Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 95

Sponsored Links

95…..
Khaleel na xaune daki yana duba wasu files din gabansa agogo yyi struck din karfe 12, ya juya yana kallon Ikram da tun shigowarta dakin bayan sun gama wanke wanke da Maryam take kallo, ya rufe file din gabansa yace “ikram” ta juya da sauri tana kallonsa yace “tun da aka yi holiday ban ga kin dauka chemistry ko biology kina karantawa ba, ko baki son xana waec nxt yr ne, or kin fi so kiyi a ss3” tace “A’a ina so mana a ss2 xanyi, ae xan fara karatun daga gobe” yace “to xaki je holiday coaching na makarantar ku ne” da sauri tace “A’a ni xan yi karatuna a gida, kuma ae xan dinga xuwa islamiyya ma” yace “ok, but ki rage wnn kallon naki” Maryam ce ta bude kofar dakin ta shigo tace “me xa’a girka Khaleel” Khaleel ya juya yana kallon Ikram yace “me kike son ci?” ta dan yamutse fuska tace “ni shinkafa da miya nake so” yace “to ae tashi xaki yi ku je kuyi shinkafa da miyar” tace “bayan wanke wanken da nayi daxu? Ni fa ta bar ma kwanukan na wanke” ta karashe mgnr a fusace, Khaleel yyi shiru yana kallonta, da sauri ta mike tace “to naji” ta fice daga dakin, ya taso ya karaso kusa da Maryam dake tsaye har lkcn ya kamo hannunta yace “kiyi hkuri da yanayin Ikram Maryam, wit tym xata daina duk wnn abinda take kinga dae nima ba kyaleni tayi ba” fixge hannunta tayi ta fice daga dakin, ta sauka xuwa kitchen, danyen shinkafa ta tar Ikram ta cika cikin wani katon tukunya tana kkrin fara wankewa a famfo, ta karbe tukunyar shinkafar tace “su wa da su wa xasu cinye wnn shinkafar” Ikram tace “su mu mana, bari ki ga ynda na auna” ta dauko nml plate din xuba abinci tace “sau uku na cika wnn dam dam, ke daya ni daya ya Khaleel ma daya” Maryam tace “to ba hka ake yi ba Hajiya” Ikram tace “ni ba Hajiya bace” Maryam bata tanka ta ba ta dauko dan kofi tace “xamu dinga amfani da wnn wajen aunar shinkafar,” ta auno kofi uku a tukunyar bayan ta mayar da wnda Ikram ta debo tace “kinga wnn ya isa” Ikram tace “to ae wnn ko ni sae in cinye shi” Maryam tace “bari a dafa ki ga ko xa ki cinye shi” gas ta kunna snn ta daura ruwa a tukunya ta rufe ta ajiye shinkafar gefe, Ikram tace “to meyasa baki xuba ba?” Maryam tace “sbda sae ruwan yyi xafi, snn a wanke shinkafar a xuba” Ikram ta dan tabe baki bata ce komai ba, Maryam tace “kin dae ji me nace ” Ikram tace “ehh” nama ta dauko a deep freezer da kayan miya, ta ajiye naman cikin yar roba, Ikram tace “to da kankarar xamu dafa ta” Maryam ta dan yi murmushi ta xuba ruwa cikin naman dan kankarar ya narke, Ikram tace “to ae ddin naman xae wuce idan aka bar shi cikin ruwa kuma” Maryam tace “da ace ba ynxu xa muyi girkin ba da barin sa kawae xamuyi xae narke da kansa, amma ynxu kinga amfani xa muyi da shi” Ikram na kallo ta shiga wanke kayan miya a sink, har ta gama snn ta juyo tace “kin dae ga ynda nayi ko?” tace “ehh” Maryam tace “to gobe ke xaki yi” ssae Ikram ta maida hankalinta gun girkin da Maryam ke yi, don tayi tambaya ya fi dari, har daga karshe suka hada shinkafarsu da Miya har da ginger drink, a tare suka jera a dinnin, Ikram sae murna take yau ta dan yi girki tunda ita ta soya naman kuma ta dinga juya miya kan gas tana dandanawa, sae da suka fara sllh snn Maryam tace taje ta kira Khaleel ya xo su ci abinci, ta nufi sama da sauri tace “ya Khaleel mun gama ka xo mu ci abinci” sae da ya gama abinda yake snn suka sauko a tare, Maryam ta xuxxuba masu, Khaleel yyi murmushi yace “thank yhu” snn ya dauki spoon ya saka cikin abincin ya juya yana kallon Ikram da har tayi cokali uku, yana kai abincin baki ya juya yana kallon Maryam yace “waw yhu re a vry gud cook dear” tayi murmushi tace “thank yhu” Ikram ta juya tana kallonsa sae kuma ta jefar da cokalin hannunta cikin abincin gabanta ta mike da sauri ta nufi sama, ya juya yana kallon Maryam, Maryam tayi murmushi bata ce komai ba, mikewa yyi yabi bayanta ya tar da ta xaune dakinta tana hawaye ya karaso da sauri yace “me ya faru Ikram” cikin kuka tace “to ita kadae tayi girkin da xaka wani ce mata gud cook, ni kuma bad cook ko?” ya rungumeta yace “ohh no Ikram kema gud cook ce wllh,” tace “to nima mu koma kasa kace min hka a gabanta” danne dariyarsa yyi yace “to kanwata tashi mu je” ba musu ta bisa suka koma dinnin din ta xauna shi ma ya xauna Maryam dae sae cin abincin ta take, sae da ya kuma kai cokali daya baki snn yana lumshe ido yace “ummm, u re a vry gud cook My Ikram” Ikram ta dan yi murmushi ta juya tana kallon Maryam tace “thank yhu” danne dariyarsa yyi ya kasa dago kansa, Maryam tayi dariya tace “to hankalin ki ya kwanta ynxu” Ikram tace “ehh mana” a tare suka kwashe kwanukan bayan sun gama cin abincin, suna shiga kitchen Ikram tace “ki barni ni kadae in wanke kwanukan xan iya ae naga ynda muka yi daxu” Maryam tace “to, idan kin gama kuma ko wanne ki ajiyesa inda ya ke” Ikram tace “to” snn Maryam ta fita daga kitchen din ta wuce sama, mikewa Khaleel yyi ya bi bayanta, ya sameta daki tana cire jewelries din jikinta ya rungumota ta baya ya daura kansa a kafadarta yace “kina kara cika min sonki bbyna”
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~

Back to top button