Nasarar Rayuwata 37
*Talented writers forum*
*37*
Da safe around 11am tana breakfast a sitting room da plate din indomie da tea gidan shiru Bata da lectures sai 2 , inna da maman Nana sun tafi kasuwa duba shagonta Abba kuwa yayi tafiya zuwa Maiduguri donhaka gidan shiru, tana sanye da fararen pyjamas nata Riga da wando masu tsantsi sai qamshin arabian touch oud pitch ke tashi a jikinta da body mist ,kitson calabar kananu ne a kanta anyi kwalliya da iron beads in between sun zube a gadon baya da kafada, tana sanye da abin kwalliyar hanci silver color sai daukar Ido yake ga Wasu single rings guda 4 a jere tayi Wani cool kyau duk da cewa batayi wanka ba Amma she look extremely beautiful she looks like a celebrity, door bell yayi ringing ta dauka ko su inna ne donhaka Bata dauki hula ba haka ta sauka kasa ta Bude kofa, idanunsa suka fada cikin nata ta tsaya tana kallonsa Babu ko keftawa . Lumshe idanu yayi yace ” Baki taba ganina bane wannan kallo haka” ta juya baya tabar kofa a Bude yabi gefenta ya wuce ta Maida kofar ta rufe har ya fara Hawa staircase tace ” inna fa Bata nan ” ya dan juya ya kalleta tare da d’aga gira yace ” and so? do you want me to leave” tabe baki tayi tayi ya cigaba da tafiya har ya haura zuwa second floor nan ya yada zango . ta shigo tamkar mara gaskiya ta koma kusa da plate din indomie da take ci tasa hannu zata dauka ya rigata daukan fork din , ta d’aga Kai suna kallon juna yace ” am hungry banyi breakfast ba ” ta turo Baki tace ” ka bari na dafa Maka Wani toh ” ” ba ke kika dafa wannan bah ” turo Baki tayi batace komai ba, ya jawo plate din ya fara ci a hankali half done yaji onion leaves da peppe ga qamshi yaji dadin indomien Yana ci Yana lumshe Ido ta tashi cike da haushi ta wuce kitchen ta dora Wani , tana wajen ta gama dafawa ta juye a plate ta koma falon har ya gama ci Yana Shan tea nata da ta bari. Batayi magana ba ta zauna tana kallon screen din waya tana son Kiran Ummeey, ganinsa tayi kusa da ita ya saka fork Yana diban indomie. ware Ido tayi ” wai lafiya malam” murmushi yayi yace ” u know how to cook I enjoy d meal thanks” batayi magana ba ta saka nata cokalin suna ci tare cikin plate d’aya har suka gama ta tattara ta Maidasu kitchen ta dawo falon tana waya da Ummeey sai dariya take, Yana kallonta da gefen Ido tayi mugun masa kyau ga qamshin turarukanta na fusgarsa gaskiya ta waye sosai ta canza he wish to have her soon , tana gama wayar ta tashi tace ” Yaya ni zan shiga ciki ko akwai abunda kake bukata” ” umm ki zauna magana zamuyi” Babu gardama ta koma ta zauna, ya juya suna fuskantar juna ” meyasa kike yawo Babu hijab bayan da bahaka kike bah ” tayi dan jimm tace ” sometimes Ina sakawa ai ” toh Ina son daga yau ki koma saka hijab kullum please ” saboda me ?” ta tambaya Kai tsaye , ” Nima I don’t know but kawai Ina son kina sakawa please”
“Ok nagode” daga nan ta tashi yace ” Baki da lectures ne?” Sai around 1:30 zan tafi ” ” ok kije ki shirya kizo akwai inda zamuje ” ka kira inna ka fada mata, Kuma ni ..ni Ina zamuje ” just do wat I say ” Bata Kara kallonsa tasa Kai ta wuce bedroom nata, Sauke numfashi tayi batasan meyasa ba duk lokacin da suke tare takan rude ta rasa natsuwarta. Wanka ta shiga bayan ta fito ta saka wata doguwar Riga Latvia me kyau maroon color yayi fitting din fair skin nata tayi rolling da scarf din rigar ta dauki Wani golden side bag da takalminsa palms masu kyau da sari , wayarta ta cire ta fara Neman layin inna ringing biyu ta d’aga nan take shaida masa zasu fita da Ayman inna tace ” dazu ya kirani ya fadamin, ki kula da kanki Allah ya tsare” Ameen ” ta amsa a sanyaye toh Ina zasuje ne haka , tana ta sake sake cikin zuci ta duba time to 12 haka ta fito duk da batayi makeup ba sai eyeliner da ya zame mata jiki da maroon lipstick tayi kyau sosai Bata saka powder ba tayi cool kyau haka. Ayman na waya tamkar baya son magana Yana magana kasa kasa batajin me yake cewa har ya gama ya juya Yana kallonta, Wani kallon up and down ya mata ta juya tana kallon gefe. Zama tayi bisa kujera yace ” kullum haka kike fita, are u trying to impress ur lecturers” tayi banza dashi don ta fara gajiya da takurawa rayuwarta da yake son Yi, ” am talking to you” ta Bata fuska tace ” don Allah ka rabu dani ” tayi maganar tamkar zatayi kuka, Wani kallo ya mata ya Sauke numfashi yace ” ok let’s go ” “12 ya kusa yanzu Nana zata dawo ta zauna a gidan ” shiru sukayi ya Maida hankali bisa waya ita kuwa sai hararinsa take nan ta dauki waya ta Bude Whatsapp ta fara chatting da friends nata, Whatsapp video call aka kirata Mahfouz ne kamar bazata d’aga ba kawai tayi picking tana kokarin saka earpod nata suka hadà Ido ta kauda Kai ta gyara kwanciya bisa kujera ” hey bro ” murmushi tayi idanunta na bisa screen din wayar tana saurarensa tace ” no… bahaka bane kaima kasan I can’t do that kawai am kinda busy ne ” zuciyarsa sai tafarfasa yake he is trying to control himself lallai yarinyar nan tayi Nisa wato har video call take da Maza , ya rasa wane mataki zai dauka akanta yanzu duk Wani move din da zaiyi asirin zuciyarsa zai iya tonuwa har a fara zargin ko sonta yake Wanda shikuma bayason Hakan ya faru, yafison sai lokacin yayi kawai zai fito musu unexpected. Kallonta yai da gefen Ido tana Wani narkewa tana zuga shagwaba ganin bazai jure Hakan ba yasa ya tashi ya fice daga falon tabi bayansa da Ido , ta cigaba da waya har na tsahon Wani lokaci kafin suka gama ta kashe. 12:30 door bell yayi ringing ta tashi ta sauka ga mamakinta Yana Zaune a falon kasa Yana kallon football, Bude kofa tayi Nana ce cikin kayan makaranta ta gaisheta ta amsa tana mata sannu da dawowa, Nana ta gaida Ayman ya amsa mata daga haka ta wuce sama hajjo kuwa tana son ce masa su tafi ta rasa ta Yaya zata fara. Sama ta koma ta zauna har after 1 kawai ta tashi ta koma d’akinta tayi alwala tayi azahar sannan ta fara Shirin zuwa lectures gashi driver baya nan sun fita da inna dole tayi booking din bolt, tana Bude app din bolt ta fita zuwa falon Yana hakimce bisa kujera tasa Kai zata wuce ” I’ve been waiting for you” ta juya don tabbatar ko da ita yake kallonta yake ta rasa amsar da zata basa , ya tashi cikin kwalisa yayi hanyar fita tana tsaye ta zuba masa Ido mamaki yake Bata Yana Abu cike da gadara kamar Wani basarake, bin bayansa tayi sai Kuma ta koma ta sanar da Nana cewa zata wuce skul tazo ta kulle kofa.
A mota ta samesa Fauzan ne ke Jan motar Ayman kuwa yana gidan gaba , sun gaisa da Fauzan daga nan yaja mota suka tafi. Ita dai hankalinta nakan waya batasan inda suka nufa ba , a harabar For you super market na wajen adetekunbo ademola street dake wuse 2, Fauzan ya rigasu sauka ganin Bata da niyyan fitowa yasa Ayman ya waigo ya kalleta yace ” let’s go ” ta hada rai tace ” ni zan jiraku a nan ”
Ya fito ya Bude bangaren da take Yana nade hannun rigarsa tayi saurin d’aga Kai tana kallonsa ” wat are you trying to do?” Murmushi yayi yace ” is like you are tired bari na taimaka na d’aga ki ” da sauri ta ture hannunsa ta sauke kafafunta a waje tana Shirin tashi ya koma baya Yana Wani dariya kasa kasa ta juya tana kallonsa a wannan lokacin Fauzan yayi snapping nasu Wani hoto me Karen kyau. Suka jera suna tafiya they look so good together duk inda suka wuce sai kallonsu ake suka shiga cikin building din, Kai tsaye layin hijabai ya nufa ya juya Yana kallonta yace ” ki zabi duk kalolin kayanki, daga yau bana son Kara ganinki da veil ” turo baki tayi tace ” don Allah ka kyaleni kar kayi asarar kudinka ni ba sakawa zanyi ba, Kuma ..Kuma ni Ina da wasu a gida ” Wani kallo ya mata bai sake magana ba ya fara zaban kalolin hijabs da jalbab masu kyau har iya son ransa daga nan ya koma bangaren turaruka ya zabi kalolin da yake so ” kina bukatar Wani abu ne” “No thanks” daga haka ya wuce wajen biyan kudi ya Mika ATM suka hada kayan Wani ya dauka zuwa mota.
Sai faman Jan tsaki take cikin mota tana duba time 2:15pm hanyar makarantarsu suka dauko bayan 25 minutes sukayi parking harabar school din ta Bude mota tace “thanks” daga haka ta fice , Ayman yabi bayanta da kallo bayan ta tafi yace ” zamu Jira sai ta fito ” angama ranka shi dade” Fauzan Yana jinjina lamarin soyayyar da Ayman yakewa wannan baiwar Allah.