Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 36

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*36*

*Quraish street Jeddah Saudi Arabia*

Yana zaune a balcony bisa wasu kujerun hutawa Yana rike da glass cup da lemon juice a ciki idanunsa na bisa screen din waya yayi wata y’ar kiba sai sheki yake duk macen da ta kallesa dole zata sake kallonsa yayi kyau fiye da zaton Mai tunani, kasar ta karbesa sosai shiyasa da ya kammala karatunsa yaki komawa gida yanzu shekara 2 da watanni rabonsa da gida , shekarun aurensa kenan video call suka gama da Aman Wanda yake nuna masa Fahad har Yana tsokanarsa da cewa shi ragone tunda ya kasa samun d’a sai dai murmushi baice masa komai ba amma cikin zuciyarsa ya ayyana cewa shi ba ragon namiji bane. Yarima Ayman kenan Wanda yanzu kudi sun zauna saboda kasuwancin nasa yayi albarka don ya sake Bude Wani company a nan Jeddah ya gama masters nasa Bai koma gida ba ya cigaba da kasuwancinsa, Yana son zuwa Nigeria ganin muradin zuciyarsa amma da ya samu labarin ta fara zuwa makaranta sai ya dakata Yana ganin ba yanzu bane lokacin da ya dace ya bayyana sirrin zuciyarsa duk da cewa bashi da tabbas ko zata karbesa ko tayi Nisa cikin son Wani, bugun a ya dada tsananta Yana Jin Wani irin bacin rai ya rasa yaya zaiyi nan take yaji Yana bukatar zuwa Nigeria don sanin halinda take ciki, Fauzan ya fara nema a waya yace ya samo musu flight tickets Amma Banda Failuzaa don ba dadewa zasuyi ba. Ya kashe wayar ya ajiye Yana Maida numfashi gaba d’aya kishinta yake Yana ta imaginations kala kala a kanta, Failuzaa ce ta fito rike da fruits salad cikin bowl tazo ta zauna kusa dashi ” my prince kasan me ? ” Lumshe Ido yayi Yana jiran me zata fada yanzu ta Saba da halayensa donhaka ta cigaba da magana ” I have that feeling that am pregnant” ware Ido yayi Amma still Baiyi magana ba tace ” yes..cos I missed my period so.. ” ki shirya gobe kije hospital ” Bai bari ta karasa ba Yana gama magana ta dauki cup nasa ya koma cikin gida, a sitting room ya yada zango Yana Jin Wani farin ciki he wish that zai nuna mata how happy he is da wannan labarin Amma sai ya tabbatar zai Bata gift na musamman. Failuzaa ko haushi ne ya isheta haka ta ajiye fruit salad din taji ya fita daga ranta ta dauka zataga farin ciki a fuskarsa idan ya samu wannan kyakkyawar albishir Amma Sam bahaka ba gaskiya ta kasa Gane Ayman wane irin mutum ne shi, yau aure shekara 2 da watanni Amma Babu shakuwa ta soyayya sai dai sauke hakki gaskiya dole ta nemi mafita yanzu ta gaji da halayen nasa. bayan Isha ya shaida mata zasuyi tafiya Amma bazasu Dade ba dashi da Fauzan nan ta tada daru akan lallai sai dai su tafi tare da waye zata zauna yace ” ga Mai aiki ga driver me Kuma kike bukata me kika Rasa ” gaskiya ni bazan iya zama ni kadai ba wallahi sai dai mutafi tare ko ka fasa tafiyan, salon kaje wata ta nanike min Kai gaskiya aa ” murmushi yayi yace” ohh..is that your only problem ” hararinsa tayi tace ” da me tunaninka ” u know I don’t have time for all these right” ” I know but lokacin da zasu kanainaye ka u won’t understand” smiling at her ya rike hannayenta suka zauna bakin gado yace ” look ..ki kwantar da hankalinki Ina son gobe driver yakai ki hospital kiyi test ok, I’ll be waiting for the results ” cike da murna tace ” da gaske, are you happy about us having a baby ” gyada Kai ya mata yace ” why not… c’mon it’s our baby after all ” nan ta kankameshi tana dariya ya lumshe Ido tana son jawo masa wata fitina , aikuwa Bai tsira ba sai da ta fance wannan daren kafin suka kimtsa ya shirya kayan da zai dauka tana makale dashi duk inda yake .

___________
*Abuja Nigeria*

Hajjo an shiga second semester 100 level ta Kara wayewa sun Hadu da new friends amma Basu yawan shiga cikinsu ita dai daga ita sai besty dinta Ummeey kullum suna tare lectures kadai ke rabasu, Abba ya siyawa inna mota Lexus Rx dashi Ake kawo hajjo makaranta a Kuma dawo daukanta kullum. Hajjo ta zama wata classy lady komai nata daban yake ko dressing nata is different har anfara noticing nata a school din nan kuwa samari sukace salamu alaikum kullum sai an tare ta da Kalmar so Amma Bata Basu chance, ga dai sultan da Mahfouz ta kasa Gane wane irin relationship take dasu duk sun shaku Kuma kowa da matsayin da ta ajiyesa. ta koma gida a gajiye sanye take da jump suit brown ta dora milk kimono cardigan dogo har kasa a sama mara nauyi da wasu aoura silky slippers Brown sai clutch bag multicolor, tana rike da handout guda d’aya sai phone nata ta shigo falon da sallama Yana waya shi kadai sai Sadeeq dake zaune a lap nasa, TV na kunne cartoon ne hankalin Sadeeq na wajen yaron yayi wayo watansa shida Amma girman jikinsa zaka dauka dan shekara d’aya ne. Cike da mamaki take kallonsa har ta manta when last ta gansa at least dai 4 years ko 5 haka gaba d’aya ya canza ga Wasu beard da ya tara ya Kara haska fuskarsa, dauke Kai tayi zata wuce d’aki kamar daga sama taji cool voice nasa Yana cewa ” Baki iya gaisuwa ba koh ” cike da yanga ta juya ta rausayar da Kai tana masa Wani irin kallo me narkar da zuciya tace ” u were on call Daz y, Ina yini ” “dawo nan ki zauna ” Babu gardama ta koma falon ta zauna opposite direction nasa nan Sadeeq ya fara mata dariya tana masa wasa ” oyoyo my fine fine sweetie come…” ta Mika hannu yaron Yana ta tsalle kamar zai Fadi nan tasa hannu zata daukesa hannayensu suka sarke da juna ta d’aga Ido tana kallonsa suka hada Ido ta sauke Kai ta karbi yaron yayinda bugun zuciyoyinsu ya karu. Zaman falon ya gagareta Kai tsaye ta wuce bedroom da Sadeeq tana shiga ta diresa bisa gado ta kwanta gefe tana sauke numfashi, Ayman ya jingina jikin kujera ya kulle idanunsa Yana Jin Wani shaukin sonta na fusgarsa he wish to spend the rest of his life with this fellow he darm love her Yana Jin Wani bakon yanayi na ziyartar zuciyarsa kamar ya tashi ya biyota d’akin. Inna ce ta fito tana ce masa ” kayi hakuri na barka Kai d’aya” murmushin karfin Hali yayi Yana Bude ido ” lafiya naganka Wani iri ?” “No Babu komai inna I think zan wuce gidan Aman mugaisa ” ” ok toh yaushe zaka dawo ” ” uhmm maybe gobe ” Allah ya kaimu ” ya tashi tsaye ya tura hannu cikin aljihu sannan yace ” inna yarinyar nan kamata tana saka hijab idan zataje school ” au ta dawo ne ”
“tana d’aki tare da Sadeeq ” ok insha Allah zan mata magana Amma gaba d’aya yanzu Bata son hijab idan kayi magana a dinga kaucewa ” sallama sukayi ya fita Fauzan na Saman mota yazo ya tayar suka dau hanyar gidan Aman. Inna ta tura kofar tare da sallama ta samesu kwance tanawa Sadeeq wasa , zama tayi kusa dasu fuskarta dauke da murmushi “Yan mata nah an dawo ” uhmm Ina yini innarmu ” lafiya Alhamdulillah ya karatun, Kinga yayan naki Kun gaisa kuwa ”
“Ehh mun gaisa Amma inna kinsan ya canza dakyar na Ganesa,kinsan ya dade baizo bah ” ehh kinsan yayi aure Yana can saudiya tare da matarsa ” tabe Baki tayi tace” ohh ashe yayi aure ” yace na fada Miki ki daina fita Babu hijabi ”
“Toh shi Ina ruwansa dani inna naga dai ni ba matarsa ba ce ” gidanku, shi yayanki ne Yana da iko a kanki ” tura Baki tayi Bata sake magana inna ta tashi ta fice. Zancen auren nasa ya tsaya mata a rai kome yasa oho haka nan taji Wani abu Kuma ta kasa gane menene shi, ta dauki Sadeeq suka wuce d’akin maman Nana ta ajiyesa sannan ta dawo ta watsa ruwa ta haye gado tana Jin zuciyarta Babu dadi har yunwar da take ji ya kaurace mata.
Ayman kuwa yana cikin mota sai lumshe Ido yake Yana tuna kyakkyawar fuskar tata lallai ta Kara girma tayi kyau sosai Komai nata gwanin sha’awa amma wannan dressing din nata zai jawo attention na Maza wajenta dole ya dauki mataki kafin yabar kasar yasan inna bazata hanasa abunda yayi niyya ba donhaka gobe dole ya koma ya taka mata birki, anya ma zai iya jira ta kammala karatun nata kuwa? Idan Wani ya rigasa Kuma yaya zaiyi? Sauke numfashi yayi take yaji Kansa na ciwo baya son matsala nan da nan Kansa zai fara ciwo haka ya koma ya kwanta jikin sit ya cigaba da tunani da lissafin abunda ya dace yayi.

Back to top button