Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 39

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*39*

Sallama sukayi Fahad ne kadai a falon Yana kallon cartoon ganin Ummeey yasa ya tashi da gudu ya rungumeta Yana oyoyo anty” my boy how are you ” fine anty” ta kallesa tace” u didn’t greet d other anty ” ya Kalli Hajjo yace ” good evening anty ” murmushi ta sakar masa tare da shafa Kansa tace ” how are you feeling ” fine ” ya koma jikin Ummeey ya kwanta tana masa wasa tare da Ciro crackers ta Mika masa, suna kallon cartoon sun share 10 minutes kafin aka turo kofa anty zee ce cikin wata short gown ga Brazilian wool an Kitsa mata bob Marley sai zuba qamshi take tana tauna chewing gum da karfi sai Kara yake fuska yasha makeup , tana kallonsu ta tabe baki ” yaushe kika shigo y’ar nema ” ta zauna kusa da Ummeey din tana kallonta ” kindade ne tun dazu Ina tare da sweet hrt Yana ta min rigima kamar Fahad ” murmushi Ummeey tayi cike da Jin kunya tace ” ga kawata da nake yawan Baki labarin meet my best friend” Wani kallon up and down tayiwa hajjo tace ” sannunki koh ” ganin yadda tayi yasa hajjo ma ta basar Bata gaisheta ba tace ” yawwa sannu ” daga haka ta Ciro wayarta tana chatting don Bata daukan raini a rayuwa , zee tana ta zuba iyayi ga Wani kishin Hajjo ta taji har cikin zuciyarta saboda a duniya ta tsani wata mace tazo gidan mijinta na nan. Yanzu idan Aman ya fito yaga hajjo Kuma ya zatayi tsaki ta ja a fili batasan da Hakan ba , Ummeey tace ” ya dai ” kamar Yaya y’ar rainin wayo ”
” Toh anty naga kina faman Jan tsaki ke d’aya ” ” uhmm..kuzo mu koma downstairs sweetie na barci kar a tashesa ” Ummeey ta mike tana kallon hajjo tace” kawata muje downstairs Kinga masu miji wai kar a tashesa, Allah dai ya nuna mana namu mazajen ” murmushi hajjo tayi ta fahimci inda zee ta dosa wato irin matan nan ne masu mugun kishi, suna sauka Mai aiki ta kawo musu drinks ko kallonsu hajjo batayi ba tana danna waya kamar ance ta d’aga Kai caraf idanunta suka fada cikin hoton Aman tare da anty zee suna rungume da juna, dakyar numfashin ta ya daidaita tana Jin kirjinta ya mata nauyi ta sunkuyar da Kai dai dai nan taji dariyar anty zee ta takun takalmansu a staircase da alama suna saukowa, Yana makale da Fahad d’ayan hannunsa na bisa kafadan zee suka sauko hajjo ta tsinci kanta da son kallonsu aikuwa carab idanunta suka fada cikin nasa, saura kadan Aman ya Fadi a wajen cikin in Ina yace ” ah..ah anty Ummeey yau ..yau kece a gidan nan ” zee Bata Gane halinda yake ciki ba hankalinta nakan hajjo da ya kura musu ido, dakyar Hajjo ta saita kanta tana sunkuyar da Kai tana kallon waya Amma gaba d’aya batasan me takeyi ba. dama anty zee ce matar Aman nata wayyo Allah yanzu ya zama dole ta rabu a Aman ko saboda alakarta da Ummeey, basarawa Aman yayi ya fara hira da Ummeey hajjo kuwa Bata d’aga kanta ba yayi duk yadda zaiyi ya gano halinda take ciki Amma ya kasa , haka ya sallami Ummeey ya fice daga gidan bayan zee ta rakasa har bakin mota. Hajjo ta daidaita nitsuwarta tace ” ya kamata mu koma gida magariba ya kusa ” ko ruwa Baki Sha ba ” no ..no am ok let’s go please” ok” daga haka Ummeey ta dauki fanta guda d’aya ta rataya jaka suka kama hanya a bakin kofar shiga suka Hadu da anty zee nan Ummeey ta mata sallama ita kuwa hankalinta na gun hajjo cikin zuciyarta kuwa taji tsanar yarinyar wato tafi karfin ta gaisheta bayan tana matsayin yayar kawarta, cikin mota Babu Wanda yayi magana Ummeey ta lura da mood nata amma batayi magana ba har aka sauketa a kofan gida Ummeey tace zata tsaya tayi sallah, driver ya ajiyeta ya tafi tace zata koma da kanta tayi Hakan ne saboda tana son bawa kawar tata hakuri bisa Halin da anty zee ta nuna mata.
Aman ya rasa meke masa dad’i a duniya yai Kiran duniya hajjo taki picking ya mata message yayi duk abunda zai dace amma ya kasa samun kanta gaba d’aya hankalinsa ya tashi gashi baisan gidansu ba bare yaje ya sameta , mafita d’aya ne wato ya kira Ummeey ta basa address din gidan toh Amma idan yayi Hakan asirinsa ya gama tonuwa wajen zee don yasan halinta da mugun kishi, yayi parking a kofar gida ya rasa mafita yanzu ne ya Kara tabbata cewa bazai iya rayuwa Babu hajjo ba tabbas yayi zurfi cikin kogin sonta, toh meyasa take fushi haka bayan dama ya fada mata yayi aure toh kodai saboda Bai mata magana ba, haka dai yayi ta sake sake ganin magariba tayi yasa ya wuce masjid dake kusa da gidansa.
Sai bayan Isha Ummeey ta shirya komawa hajjo ta karbi key din mota wajen inna zata Kaiwa driver dayake a bakin gate din shiga estate din suke zama dakunansu na daga farkon shiga , suna trekking Ummeey ta kalleta tace ” am so sorry da abunda ya faru gidan anty zee, wallahi haka halinda yake ni gaba d’aya ta sani Jin kunya d way she treated you wllhi ” haba dai is Normal ai ba Wani abu ni Banga laifinta ba don tayi kishin mijinta ” ai tana masa Wani irin mahaukacin so ne am telling you, duk ranar da zai Kara aure akwai aiki aswear ” jinjina Kai hajjo tayi suna tafiya suna hira har bakin gate driver na hangosu ya taso yazo suka gaisa ta fada masa zai sauke Ummeey ya karbo car keys din.

________
The next day Aman ya rasa mafita saboda har wannan lokacin hajjo Bata picking calls nasa , text ya rubuta mata Yana hadata da Allah da annabi tayi picking call nasa zasuyi magana. tana kwance ta karanta text din ta kurawa wayar Ido sai ga Kiran nasa ya shigo kamar bazata d’aga ba sai Kuma ta dauka tayi shiru batayi magana ba, ajiyar zuciya yayi kafin yace ” am very sorry baby please n please karki sake punishing dina dis way wallahi zan iya mutuwa ” tabe baki tayi da batayi niyyan magana ba Amma Jin kalamansa yasa tace ” Kai dai ka shiga uku da yaudara, nice zakawa dadin baki bayan a gaban matarka ko kallona ka kasa Yi please say something else ” I swear to almighty hajjo I’m madly in love with you kinji na rantse Miki Kuma wallahi bazan iya rabuwa dake bah” lumshe Ido tayi tana Jin zuciyarta na sanyi wanda rabonta da Hakan tun jiya , ” kina kina kyakkyawa Tah, please ki yafemin am so sorry please ” shiru tai tana sauraronsa, ” don Allah ki bani address naku nazo na rarrashi kaya nah ” murmushi Mai sauti tayi tace” a’a wllhi kayan ka zee tana gidanka ” haba mana fine girl please…” Ya fada a shagwabe ta juya idanu ” Aman stop it” wallahi zan iya Miki kuka matukar bazaki bani damar ganinki a yau ba ” please Aman not today” ta marairaice ” haba mana princess why..don Allah ni I want to see you ” shagwabe fuska tayi tamkar Yana kallonta” nidai um um banson ganinka ” ” ni din Kuma baby nah , please mana nace sorry fah I’ll explain idan nazo ” sauke numfashi tayi tana lumshe Ido tabbas Aman shine farin cikin rayuwarta, Wani call ne ya shigo sultan ne ke kira ” hey Beb are you there ”
“Yeah..Ina jinka ”
“Toh ni kice Wani abu ” toh nace Wani abu” dariya suke haka suka cigaba da hira gwanin sha’awa har sun manta cewa sun Bata . Haka rayuwa ta kasance har hutunsu ya kare suka koma 300 level soyayyar hajjo da Aman kuwa yayi karfi har sunajin bazasu iya rabuwa ba, tana waya da Mahfouz da sultan Amma ba kamar da ba har suna complain cewa ta canza ita ko ta nuna musu cewa school ne ya riketa ana haka auren sis khairiyya ya tashi sunyi anko na duk events din da zaayi sokoto zaa kaita donhaka suka fara Shirin biki gadan gadan.
Ayman ya sauka Nigeria daga Sudan suke tare da iyalansa gidan Aman suka yada zango saboda Aman ya dage lallai gidansa zasu zauna kafin su wuce , Ayman yace zasuyi wata d’aya saboda wata kwangilar sabon kamfanin da zai gina na sarrafa kayan abinci irinsu taliya shinkafa har su masara da dawa, ya shirya cikin kaftan farare da hular zanna da royal Caribbean shoes yayi kyau matuka sai zuba qamshi yake. Zee tare da Failuzaa suna falon kasa ya sauko zai wuce ya dan Kalli Failuzaa yace ” zan fita akwai abunda kike so ne a taho Miki dashi ”
“No..Babu komai sai milk din meenal ne ya kare ”
“Haba Failuzaa shine Baki fadamin ba, so kike ta zauna da yunwa ” sorry ” ta furta don tasan akan meenal zai iya ci mata mutunci , kada Kai yayi ya fita Fauzan na jiransa da mota a waje. Zee ta tabe Baki tace ” Amma kina fama da wannan mijin naki, mutum ba fara’a ba magana sai uban mulki haka kuke rayuwa” kedai bari sis..haka nake fama dashi Babu soyayya sai hakuri da biyayya ”
“Cabdi ni kuwa idan Babu soyayya ai Babu zaman aure Ina zan iya , ke yanzu a haka Yana nemanki kuwa ” hmm sai da nakai kaina , ke idan ta halinsa ne sai dai mu zauna haka ” zee ta gyara zama dama irin hirar da tafi so kenan kamar ( shatu dambatta ..lol)
“Kodai bashi da lafia ne” lafiyansa kalau girman kan tsiya ne dashi wallahi ” toh bari kiji dole ki tashi tsaye kafin ku koma ni zan kaiki gun wata ta shiryaki don ubansa idan yazo sau dole yabi kowane dare ya dawo ” ” Allah sis” Allah wallahi ke wayace Miki ana zama haka nan, ku Yan Sudan haka kuke aure ne sai uban kayan qamshi Babu kayan harka ai ba bayani kenan ” dariya suke harda tafawa.

Ayman na gaban mota sunzo kusa da gate din Amina court ya hango motar Aman, ya kurawa motar Ido kamar dai ta Aman din ce toh meyake Yi a nan? Cike da mamaki yake bin motar da kallo yace Fauzan ya sauka yaje yayi confirming Allah yasa ba abunda yake zargi bane, Fauzan yayi parking ya fito kamar Yana waya yaje kusa da motar hajjo ce gaban mota Aman na driver seat suna hira cikin nishadi haka Fauzan ya juya ya koma Baiyi magana yaja mota suka karasa ciki. Ganin baice komai ba yasa Ayman ya gane kan zancen take yaji zuciyarsa na harbawa Yana ganin Wani duhu a wajen a hankali yake tafiya har ya karasa yayi knocking aka Bude masa, a falon kasa ya sameta nan suka zauna ta tarbesa kamar yadda ta Saba tana tambayarsa yaushe yazo kasar. Suna hira sama sama Sadeeq na makale a jikinsa gaba d’aya ciwon kai yake ji inna ta gane halinda yake ciki take tambayarsa meke faruwa yace Babu komai, bayan Yan mintuna ya kalleta yace ” inna yaushe Aman ya fara zuwa hira wajen sanyin idaniya ”
“Aman Kuma? Aman dai da na sani ko Wani daban ?” ta tambaya cike da mamaki ” Aman din dai da kika sani yanzu na wucesu cikin mota suna tare ” mamaki ne zalla a fiakar inna shine Hajjo Bata taba fada mata bah, wayarta ta dauka ta fara Neman layin Hajjo ta d’aga bayan yayi ringing” duk inda kike kizo Ina son ganinki yanzu ” kit ta kashe wayar tana huci, inaa.. Hajjo da Aman hadin bazai taba faruwa ba har yau Bata manta da fuskar Ammi ba da irin kallon banzan da ta mata.

Back to top button