Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 57

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*57*

Jawota yayi a jikinsa bayan ya jingina da gado tana kwance kanta na bisa kirjinsa ya fara magana kasa kasa
“Nana Aishatah Ina son ki bani dama mu Bude sabon babin rayuwa Mai dauke da tarin so da kauna da matukar kulawa da juna, bana son tilasta Miki duk abunda kike so shi zanyi donhaka zan Baki dama sai ranar da kika fara Sona zuciyar ki ta amince dani a wannan ranar zamu kasance Abu guda ” shiru tayi tana sauraronsa kalamansa sun karya mata zuciya tabbas Ayman daban yake cikin Maza salonsa daban yake komai nasa daban ne ya iya lafazi ya iya tattalin mace ya iya….
“Qalbee nah “…
Lumshe Ido tayi sunan Yana ratsata a duk lokacin da ya furta takan tsinci kanta cikin wani yanayi Mai wuyan fassara , iska a hura mata a fuska
” Tunanin me kike hearty”
Shiru tayi don Bata San me zata ce dashi ba, habarsa ya dora bisa kan nata ayayinda hannayensu ke sarke da juna ” please Ina son ki saki jiki dani I want to be your friend bana Jin dadin yadda kike ignoring dina Allah ”
Murmushi tayi tare da furta ” kayi hakuri toh ”
bakin nata ya kama Yana shafa lips nata Yana Jin farin ciki na ratsashi lallai aure ni’ima ne idan ka samu Wanda kake so,
” Tell me your best gift and favorite color ”
Lumshe Ido tayi saboda laushi da sanyin hannunsa dake bisa lips nata Yana saukar mata da kasala ” Qalbee nah!
“Uhmm.. ta amsa , ya shagwabe fuska ya d’aga ya dawo saitin fuskarta suna kallon juna yace ” Ina ta magana kika shareni is not fair fah…”
“Sorry ” ” haba Qalbee gaskiya bana Jin dadin yadda kike behaving towards me ”
“am sorry Yaya..
Lumshe Ido yayi ” sorry.. sorry for how long nidai don Allah ki daina ” ya karasa maganar tamkar zaiyi kuka, rausayar da Kai tayi” toh ba nace bazan Kara ba ”

“Toh answer my question” “ok.. pink , lemon green n black are my favorites n my best gift is perfumes I love them much ”
Ya cusa Kansa bisa wuyarta Yana cewa ” wow… shiyasa kullum kike cikin qamshi, nima perfume is my favorite gift sai Kuma wrist watch I love them too, Color Kuma black sai white then sea green ” Yana magana lips nasa na shafa fatar neck nata Wanda ya jawo mata kasala numfashi take fitarwa a jere, yaki barin jikin nata ya cigaba da magana” in terms of food Kuma I love traditional dishes musamman tuwo, Ina son tuwo sosai tun Ina karami Umma tana bani saboda kinsan abincin Sudan daban da na nan, toh ita Kuma ta Saba da nasu shiyasa even sultan Yana son tuwo sosai yafison girkinta akan na servants sai few years ago ta daina masa girki ”
dakyar ta hadiye miyau saboda Wani yanayin da take ciki yadda yake magana lips nasa na gugan fatar jikinta ga Kuma numfashinsa dake sauka bisa skin din wuyarta, yagane halinda take ciki yasa ya d’aga dara daran idanunsa ya saitasu bisa nata kurr..suka kurawa juna Ido, kallonta yake sama da kasa Yana karewa fuskar nata kallo Yana murmusawa hajjo dai ji take tamkar zata Suma saboda Yana jefata wata duniya daban komai nasa daban yake,
” Kyakkyawa tah I told you bazan Miki komai ba sai da yardar ki trust me but naga a tsorace kike please feel free ok ”

Yana magana cikin Wani salon Jan hankali gaskiya Ayman ya kware da iya sarrafa mace, gaba d’aya bugun zuciyarta da karfi yake fitowa har Yana ganin yadda kirjinta ke Hawa sama da kasa, kallonsa take ba tare da kawar da Kai ba tana son kare masa kallo tabbas duk inda Ake Neman kyakkyawa Ayman ya taka wannan matsayin gashi ba fari ba haskensa irin na fresh din nan ga sajensa hade da gemu da sumar Kansa duk sheki suke ga lips nasa dan dai dai ga dogon hanci ga manyan sexy eyes Wanda kullum suke a lumshe ga shape nasu kamar….
“Qalbee wannan kallo haka” gira ya d’aga mata, ta runtse Ido cikin Jin kunya , yakai bakinsa saitin kunnenta yace ” duk kyauna bankai Qalbee nah kyau ba, ke din ta musamman ce I love you matata Allah ya barmin ke har karshen rayuwata” ajiyar zuciya ta sauke cikin zuciyarta kuwa da Ameen ta amsa Wanda ita kanta batasan dalilin amsawan ba,
” Let’s sleep bacci nakeji kinsan nagaji dayawa yau ” gyada masa Kai tayi ya raba jikinsa da nata ya tashi ya shige toilet, tana nan inda ya barta har ya fito Yana kallonta yace ” kije kiyi alwala kwanciya da alwala Yana da kyau sosai”
Babu gardama ta tashi , bayan ta fito ya Bude sif nasa ya Mika mata Wani qaton hijab tana kallonsa da mamaki wato Yana da komai a d’akin, turare ya dauka ya fesa mata sannan ya shimfida abin sallah suka jera ya jasu sallah raka’a biyu sukayi bayan sun idar ya d’aga hannayensa sama Yana jera adu’o’i Wanda hajjo sai da tayi mamaki dama haka yake da ilimin addini, sun share 10 minutes Yana musu adua kafin ya rufe da fatiha ya shafa.

Gadon suka koma nan ma sai da ya musu adua yayin kwanciya bacci ya kashe wuta ya juya ya rufe idonsa Bai jawota jikinsa ba ya barta ta dan samu sarari peck ya manna mata tare da furta ” good night love”
ya juya mata baya ya rufe Ido Yana jiran bacci yazo, hajjo ta kurawa bayansa Ido tunani kala kala ke yawo cikin zuciyarta tana fatan wannan soyayya ya dore har abada saboda tasan Aman ya mata Nisa bazata sake samunsa ba har abada a haka har bacci yayi awon gaba da ita, numfashinta yasa ya gane lallai tayi bacci nan ya juya Yana kallon yadda take bacci cikin kwanciyar hankali Yana murmushi Yana Jin kaunarta na Kara mamaye kowane bangaren jikinsa a haka har yayi baccin.

*4 days later*

Abubuwa dayawa sun faru cikin wannan Yan kwanakin da sukayi tare Ayman Bai fasa nuna mata zunzurutun soyayya da kulawa ba Wanda ya fara jefa zuciyar hajjo cikin qalubale tuni zuciyarta ta aminta dashi amma gangar jikinta baisan da Hakan ba Gani take tana masa biyayya kamar yadda aka umarceta ne Kuma Babu Wani abunda ya shiga tsakaninsu har izuwa wannan lokacin.
Yan uwan Failuzaa 3 suntaso daga Sudan sunzo yaune zasu rakata gidan mijin nata , wasu kamfanin home decorators suka dauka suka taho tare dasu aka kawo mata sababbin furniture masu kyau da tsada an fitar da tsohon har gado da komai aka canza mata, sai wajen karfe 3 aka gama shirya komai yadda ya dace nan suka bankada turarukan wuta Wanda dayawa magunguna ne a ciki nan gida ya kaure da qamshi, Hajjo tana part nata tana Jin hayaniyarsu tana Jin Wani iri cikin zuciyarta wato yau matar gidan ta dawo kenan.
Bayan magariba akayi sallama a kofar falonta ta tashi ta Bude wata mata fara wacce at least zatayi 35 years ce tsaye a bakin kofar murmushi hajjo tayi tace” Bismillah barka da zuwa”

Murmushi ta mayar mata” yawwa amarya sannu ”
Suka shigo tare ta zauna tana raba Ido hajjo na satar kallonta ” Ina yini ”
Hajjo ta katse Shirun
“Lafiya amarya ya gida ya bakunta” “lafiya Alhamdulillah”
“Allah Sanya alheri ni yayar abokiyar zamanki ce dazu muka rakota ta dawo, naga Baki shigo ba shiyasa nace bara nazo na duba ” tana magana hausar nata Baiyi kwari ba , murmushi hajjo tayi
“Allah Sarki ai bansan ta dawo ba da na shiga dayake TV a kunne shiyasa banji motsin naku ba ”
“Allah Sarki sannu amarya ”
Tashi hajjo tayi matar Tabi bayanta da kallo , ruwa da lemu ta kawo mata tana godiya, bayan kamar minti 12 tace zata koma godiya hajjo tayi tace gata nan shigowa.
Bayan fitar matar waya ta dauka ta fara Neman layin Ummeey ringing biyu ta d’aga suka gaisa hajjo tace ” ke shawara nake nema , matar gidan ta dawo shin ya kamata naje na mata sannu da zuwane ko Yaya ” dariya Ummeey tayi tace ” ke sabuwa ke yakamata a Miki sannu da zuwa ba ita ba, kiyi zamanki sai lokacin da mijin ya hadaku sai ku gaisa ki duba irin tarbar da zata Miki ”
“Ok nagane tanz kawata ya school ”
“Ke bazaki koma bane ankusa fara test fah ”
“Zan koma week din nan insha Allah bari ya dawo yau na fada masa ”
“Iyye kaji masoya toh Muna zuba eyes Muna jiran zuwanki ” y’ar hira suka taba kafin ta kashe wayar yanzu ne za’a fara asalin zaman wato daga yanzu ba kullum zata kwana d’akinsa ba koh…tabe baki tayi ta koma bisa kujera ta zauna tana kallon news har akayi Isha ta tashi tayi . Sai karfe 10 taji tsayuwar motarsa , bayan 30 minutes ya shigo part nata ta masa barka da zuwa ya zube bisa kujera ” wash… Qalbee am darm tired today, ya gidan ”
“Alhamdulillah ya aiki ”
“Aiki Alhamdulillah gaskiya gobe zan huta a gida nagaji sosai tun safe ban zauna ba , me kika dafa mana?”
“Tuwon semo na Maka da miyar kuka Allah yasa kana ci ” murmushi yayi
“Mezai Hana as far as ke kika girka , muje ki shiryani kizo ki bani a Baki ”
“Amma dai kasan akwai baqi a gidan Bai kamata naje part naka ba ”
Kayataccen Murmushi yayi ya Gane me take nufi
” Don’t worry gobe ne zaki fita girki let’s go ” yayi gaba ya ajiye mata suit nasa, Jim ..ta dan tsaya sai Kuma ta tashi Bata da zabi ta dauki rigar tabi bayansa har ya shige falonsa, a hankali ta tura kofar gabanta ne ya Fadi Ras…. Failuzaa ce rungume dashi ta Wani kankamesa da sauri hajjo ta juya ta koma, murmushin Jin dadi Failuzaa tayi tare da cewa ” ohh..ashe amarya tana nan yanzu na manta ba ni kadai bace da Kai ”
runtse Ido yayi
” But kinsan dai gobe ne zan raba muku kwana koh ”
” Yeah..but bazai hanani hugging din mijina ba cos I missed you so much”
“Ina meenal take ?”
“ta jiraka baka dawo ba tayi bacci ”
“Ok zaki iya tafiya sai da safe ” hada rai tayi
“Korata kake saboda amaryar ka koh ” lumshe idanunsa yayi kafin yace
“Bana son problem Failuzaa am tired I need to rest please” tabe baki tayi sannan ta juya cikin bacin rai ta fice daga falon nasa , Wani mugun kallo ta jefawa part din Hajjo kafin ta wuce. A haukace ta shiga part nata anty Maryama ce a falon tabi kanwar tata da kallo tana tabe baki, anty Sailuba ta fito suna kallonta Sailuba tace ” kin nuna masa Halin naki koh, ke yaushe zakiyi wayo ne wai”
“Rabu da ita Allah yasa ta Bada kanta gaban yarinyar ta ankarar dasu ” Maryama ce ta karbi zancen, Failuzaa ta zauna tace ” wallahi kunsan dai Ina son mijina Kuma dole nayi kishinsa ”
“Ke wawiya kwantar da Kai zakiyi ki Sace zuciyarsu duka da ladabi ki samu ki shige jikin amaryar a nan ne bukatarmu zata biya ko kin manta bayanin da mamma ta Miki a waya ”
Sauke numfashi tayi ” Kash…wallahi na manta totally amma insha Allah zan kiyaye zan Basu mamaki ” haba ko kefa ke dawo nan kiji Karin bayani ” Maryama ta fada nan fa suka fara mata huduba Wanda ni kaina bansan iya abubuwan da suka fada mata ba sai murmushin Jin dadi take.

Ayman yayi wanka ya shirya cikin armless shirt fari mara nauyi da 3 quarter off white pants ya fesa turarukansa masu qamshi ya saka takalmin Versace Eros masu mugun laushi ya taje Kansa da sajensa Yana kallon kyakkyawar fuskarsa Yana murmushi ya tuna yadda ta juya ta koma, lumshe Ido yayi da alama dai ta fara kishinsa Wani nishadi yake haka ya zuba hannaye cikin aljihu ya wuce part nata.
Sallama yayi ya tura kofa ga mamakinsa Bata kulle kofar ba tana Zaune ta harde kafafu tana kallon Wani indian film ta amsa sallama ba tare da ta Kalli inda yake ba. Qamshin turarensa ne ya shaida mata iya zauna kusa da ita Sam taki kallon bangaren da yake,

” Am hungry please a taimaka a bani abinci” batayi magana ba ta tashi tsaye ta fara tafiya cikin takun nata na kasaita ta wuce dinning area ta hado abincin bisa tray ta kawo tare da Jan Wani stool ta ajiye masa a gaba ta koma ta zauna, kallonta yake baice komai ba ya jawo abincin ya zuba yadda yake bukata Yana ci a hankali har ya gama ya dauki ruwa cikin gora sannan ya jingina bisa kujera, tashi tayi ta tattara ga yunwan da takeji Amma bazata iya ci ba saboda zuciyarta na mata zafi ta rasa dalili. ta fitar da KAyan ta dawo ta zauna ta cigaba da kallon da take Amma Bata Gane komai tun bayan shigowarsa saboda kayan sun balain fito da kyaunsa na asali,
“Qalbee tashi mu koma can falon ”
“Wane falo kenan ?”
Murmushi yayi” falon mijinki ”
“Gaskiya bazan iya zuwa ba saboda kar na shiga hakkin wata ” murmushi ya sake Yi Wanda sai da hakoransa suka bayyana
” Amma dai kinsan bisa ka’ida sai kinyi 1 week kafin ta karbi kwana koh”
“Kai kasan wannan ni bansani ba ”
“Kinsan komai stop pretending tashi mutafi ”
“Nidai a nan zan kwana ”
Shiru yayi baya son hayaniya donhaka ya koma ya kwanta jikin sit din, zuciyarta na dada tafarfasa wato so yake ta sake biyosa yaje ya wulakanta ta irin na dazu bayan yasan matarsa zata iya zuwa kowane lokaci, dubi yadda ya basar tamkar Babu abunda ya faru ko hakuri Bai bayar ba…Wani guntun hawayene ya fito tana saurin tarewa tasa hannu zata share yayi sharaf ya rigata , lallausan palms nasa ya saka Yana share mata hawayen daga bisani ya jawota izuwa jikinsa dama abunda take bukata kenan a wannan lokacin don yadda zuciyarta ke mata so takeyi tayi kuka ko zataji sanyi, shafa fuskarta yake ba tare da yayi magana ba nan ta cigaba da kuka hawayen da take boyewa suka fara gangarawa Yana share mata tare da Kara kankameta,
“Shhhh…is ok kiyi hakuri my baby am sorry ok ” dakyar ya samu ta daina kukan sai faman ajiyar zuciya take .

Back to top button