Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 10

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*10* last free page

*gen ..gen Allah ya kawo mu lokacin free pages are now over, bati readers a hanzarta a biya 300, masu satowa tohm u r on ur own na barku da amana muje zuwa fans love you all*

*Birnin sennar*

Ayman na zaune gaban Umma ya sunkuyar da kai yana kallon darduma tace ” yarima ba magana nake maka ba ,meya kawo ka gida cikin gaggawa haka?” Shiru yayi ya kasa magana saboda idan ransa ya baci baya iya magana a wannan lokacin, fauzan ne ya risina cikin girmamawa yace ” Allah taimaki Fulani ya ja zamani ya kara miki lafiya da arziki, ranki ya dade a jiyane muka samu sakon mai martaba sultan akan yana son ganin yarima cikin gaggawa ” tashi tayi ta xauna zuciyarta na dukan uku uku ” sultan da kansa ya aika muku da wannan sakon ka tabbata ?” “Na tabbata ranki shi dade, wannan shine dalilin zuwan namu ” shiru tayi wani zufa ya fara qeto mata dakyar tace ” tashi kuje Ku huta, kafin sultan ya nemo Ku ” nan suka tashi Ayman na tafiya a hankali tabi bayansa da kallo cike da tausayawa yaron yana da zurfin ciki bazaka taba sanin damuwarsa ba don ko mutuwa zaiyi bazai ce komai ba koda kashesa zaayi, wayar intercoms ta danna nan hadimanta suka shigo cikin girmamawa tace ” Ku kiramin wazirin babba ” ” an gama ranki shi dade ” daga haka wasu suka fice, cikin kankanin lokaci suka dawo da sakon cewa yana zuwa. Bayan mintuna kadan dogarin kofa ya sanar da isowan waziri Babba nan hadiman suka watse saboda sunsan idan Fulani ta nemi ganawa da waziri toh lallai magana ce mai muhimmanci, da sallama ya shigo ta masa izinin zama ya kwashi gaisuwa irin ta fadawa, wata yardajjiyar baiwar Fulani ta fara magana ” Allah taimaki waziri babba, Gimbiya Fulani tana son sanin dalilin dayasa mai Martaba sultan ke Neman yarima Ayman cikin gaggawa ” ” Allah taimaki Gimbiya Fulani Fulani ya baki nasara , bani da hurumin bada wannan labari Allah kadai yafi sani sai mai Martaba sultan amma nayi alkawarin idan ya gana da yarima nine farkon Wanda zai baki labarin abunda ke faruwa ” rufe ido tayi ta sake budewa waziri ya gane me take nufi donhaka ya tashi yana cewa ” na barki lafiya ranki ya dade Allah yaja zamani ” daga nan ya fita, wannan baiwar mai suna maisaratu tace ” Allah kara miki lafiya, ki kwantar da hankalinki yanxu zan tafi wurin sarkin fada da sarkin gida nasan bazan rasa samun wani labari ba” daga haka ta fice Fulani ta sauke wani boyayyar ajiyar zuciya.
Gimbiya suhail na tare da kuyanganta jakadiya ta shigo da sauri tana hada zufa nan suhail ta d’aga hannu sauran sukayi waje ” jakadiya bani labari ” ” Allah ya tsare yar sarki jikar sarki, wllhi akwai abunda ke shirin faruwa a wannan masarautar Wanda bamusan dashi ba , yau da sassafe jirgin sultan ya sakko a bayan masarauta aka shaida min yarima babba ne tare da bawansa , sannan dazu naga fitowar waziri babba a bangaren Gimbiya Fulani ” tashi suhail tayi ta tsaya tace ” tabbas jakadiya kin kawo labari mai muhimmanci, ki kira waziri karami maza a tura masa zinari mai yawan gaske da rakuma 5 ya tabbata daga yanxu zuwa azahar yazomin da labarin abunda ke faruwa Wanda sultan ke shirin aikatawa ” ” angama ya uwargijiyata Allah kare mana ke sarauniyar sennar maman sarki Aseem ” ” jakadiya! Na baki shanaye manya guda biyu, kije ki amso wajen maina ” ” godiya nake sarauniya Allah kara girma ya kashe makiyanki ya haukatasu baki d’aya “. Murmushi Gimbiya suhail take ta koma ta xauna tana karkada kafafu.

*****************
*Abuja Nigeria*

Aman na zaune tare da hajjo suna hira cikin nishadi yana matukar jin dadin hira da ita yana kare mata kallo gaskiya hajjo tana da wani kyau mai sanyi Wanda sai ka kalleta sosai zaka gane hakan ” kallon me kake min nifa bana son sa ido, tun ana kallon kyaun mutum har ana ganin muninka ” dariya yake yace ” kai besty kin iya zare manyan maganganu Allah, kinsan kina burgeni sosai Allah yasa ki auri yaya na naci gaba da tsokanarki ” hararinsa tayi tace ” wannan tsohon ne zai aureni Allah ya kiyaye ” ” look at you yayana da mufti menk waye tsoho a cikin su ” ” toh ai yayan ka bai iya turanci kamar mufti ba kuma nasan baya jin larabci ” ” waya gaya miki ,Nide ki taimaka ki auri yayanmu don ina son zama dake har abada dama matarsa d’aya ce sai yaransu biyu shikenan fa” turo baki tayi tace ” Ni bazan aureshi ba, ” ” haba kawata ” ” Ni ba kawarka bace naga kai ba mace bace ai ” ” haba besty bakisan mace da namiji suna zama kawaye ba ” ban taba sani ba sai yau ” ” toh nidai don Allah ki amince na zama babban abokinki Wanda duk duniya bayan inna sai Ni na zama na biyu” hararinsa tayi ” Kaine baba na koh dole ka zama na biyu ” murmushi yayi ” sorry na manta nine na uku ,kin amince please ” ya karasa maganar yana kama kunne tana kallonsa tana dariya ” kyakkyawan farin saurayi dan gaye ina zaka zama abokina ” ” nidai ki amince don Allah ” ” shikenan nan na amince ” murmushi yayi ” thanks besty am grateful ” ” Ni nasan me kake cewa Ne” don’t worry zan koya miki ” ” da naji dadi sosai dama ina son koyan turanci sosai ” haka ta cigaba da surutu yana dariya har magrib ya gabato tace zata koma dama ta bar pure water din wajen mmn Nana ,ya cire kudi ya mika mata taki karba ” idan na karbo inna tah zata min dukan tsiya ” kuma baraki mata karya ba ” ” karya babu kyau kullum tana fada min kada nayi karya ” murmushi yayi yace ” lallai inna ta iya tarbiya ” chocolate ya mika mata dakyar ta karba sukayi sallama yana daga mata hannu ya tafi.
Zee tazo gidan yafi sau uku tana Neman Ayman bata samunsa a karo na hdun ta hadu da aman suka gaisa tace masa ” idan bazaka damu ba mintu biyu please ” zama sukayi Aman yace ” go ahead ina sauraronki meke tafe dake ?” ” I don’t know how to say it but Allah ya jarabceni da qaunar dan uwanka but bai damu dani ba kodai yana da wacce zai aura ne?” Murmushi Aman yayi ” gaskiya bazan boy’e miki ba Ayman bashi da lokacin ki, asali baki gabansa kuma a halin yanxu ya tafi gida zancen aurensa da wata yar sarki a can kasar tasu ” ” what? Aure? gaskiya bai min adalci idan har ya auro wata bani ba ,saboda a duniya ban taba son wani da namiji irin yadda nake son Ayman ba please ka taimaka idan ban auri Ayman ba rayuwata na cikin hatsari domin nayi nisa cikin tarkon sonsa ” ” Ni kuma wane taimako zan miki ” ” kawai ka gayamin wacece yarinyar da zai aura ” ” yarinyar jinin sarauta ce amma bansan wace masarautar bane ” numfashi ta sauke ” lallai akwai aiki a nan gaba don wllhi bazan taba bari wata ta auri yarima bayan Ni ina raye ” ” toh ya zakiyi? ” murmushi tayi ” Ni nasan me yakamata nayi nagode, bani numbar wayarsa ” bani dashi ” serious, kuna gida d’aya ” wllhi I don’t have ” nan ta juya ta shige mota driver yaja suka tafi.

______________

Ayman na zaune a dakinsa dawowarsa kenan daga wajen sultan kansa ya tallabo yana tunani wannan wace irin rayuwace he is 25 da yan watanni shine ake shirin masa auren gida kamar wani tsoho Sabreena ta fiye rawar kai baya son mace Mara nitsuwa da yawan surutu Sam bata cikin tsarin irin matan da yake bukata a rayuwarsa, ga zancen nadin sarauta zaa nadashi yarima mai jiran gado a ranar auren nasa, shikenan yanxu ko makaranta bai gama ba zaa mishi aure bai taba nadamar rashin karatun da yake ba sai a wannan rana da a ce ya kammalla karatunsa da bashi da matsala, ya lumshe ido yana tuna wasikun nasa yau kwana uku kenan bai samu wasikar ba yana jin wani babu dadi a ransa yana son sanin yarinyar baisan dalili ba amma yana son ganinta murmushi yake yana lumshe idanu , Fulani ta shige tare da sallama ” barka da shigowa Umma nah ” ” barka dai yarima , na samu labarin abunda yake faruwa Allah ya sanya alheri amma naso a ce ka gama first degree naka kafin kayi aure , Allah yasa hakan shine mafi alheri a rayuwarku ” ” ameen nagode amma sultan yayi alkawari zan cigaba da karatuna bayan auren bansan ya mutanen masarautar tasu zasu dauki zancen ba” ” Allah ya baka nasara ” ” amin Umma gobe zan wuce da safe saboda lectures ” ” Allah taimaka zan bada sako a kaiwa Ammin Ku ” ” Allah kaimu ranki ya dade ” murmushi tayi ta tashi ta fita. Da safe karfe 8 private jet na masarautar ta sauka a airport din Abuja motoci na jiransu daga nan suka wuce gidan SGF , Ammi bata tashi daga bacci ba donhaka yayi breakfast kawai yayi shirin xuwa school saboda a yau yayi alwashin sanin wacece yarinyar dake aiko masa da love letters. Sun fito lectures yana zaune a bayan mota a can inuwar wata bishiya suna hutawa daga shi sai Fauzan, motoci 5 suka doso inda suke baisan meke faruwa ba saboda hankalinsa na bisa waya fauzan kuwa zuba ido yayi yana son sanin suwanene, parking akayi aka bude mata mota zee ce ta fito cikin takun kasaita ta karasa inda yake ” Hi sweetheart I rily missed you, ya kake ya hanya ” ko motsi baiyi ba bare ayi tunanin zaiyi magana, ” haba Prince meyasa kake wahalar da zuciyata please ka amshi soyayya ta ” kallo d’aya ya mata ya dauke kai ya d’aga hannu fauzan yazo kusa dashi ya masa rada a kunne, fauzan ya juya wajenta yace ” kiyi hakuri yarima yana da wacce yake so da kin taimaki kanki kin daina wahalar da kanki wajen bibiyarsa da yafi miki sauki ” murmushi tayi tana kallon yarima tace ” Zee bata taba Neman Abu ta rasa ba a rayuwarta saboda haka ka zuba ido ka gani zan baka mamaki ” ta juya ta tafi cike da jin haushin rashin samun nasara ta rasa meyasa Ayman yake da tsananin taurin kai, maza nawa ke Neman Hulda da ita amma bata basu chance ba sai shi sannan yana wulakanta ta don sabar rainin wayo bazai mata magana ba sai servant dinsa dama haka jinin sarauta suke da girman kai gaskiya Ayman daban yake cikin maza ajin nasa yayi yawa amma ya zama dole ta mallakeshi don ya hadu karshen haduwa. da yamma Aman yaje gun hajjo suka xauna a bakin kofar malam Dalha inda ya koma dandalin zamansu suna hira da dariya ” kawata my besty ” turo baki tayi ” Ni ba kawarka bace ” ” toh Ni waye naki ne ?” rufe fuska tayi cikin jin kunya , a dai dai lokacin almajirin ke nuna hajjo da yatsa gaban Ayman ya fadi ya juya ya kalli bangaren dasuke ya sake kallon almajirin ” kana nufin wancan ita take baka wasika ka kawomin ” gyada masa kai yayi ” ehh ita take bani sunanta hajjo ” komawa yayi jikin mota ya jingina Kansa na tsarawa ya bude mota kawai ya shiga yace driver su tafi.

*pay your 300 and enjoy d rest of d story, contact 07030077024 for payment details thanks* *Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*10* last free page

*gen ..gen Allah ya kawo mu lokacin free pages are now over, bati readers a hanzarta a biya 300, masu satowa tohm u r on ur own na barku da amana muje zuwa fans love you all*

*Birnin sennar*

Ayman na zaune gaban Umma ya sunkuyar da kai yana kallon darduma tace ” yarima ba magana nake maka ba ,meya kawo ka gida cikin gaggawa haka?” Shiru yayi ya kasa magana saboda idan ransa ya baci baya iya magana a wannan lokacin, fauzan ne ya risina cikin girmamawa yace ” Allah taimaki Fulani ya ja zamani ya kara miki lafiya da arziki, ranki ya dade a jiyane muka samu sakon mai martaba sultan akan yana son ganin yarima cikin gaggawa ” tashi tayi ta xauna zuciyarta na dukan uku uku ” sultan da kansa ya aika muku da wannan sakon ka tabbata ?” “Na tabbata ranki shi dade, wannan shine dalilin zuwan namu ” shiru tayi wani zufa ya fara qeto mata dakyar tace ” tashi kuje Ku huta, kafin sultan ya nemo Ku ” nan suka tashi Ayman na tafiya a hankali tabi bayansa da kallo cike da tausayawa yaron yana da zurfin ciki bazaka taba sanin damuwarsa ba don ko mutuwa zaiyi bazai ce komai ba koda kashesa zaayi, wayar intercoms ta danna nan hadimanta suka shigo cikin girmamawa tace ” Ku kiramin wazirin babba ” ” an gama ranki shi dade ” daga haka wasu suka fice, cikin kankanin lokaci suka dawo da sakon cewa yana zuwa. Bayan mintuna kadan dogarin kofa ya sanar da isowan waziri Babba nan hadiman suka watse saboda sunsan idan Fulani ta nemi ganawa da waziri toh lallai magana ce mai muhimmanci, da sallama ya shigo ta masa izinin zama ya kwashi gaisuwa irin ta fadawa, wata yardajjiyar baiwar Fulani ta fara magana ” Allah taimaki waziri babba, Gimbiya Fulani tana son sanin dalilin dayasa mai Martaba sultan ke Neman yarima Ayman cikin gaggawa ” ” Allah taimaki Gimbiya Fulani Fulani ya baki nasara , bani da hurumin bada wannan labari Allah kadai yafi sani sai mai Martaba sultan amma nayi alkawarin idan ya gana da yarima nine farkon Wanda zai baki labarin abunda ke faruwa ” rufe ido tayi ta sake budewa waziri ya gane me take nufi donhaka ya tashi yana cewa ” na barki lafiya ranki ya dade Allah yaja zamani ” daga nan ya fita, wannan baiwar mai suna maisaratu tace ” Allah kara miki lafiya, ki kwantar da hankalinki yanxu zan tafi wurin sarkin fada da sarkin gida nasan bazan rasa samun wani labari ba” daga haka ta fice Fulani ta sauke wani boyayyar ajiyar zuciya.
Gimbiya suhail na tare da kuyanganta jakadiya ta shigo da sauri tana hada zufa nan suhail ta d’aga hannu sauran sukayi waje ” jakadiya bani labari ” ” Allah ya tsare yar sarki jikar sarki, wllhi akwai abunda ke shirin faruwa a wannan masarautar Wanda bamusan dashi ba , yau da sassafe jirgin sultan ya sakko a bayan masarauta aka shaida min yarima babba ne tare da bawansa , sannan dazu naga fitowar waziri babba a bangaren Gimbiya Fulani ” tashi suhail tayi ta tsaya tace ” tabbas jakadiya kin kawo labari mai muhimmanci, ki kira waziri karami maza a tura masa zinari mai yawan gaske da rakuma 5 ya tabbata daga yanxu zuwa azahar yazomin da labarin abunda ke faruwa Wanda sultan ke shirin aikatawa ” ” angama ya uwargijiyata Allah kare mana ke sarauniyar sennar maman sarki Aseem ” ” jakadiya! Na baki shanaye manya guda biyu, kije ki amso wajen maina ” ” godiya nake sarauniya Allah kara girma ya kashe makiyanki ya haukatasu baki d’aya “. Murmushi Gimbiya suhail take ta koma ta xauna tana karkada kafafu.

*****************
*Abuja Nigeria*

Aman na zaune tare da hajjo suna hira cikin nishadi yana matukar jin dadin hira da ita yana kare mata kallo gaskiya hajjo tana da wani kyau mai sanyi Wanda sai ka kalleta sosai zaka gane hakan ” kallon me kake min nifa bana son sa ido, tun ana kallon kyaun mutum har ana ganin muninka ” dariya yake yace ” kai besty kin iya zare manyan maganganu Allah, kinsan kina burgeni sosai Allah yasa ki auri yaya na naci gaba da tsokanarki ” hararinsa tayi tace ” wannan tsohon ne zai aureni Allah ya kiyaye ” ” look at you yayana da mufti menk waye tsoho a cikin su ” ” toh ai yayan ka bai iya turanci kamar mufti ba kuma nasan baya jin larabci ” ” waya gaya miki ,Nide ki taimaka ki auri yayanmu don ina son zama dake har abada dama matarsa d’aya ce sai yaransu biyu shikenan fa” turo baki tayi tace ” Ni bazan aureshi ba, ” ” haba kawata ” ” Ni ba kawarka bace naga kai ba mace bace ai ” ” haba besty bakisan mace da namiji suna zama kawaye ba ” ban taba sani ba sai yau ” ” toh nidai don Allah ki amince na zama babban abokinki Wanda duk duniya bayan inna sai Ni na zama na biyu” hararinsa tayi ” Kaine baba na koh dole ka zama na biyu ” murmushi yayi ” sorry na manta nine na uku ,kin amince please ” ya karasa maganar yana kama kunne tana kallonsa tana dariya ” kyakkyawan farin saurayi dan gaye ina zaka zama abokina ” ” nidai ki amince don Allah ” ” shikenan nan na amince ” murmushi yayi ” thanks besty am grateful ” ” Ni nasan me kake cewa Ne” don’t worry zan koya miki ” ” da naji dadi sosai dama ina son koyan turanci sosai ” haka ta cigaba da surutu yana dariya har magrib ya gabato tace zata koma dama ta bar pure water din wajen mmn Nana ,ya cire kudi ya mika mata taki karba ” idan na karbo inna tah zata min dukan tsiya ” kuma baraki mata karya ba ” ” karya babu kyau kullum tana fada min kada nayi karya ” murmushi yayi yace ” lallai inna ta iya tarbiya ” chocolate ya mika mata dakyar ta karba sukayi sallama yana daga mata hannu ya tafi.
Zee tazo gidan yafi sau uku tana Neman Ayman bata samunsa a karo na hdun ta hadu da aman suka gaisa tace masa ” idan bazaka damu ba mintu biyu please ” zama sukayi Aman yace ” go ahead ina sauraronki meke tafe dake ?” ” I don’t know how to say it but Allah ya jarabceni da qaunar dan uwanka but bai damu dani ba kodai yana da wacce zai aura ne?” Murmushi Aman yayi ” gaskiya bazan boy’e miki ba Ayman bashi da lokacin ki, asali baki gabansa kuma a halin yanxu ya tafi gida zancen aurensa da wata yar sarki a can kasar tasu ” ” what? Aure? gaskiya bai min adalci idan har ya auro wata bani ba ,saboda a duniya ban taba son wani da namiji irin yadda nake son Ayman ba please ka taimaka idan ban auri Ayman ba rayuwata na cikin hatsari domin nayi nisa cikin tarkon sonsa ” ” Ni kuma wane taimako zan miki ” ” kawai ka gayamin wacece yarinyar da zai aura ” ” yarinyar jinin sarauta ce amma bansan wace masarautar bane ” numfashi ta sauke ” lallai akwai aiki a nan gaba don wllhi bazan taba bari wata ta auri yarima bayan Ni ina raye ” ” toh ya zakiyi? ” murmushi tayi ” Ni nasan me yakamata nayi nagode, bani numbar wayarsa ” bani dashi ” serious, kuna gida d’aya ” wllhi I don’t have ” nan ta juya ta shige mota driver yaja suka tafi.

______________

Ayman na zaune a dakinsa dawowarsa kenan daga wajen sultan kansa ya tallabo yana tunani wannan wace irin rayuwace he is 25 da yan watanni shine ake shirin masa auren gida kamar wani tsoho Sabreena ta fiye rawar kai baya son mace Mara nitsuwa da yawan surutu Sam bata cikin tsarin irin matan da yake bukata a rayuwarsa, ga zancen nadin sarauta zaa nadashi yarima mai jiran gado a ranar auren nasa, shikenan yanxu ko makaranta bai gama ba zaa mishi aure bai taba nadamar rashin karatun da yake ba sai a wannan rana da a ce ya kammalla karatunsa da bashi da matsala, ya lumshe ido yana tuna wasikun nasa yau kwana uku kenan bai samu wasikar ba yana jin wani babu dadi a ransa yana son sanin yarinyar baisan dalili ba amma yana son ganinta murmushi yake yana lumshe idanu , Fulani ta shige tare da sallama ” barka da shigowa Umma nah ” ” barka dai yarima , na samu labarin abunda yake faruwa Allah ya sanya alheri amma naso a ce ka gama first degree naka kafin kayi aure , Allah yasa hakan shine mafi alheri a rayuwarku ” ” ameen nagode amma sultan yayi alkawari zan cigaba da karatuna bayan auren bansan ya mutanen masarautar tasu zasu dauki zancen ba” ” Allah ya baka nasara ” ” amin Umma gobe zan wuce da safe saboda lectures ” ” Allah taimaka zan bada sako a kaiwa Ammin Ku ” ” Allah kaimu ranki ya dade ” murmushi tayi ta tashi ta fita. Da safe karfe 8 private jet na masarautar ta sauka a airport din Abuja motoci na jiransu daga nan suka wuce gidan SGF , Ammi bata tashi daga bacci ba donhaka yayi breakfast kawai yayi shirin xuwa school saboda a yau yayi alwashin sanin wacece yarinyar dake aiko masa da love letters. Sun fito lectures yana zaune a bayan mota a can inuwar wata bishiya suna hutawa daga shi sai Fauzan, motoci 5 suka doso inda suke baisan meke faruwa ba saboda hankalinsa na bisa waya fauzan kuwa zuba ido yayi yana son sanin suwanene, parking akayi aka bude mata mota zee ce ta fito cikin takun kasaita ta karasa inda yake ” Hi sweetheart I rily missed you, ya kake ya hanya ” ko motsi baiyi ba bare ayi tunanin zaiyi magana, ” haba Prince meyasa kake wahalar da zuciyata please ka amshi soyayya ta ” kallo d’aya ya mata ya dauke kai ya d’aga hannu fauzan yazo kusa dashi ya masa rada a kunne, fauzan ya juya wajenta yace ” kiyi hakuri yarima yana da wacce yake so da kin taimaki kanki kin daina wahalar da kanki wajen bibiyarsa da yafi miki sauki ” murmushi tayi tana kallon yarima tace ” Zee bata taba Neman Abu ta rasa ba a rayuwarta saboda haka ka zuba ido ka gani zan baka mamaki ” ta juya ta tafi cike da jin haushin rashin samun nasara ta rasa meyasa Ayman yake da tsananin taurin kai, maza nawa ke Neman Hulda da ita amma bata basu chance ba sai shi sannan yana wulakanta ta don sabar rainin wayo bazai mata magana ba sai servant dinsa dama haka jinin sarauta suke da girman kai gaskiya Ayman daban yake cikin maza ajin nasa yayi yawa amma ya zama dole ta mallakeshi don ya hadu karshen haduwa. da yamma Aman yaje gun hajjo suka xauna a bakin kofar malam Dalha inda ya koma dandalin zamansu suna hira da dariya ” kawata my besty ” turo baki tayi ” Ni ba kawarka bace ” ” toh Ni waye naki ne ?” rufe fuska tayi cikin jin kunya , a dai dai lokacin almajirin ke nuna hajjo da yatsa gaban Ayman ya fadi ya juya ya kalli bangaren dasuke ya sake kallon almajirin ” kana nufin wancan ita take baka wasika ka kawomin ” gyada masa kai yayi ” ehh ita take bani sunanta hajjo ” komawa yayi jikin mota ya jingina Kansa na tsarawa ya bude mota kawai ya shiga yace driver su tafi, suna tafiya yana tunani kodai dama can Aman tayi niyyan turowa letters din akayi kuskure yaron yana kawo mishi amma da zata sanar da Aman cewa tana rubuta masa letters , fuskanta yake hangowa a ranar da ya fara ganinta lokacin da Aman ya mareta she is so cute da farko yayi niyyar fuskantarta ya fayyace mata sirrin zuciyarsa na son kusanci da ita amma kash..Aman yayi Katanga tsakaninsu, lumshe ido yayi ya kwanta jikin seat yana jin zuciyarsa ta masa nauyi.

*pay your 300 and enjoy d rest of d story, contact 07030077024 for payment details thanks* this is just d beginning hurry n patronise yanxu aka fara labarin soyayya da tarkon qauna sarkakiya da ilmantarwa da nisadantarwa na gaba ,muje zuwa Ku biya 300 kacal don samun cigaban labarin nagode da kulawa.

Back to top button