Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 15

Sponsored Links

Page 1️⃣5️⃣

 

Goge hawayen Daya zubo a idonta tayi Sannan tace”yanzu duk bawan nan ba muyi isha semu kwanta yau da wuri zanyi bacci” sallah sukayi kafin suka Dan taba hira kirane yashigo wayar FANAN dubawa tayi taga Ashe zeenat ce picking tayi tasa akunne “assalamualaikum zeenat yakike? “Lfy Lau ya gida yasu mama dama ya azaad dazun mungama cin abinci yatashi ze haura sama shine yafadi Amma yanzu ya farfado shine ummi tace nakiraki Dan Allah gobe kizo da wuri”zeenat tagama magana tana jiran amsan FANAN ajiyar zuciya FANAN tayi Sannan tace”Allah sarki in sha Allah zanzo da wuri kigaishe da kowa ” sallama sukayi kafin ta ajiye wayar suhaima ce tace”ayyah jikin patient din nakine yatashi eh wlh kekam gobe dole infita da wuri Allah yakaimu Ameen kwanciya sukayi tare dayin adduah.

 

 

Washe gari karfe 5:00am suka tashi nafila sukayi kafin aka shiga masallaci bayan sun idarne FANAN tace “bari inje in fara aiki” okay sena fito kitchen tawuce tahada kayan wanke_ wanke tayi tazo tayi shara da mopping sannan tadaura abin karyawa karfe 7:30 tagama komai tashiryasu afalo sannan Takoma tashiga wanka fitowa tayi tasamu suhaima nata sharara baccinta hankali kwance “ke mayyar bacci dallah tashi kije kiyi wanka kizo muyi breakfast” mikewa suhaima tayi tana salati da Mika kafin ta harareta “nifa bansan irin haka dole SE tare zamu karya Ina bacci na me dadi kin wani tasheni” Koh kulata FANAN batayi ba kayanta tadauko a wardrobe Riga da skirt ne na atamfa orange da touch din Baki sakawa tayi skirt din yadan kamata fakin din gashinta tayi tasa ribom Baki harta dauko dankwali zata daura seta fasa, shafa powder tayi tasa kwalli a idonta sannan tafesa turare hijab dinta Baki tasaka dogo harkasa me hannu daukan handbag dinta tayi da plate shoe
Hartazo fita tajuyo takalli suhaima data koma bacci dudduba dakin tayi can taga guntun pure water taje setin fuskanta tadaga ledan tafara sheka mata ruwan afuska azabure ta mike tafara banbami aikuwa dasauri FANAN tabar mata dakin tana dariyan mugunta falo tashiga taje dakin mama haduwa sukayi da mama tana kokarin fitowa gaisheta tayi “nagama abun karyawan” to muje falon suka dawo Basu fi mintuna dashigowa ba su ya Usman suka shigo suna musu “Kai wlh zanbaka shawara ka koma man city kawai” inji ya Usman “allah yakyauta mu ai Madrid bagudu baja da baya karka ga Dan abdulkareem benzema yabar Madrid kuyi tunanin yawargaje zamu dawo” dariya sosai ya al Ameen yayi kude kawai yanzu kunzama losers oho koma de Meye munji gaida mama sukayi kafin fanan ta gaishe dasu amsawa sukayi Al Ameen yace “Ina suhaima bangantaba kode haryanzu tana baccin asara” ya al Ameen natasheta tana zuwa okay zuba musu abincin tayi alele ne da Miya SE farfesu da kunun gyada Basu faracin abincin ba seda baba yashigo duka gaishesa sukayi zama yayi Yana amsawa gaisuwan nasu kallon su yayi duka kafin yace Ina suhaima , suhaima Dake bakin kofan shigowa tace baba gani nan karasowa falon tayi tana gallawa FANAN harara dariya kasa _kasa fanan takeyi Dan tasan abinda ta aikata gaida mutanen falon tayi kafin tazauna suka fara karyawa abinci sukeci Amma daga zaran suhaima da fanan sun hada ido hararanta suhaima takeyi itakuwa FANAN abin dariya yake bata harara suhaima tawatsa mata wani irin dariya ta fashe dashi Wanda seda falon yadauka kowa yatsaya yazuba mata ido takai kusan 3mint tana dariyar kafin ta tsaqaita ganin datayi kowa yazuba mata ido suna kallonta da mamaki ne yasa tashiga nutsuwarta gaba Dayansu sunkasa dauke idonsu akanta mama kam ta gumi tayi tana kallon iKon god baba ne yace “FANAN fatan de lafiyanki kalau” eh baba tana sunkuyar dakai to Allah yasa ya Usman ne cikin zolaya yace ” majinyatan mu na gida Dana asibiti Allah yabasu lfy dariya sukayi duka suna Ameen bayan sungama ne FANAN tace zan tafi as usual kudin transport baba yabata Yana mata adduah dawowa lafiya kallon suhaima tayi tace “yar uwa yau ba rakiyane ” eh din bazaa rakaba fita tayi tana yar dariya.

Baba ne yace “ohhh FANAN Allah yashiryeki” mama ce ta amsa da Ameen kome yasata dariya haka se Allah ya al Ameen Dake Shan kunu ne yafara fadin “aiduk abinda sukeyi ita da suhaima Ina kallonsu suhaima ce ke hararanta itakuwa hararan ne yabata dariya shine take dariya” hhhhhhh Abin dariya yabasu baba yace “alamu sun nuna yau fa sun kwabe anyi fada kenan “.

 

 

Shiga falon tayi da sallama abakinta dukkansu afalo ta samesu Banda azaad Dake dakinshi Yana bacci, yaseer ma yazo Dan agidan yakwana gaidasu tayi kafin tamusu yame jiki amsawa sukayi dasauki alhamdulillah ummi ce tace ” ki haura Yana ciki ” to ummi haurawa upstairs tayi tashiga part dinsa afalo ta tsaya tana tunanin yatashine ko Yana baccin yankewa tayi baride inje induba ajiye jakanta tayi afalonshi tashiga dakin kwance tasameshi Yana bacci bubbuga filo tafarayi Mr azaad katashi ahankali yafara Bude idonshi dasuka Dan kumbura kadan gashi yayi ja idon shine yasauka akan fuskanta ahankali yamike yazauna abakin gado farar jallabiya ce ajikinshi tunda suka dawo daga masallaci be cire ba yakwanta babu Wanda yayi magana acikinsu tashi yayi yashige toilet zama tayi akan kujera tana jiranshi bayan kaman 30mint yafito sanye da towel direct gaban mirror yaje yagama duk wani abinda zeyi kafin yashige dressing room dinshi FANAN kuwa tunda tazauna tafara game awayarta bata Kara dagowa ba fitowa yayi sanye da Riga armless fari jikin rigan anyi manyan rubuta MAN IS BORN TO HUSTLE da dogon wando na jeans zama yayi akan gadonshi yafara latsa wayarsa sunfi 30mint ahaka gajiya tayi da zaman tace ” kasa akawo maka breakfast kayi insamu inma alluranka” ko dago Kai beyiba balle yasan ana mishi magana gajiya tayi takira zeenat” zanma yayanku allura gashi be ci komai ba” to kawai zeenat tace ta katse Kiran 5mint latter tashigo da kayan abinci Yaya mezansa maka be mata magana ba ya mata nuni da ta Bude duka food flask din Bude su tayi kulan farko yam balls ne aciki nabiyu Kuma chips ne dasukaji egg SE na ukun farfesun naman rago ne yaji kayan hadi se tiriri yakeyi nuni yamata da farfesun zuba mishi tayi Ta ajiye mishi a table din Dake gabansa kafin tahada mishi tea tafita. Fanan kuwa tacika fam kamar zata fashe gaba Daya yagama bata mata lokaci sewani Jiji Dakai yakeyi mtsssw tsaki taja Wanda batasan yafito ba dagowa yayi ya kalleta hada ido sukayi takawar da kanta gefe taci gaba da game dinta seda yakwashe mintoci kafin yagama hamdala yayi cikin sexy voice dinshi yace” am done kizokiyi abinda zakiyi I have something to do” sake Baki FANAN tayi tana kallonshi wato shi yanada abinda zeyi nice banida abinyi lallai wannan yacika babban Dan renin hankali mikewa tayi tadau ruwan alluran taja a syringe da cotton hannunshi yamika mata ta daure tasamo jijiya kafin tamishi alluran tasamai cotton dustbin taje tayar da syringe din maganinshi taballa mishi tabashi da ruwa yakarba yasha sannan ta tambayeshi “yanzu Meye yake damunka” kamar bazeyi magana ba yace “nothing” fita tayi a dakin tadau jakanta tabar part din falo tadawo tasamesu sunata hira zama tayi kusa da anty Amina suna hira, shigowa tayi falon batare da tayi sallama ba Kai tsaye inda fawwaz yake taje tatsaya ” Kai Ina baby yake ” juyowa su ummi dasu FANAN sukayi Dan basusan da shigowanta ba sanye take da wando crazy Baki se wata yar ficikan Riga pink kan nan babu Dankwali yasha attachment two color kafarta sanye da takalmi Sau ciki Shima pink fuskan nan yasha uban makeup FANAN kam mamakine yakamata Amma wannan kam arniya ce fawwaz kuwa cigaba da kallon ball din dayakeyi yayi beko dago Kai ba ganin baze kulata bane yasa takarasa kusa dasu ummi “hi guys Ina baby yaje” zeenat ce ta iya ” kulata kinbamu ajiyansa ne” to karamar mara kunya banyi Dake ba kikama kanki Dani tam duk abinda sukeyi ummi batace musu ci kanku ba haka anty Amina ma FANAN kam Takoma yar kallo ” tunda bawanda ze iya fadamin inda yake zanje indubasa da kaina” takarasa maganar tana nufan part din Azaad ganin baya falo yasa tawuce dakinsa akwance tasameshi zuwa tayi takwanta akanshi tana fadin “baby wake up am here” Bude ido yayi yaganta kwance ajikinshi tashi yayi yadan tureta daga jikinsa Yana fadin “aneesa meyasa Baki da hankali ne wai yanzu haka Kika fito daga gida kamar wata arniya ” kallon jikinta tayi tace “baby what’s wrong with my dress tell me if there’s something wrong on it ” takaicine yakamasa wato ita bata masan shigar datayi be dace ba harwani tambaya take what’s wrong with her dress unbelievable Kuma wai ahaka ita ze aura yafada duniyar tunani yaji tana fadin “baby when are we going back to US ” ke bansaniba ko dole sedani Zaki koma please don’t disturb me aneesa kukan shagwaba tafara mishi tashi yayi ya dauki wayarsa yafita falon kasa yadawo tana biye dashi abaya gaida ummi yayi da anty Amina suka amsa yajikin naka dasauki kawai yace pressing phone dinshi yafara karasowa aneesa tayi tazauna a kujeran dayake tamanne dashi tana mishi magana ko kulata beyi ba yaci gaba da abinda yakeyi yaseer ne yace aneesa nikam bakyajin kunyane ga surkanki akusa Amma kina irin wannan abun murguda mishi Baki tayi Ina ruwanka ummi de tashi tayi abunta tayi sama anty Amina ma bayanta tabi yarage su zeenat ne afalon kallo takunna musu a TV tashan MBC action suna kallo areef ne yace ” zeenat kaimana tashan MBC 2 nasan yanzu suna day breaking” to tace Dan batama San wani film bane shiga tayi aikuwa sukaga anhasko inda wata horror takecin kayan cikin wani ihu suka fasa da ita da FANAN yaseer da fawwaz mezasuyi inbanda dariya harda rike ciki kallon su kawai azaad yayi yadaga musu tsawa “wani irin haukane wannan” shiga cikin rigan nutsuwar su sukayi gashi areef yace baze canza Tasha ba SE rokonsa sukeyi karshema cillawa fawwaz remote din yayi.ganin hakane yasa FANAN da zeenat suka rungume juna da anyi abin tsoro suyi ihu mazan Kuma SE dariya sukeyi Banda azaad da aneesa datayi bacci tana kwance akan kafadar azaad wani wajan dayafi ko Ina tsoro aka nuna wani mutum horrorin suka kwantar suka dauko katon guduma sukayi kaca_kaca da kanshi yatarwatse wani irin ihu suka buga hannu FANAN takai tana ihu tana nuna TV wani irin spark TV yakeyi Yana kawowa Yana daukewa duk Basu luraba still hannun nata nasetin TV duk motsine da zatayi se tv yayi spark tun Basu ankaraba harsuka dawo da hankalinsu wajan itakuwa batama San tanayi ba dungule hannunta tayi da karfi tsabar tsoro tana kokarin rungume zeenat fat!fat!fat! TV yatarwatse yayi condem SE hayaki yakeyi zaro ido sukayi suka kalli TV sesu kalli FANAN ganin suna kallonta ne yasa tace meyafaru ya yaseer nuna mata TV yayi zeyi mata maganan abinda tayi azaad yayi saurin mishi signal da ido akan yayi shuru domin daga gani batasan tayi hakan ba Amma gaba Dayansu sun tsorata da abinda yafaru karasawa tayi kusa da TV tayi tace “subhanallhi meyasameshi yayi haka” bata gama rufe Baki ba jiri yadibeta zata fadi cikin zafin nama azaad ya rungumota kafin ya Ankara harta Suma daukanta chak yayi kamar yar baby ya kwantar da ita akan kujera ana kwantar da ita su ummi suka fito tana fadin ” nikam yaran nan lafiya kuke mana ihu ” sauka idonta yayi akan FANAN Dake kwance akan sofa dasauri suka karaso meya sameta fawwaz ne yabasu labarin abinda yafaru dukkansu mamaki yacikasu anty Amina ce tace” to me hakan yake nufi shafa kan FANAN takeyi ahankali Kuban ruwa Mika mata ruwa zeenat tayi shafa mata tayi afuska ajiyar zuciya tayi ta tashi tana rike kanta Dake mata azaban ciwo murya narawa tace “wayyo kaina zefita ya Allah,ummi kaina ” kwantar da ita ajikinta ummi tayi “sannu kinji bari Kisha magani zedena to aneesa data danyi baccine tafarka tazo gun azaad baby natafi gida okay kawai yace mata kafin ta tafi ……

 

Tom semun hadu gobe in da Rai da lfy muhadu a comment section

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by (MRS ISHAM )

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

 

____________________________________________

Back to top button