Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 53

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*53*

Bayan mintuna 15 aka turo kofa a hankali tare da sallama Wani qamshin turare ne ya bugi hancinta bata gane qamshin ba , gabanta ya Fadi bugun zuciyarta ya karu batasan dalili ba haka kurum ta tsinci kanta da faduwar gaba ya karasa cikin takun kasaita ya zauna gefen gadon kallo d’aya ya mata ya dauke Kai baisan ta Ina zai fara ba yasan yanzu dai tasan wanene mijin nata toh shi me zai ce mata daga haka ya juya ya fice daga d’akin, bayan minti 5 ya dawo ya ajiye ledoji sannan ya sake fita ya rufe mata kofa. Hajjo ta gaji da rufe fuska ta Bude tana sauke numfashi kallo d’aya tayiwa ledojin ta dauke Kai haushinsa ne ya kamata wato ta shigo gidansa zai fara wulakanta ta koh shikenan zata dauki mataki, kayan jikinta ta cire ta Bude wardrobe ta dauki kayan bacci doguwar Riga Latvia armless ta saka ta Kara fesa body mist nata ta kwanta tare da yin adu’o’in bacci.
Ayman kuwa ya kulle ko’ina Fauzan Yana can d’akinsa donhaka ya kulle site din sanin cewa Failuzaa Bata nan ya koma d’akinsa wanka ya sake Yi tare da alwala ya saka jallabiya yazo Yana jera nafilfilun nuna godiya ga ubangiji yau burinsa ya cika, ya Dade Yana adua akan Allah ya Basu zaman lafiya ya Kade fitina kafin ya kwanta, bacci ya kaurace masa toh yanzu idan tana zaune tana jiransa fah shin ya kyauta kuwa, bit…ya tashi ya wuce part din nata Yana zuwa ya Murda kofa ya jishi a kulle murmushi yayi ya juya ya koma d’akinsa Wanda yake wajen Wani corridor dake tsakanin part din matan .

Bayan tayi sallar asuba ta shiga wanka ta fito taci kwalliya cikin doguwar riga material me stones fitted gown ne ya matseta ya mata kyau sosai , gado ta koma ta kwanta tana azkar saboda yanzu dole rayuwa sai da azakar tana rike da counter ta kulle ido a haka bacci ya dauketa , Ayman yazo yayi knocking shiru haka ya wuce shi a tunaninsa haushin auren takeji shiyasa take haka.
Abinci aka kawo daga gidan inna Fauzan ya shigo dasu ya shirya a table ya debi nasa ya koma d’aki yaci domin zasu fita Ayman na da meeting da wasu larabawa masu son zuba hannun jari cikin kamfaninsa.
Ya shirya cikin manyan kaya da babbar Riga ya fito ango sak sai zuba qamshi yake ya sake knocking still kofar a kulle take haka ya girgiza kai Yana murmushi y’ar rigimar inna kenan maybe sai ya kira inna tazo tayi aikin rarrashi, haka ya wuce mota Fauzan ya fito suka tafi gidan ya rage sai maigadi.

Baba ya amince da auren maman Nana ya Yusuf ya biya sadaki tun mutanen da sukazo bikin hajjo Basu watse ba aka daura auren nasu Kano zasu koma saboda Baba Yana son fara business a can, maman Nana ta rasa da wane Baki zata godewa inna saboda ta mata halacci a rayuwa dama zuwan ta gida ta samu mijin nata ya koma garin nasu har ya sake sabon aure amma Bai nemi sanin halinda take ciki a wannan lokacin ne ta karbi takardar ta na saki bayan ta dawone taka fadawa inna yadda sukayi, washegari ne zasu koma Kano inna ta hadawa maman Nana Sha tara na arziki Amma awajen inna zasu bar Nana ta cigaba da zama saboda karatun da ta fara. da yamma Ayman yazo tare da Fauzan dama shi bashi da tarin abokai sunzo gabatar da gaisuwa gun surukai bayan sungaisa da mazan suka shiga falon inna bak’in nata sun dan ragu wasu Kuma suna nan Basu tafi ba, inna ta fito falon dauke da murmushi a fuska ” A’a kaga malam ango irin wannan kwalliya haka ”
Murmushi yayi ya zauna Yana kallon ta yace ” inna yanzu nifa ba dan gidan ki bane yanzu na zama in-law”
“Wallahi baka Isa ba har gobe Kai din dan gidan inna ne ba ruwana kaje can ka nemi surukuwa bani ba ” sun gaisa cikin mutunci Fauzan na faman murmusawa burinsa ya cika ya faranta ran uban gidan nasa, ” Ina amaryar taka”
“Tana can tana aikin shagwaba sai kije kiyi rarrashi ta kulle kanta a d’aki taki fitowa ”
“Tasha zamanta idan ta gaji ta fito ”
ya marairaice ” haba inna so kike yunwa ya mata illa, sanyin idaniya ce fah koh kin manta ”
“Kai me aikin ka da baza kayi rarrashin ba sai kazo ka fadamin”
“Inna kulle kofa tayi fah taki budewa ”
“Ni ba wannan ba…yaushe uwargidan zata koma gara kayi magana kar a shiga hakkin y’ar mutane saboda kana ganin Yan uwanta sunyi nisa”
Shiru yayi ya sunkuyar da Kai da Yana da Halin rabuwa da ita na har abada ma da sai yafi kowa murna. Nasiha inna ta masa akan adalci tsakaninsu daga karshe ta kawo masa kunun aya sukayi sallama suka tafi.

Waya inna ta dauka ta kira layin Hajjo tana d’agawa ta fara fada akan meyasa zata kulle kanta a d’aki hakuri ta bayar sai Kuma ta koma rarrashin da nasiha kafin takashe waya, sauran kayan ta da baa Kai ba aka hada inna ta kira Ummeey a waya akan tazo ta Kai mata tare da Nana.
Hajjo ta fito falonta tana bin falon da kallo hamdala tayi da ni’imomin da Allah ya mata , abinci ta zuba cikin plate ta zauna tana ci tana Jin zuciyarta Yana mata Wani irin nauyi lallai namiji kenan wato zaman da zasuyi da Aman kenan, haka zai wulakanta ta saboda Yana tsoron matarsa shiyasa yake Wani shareta haka ta jagwalgwala abincin ta Maida sauran kitchen ta ajiye, a nan ta tsaya ta karewa kitchen din kallo Wani tafkeken kitchen ne Mai girman gaskiya ta Kalli bangaren dama ganin sababbin kaya yasa ta gane lallai sune kayan ta baza ta iya ba dole ya raba musu kitchen saboda tun farko Bai ce mata zai hadasu gida d’aya ba donhaka sai dai ya kashe d’ayan bedroom din part nata ya Maida mata as kitchen Batason duk Wani abu da zai hadata da matarsa Batason hayaniya.
Ajiye plates din tayi ta juya tana Jin Wani sabon bacin rai a zuciyarta ta kama hanyar komawa part nata sai Kuma ta tsaya… toh amma lokacin da sukaje da Ummeey bahaka gidan yake ba wancan gidan duplex ne wannan Kuma blocks of flats ne wato don wulakanci ya kama gidan saboda ya hadasu , Jin shiru agidan ta fara tunanin kodai ita kadai ce kofar part din Failuzaa ta kalla kamar zata shiga sai Kuma ta juya ta koma toh ita me nata a ciki, tazo dai dai shiga falon ta nan tabi kofar part nasa da kallo Wanda yake in between parts din biyu wato nan ne part nasa, Kai tsaye ta Bude kofa wow… Falon ya tsaru iya tsaruwa kamar kana kasar waje komai na falon sea green ne ga Wani tafkeken TV Kai komai na falon abin kallo ne ga manyan frames na sunayen Allah kala kala Babu hoto ko d’aya a falon sai sunayen Allah. Wani qamshi me sanyi ke tashi ga humidifier a kowace kusurwa ga Kuma diffusers ga sanyin AC ga Kuma hasken wutar light blue Yana dim abin dai gwanin sha’awa , zama tayi bisa kujera tana bin falon da kallo ya burgeta matuka lumshe Ido tayi tana shakar qamshin me dad’i, wayarta yayi ringing Ummeey ce ta d’aga “ke amarsu Ina kika shigane munzo tun dazu Baki ciki ”
“da gaske, Gani nan fitowa ” ta Bude kofar part din suka hada Ido da Ummeey wacce take tsaye bakin kofar falonta “iyye manya har an kwantar da Kai ana soyewa ni Ina can Ina tunanin halinda zaki shiga idan kuka Hadu ”
“Mtsww..banson iskanci dama abinda ya kawoki kenan ” suka koma ciki Nana na zaune ta gaisheta hajjo ta amsa tana tambayan mutane gidan, kayan garanta ne Wanda suka rage sai wasu kayan da ta bari suka kawo ta dauka ta Adana ta cire musu kayan kwalliya da turaruka kyauta suna godiya ta musu tayin abinci suka ce a koshe suke ga ma Wani can sun kawo musu dinner, hira suke Ummeey tace” Nana tashi mutafi magariba tayi nasan mijin ta na hanyar dawowa, inna dai tace ki saki ranki ki kwantar da hankalinki shi din ba bakonki bane idan akwai Wani abu ki kirata ”
Har bakin kofar entrance ta rakasu ta koma ciki.

Wanka ta sake Yi dole ta ci kwalliya yadda zata dauke hankalinsa don taji dadin rama wulakancin da ya mata, Wani English gown ta tsaka me tsagu ta gaba har guiwa Kuma armless ne ta saka diamond earrings da Wani single necklace mara ado ta fesa turaruka masu karfi ta zuba kananun kitson da aka mata ga qamshin mayataccen humra dake tashi a jikinta, ta sake kunna turaren wuta a burner gaba d’aya part din ya hargitse da qamshi, dama tayi alwala donhaka ta zauna har aka kira sallah ta dauki wata doguwar hijabi har kasa tayi sallah a natse, tana idarwa ta koma gaban mirror ta saka kwalli da eyeliner sai gum pink lipgloss me shining ta Kalli fuskarta tana murmushi Aman zaka gane kurenka , ta cire hijabi ta koma falonta ta kunna TV dai dai nan aka Bude gate din taji karar tsayuwar mota gyara zama tayi tana kallon star life.
Bangarensa ya fara zuwa yayi wanka ya saka Arabian jallabiya milk color mara nauyi ya fesa jikinsa da turaruka ya taje sajensa Yana kallon fuskarsa a mirror Yana murmushi yau burinsa ya cika ya mallaki hajjo a matsayin matarsa ta Sunna halak malak, a hankali ya Sauke ajiyar zuciya ya furta Alhamdulillah… Yana lumshe Ido daga haka ya juya ya fara tafiya cikin takun kasaita zuwa part nata.

Back to top button