Nasarar Rayuwata 52
*Talented writers forum*
*52*
*Masoyan Aman Ina Mika sakon Jaje dayawa bakuji dadin wannan lamarin ba amma kusani akoda yaushe haka Allah ke tsara lamarinsa Kuma mutum baya auren matar Wani matar mutum kabarinsa*
Jikin Aman yayi tsanani suna dawowa aka wuce dashi Turkish hospital dake Jabi emergency Ayman da Fauzan ne tare dashi sai Dady bayan an basa gado likita ya dubashi an saka masa drip ya samu bacci kafin suka kira Ammi suka sanar da ita, wannan lokacin tana tare da bak’i ga Kuma zee ta shigo Failuzaa ta d’aga musu hankali sai faman rarrashinta ake. Ammi na gama waya ta juya ta Kalli zee tace ” tashi Maza mu wuce asibiti mijinki na kwance rai a hannun Allah na tabbata akan rashin auren wannan shedaniyar yarinyar ce zai janyowa Kansa hawan jini a banza Kai nidai Ina ganin jaraba ni Amina , tashi mu tafi”
Fulani ta tambaya meke faruwa nan ta zayyana musu halinda ake suka tashi harda Fulani akan zasu tafi tare, Ammi tace
“Kinga ki zauna tare da bak’in bari muje mu dawo sai ku tafi dasu Mami daga baya”
Hakan kuwa akayi Ammi da zee sai mom din zee da hajiya Suwaiba da anty maimuna sai anty sofy su suka tafi asibitin, hankalin zee a tashe Gani take tamkar Aman na gab da mutuwa sai kuka take ana Bata hakuri.
Fulani kuwa ta cigaba da rarrashin Failuzaa tana nuna mata kaddara ne amma taki daina kukan, Ayman ta kira tace masa yazo tana son ganinsa don ya zama dole su tattauna akan ya bikin zai kasance tunda haka lamarin ya sauya kida ta sauya dole rawa ya sauya.
Wasa wasa har dare Hajjo Bata samun Aman tun Yana shiga baa picking har ya koma an kashe wayar gaba d’aya, hankalinta ya tashi matuka bayan sallar magariba ta fara tunanin shin ko lafiya kuwa ta rasa waye zata tambaya, ta kasa boye damuwar ta gashi an fasa dinner shin meke Shirin faruwa ne kodai kalubalen da kawu Bakura ya fada mata ne ya fara tunkarar ta daga yanzu, haka dai ta cigaba da tunani dakyar tayi sallah Amma ta kasa cin abinci sai da anty Balqis ta kawo mata Wani farfesun nama da aka dafa da magani ta tisata a gaba dole ta cinye ta Mika mata Wani Nono me magani a ciki ta shanye kafin ta fita tabar d’akin. Cikin wannan dare Fulani da kanta tazo wajen inna tare da anty Dada suka tattauna game da yadda abin yazo musu a bazata inna ta nuna Babu wata matsala Fulani ta Kara Basu hakuri suka nuna mata Babu komai dama haka Allah ya kaddara , sun roki alfarma cewa kar a dakatar da bikin a cigaba zuwa anjima masu daukar amarya zasu karaso saboda Babu dinner , kayan amarya da akayi jere a gidan da Aman ya kama a can za’a barsu amma yanzu gidan Ayman za’a kaita idan yaso gobe sai a sake sabon jere, inna ta nemi alfarma da abari gobe idan aka gama shirya mata daki sai ta tare sun amince daga nan sukayi sallama suka koma.
Karfe 9pm Yaya Yusuf ya kira hajjo a falonsa ta tashi sanye da jalbab har kasa duk inda ta wuce sai qamshi ke tashi ta karasa cikin falon tare da sallama Babanta ne tare da Abba ( ya Yusuf) sai inna da anty Balqis da Goggo Dija ( kanwar Baba) da Goggo Hapsy y’ar uwan Baba, ta nemi waje ta zauna tare da d’aga musu gaisuwa.
Shiru ne ya ziyarci falon daga bisani Baba yayi gyaran murya ya fara mata nasiha me ratsa jiki akan ladabi da biyayya da Kuma bawa ya rungumi kaddara a duk yadda tazo mata, Abba ya karba ya dora nasa Yan uwan Baba kowacce tayi nata nasihar sannan suka shaida mata cewa gobene zata tare , anty Balqis ta rike hannunta suka koma d’akin maman Nana Babu kowa a ciki nan ita Kuma ta dasa nata sabon karatun akan kissa da kisisina da iya zama da miji da Jan hankalin miji Wanda har hajjo ta fara Jin kunya sai Kuma ta dora akan zama da kishiya nan jikin hajjo yayi sanyi ita ta manta cewa tana da kishiya gaba d’aya ta cire budget nata a ciki, sai wajen 10:30 ta koma d’akinta inda ta samu wasu kawayen nata har sunyi bacci, waya ta dauka ta sake trying number Aman off tsaki ta ja ta jefar da wayar ta nemi waje ta kwanta dakyar bacci ya saceta.
Aman Bai Farka ba sai 12 na dare tea yasha ya koma ya kwanta zee take tare dashi ko magana bayason Yi hajjo kadai yake bukata a wannan lokacin amma yasan ta masa nisa na har abada , wata zuciyar tana aibata shi akan abunda ya aikata wata zuciyar kuwa tana nuna masa yayi dai dai haka ya cigaba da tunanin hajjo da irin halinda zata shiga idan ta samu wannan labarin da Kuma yadda zata daukesa, da safe Ayman yazo ya dubasa da sauki sosai Yana zaune kusa dashi ya Kalli Aman yace
“Y…man meyasa ka aikata hakan kasan yarinyar nan irin sonda take Maka yanzu ta Yaya zata karbi wannan zancen ” murmushi yayi ya lumshe Ido
“Hakuri zatayi bro…a hankali zata fara sonka watarana, u deserve her more than I do, Kai ka fara sonta kafin ni Kuma na tabbata Kai zaka fini riketa ” hawaye ya cika idanun Ayman yace ” wannan ba dalili bane man… Kuna kaunar juna da Kai da ita am sure zata tsaneni bazata taba Sona ba meyasa kayi Hakan y…”
Hannunsa Aman ya rike Yana hawaye ” kayi hakuri zan iya sadaukar da komai akan ka bare soyayya ba Wani Abu bane, tun lokacin da Fauzan ya fadamin komai dangane da irin soyayyar da ka dade kake boyewa da irin dawainiyar da kayi a kanta na tabbata Kai Kafi cancanta da aurenta daga wannan lokacin na samu Dady na fada masa komai Kuma nace I’ll surprise you, shiyasa ban fada Maka ba ” kuka suke tamkar kananan yara suka rungumi juna suna hawaye abin tausayi, Fauzan da Kansa sai da yayi hawaye ya fita yabar d’akin zee kuwa tabe baki tayi ita dai koma menene tafi kowa murna ta tabbata aikin malam Suleja ne ya kama mijin nata yanzu Failuzaa ce da alakakai Sun Dade a asibitin kafin suka tafi. Fulani ta kirasa akan zancen inda zai ajiye amarya yace shi bazai raba gidansa ba gida d’aya zasu zauna donhaka a can za’ayi jeren can Asokoro kwame k street . Dama can gidan babba ne me falo 3 da dakuna 5 sai kitchen da dinning area sai bq ta waje me dakuna 2 da falo sai d’akin maigadi.
kayan Dake d’ayan falon aka fitar aka shigar da kayan Hajjo sai 2 bedroom dake cikin falon aka shirya komai nata kayan kitchen kuwa aka fitar dashi zuwa kitchen suna shiryawa suna tausaya mata hadà kitchen da kishiya , har bayan la’asar aka gama shirya part din nata wasu suka zauna wasu ko suka tafi gida zasu rako amarya bayan Isha.
Aman ya nemi ticket da iyalansa a wannan daren da za’a Kai hajjo d’akin mijinta a wannan daren jirginsu zai tashi zuwa kasar England bayan ya rubuta leave ya ajiye Akai zuwa office nasu Yana bukatan jinyar Kansa daga wannan ciwon soyayya da ya afka ciki, hankalin Ammi ya kwanta sai hamdala take da aka fasa wannan auren. da misalin 8pm aka dauko amarya motoci 5 ne gidan Ammi suka fara zuwa bangaren Dad aka kaisu Yana nan ya karbesu da mutunci ya musu adua da fatan alheri sannan aka wuce part din Ammi, tana nan tare da Yan uwanta dasu Fulani anty Balqis ce a gaba suka gaisa Ammi na Wani Shan qamshi anty Balqis ta nuna tamkar batasan tana Yi ba suka gaisa ta gabatar da hajjo gaban Fulani da Yan uwan Dady tana Neman su rike amanarta nan suka karba suna zuba adu’o’i da fatan alheri hajjo dai ko fuskarta Babu Wanda ya gani don ta jawo mayafin ta rufe fuska lub sai qamshi ke tashi daga karshe akayi adua suka tashi zasu tafi wata kuyanga ta kawo musu Wani trolley me kyau ta ajiye agabansu tace kyauta ne daga uwar ango gimbiya Fulani matar sultan, godiya sukayi nan ta Bude lesuna ne masu kyau da tsada guda 10 sai bandir na kudi bandir 5 Yan dubu dubu sai Arabian perfumes masu kyau , guda matan suka sake suna shewa tabe baki Ammi tayi batasan da wannan kayan ba sai yanzu , godiya hajiya luba tayi tana nuna farin ciki akace musu haka al’adar masarautar Sennar take daga nan suka tashi zasu tafi da amarya gidanta , Failuzaa tana can rakube tana kallon komai saboda taki komawa gidan Fulani tace a bari ta huce kafin ta koma.
Motocin sunyi parking a kofar gidan aka wangale gate suka shiga anty Balqis ta fada mata ta karanta hasbunallahi kafa 7 da falaki da Nas da ayatul kursiyu kafin ta shiga haka ta karanta tana Jin faduwar gabanta na dada tsananta har suka shiga ciki ana yabon gidan , can wata y’ar uwar babanta tace ” toh bazamu kaita wajen uwargida bane su gaisa ”
Anty Balqis tace ” uwargida tayi yaji tana can gidan iyayen nasa ”
“Toh…yaji Kuma, inane bangaren ita hajjo ?”
“Gashi can shine na farko ” mamaki hajjo take meya kawosu gidan zee bayan Aman yace mata bazai hada musu gida ba, sai da suka shiga bedroom nata ta zauna kafin ta Bude fuska, Yan uwa da kawaye suka zagaya suka Kalli ko’ina sun dawo kenan anty Balqis tace ” ku tashi karfe 9 tayi ba zama zakuyi kuzo mu tafi mijin nata zai dawo ” adua suka fara suna mata fatan alheri da Kuma sai da safe rike hannun Ummeey tayi tana cewa ” besty ke nan zaki kwana fa sai gobe ”
Fisge hannun tayi tana dariya ” rufamin asiri amarya ”
tanaji tana gani suka watse aka barta gidan yayi shiru bakajin komai sai kukan karnukan makota , bayan tafiyan nasu da kamar minti 30 tana trying number Aman switch off yake nuna mata tabe baki tayi tana tunanin kodai wayar ta Bata gun rububin bikin ne oho, gyara kwanciya tayi bisa katafaren gadon nata alamar Bude gate taji murmushi ne ya subuce mata Wata ajiyar zuciya ta sauke na samun relief at last dai zaizo ya mata bayani meyasa ya kashe waya tun jiya, veil din ta sake dauka ta lullube kanta daga sama ta rufe fuska ta gyara zama bisa gado tana jiran shigowarsa.