Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 43

Sponsored Links

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 43…… Mami ta karaso kusa da su fuskarta daure tana kallon Ikram tace “me kike yi a nn” Ikram ta bata fuska kmr xata yi kuka tana nuna mata Khaleel tace “ko ba shi bane ya xuba min ruwan tea a uniform dina shine sae ya kawo ni dakinsa wae don kar ki ganni kuma yaje ya dauko min wani uniform, shine kuma naga yana kallona da nake sa uniform din……” tsawa Mami ta daka mata tace “fita kar in buge maki baki na aike ki gun Khaleel, ko nace ki je kusa da shi?” ta juya tana kallon Khaleel da ya kasa daina kallon Ikram, ranta a bace tace “a kan wani dalili ka xuba mata ruwan tea a jiki Khaleel?” ya marairaice mata yace “wllh Mami bani na xubar mata tea a jiki ba karya take min” Mami ta masa mugun kallo ta kwashi uniform din da ya cire mata ta watsa masa su tace “to ka tabbatar ka wanke su ka shanya kafin ka bar gidan nn don bbu bawan ku” tana kai wa nn ta fixgo Ikram dake tsaye tana kakalo hawaye tayi waje da ita, wani tean ta kuma hada mata ta koma sama ta dauko jakarta da takalmanta, khaleel ya dde tsaye bayan fitarsu daga karshe ya cire suit din jikinsa yyi unbotton din hannun rigarsa ya cire tie din wuyarsa ya duka ya dauki uniform din ya shiga bathroom dinsa ya shi ga wankewa don ba wuta bare ya saka cikin machine, yana gama wankewa ya fito xae je shanya shi a garden ya tarda su a falo Mami na gyara mata takalminta, kallo daya Mami tayi masa ta dauke kanta tace “kuma ka tabbatar ka gyara dinnin din can kafin ka bar min gida, don bbu me gyara maka” Ikram tace “Mami shi ma xae yi latti fa, kice mama jummai ta taya sa gyarawa” Mami ta galla mata harara tace “rufe min baki” ta turo bakin kmr xata yi kuka tayi shiru, jummai dake kitchen tana jin su tace “Mami ya bar shi kawae xan gyara ae aikina ne” Mami tace “ae kuwa sae ya gyara kafin ya bar gidan nn, wani ya xubar masu, aikin dake gabanki ma ya isheki” sch bus ne ya shiga horn bakin gate, Mami ta dauki car key dinta da mayafi ta kama hannun Ikram ta sallami jummai suka yi kofar fita, Ikram ta juya tana kallon Khaleel dake tsaye stairs yana kallonsu ta daga masa hannu snn suka fita daga falon, jummai tayi dariya tace “je ka ka gama shirinka kayi tafiyar ka babana xan gyara” murmushi kawae yyi ya haura sama. Ikram kmr xata yi kuka tace “Mami to yaushe xaki dawo ni bana son wnn gidan nasu mutane sun yi yawa ciki, sae suyi ta kallona, ni ki bar ni wajen yaya Khaleel in dinga kwana da shi, yaya Khaleel kace Mami ta bar ni wajen ka” Khaleel ya galla mata harara ta madubin mota yace “wa xa a bar ma ke” Mami tace “nace gobe idan jummai ta dawo xata xo ta dauke ki ki tsaya wajenta kafin in dawo” Ikram bata kuma cewa komai ba sae xumbure xumburen da take har suka isa gidan, bayan sun fito Mami tace ma Khaleel “xan kiraka idan na tashi komawa gida” yace “to Mami” ya juya yana kallon Ikram ya daga mata hannu yana mata gwalo, ta murguda masa baki Mami ta ja ta suka shiga cikin gidan, basu tar da kowa cikin falon ba Mami ta haura sama da ita tayi sallama dakin Momy suka shiga, tana xaune kan darduma rike da caxbi alamar ta idar da sllh knn, ta mike tace “A’a sannunku da xuwa daga ina hka” Mami tace “wllh daga gida muke” ta xauna suka gaisa snn tace “sauri nake wllh Hajiya, yau da daddare xan kama hanyar germany, may b in yi sati daya, shine na kawo maki dota na ta dinga tafiya sch da islamiyya daga nn kafin in dawo, jummai me mana aiki jiya ta tafi kauye gun yar ta ta haihu, kila ita ma tayi sati daya” Momy tace “to shknn Hajiya ae wnn ba matsala bane, kayayyakin ta fa” Mami tace “khaleel xae kawo mata gobe, ynxu kayan makarantar ta kawae na xo da” Mami bata wani dde ba ta sallami Momy bayan ta kira Khaleel yace mata yana kofar gida, kuka Ikram ta shiga yi wae ita baxata xauna ba, momy tace “haba Ikram baki san ni bane” dafa ta Mami tayi tace “gobe xan xo in dauke ki dotana amma fa sae naga kin daina kukan nn” shiru Ikram tayi tana kallonta, Momy ta dauko chocolate dayawa ta mika mata ta karba tana kallonsu, Mami tayi dariya tace “kmr ko kinsan dotan nawa akwae son chocolate” Momy tayi dariya tace “ae naga yanda tayi ta murna wancan ranar da Aliyu ya bata” Mami ta dan yi still kmr warce ta tuna abu, sae kuma ta juya tana kallon Momy tace “don Allah kar ki bari Aliyu yana shisshige mata bana so” Momy tayi dariya tace “sbda me Hajiya” Mami tace “hka nn kawae bana so” ta daga ma Ikram hannu snn ta yi sallama da Mami ta fita daga dakin.
[2/25, 08:35] Zjy:

Check Also
Close
Back to top button