Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 27

Sponsored Links

Tsit gidan ya yi baka jin motsin kowa, sai sautin kuka Sadiya da ke tashi, dan kowa yana mafakarsa ya ɓuya. Inna duk da sanyin da ake amm sai jabga uban gumi take saboda tsabar tsoro da kuma yanayin da take ciki, uban buhhunan da ta libgawa kanta kaɗai sun ishe ta da zafi sai zufa ke ta faman kwaranyo mata tana sanya hannu tana gogewa.

“Oh Allah mutubi am, in ji fulani wai yau ni Azumi ce cikin buhhuna rufe sai kace masara, da a ce wani zao yiwa Tasalla video na ya tura mata da na san sai na gaggara komawa gida saboda tsoron abin da zan je in tarar, yo ni da nake ƙafafa da birni kullum ina mata gorin bata ƴan uwa a birni amma a tura mata videona ina ƙunshe a buhu ni ba tafasa ba sai ka ce wata kukar kaɗi”

Cewar Inna ta haɗa hawayen da gumin ta goge, tana tuna duka -duka ba a ɗauke wasu lokuta masu yawa ba da ta baro cikin freezer yanzu kumangata ƙasan benci rufe da buhu.

“Allah ka yafe mana idan saɓo muka yi amma lallai muna haɗuwa da jarabawa musamman ni Azumi” Cewar Inna tana hararo abubuwan da suka faru da ita daga barowarta ƙauye zuwa birni.
Dariya ta ƙyalƙyake da ita marar sauti sai da ta yi dariyarta son ranta har sai da dariyar ta tsagaita dan kanta sannan ta ce.

“Kai Allahu akbar Imirana Baban miciji ana can garƙame a cikin tukunya, yau dai ƙarshen tsafta da karkaɗar jiki sun ƙare tun da ana cikin sauran ruwan wankan jego luntsum” Ta faɗa tana ƙara dariyar ƙeta.
Jim kaɗan ta yi shiru kamar ruwa ya cita, can kuma da ta tuna kicin ɗin a kulle babu hanyar da micijin zai shigo ko da ya ji motsi ko magana sai ta dage ƙarfinta ta ce

“An ɓuya? An ɓuya?? An ɓuya???” Ta faɗa tana dakatawa dan jin abin da zai wakana, aikuwa kafin laɓɓanta su gama haɗuwa wuri ɗaya sai ta ji ƴan cikin loka suna ta surkune surkune alamar sun, a gyara zama dan jin abin da Innar ke faɗa sai suka ɗauka wani abu ne na da ban.

Jin babu wanda ya kulata sai ta yi shiru ta shiga addu’a a kan Allah ya kawo musu ɗauki dan bata fatan su kwana a halin da suke ciki yanzu.

Ƙaran bugun ƙofa ne da ake wanda aka kasa dainawa ya sanya Sadiya tashi tana goge hawayenta ta tafi domin ta buɗe, dan har lokacin Hassan na a yadda yake. Gabaɗaya mutanen da ke maɓoya sai suka shiga ƙara gyara zama saboda duk a tunaninsu miciji ne ke ta aikin buga jikin ƙofar gidan.

“Mamar Sadiya a ina kika samu mafaka ne, dan Allah, faɗa min ko cikin raɗa ne idan gurin da kike ya fi nan wasaci sai in lallaɓo in fito dawo wurin naki, dan ban ga alamar za mu fito a ƙanƙanin lokaci ba, kuma ƙasan gadon nan yadda kika san matsin kabari da ake bada labari haka nake ji ba na iya ko da kataɓus a danƙare nake a wuri guda” Cewar Hajiya tana nishi kamar an ɗorawa raƙumi kayan da suka fi ƙarfinsa.
Hannu Mama da ke cikin wardrobe ta sanya ta ɗan bugi jikin wardrobe ɗin, dan ita bata ma ƙaunar ta buɗe bakinta saboda gudun tsautsayi.

“Haba Mamar Sadiya kin fini son ranki ne da ba zaki buɗe baki ki ce min kina cikin sif ba, kuma da alama ma a ta Imran kike inda yake ajiye kayansa ko nauyi da kunya bakya ji ki shiga lokar kayan sirikinki?” Hajiya ta faɗa cikin ƙarfin halin matsin katakwayen da suka mata ƙawanya a ƙasan gadon.

“Wai Hajiya Amina menene haka, dan Allah sai kin jawo micijin nan ya shigo ɗakin nan, tun da kika ji na yi shiru ai sai ki kama bakinki ki yi shiru, da na miki alamar da inda nake ta hanyar buga katakon lokar ai idan za ki dawo nan ɗin sai ki fito ki dawo mu kwatsu, amma kina ta maganar siriki, sirikin da ya damƙeni a gudun famfalaƙin da miciji ke zagaya mu, menene saura kuma ya rage ai babu shi wa ya san a inda yake yanzu, ko ke kika samu lokar Sadiya tuni zaki manta da surukantaka ki afka ciki babu shiri”

Wani bugu da aka yiwa ƙofar gidan ne ya sanya suka yi shiru, me ƙunshi da ke ƙunshe cikin loka sai kuka take hawaye ne ke ta kwaranya dan zuwa yanzu babu abin da ta fi buƙata sama da ta samu ruwa ta wanke fuskarta zuwa wuyanta, dan gabaɗaya sai yanzu ta gama jin lallan fulawar ya gama baibaye fatarta da uban raɗaɗi.

“Wayyo Allah na shiga uku na, tsohuwar nan ta taƙaitani ta cuceni ya fi cikin carbi, lallan da ko a farce aka sa maka shi sai ka gwammace kiɗa da karatu amma ta min wannan ɗanyen aiki dashi, irin zafin da yake min a fata wallahi gwara ta rufeni a cikin freezer ta rama a kan wannan abin, ta min asarar bilicin ɗina, da na kwaile fuskata duk tattalin arziƙina da nake samu a ƙunshi a siyen man gyaran fata yake ƙarewa amma a ce yanzu ta maidani baƙaƙirin kamar tukunya da wane ido ma zan fita waje” Ta faɗa tana sanya hannu ta janyo wata farar shaddar Imran ta gogo fuskar tare da sakin wani kuka marar sauti

Imran kuwa da ke cikin tukunya duk ruwa ya gama jiƙa masa jiki gashi a ringishe yake shi ba a kwance ba shi ba a karkace ba, hannu kawai yake sanyawa yana kore ruwan da ke barazanar shigar masa hanci dan ruwan da ɗan damarsa. Idanu ya ɗaga ya sauke a jikin murfin tukunyar ta ciki, cikin tausayawa kansa ya ce.

“Haihuwa me jaye -jaye Allah ka sanya mu haifo alkairi, kar mu haifi abin da zai zama sharri garemu da wasu ma baki ɗaya, ni Imran babban yaro wanda ko giftawa na yi sai ƙamshin jikina ya gama buɗaɗe hancin mutane amma yau ni ne a cikin tukunya a rufe ina tsilla idanu kamar kwarton da aka kama, ni ba naman kai ba amma ina cikin tukunya da ruwa a rufe wuta kawai ta rage a kunna na zama naman da za a kai baki” Ya faɗa yana jin saukar ruwan hawayensa.
Sadiya kuwa cikin sanyin jiki ta sanya hannu a hankali ta buɗe jamlock ɗin, tana addu’a da fatan ba wani bane hallaw zai kawo kansa, dan ita ko kaɗan bata ƙaunar mutane suna zuwa suna ganin Hassan a suffar miciji, wani in ya gane baiwace wani in ya tafi ya rinƙa yawo da zancen kenan gashi baka san bakin wani ba. Idanu ta sauke a kan Lawal maƙocinsu na can gaba da su, ustaz ne dan shi ne ke jan sallah a masallacin ahlis sunna na unguwar, sanye yake cikin farar jallabiya, da farin dogon wando, sai hula irin tashi da ƙwawar nan a kansa , da jan hirami rataye a wuyansa, sai carbinsa irin counter ɗin nan wanda ake dannawa.

“Assthalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu, ya Sthadiyya” Ya faɗa lokacin da ya ga Sadiya ce ta buɗe ƙofar, gashi dama maganarsa ma irin ta ustazai ce ana yi ana saka gunna da ƙalƙala.
Ya yi sallamar yana ɗan kauda kai gefe irin baya son nan ma ya kalleta saboda shi ustazu ne.

Sallamar ta amsa masa cikin sanyin murya, da shaƙewar muryarta kana ji ka san ta aha kuka babu lefi. Jin muryarta sai da shek Lawal ya saci kallonta ta gefen ido, ganin yanayinta sai ya ce a ransa.

“Iko sai Allah, Sthadiya kuma fuska da alamar kuka, wataƙila ba a kawo haƙiƙa ba ne(Ragon suna) Kuma suna har ya rage saura kwana biyu, ashe kowa yana jin yanayin garin”

“Sannu da zuwa ya shek bismillah” Ta faɗa tana juyawa cikin sanyin jiki ganin sai satar kallonta yake ita kuma bata son kallo shi kuma duk da ana kiransa uztaz amma kallon mata ne da shi sai dai yana yin kallo saisa -saisa ne dan kar a gane shi. Ganin ta juya sai ya shigo tare da sakin ƙofar yana sakawa kuwa iska ta maida ta rufe.

“Ya subhanallah! Iska a yi haka kuma ki rufe liman, kuma shek a cikin gidan matan aure daga zuwa barka” Ya faɗa cikin muryar ustazai, ita dai Sadiya bata ce masa komai ba, haka ya shigo gidan ma bakinsa da sallama, sake amsawa ta yi, tana cewa ya shigo falon.

“Toh, toh” Ya faɗa yana tsegumin ƙarewa tsakar gidan kallo, dan sau ɗaya ya taɓa shigowa lokacin da aka kwantar da Imran a asibiti da aka taso shi ya zo ya masa sannu. Kallon da yake kuwa tsegumi ne da gulma dan yana so ya ga a kan abin da Sadiyar ta yi kuka, da ya ga bai hango ragon suna ba sai zarginsa ya zama gaskiya na cewa kukan rashin ragon suna ne da ba a kawo ba.

“Amma kuwa Imran ka yi wawta, kuma ba Sthadiya kawai ka yiwa baƙinciki ba har da mu dan na san dai za ta aikawa Barira naman suna kuma ni ma ai Barira ta ajiye min ko da tsoka ɗaya ne” Ya faɗa a ransa yana me kutsa kai cikin ɗakin. Zaunawa ya yi yana ƙarewa falon kallo yana yaba kyau da kuma tsaruwa na falon.
“A masu ƙaramin ƙarfi dai iyayenta sun yi ƙoƙari” Ya faɗa yana danna carbinsa tare da yin mismis da baki alamar ko yaushe dai basa yin sake da yin hailala da salatin annabi S A W. Gaisawa suka yi ya mata barka, da fatan Allah ya raya, ganin tun da ta ce amin bata sake magana ba sai wasa da yatsunta wanda suka sha ƙunshi take, yatsun ya kalla yana jinjina ƙoƙarin wacce ta zana ƙunshi, ya ce.

“Imran ɗin baya nan ne?”
Shiru Sadiya ta yi da ta tuna inda Abban twins ɗin yake, dan ta ji lokacin da Inna ta ce ya yi hanyar wajen murhu wataƙila ma yana cikin tukunyar kamar yadda Innar ta faɗa.

“Eh baya nan” Ta faɗa dan ta san dai har ya bar gidan Imran ba zai fito ba, bare ya gane ƙarya ta masa.

“Allah sarki, ko zaki samo mini ruwa in ɗan sha maƙoshina ya bushe, ba daga gida nake ba daga masallacin la’asar nake” Ya faɗa yana ɗan shafa gemu.
“To ” Ta ce ta tashi ta nufi frige.

“Wato ainifin ba mai sanyi ba sabo mura ta mun kamu me ƙarfi” Ya faɗa cikin yiwa maganar tasa kwaskwarima irin ta ustazai.

Ɗan jim ta yi tana jinjina ƙoƙarin mutumin, shi da ya zo barka, barkar ma daga maƙota amma har yake neman ruwa, haka dai ta kama hanya ta fita tsakar gidan tana addu’ar Allah sa dai shek ya tafi ba tare da matsalar da suke ciki ba ta bayyana kanta.

Ƙoƙarin sanya takalminta take amma kuma ganin Hassan na warware jelarsa sai ta dakata, tana ɗan kallon Ustaz ɗin da fatan Allah sa kar ya lura.

“Ɗan kula Sthadiya kin san daga nan wajen wani wa’azi zan je da ake gabatarwa a can masallacin sama damu duk laraba da yamma” Ya faɗa yana ɗan satar kallonta, tana shirin bashi amsa sai ganin micijin ta yi ya taso kamar wanda yake tafiya a kan iska, bai yi masauki ba aai a tsakiyar gidan, ya ɗaga kai sama ya fasa kansa alamar sara tare da sakin wani ƙara me kamar hamimiya.
Ya yi sallamar yana ɗan kauda kai gefe irin baya son nan ma ya kalleta saboda shi ustazu ne.

Sallamar ta amsa masa cikin sanyin murya, da shaƙewar muryarta kana ji ka san ta aha kuka babu lefi. Jin muryarta sai da shek Lawal ya saci kallonta ta gefen ido, ganin yanayinta sai ya ce a ransa.

“Iko sai Allah, Sthadiya kuma fuska da alamar kuka, wataƙila ba a kawo haƙiƙa ba ne(Ragon suna) Kuma suna har ya rage saura kwana biyu, ashe kowa yana jin yanayin garin”

“Sannu da zuwa ya shek bismillah” Ta faɗa tana juyawa cikin sanyin jiki ganin sai satar kallonta yake ita kuma bata son kallo shi kuma duk da ana kiransa uztaz amma kallon mata ne da shi sai dai yana yin kallo saisa -saisa ne dan kar a gane shi. Ganin ta juya sai ya shigo tare da sakin ƙofar yana sakawa kuwa iska ta maida ta rufe.

“Ya subhanallah! Iska a yi haka kuma ki rufe liman, kuma shek a cikin gidan matan aure daga zuwa barka” Ya faɗa cikin muryar ustazai, ita dai Sadiya bata ce masa komai ba, haka ya shigo gidan ma bakinsa da sallama, sake amsawa ta yi, tana cewa ya shigo falon.

“Toh, toh” Ya faɗa yana tsegumin ƙarewa tsakar gidan kallo, dan sau ɗaya ya taɓa shigowa lokacin da aka kwantar da Imran a asibiti da aka taso shi ya zo ya masa sannu. Kallon da yake kuwa tsegumi ne da gulma dan yana so ya ga a kan abin da Sadiyar ta yi kuka, da ya ga bai hango ragon suna ba sai zarginsa ya zama gaskiya na cewa kukan rashin ragon suna ne da ba a kawo ba.

“Amma kuwa Imran ka yi wawta, kuma ba Sthadiya kawai ka yiwa baƙinciki ba har da mu dan na san dai za ta aikawa Barira naman suna kuma ni ma ai Barira ta ajiye min ko da tsoka ɗaya ne” Ya faɗa a ransa yana me kutsa kai cikin ɗakin. Zaunawa ya yi yana ƙarewa falon kallo yana yaba kyau da kuma tsaruwa na falon.
“A masu ƙaramin ƙarfi dai iyayenta sun yi ƙoƙari” Ya faɗa yana danna carbinsa tare da yin mismis da baki alamar ko yaushe dai basa yin sake da yin hailala da salatin annabi S A W. Gaisawa suka yi ya mata barka, da fatan Allah ya raya, ganin tun da ta ce amin bata sake magana ba sai wasa da yatsunta wanda suka sha ƙunshi take, yatsun ya kalla yana jinjina ƙoƙarin wacce ta zana ƙunshi, ya ce.

“Imran ɗin baya nan ne?”
Shiru Sadiya ta yi da ta tuna inda Abban twins ɗin yake, dan ta ji lokacin da Inna ta ce ya yi hanyar wajen murhu wataƙila ma yana cikin tukunyar kamar yadda Innar ta faɗa.

“Eh baya nan” Ta faɗa dan ta san dai har ya bar gidan Imran ba zai fito ba, bare ya gane ƙarya ta masa.

“Allah sarki, ko zaki samo mini ruwa in ɗan sha maƙoshina ya bushe, ba daga gida nake ba daga masallacin la’asar nake” Ya faɗa yana ɗan shafa gemu.
“To ” Ta ce ta tashi ta nufi frige.

“Wato ainifin ba mai sanyi ba sabo mura ta mun kamu me ƙarfi” Ya faɗa cikin yiwa maganar tasa kwaskwarima irin ta ustazai.

Back to top button