koma sosai mutuwar mansoor ya taba su fawwaz dukda bawani shiga harkanshi sukeyi ba saboda rashin kunyar dayake musu baya ganin kowa da mutunci kuma ko sun dakeshi hakan baze hana yakara musu wani rashin kunyar ba , haka zeje yafadawa mommy ita kuma tashigo part dinsu ta musu rashin mutunci tayi gaba .
duk wannan gaisuwan da akeyi da zaman makoki ko idon zeenat baa gani ba ko lekasu batayi ba tana can ta kulle kanta adaki tana kukan nadaman halin dataga kanta aciki abin na mugun damunta gashi kuma bata isa tafadawa kowa ba kugin yunwa cikinta yafara nan take halittar jikinta yafara sauyawa dogayen hakwara da yatsunta sun fito idonta yarine yayi jaa kuka takeyi da dan karfi dan yau kam tayi niyya sede in mutuwa zatayi sede tayi amma bazata karacin naman kowa ba tun tana iya jurewa harta kasa , fanan tana zaune a main falo dan batason yawan hayaniya sosai tabar wajan zaman makokin ita daya a falo , tana nan tana tunanin yanda zata shawo kan lamarin zeenat kenan taganta ta diro daga can upstairs ta dira a gabanta kamar wata yar biri tashi fanan tayi tana ja da baya zeenat na binta harsuka kai dungun gini yanzu kam fanan tagama tabbatarwa kanta zeenat mayyace , kafa mata hakwara tayi awuya zata fara shan jininta yaseer ya cafketa ta baya gam yariketa yaki sakinta .
kokarin fin karfinshi takeyi dan girgizan da takeyi yawuce iya karfin zeenat da akasani , fashe musu da kuka zeenat tayi tana ” wallahi mutuwa zanyi in bansha jini ba dan Allah ku taimakeni kubani in kuma ba haka ba zan iya mutu ” hawayene yakebin fuskan fanan dan jitayi duniyar ta dena mata dadi tama kasa karasa wajan yaseer da yake kokuwa da zeenat, son da yake mata ne yasa lokaci daya tausayinta yayi tasiri aranshi hannunshi yamika mata aikuwa karaff ta damki hannun yaseer din tasa abaki ta fara tsotsan jinin shi cike da tausayi suke kallonta shigowar Mr azaad kenan yayi karo da mugun gani da wani irin speed ya isa inda suke ya fincike zeenat dake shan jinin yaseer da takeyi cikin daka tsawa yace musu ” dama dukkan ku biyu baku da hankali bansani ba yaseer taya zaka bata hannunka tasha jininka ” gam yarike wuyan zeenat yasa idonta cikin nashi aikuwa nan take ta sume bin Mr azaad sukeyi da kallon tuhuma meye abinda ya aikata yanzun nan meye dalilin dazesa daga kallon idonshi zeenat zata suma, bebi ta kansu ba yadauketa cakk yanufi part din ummi da ita yakwantar da ita afalo .
Su ukun duk suna zaune a falon ummin babu wanda yacema dan uwansa kala, fanan tana yiwa yaseer dressing din hannunshi da zeenat tasha jini, daga waya Mr azaad yayi ya kira layin ummi yace mata tazo ita da abba it’s urgent, shigowa sukayi su biyar Abba,ummi, fawwaz,areef se anty amina ganin zeenat akwance bakinta da jini_jini Abba da ummi har suna hada baki wajan tambayar Mr azaad meya sameta , fada musu abinda ya gani yayi ,juyawa ummi tayi ta kalli fanan hawaye na fita a idonta jin halin da yarta ke ciki tace mata ” my feena meya sameta ” girgiza kai fanan tayi murya asanyaye tace ” ummi tun dawuwarta jiya nace naji tana karnin jini seta min karya dawani abun daban amma dukda haka ban yarda da itaba seyau na kara tabbatarwa” dama suma tunda sukaga fanan tayi hakan sunsan da walakin goro a miya amma se basu wani bawa abin mahimmanci ba.
tashi fanan tayi taje ta durkusa agaban zeenat tasa hannunta akan goshinta sannan ta rufe ido nan take tafara ganin tun lokacin da vampires union suka fara shirin bawa daya daga cikin ahalin mainasara maita harzuwa time din da daya daga cikinsu yazama karamar yarinya me tallan guiva da siyan da zeenat tayi takoma maiya da cin naman da tayi da komai da komai seda fanan tagani kamar wacce ta kunna film tana kallo . dasauri ta bude idonta ta kalli yan falon da suma ita suke kallo musamman ma Mr azaad duk abinda tagani seda ta fada musu salati kawai sukeyi zufa na keto musu ta ko ta ina duk da sun rasa abinda yahada su da vampires union,
ana haka zeenat ta tashi daga suman da tayi sauka idonta yayi akan areef dake tsayi akusa da ita , hannu takai zata rarumeshi ta ciza yayi baya , damkar gashin kanta fanan tayi suna facing din juna kafin tasa mata hannunta abaki aikuwa nan da nan tafara shan jinin fanan dakatar da ita suke kokarinyi ta daga musu hannu haka sunaji suna gani zeenat tadinga zukan jinin fanan seda suka kai almost 30mint a haka kafin dukkansu biyu suka zube a sume.

Se mun hadu gobe inme duka yakaim.
Masu comment na gode Sosai Allah yamuku albarka.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & written by ✍️
MRS ISHAM

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

Back to top button