Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 51

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*51*

*Masoyan Ayman congratulations Ina tayaku murna at long last burinku ya cika, team Aman sorry kuyi hakuri a rungumi kaddara.. nagode da soyayya ana tare ai*

Hawaye Wani na bin Wani bisa fuskokinsu anrasa me rarrashin Wani tsakanin Aman da Ayman, Fauzan ne yazo ya rike hannayensu saboda idon jama’a ya fara dawowa kansu, masaukin nasu suka koma dama jirginsu sai nan da 1 hour ne. Waya Fauzan ya cire ya kira Fulani ya sanar da ita wannan babban al’amari adua tayi da fatan Hakan shine alkairi nan da nan Fauzan ya kira Yan uwan Ayman ya sanar dasu bayan ya fadawa Fulani ta sanar da Sultan, inna ce ta fado masa a rai nan ya karbi wayar Ayman ya nemi layinta ya kirata ya sanar da ita hamdala take har Fauzan yayi mamaki ya kashe wayar. Aman kuwa kamar da wasa jikinsa ya fara daukan zafi nan take zazzabi ya rufeshi har Yana Neman bargo dama cikin hotel room suka Ayman kuwa Yana zaune ya rasa Gane wane duniya yake shin mafarki ne ko gaskiya ne.

*Abuja*

Ammi tana falo tare da wasu daga cikin kawayenta da suka zo bikin duk da cewa batayi gayyata ba Amma anzo mata Kara ciki kuwa harda mom din zee suna tare Fulani ta shigo da sallama tana rike da waya kuyanga na biye da ita ” Ammi Kinga hukuncin ubangiji koh, wato shi lamarin aure baa Yanke masa hukunci Kinga lamarin ya juya an daura auren da Ayman ”
“Ayman! Meya faru? Nan kowa ya Maida hankali kan zancen, ” yanzu Fauzan ya kira yake sanar dani yace sai sun dawo zaimin bayani ” wata daga cikinsu ta sake guda tana cewa “Alhamdulillah Kai Allah abin godiya dama Muna ta rokon Allah ya tarwatsa wannan auren ”
Ammi ta tabe baki tace ” toh me abin farin ciki Ayman da Aman duk Abu guda ne , ni yanzu nafi Jin haushi saboda Ayman ya Tara uban dukiya Kuma ni na tsani yarinyar nan bana son tazo taci arzikin ahlina ”
Kallon mamaki Fulani ke mata ta kasa magana haka ta juya ta koma bedroom cike da haushin kalaman nata ita ta rasa meke damun Ammin gaba d’aya ta canza ko saboda wannan kawayen banzan da take tare dasu ne oho, mom din zee tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha dama can boye damuwar ta take shiyasa Bata nunawa Amma lamarin auren ya d’aga mata hankali kawai nuna Halin girma take , tashi tayi kamar tana waya ta fita harabar gidan layin y’ar tata ta fara nema.

Anty zee na tare da kawaye da Kuma Yan uwanta Failuzaa anci gayu ana zaune ana iyayi suna Bata Baki fuskarta duk ya kumbura don taci kuka har ta gode Allah, wayarta na ringing ganin mom ne yasa tayi picking tana Kara rushewa da kuka ” share hawayenki y’ata kuka Kuma ya kare Allah ya kiyaye gaba Allah ya dubemu ya rabamu da jangwam ”

“Mom meke faruwa?”
“Reshe ya juye da mujiya an daura auren da Ayman ba mijin ki kome ya faru sai Allah ”
“Ayman? Wane Ayman kenan mom?”
“Wannan Dan uwan nasu dan sarki kedai na Miki murna y’ata Allah ya tsare ki da sharrin Makiya , Maza ki tashi kiyi wanka kizo tare da Yan uwan naki kuzo muyi kallo don kallo ne ya koma sama wai…”
Wani shewa ta sake har ya jawo hankalin Wanda suke falon ta zube a kasa tana d’aga hannaye sama “Alhamdulillah Alhamdulillah Allah abin godiya dama Allah ba azzalumin bawansa bane Kai Allah nagode nagode Maka ubangiji nah ”
Kallonta Ake tamkar zautacciya ta tashi tsaye tana rawa tace ” kai jama’a toh munafukai a tashi a Kara gaba aurene an fasa , Failuzaa Allah Bada hakuri da juriya annobar ta kanki ta koma sai adua ”
A firgice Failuzaa ke kallonta” bangane ba anty zee ki fahimtar dani wace annoba ”
“Kishiya mana ai kishiya annoba ce duk tabi ta d’aga min hankali cikin wata guda, toh yau Allah ya amshi rokona an daura auren da mijinki sai ki tashi ki koma gida kiyi waya Sudan a taho Miki da jiko ”
Wani wawan zabura Failuzaa tayi ta karasa kusa da ita ta rike hannunta tana jijjigata
“Don girman Allah idan wasa kike min ki daina bana so ”
“Na rantse Miki ba wasa nake ba an daura auren yarinyar tare da mijinki Allah ya shige Miki gaba ” zubewa tayi a wajen tana salati ita Bata Suma ba Amma Bata cikin hankalinta nan aka d’aga ta ana Bata hakuri Bata fahimtar komai dankwali a hannu ta tashi tana Neman handbag da waya suna d’aki tana ta waige waige zee ta riketa
“Ki nutsu ki dawo hankali nki gimbiya”
“Don Allah ki bani bag da wayata gida zan tafi yau dole dadyn meenal ya min bayani me na taba masa a rayuwa da zaimin irin wannan cin amana da cin zarafi , wayyo Allah ni marainiya an kawoni wata uwa duniya ana wulakantani ” kuka take ta dora hannu bisa Kai wasu na tausaya mata suka fara zagin Ayman wasu ko suna ganin wautarta da har ta kasa Gane cewa mijinta aure zaiyi, bag nata zee ta hado da waya da komai nata ta samu driver tace a sauketa gidan Ammi gasu nan zuwa, ita da Yan uwanta sai guda suke nan aka sake kida ana cashewa ta fada wanka yanzu ne zatayi kwalliyan kece reni dole taje daukar amarya don ta fadawa yarinyar maganganun dake cinta a zuci.

Sujjada inna tayi na godiya tana Jin Wani farin ciki na sake lullubanta dama ta Dade tana sha’awar hadasu Amma ganin Ayman Bai furta ba shiyasa tayi shiru Amma tasan hajjo ta more miji Ayman yafi kowa sanin zafinta shine nasarar rayuwarta dole shiyafi cancanta da ya aureta shi zaifi kowa Bata kulawa, nan ta fadawa anty Balqis halinda Ake ciki murna tayi don itama tasan wacece Ammi nan suka Yanke hukuncin cewa kar a sanar da hajjo saboda kar hankalinta ya tashi, sukayi shiru abinsu aka cigaba da taro cikin kwanciyar hankali inna sai walwala take ta kira Ummeey gefe ta sanar da ita Ummeey ta tausayawa aminiyar tata amma taja bakinta tayi shiru bisa umarnin inna , dama za’ayi dinner da dare amma inna ta sanar cewa anfasa dinner saboda wasu Yan dalilai don yanzu ita kanta batasan halinda Ake ciki ba sai zuwa lokacin da Yan daurin aure zasu dawo Kuma tasan dinner bazai yiwu ba saboda halinda hajjo zata shiga idan labarin ya isketa.
Aman ya mata alkawarin cewa shine mutum na farko da zai mata albishir cewa an daura aurensu ta duba time har to 4 Bai kira ba ta gaji ta fara Neman layinsa yayi ringing Bai d’aga ba murmushi tayi tasan Yana can tare da bak’i, Samira ce ta shigo ta zauna kusa da ita ” amarsu ta ango shi Kuma angon naki salon wulakancin da zai mana kenan, sai da muka gama cin buri zaice ya fasa yin dinner ”
Cike da mamaki hajjo ta kalleta tace ” waya fada Miki anfasa ?”
“Au..ke Baki da labari kenan, toh yanzu inna ta fada mana cewa anfasa ”
“Hmmm..kinsan inna yanzu haka maybe ita ta hanasa kinsanta sarai zatace bidi’a, ” Ummeey dai taji jugum tana Jin tausayin hajjo idan tasan meya faru, Salma ce ta Kalli Ummeey tace “lafiya kika buga uban tagumi haka ,ko saboda dinner din ne ” murmushi ta kirkiro ” uhmm ni ba wannan ba Ina tunanin ya zanyi rayuwa Babu besty kusa dani ba ne ”
Hararinta hajjo tayi ” toh mutuwa zanyi ne da zamu rabu ko school din barinsa zanyi ”
“Ahtoh na sani ko ku tafi wata uwa duniya honey moon a manta da karatu”
“Chabdi..Ina final year din , dako nayiwa kaina wallahi ”
“Muka sani idan soyayya ya kwaso ki ”
“Mtsww..banson iskanci karku dameni bari na kira ango nah ” shewa suke Banda Ummeey da idanunta ya cika da kwalla tana sharewa a boye, hajjo ta sake trying number switch off taji zuciyarta Babu dadi ta nemi waje ta kwanta bisa gado tana tunanin wane sungulla ne ya hanasa kiranta Koda yake Yana tare da abokansa he might be very busy.

Back to top button