Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 24

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*24*

*Wannan page din naku ne Salma, anty Asee, anty hwati, minali, balakynmu, anty sofy, Asee golden, mmn hishma, mom nasreen, Asynmama da mum twins ku sakata ku wala kuyi Juyi naku ne Allah ya barmu tare ailobiyu*

Dare ya raba inna ta kasa bacci sai Juyi take bisa katifar Hajjo kuwa tayi nisa cikin bacci tana sauke numfashi ckn kwanciyar hnkli, ta tashi ta zauna tana son yin nafila Amma jikinta a mace yake gaba d’aya tana jinta Wani iri hankalinta ya kasa kwanciya, mmn nana ta tashi zataje bayi ta kunna torch sai Ganin malama tayi a zaune ” lfy malama Baki kwanta ba kodai baki Jin dadin jikin naki ne?” Numfashi inna ta sauke ” lafiya kalau kawai na kasa baccin ne ” haba malama kodai baki hakura da wannan batu ba, kin kasa sake rai ki barwa Allah komai ” bahaka bane kawai bana Jin dadin zuciyata ce tana min Wani iri ” murmushi mmn nana tayi tare da cewa ” lallai wannan soyayyar baban hajjo dayawa yake tunda gashi har ya hanaki bacci” lumshe idanu tayi ” bazaki Gane ba wllhi tausayinsa nake , nasan bazaki yarda ba idan nace Babu digon sonsa cikin zuciyata sai zallar tausayinsa ” zuciyar hajjo ya fara bugawa da karfi saboda ta Farka tun lokacin da maman Nana ta fara magana Amma taki motsawa saboda ita kanta tana bukatan Karin bayani dangane da sauyin da ta samu inna cki, “gaskiya ba karamin mamaki zanyi ba Sabida ni a tunanina so shike kawo tausayi ashe bahaka bane” ko kadan ni awajena malam Sulei tausayin da nake masa yasa na auresa ba so bane” gyara zama Mamn nana tayi tace” malama zanso Jin tarihin wannan auren naku kuwa don ban taba Jin ana haka ba ” tabbas dole na Baki tarihin rayuwata saboda ke din kin min halaccin da bazan manta dake ba har abada, Dake da wannan yaron Kun nunamin kauna a lokacin da nafi bukata, Kun zamemin Yan uwa a lokacin da bani da kowa , Kun taimaka min dani da ya’ta Kun nuna mana gata Babu abunda zan ce muku sai dai Allah ya biyaku” Ameen ya rabbi malama Nima kin maye gurbin dangina kin debe min kewan takaici da bakin ckin da nake ciki, toh Amma yanzu ki min bayani malama misali kin daura auren bayan kin gama idda sai baban hajjo ya dawo shin aurenki da baban hajjo Yana nan ko Yaya? Sauke numfashi tayi ” kinsan shi musulunci komai Yana da ka’ida Kuma addini ne me tsari yanzu misali idan mace taje an raba aurenta Sannan tsohon mijin ya dawo imam Malik da imam Bn Hanbal sunce idan har baa riga da an daura sabon auren ba zata iya komawa gun tsohon mijin Amma idan an daura Kuma shikenan bayanin na ckn littafin almudawwana, alkubra 2/92 . Wasu malaman kuwa sun nuna cewa Koda an daura auren zaa warware ta koma gun tsohon mijin Amma nasu imam Malik yafi inganci Allah shine masani, maganar raba auren Kuma sayyidina Usman da sayyidina Umar Allah ya Kara musu yarda sunyi bayani cewa matar da mijinta ya tafi har na tsawon shekara 4 zata iya zuwa malamai su raba auren tayi idda na wata 4 da kwana 10, hakama zamanin Abdullah bin Umar da Abdullah bin Abbas sunyi Karin bayani akan haka, Wanda Iman Hanafi da imam al-qudri sun nuna cewa idan miji ya tafi na tsahon shekaru babu Wanda yasan inda yake toh lallai matar zata cigaba da zaman har sai yakai lokacin tsufan mijin wasu litattafan sun nuna cewa sai yakai 90yrs wallahu ahlam Allah dai yasa mu dace ” Allahu Akbar kedai kinji dadinki malama komai kinsani ” ah ah mmn nana ba komai ba dai , ai shi ilimi baya karewa Kuma Kinga har ynxu kan nema nake , Yana da kyau mutum ya kasance me yawan karance karance litattafan tarihi da tauhidi da fatawan malamai don Karin ilimi saboda shi jahilci duhu ne ka nemi ilmin addini da na zamani Hakan Yana da matukar amfani ” Allah yasa mu gama da duniya lafiya yanzu dai a fara bani tarihi kan labarin ya shiririce dama haka kika Saba min dabara .” Murmushi inna tayi tace ” jeki bayin idan kika dawo sai na Baki labarin” Babu gardama mmn nana ta tashi ta fice daga d’akin.

____________

Ayman mutanen 400lvl angama shirin fita yanzu sun shirya da mutumin nasa wato Aman sun shaku matuka Wani lokaci tare suke fita zuwa skul cikin mota d’aya sai idan lokacin lectures Nasu daban daban ne , ya fito cikin long sleeves white shirt da black jacket da soft leather pants sai wasu nalco leather boots yayi kyau sosai sai qamshi kake ji , dai dai nan Aman ya fito cikin shadda sky blue dinkin kaftan sai black space da ya Kara haska farar fatar tasa duk sunyi mugun kyau , murmushi Aman yayi yace ” hey Mr Romeo how was d headache ko duk na soyayya ne saboda ana Shirin rabaka da Julie” murmushi one side yayi tare da lumshe Ido Kai tsaye dinning ya nufa yaje ya zauna Fauzan ya karasa ya hada masa tea me kauri ya Mika masa. Aman ya jawo kujerar dake facing nasa ya zauna Yana Bude food warmers din, Wani qamshin arabian turarene ya daki hancinsu Babu shiri Aman ya d’aga Ido Yana son kallon me wannan turaren farace Kal Amma daga Gani harda hasken shafe shafen zamani kyakkyawa ce tana da kiba Amma ba sosai ba, tafiya take cikin kasaita ta karasa dinning din cikin yanga tana tauna gum ta make murya ” Ina kwanan ku” Aman da Fauzan ne kadai suka amsa daga haka ta juya ta wuce bangaren Ammi , Ayman tamkar baya wajen Yana Shan tea nasa cikin kwanciyar hnkli Aman ya kallesa ya ware Ido yace ” bro kasan wacece wannan ,matar da Ammi ta zabo Maka ce fah ” waat..! Ya fada da karfi tare da dire mug cup din dake hannunsa Yana ware idanu ” yes am serious jiya naji tana waya da Anty Mami naji tana cewa a turota ku fara fahimtar juna kada ka Basu matsala nan gaba , I think y’ar uncle Ahmad ce ” shiru ne ya ziyarci wajen Ayman ya rike Kansa dake tsarawa ya tashi ya koma part nasu gaba d’aya yaji ya fasa zuwa skul din Yana bukatar Hutu he need to think . Fauzan ya shigo ya samesa ya nemi waje ya zauna yace ” ranka ya dade Ina ganin Aman da gaske yake fah don Babu alamar wasa ckn wannan magana , ni I think is high time ka fito ya bayyana abunda kake boyewa a zuciyar ka my prince ” runtse Ido yayi yace ” is not the right time Fauz ” daga haka ya haye gado ya kwanta Fauzan ya karasa ya cire masa takalmin nasa da alama Yana bukatar Hutu donhaka ya kunna masa ac ya kashe wutar d’akin ya ja masa kofa ya fice. Sauke numfashi Ayman yayi Yana hango sabon fitinar dake Neman tunkarosa dole ya nemi mafita don ya tabbata idan da gaske Ammi take toh lallai sultan zai amince da zabin nata Kuma idan har y’ar uncle Ahmad ne toh Babu tantama zaa aura masa ita tunda family ne wato jinin sarauta, bugun zuciyarsa ya karu he can’t afford to lose Hajjo yarinyar ta gama shigan zuciyarsa Bata bar space ciki ba ko kadan bashi da Wani buri da ya wuce ya mallaketa a matsayin matarsa Amma Kuma she is still young Kuma Bata kammala karatun ta ba. Haka ya kasance Yana ta tunani har bacci yayi awon gaba dashi , lectures din da baije ba kenan Aman ne ya wuce shi kadai, Ammi kuwa sai wajen 11:39 ta fito breakfast tana tambayar Mai aiki ko su Aman sun fita an sanar da ita Ayman Yana nan Bata ce komai ba ta zauna tayi breakfast nata tana ci tana waya da Anty Mami har ta gama ta koma main parlor daga nan tace a kira mata bakuwar tata.
Yarinyar dazun ce ta shigo da sallama ta nemi waje kusa da Ammi ta zauna tace ” gani nan Ammi ” yawwa kina jina Baby ki saki jikinki ki dauka nan gidanku ne kin gane, Ina fatan kinhadu da yayun naki Kun gaisa” umm..mun gaisa dazu da safe ” good! Haka nake so ki saki jiki ki fara jansu a jiki sai sun shaku kafin mu gabatar da bukatarmu kingane ai, ke macece kinsan abunda ya dace” tabe Baki tayi tace ” Amma fah naga Yana da shegen ji da Kai don ko dazun Bai amsa gaisuwar ba” dallah rabu dashi haka yake amma a hankali zaku Saba kedai kina sakewa kinji ” toh shikenan Ammi ” tashi ki koma d’akin ” daga haka ta tashi ta tafi Ammi taja tsaki tace ” yaran ynxu Sam ba wayo komai sai an nuna musu” .

Back to top button