Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 23

Sponsored Links

Page….23
Duk sai naji ba daɗi wallahi abinda akewa Mai nasara yayi yawa, tunda na dawo kaduna nake kuka amma a ɓoye ga wasu mahaukatar gyaran da Mamie ta min.

…….
Zaune yake ya buga mugun tagumi, duk ya tara uban kasumba kamar wani mahaukaci yayi shiru miskilancin ya sake ka ruwa fiye da, baya magana ake amma yaki magana kuma akan kasuwancinsune. Amma ko ɗaga kai bayi ya kalli Ahmad dake bayani ba.
Cusa hannunshi yayi cikin sumar kanshi da ya tara, yaki komi fa, banda wanka da sauya kaya Yunus baya komi dan kyamar ɗakinshi yake babu mai gyara mishi, ga gidan ya koma tankar gidan mutuwa dan daga Aneesah da Balkisu kowacce ta shiga hankalinta, sai iyayen fareeda da suketa bibiyarshi ya mai da ita firr yaki sauraransi.

Karshe zaria Ubanta yaje sukayi magana da Alhajinsu yace.
“Kyale shi ta koma ɗakinta laifi yayi muka hukuntashi, shne ya dira akanta kuma ya kamata su kiyayye abinda zai shiga tsakaninsu na rashin fahimta tunda kaga ya iya saketa toh matukar suka cigaba da shige masa zai botsere musu.”

Da haka sukayi sallama koda mahaifinta ya dawo ya tambayeta mi ya haɗa su da Yunus ta shiga kame kame karshe dai ya fahimci bata da gaskiya take ya sunketa yayi mata tasss sannan yace.
“Kamar yanda kika zo da kafarki haka zaki koma babu me maidake.”
Haushi ya cikata gidan kawarta kubra taje ta faɗa mata.
“Hmmm ke kina ganin mi ya sauya shi lokaci ɗaya, mutumin da bayi magana shine har da saki.”

“Hmmm dan nace ya daki jakar Amaryanshi, kuma na gaya mishi magana fa dan har lusari na ce mishi.”

“Tashi ki tafi gidanki bazan iya rakaki ba, sabida baki san darajar aure ba mi kika nima kika rasa, komi na rayuwa Allah ya baki shine kikewa kanki bakin ciki tashi ki koma Allah ya tsare na gaba.”

*****
Yau ta kama sunday, ɗakina ya koma da zama dan shine a tsaftace zama yayi yana shakan kamshin turarena wato Jameela,  ya rasa ta inda turaren yake fitowa, kamar ance ɗaga pillow.

Sai ga Bra da pant ɗina, wanda na cire ana saura kwana biyu tafiyarmu zaria zan sakasu na ajiye nasaka wasu da Huda ta nuna min, dan har na fesa musu turare.

Lumshe idanunshi yayi ya janyo su, tare da ɗaura akan fuskarshi damke yayi yana jin wani irin kewana a jikinshi da jininshi, tuna yanda yake shakar kamshin a jikina, babu abinda ke gigitashi yasaka kanshi a kirjina ga kamshi da ɗumin jikina, ji yayi kanshi zai kunce magana ya shiga yi shi ɗaya yace.
“Miye take dashi da sauran basu dashi? Mi nake ji a jikin tane? Banda kuka da reni mi tasani?”

Take wani gefe na zuciyarshi yace mishi.
*Nutsuwarka da kwanciyar hankalinka duk suna gareta, tana da abubuwa da kai baka san dasu ba, hakuri, juriya, duk ta haɗa ga kyakyawan mu’amala, itace zaka taɓata bata ce maka wani abu ba ka tashi ga barcin da kake, ka dubi kanka ka dubi ɗakinka mana, kaima gudun hijira kayi sabida kaxamtar matanka tunda gashi babu wacce tayi tunanin gyara maka da itace kuwa kai kanka har saurin ka dawo gidanka kake..*

Mikewa yayi ya dafe goshinsa sauka yayi a gadon,  ban ɗakin ya shiga ya ɗauki shaving cream ya shafa a kasumbarshi ya shiga haskewa, yana gamawa yayi wanka ya fito..

Bai zamd ko ina ba sai ɗakinshi ya,zaro shadda sabuwa gal fara sol,yasaka sannan ya ɗauki bakin takalmi ya zura sama sama ya gyara fuskarshi ya fita daga ɗakin, yana fitowa falo ya cikaro da Fareeda, kara tsuke fuska yayi cikin masifa yace.
“Uban waye ya baki izinin dawowa?”

Sunkuyar da kanta tayi tana kokarin ɓoye ɓacin ranta tace.
“Alhajin Zaria.”

Raɓa gefenta yayi ya fice, gidan Aman Yaje ya kirashi a waya lokacin yana fama da Hindu tayi wanka sai rena mishi hankali take, kuma baya son zuwa ga Rahilah dan karsu shiga hakkin Hindu.

A mota yasami Mai nasara, gyara zama yayi yace.
“Allah ya taimaki wakilin marafa, Mi kake bukata.”

Banza dashi yayi kamar bazai magana ba ya juyar da kanshi, har na wani lokaci.

Harzuka Aman yayi cikin jin haushi yace.
“D’an iska lokacin da ka daketa kasan zaka shiga ukune ai na faɗa maka jinjira bata da sauki ni zan fita dan yau hutu ake tunda baka da abin fada.”

Buɗe murfin kofar yayi, maza mai nasara ya rike shi.
“Mi yasa ku baxaku fahimci halin da nake ciki ba? Mi yasa kuke jin zafina? Koma mi nayi ban kamaci wulakantawarku ba, duk matsalarmu iri ɗaya ce, amma mi yasa kuke ganin laifina.”

Juyawa Aman yayi cikin tausayawa yace.
“Eh laifinka muke gani, sabida ka gaza hakuri da yar sha bakwas, amma kana zaune da yan talatin da wani, Yunus bazan ɓoye maka ba kai ka lalata rayuwarka da na gidanka, kuma daga auren Maryam wasu halayarka naga ka ragesu, musaman rashin sake fuska, haka kawai zaka zauna kayita murmushi kai ɗaya, kana son Maryama amma kake bawa kanka wahala.”

“Kaii Wallahi ko sau ɗaya bana sonta, dai ina jin ba daɗine akan rashinta, ka yarda dani.”

Wani irin kallo Aman yayi mishi, me ɗauke da renin sense, ga soyayya kuru kuru har da rantsewarshi taɓe baki yayi ya buɗe motar zai fita.

Mai nasara yace.
“Aman kaima juya min baya zakayi?”
Murmushin gefen baki Aman yayi sannan yace.”Kowani cuta da maganinshi sai dai mituwa ce babu maganinta Yunus You are in love amma kake musanta min magana well zan baka shawara kaje zaria ka samo kanta idan haka ta faru zan baka final shawara.”

Yana gama faɗa haka ya juya yafita,

Jan motarshi yayi sai zaria,nan ya tarda kwandon bala’i har sai da ya kusan zubda kwalla.
“Wato dan ka maida mu marasa mutunci shine muka nemi sakin kaki bada ko Yunus ka bani sakin Yar mutane ko na saɓa maka, wai shin mi kaida Mutane ne abokan wasanka har kana sake ɗayar matarka muda muka ce ka bamu sakin maryam sai ka saki Fareeda toh bani takardan Yar mutane mara mutunci saɓo tumaki ɓallo jaki bani, kaje mugun halinka ya taimakeka.”..

Shi kanshi abin duniya ya dame shi, muka ya kasa magana mikewa yayi ya bar falon Alhaji, zuwa falon Hajiyarsu nan yayita raba ido bai gani ba,

Karewa mikewa yayi zuwa ɗakin hajiya ya sami ɗakin Wayam, babu ni babu alamata.

Gurin Mama ya dawo tace.
“Kazo dubawa kotana nan  ne? Toh mun ɗagata daga gidan nan kafin ka shiga rayuwarta.”

“Amma…”
“Dakata fitan min a ɗaki kaje can…”

Fata fata suka mishi dawows kaduna yayi ya kira Aman ya faɗa mishi, halin da Yake ciki.
Dariya Aman yayi yace.
“Ka wucce gidansu kasami Iyayenta da maganar, zaka sha mamaki yau duk inda Maryama take a chest ɗinka zata kwana.”.
Kashe kiran yayi ya nufi, tudun wada, a kofar gida yayi parkin ya tura yaro akan mijin Maryam ya zo.

Ya kabiru ne yazo ya shiga dashi cikin gidan, aka shimfiɗa mishi taburma ya zauna, gaisawa sukayi da Umma da Mama.

Cikin nutsuwa ya faɗa musu  halinda yake ciki, tare da nuna musu shine da laifi amma iyayenshi sunce ya sake maryam don Allah ayi hakuri bazai kuma ba.

D’aga labule umma tayi taga karfe biyu da rabi, kallonshi tayi kafin tace.
“Zuwa karfe shida na yamma Kabir zai kiraka.”
Godiya yayi sosai sannan ya tashi zai tafi ya ciro kuɗi zai ajiye tace.
“Yunus ɗauki abinka, mu y’a muka baka ba abin hannunka muka duba ba.”

Duk yanda yaso ta amsa amma fir suka ki karɓa koda suka fita da Ya kabir sun taɓa hira har zuwa matakin karatu, mika mishi card ɗinshi yace.
“Kazo da takardunka, dama muna niman wanda zai zauna mana a kamfaninmu na Abuja kuma mun samu.”

Godiya kabir yake kaman yayi ihu dan murna, haka sukayi sallama,

……. A cikin gida kuwa ɗaukar waya Umma tayi takira Mamie suka gaisa, cikin tsautsayi Mamie tace.
“Maryam Sajida, duba min miyar nan nakan gas,”
“Toh Mamie”

Aikuwa kashe kiran Umma tayi tasaka hijab dinta sai gidan Mamie, muna tsaka da hira mamie na faɗa min.Umma takira fa, take naji yan hanjina sun kaɗa.
Muna cikin maganar ta shigo da sallama bayan Mamie na b’oya.

Tunda tayi sallama suka gaisa Mamie ta kama hannunta suka shige ɗaki,har kusan la’asar basu fito ba.

Koda suka gama kai ruwa rana, suka fito wani mugun kallo tayi min sannan tace.
“Rahilah da Rahimah kowacce tana makale a ɗakinta dan.rufin asiri shine dan kuskure irinta ɗan Adam kika, fito zaki kashe aurenki Hmmm Maryama ki zauna ai daɗin abin bake ɗaya na haifa ba.”

Tana gama faɗar haka ta juya kan Mamie tace.
“Yanzun Yunus zaizo ɗaukarta.”

“Wayyo Allah Umma kashe ni zaiyi.”
“Allah ya jikan wanda ya rigamu gidan gaskiya, karewar kasheki ya jefa ki cikin rami.”

Kuka nasaka da ihu har da birgima haushi ya kamata ta samu tayo kaina ta shiga niman dukana mamie ta shiga tsakaninmu tace.
“Wai don Allah ke baki da zuciyane dukarta yayi fa har akan nono kuma ana hukuntashi kice zaki maida mishi da ita.”

 

Back to top button