Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 15-16

Sponsored Links

1⃣5⃣&1⃣6⃣

 

……………… Ta kwana da matukar tunani a wannan daren, Rayuwar ta da Ahmed, distance relationship, hatred tsakanin ta da y’an uwan shi, musamman Khaleel, she don’t really know why, bata kaunar ganin shi, idan akwai Wanda zata nunawa tsana itace mommy wadda ta hanata sakewa a Rayuwar Auren ta, but why him? So take ta nemo Amsar takasa, juyi takeyi cikeda mutuwar jiki, idan tace bata cikin damuwa tayi karya, Ace Auren ta wata cikin na biyu ba kwanciyar hankali, batasan dadin miji ba batasan dadin zaman Aure ba infact ba Abinda ta karu dashi sai girki da gyaran gidan, Wanda anayi ne domin a kuntata mata, basusan ta horu da aiyuka agidan ubanta ba, ba aikin da zai gagare ta, tsoranta daya a rayuwa kar a rabata da mijin ta, domin duk Abinda ke faruwa soyayyar shi bata ragu a zuciyar ta ba, sai ma karuwa da tayi duk wani moment ita da Ahmed idan ta kadaici cikin farin ciki take kasan cewa, idan tana tuno su, tasani duk ranarda ta samu freedom da mijin ta zaman su zai yi d’ad’in gaske. Bata cire tunanin wata rana zatayi farin ciki ba, Wanda tana fatan tayi nasara insha Allahu. Tashi tayi tareda yin sallah ta roki Allah akan ya cire idanun ta akan duk Abinda zai faru da kuma Wanda ya faru a baya, tareda neman juriya da nasara a rayuwar ta ta yanzu da kuma nan gaba.

Washe gari aka tashi da shagalin biki, Wanda tun da safe jikin ta yagaza dauka daka kalleta kasan tana cikin tsananin damuwa da kadaici, Ahmed ya boyewa ganin ta baki daya, Wanda batada masaniyar baida lafiya ne, Saida khaleel ya kawo mai likita batareda sanin kowa ba.
Yana tareda d’an uwan shi har safe bai runtsa ba Abu biyu ke damun shi a zuciya, why yayan shi keda mugun hakuri? And wani gefe kuwa kanshi yake tuhuma, why why why? Domin shi karan kanshi da baida karfin zuciya cikin wata biyun nan da ya ga likitan zuciya, he is in big trouble, big mess Wanda yasani shi karan kanshi, he is a fighter domin duk Wanda ke yaki da zuciyar shi shine babban jarumi, Wanda kowa yasan yaki da zuciya Abune mai matukar wahala.
Dafashi da akayi yasa ya dawo cikin hayyacin shi tareda kallon yayan nashi, daya tashi zaune yana murmurshi kadan, kana ganin shi kasan cikin jinya yake. “All night bakayi bacci ba khaleel, why kuma kasan yau ranar Auren kane dole ka raya wannan daren. “Yaya ya jikin naka? “Alhamdulillah inajin sauki a jikina, ya Naziya kagan ta? how is she? ” Yaya all you worried about is her? Why bayan ita bata damu da neman kaba if tasan Abinda ya dace me zai hana ta nemeka? “Kafada mata banda lafiya? “Nop Yaya. “Kaga batada masaniya, and please Khaleel take care of her, that girl deserve to be happy. “How Yaya bayan kaine zaka kula da ita she needs you more than me, kaine mijin ta. “I know khaleel. Ya Rungumo shi a jikin shi, yace “you have alot of responsibility, mommy, Fauziya and our company, I know you are stronger than me. “Yaya please stop All this you know you’re breaking my heart, Yaya I have something in mind, Wanda bai kamaci in sakashi a zuciya ta ba I hate myself please forgive me. “What is that khaleel, me kakeso I promise to give it to you koda rayuwa tace saboda kaine farin ciki na. Wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro a kwayar idanun shi for the first time, yaji he need them, saboda sometimes tears heal some wounds.
“Noo Yaya bana son destiny din da zai zamo musayar rayuwar ka, I don’t want that destiny, but Yaya is really painful, bansan yanda zanfada maka ba and please don’t ask me too much question bazan iya amsaka ba. “Is OK bazan tanbaye ka komai ba, but dole inji dalilin zubar hawayen jarumin kani na, what is that, meye ya taba zuciyar the stone heart Ibrahim khaleel? “Yaya. “No am not asking the new ango but am sure kana kukan farin ciki ne yau zakayi Aure and you will last on bed more than me. Yafada yana daga gira daya, ya tuno da irin question din da yamai ranar da sukayi hira a dakin shi da Naziya. Dafe kanshi kawai yayi tareda sakin yayan nashi, “Hmmm yaja dogon Ajiyar zuciya, “I know kani na sai yafi thirty minutes. Mikewa yayi cikin sauri, am coming Yaya bari inje cikin gida. Yafita fuuu dagashi sai guntun wando yau ko singlet babu a jikin shi yama manta da taron matan dake gidan, burin shi ya ganshi a cikin gidan.
Dayake kowa na sha’anin gaban shi sannan kuma an Waye ba wani Abu bane don haka no one care, har ya shiga main palo, dai dai taci kukan ta tayi nak har wani zazzabi takeji ta fito jikinta kamar ba ruwa ba Wanda ya damu da ciwon zuciyar ta. Taga shigiwar khaleel fuuu ya wuce dakin shi, bayan shi ta hanga yana shigewa Wanda dole ta bishi taji inda zataga Ahmed domin ta gaza zuciyar ta tayi rauni, ta leka dakin khaleel din yafi sau goma tun jiya dukan su basa ciki, infact ko gyaran datayi bai baci ba.
Shiga yayi ya kalli gadon cike da wani irin zafi zuciyar shi keyi Wanda bai taba jin irin shi ba, ya fisge zanin gadon ya jefar tareda zubewa kasa yasaki wani irin kuka mai karfi kadan Wanda ba Wanda zai jishi,

Tayi matukar tsorata da kuma jin mamakin kukan namiji, tun dosowar ta kofar dakin kuma tanada yakinin a cikin dakin khaleel yake fitowa, wake kuka haka? Bude kofar tayi cikin Sauri, ya dago fuskarshi karab cikin idanun ta, tayi matukar girgiza, bata taba kawo zata ganshi yana kuka ba, meye yasa shi kuka haka ? The great mai girman kai, this is serious, kokarin juyawa tayi kawai domin a tunanin ta koma meye ba hurumin ta bane. “Wait. Yafada cikin sanyi tareda mikewa yana share hawayen shi, tsayawa tayi cak har ya iso wurin, hijabin dake jikin ta tarike gefen shi gam tana jiran taji me zaice, saida ya matsa ya tura kofar ya datse, ta zaro idanun ta, “meye na rufeni a dakin ka, bana son rainin wayau ka bude min kofa intafi. Tafada bakin ta na rawa kamar zatayi kuka, “Hmmm, me kike nema? “Mijina. Tafada kai tsaye batareda ta kalli y’an da ma yake ba, “bakida lafiya ne? Saurin dago kanta tayi ta kalle shi akaron farko tun shigowar ta, da gudu ta datse makullin idanun ta, “Auzubillahi. Tayi saurin ja baya, Wanda Abun yayi mugun batamai rai fiyeda tunani,
Bata taba ganin bear chest din namiji ra’ayil aini ba sai yau ga kirjin nashi da shegen fadi da wata irin suma mai tada tsigar jikin mace,
Fisgo hijabin ta da yayi cikin zafin rai yasa tafara istigifari tareda bude idanun ta tana mai kallon that’s why I hate you, “you are behaving like baki taba ganin namiji ba kaya ba, kina Abu kamar wata saliha, look karki daukeni jahili ko mara sanin iyakar shi, I know my limit shiyasa kike tsaye agaba na batareda wani Abu yafaru dake ba, ni kikeyiwa a’u’ziya? kamar Kinga shedan. Cikin tsiwa da zafin zuciya tace “meye banbancin ku da shi, kana ratsa mata tsirara bayan kasan haramcin Abun sannan wuce limit! yes you cross All the limit da ka rikemin hijabi now let me go. Tafada cikin karaji, saurin sakin hijabin yayi tareda sai daita kanshi yana shafo sumar kanshi tareda d’an naushin iska.
“Am sorry, kiyi hakuri am worried ne because my brother is sick tun jiya. Saurin natsuwa tayi tareda sakin jiki tace “Ina yake? Jikin ta na rawa, yana part d’in mu na waj… Ko gama sauraran shi batayi ba ta bude kofar ta fice da sauri,
She knows it shiyasa itama batada lafiya, saboda Ahmed d’in ta is sick,
Tana fita ya datse kofar tareda zubewa kasa ya hade kai da guiwa, “khaleel you are so dead. Ya furta yana sakin Kara.
Da taimakon mai aiki tasan inda Ahmed din yake Wanda shine karon farko data shiga wannan part din Wanda ya kamata ta kasance a ciki, tundaga falon take zuba ido domin tasan dukiyar dake ciki bata malam bace, infact ko kudin labulen dake cikin falon zai siya kaf kayan dakin ta, wani irin karyewa zuciyar ta tayi takasa daga kafarta daga nan ta zube, shikenan tata takare za ashiga tsakanin ta da mijin ta domin tasan burin mommy ya cika ta Auro mai burin ranta,

Jin kukan ne yasa yafito daga bedroom ya ganta a wurin da gudu ya karaso gaban ta, “Naziya Naziya, ya zube tareda rikota zuwa jikinshi, “Am sorry please, Allah yagani kukan ki yafi komai daga min hankali please kiyi hakuri komai nada dalili believe me, dago kanta tayi ta ce”harda guduna kadawo dakin Amaryar ka tun bata tareba, Ahmed meye ribar zama na a karkashin inuwar Aurenka? “Soyayya ta Naziya, soyayyar kice Ribar Auren mu, Wanda nayi miki Alkawari muddin baki tare cikin gidan nan ba bazan taba samun farin cikina ba kece walwala ta kece farin cikina, am sick Naziya saboda damuwa datayi min yawa zuciya ta na ciwo. , Hawayen ta tayi saurin sharewa, “Ahmed Ina son zama dakai, ka koyamin sonka duk da bamu zauna tare ba, halin ka hakurin ka tarbiyar ka, Ina son halayen ka, kaddarar rayuwar mu, nadauka am not blaming you for that shine kaddarar mu, please karkayi ciwo zan shiga damuwa kaji, tafada tana shigewa cikin jikin shi da kanta kuma a karon farko, taji ta iya sakin jiki dashi batareda kunya ko nuku nuku ba, Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zaman shi dakyau tareda rungume ta gam a jikin shi shima, “Wow Naziya sarkin kunya yau ta rungume ni haka? What a lucky day, kice intashi ingirgice kawai mu shige daga cikin dakin mu yau. Sunne kanta tayi cikin kirjin shi tana jin kunya, tareda kokarin tashi ta gudu, “no karya ne yarinya kinkawo kanki don haka let go inside ki bani Abinci inci domin rabona da Abinci tun shekaran jiya, “why? Tafada cikin damuwa, “because am worried about you kullum Ina tunanin Ina shiga hakkin ki idan namutu ubangiji zai tanbayeni hakkin ki Naziya, kiyafemin kinji. “No bakayi min komai ba, muje in hada maka Abincin kaci, akwai komai a ciki ne? “Yes let go, yafada yana Rungumo kugunta. Ya dade a tsaye yakasa shigowa falon yana ganin yanda take shigewa jikin Ahmed, komawa yayi kan kujera ya zauna tareda runtse idanun shi gam only God knows what is going on in his mind,

Dagewa tayi ta shirya mai girki lafiyayya domin takara zama expert yanzu saboda shine kawai aikin ta a gidan, yana biyeda ita har cikin kitchen din, yana shige Mata harta gama yace suje falon domin yaji muryar khaleel na waya, kuma shima tunjiya baici komai ba saboda yaga yayan shi baici ba, tayi mugun jin haushin shi domin ya katse musu lokacin mai dadi ta hanyar zuwa musu gida,
Fitoda komai yana tayata, yana zaune a wurin batareda ya motsa ba, idanun shi a rufe har suka jera Abincin, tana gefen Ahmed yasa hannu ya cire hijabin jikinta batareda ta shirya ba, doguwar riga ce a jikinta mai kyau ta kanti, wadda ta d’an kamata shiyasa take yawo da hijabin, saurin kallon shi tayi tareda narke fuskar ta “kana so ingudu ne? “No wife inaso inyi kallon matata ne, Kinga yanda kikayi kyau, and,,ya matsa daidai kunnen ta ya rada mata “this your chest baby please agama abani hakkina I need them very badly.
Hannu tasa ta datse fuskar ta tana girgiza kai, “Allah zantafi fa. Cikeda wata irin murya mai daukeda tsantsar shagwaba mai burge y’an maza, Wanda saida khaleel ya daure ya kalleta, a yau yake ganin dariyar ta da kyau hade da farin cikin ta, he feels a little happy one side, ga dimple d’in ta wow,. “Yaya Am hungry yafada domin katse moment din, “let eat brother, ta zuba musu tareda cewa “wannan Abincin ai wasu basu san dadin irin shiba, oh zaka iya cin Abincin mu na Nigeria ba kyankyasai ba. “For the first time a lokacin yaji wata irin dariya tazomai, shima Ahmed Saida ya dara, “ke Waye yafada miki sunan su kyankyaso? ” oho nidai ai mutum ba Abinci yakeci ba sai tarkace, daga kunama sai k’wari.
“Hmm, kawai yace yafaracin Abincin shi batareda yace tak ba yaci sosai saida ya kusa cinyewa tace “little brother inkara maka ne? Dago kanshi yayi ya kalleta wani iri kafin yace “am OK Aunty babba tanks. Ya mike, “Wow Wato kasan Aunty karama na zuwa ko? Harara ta watsawa Ahmed d’in tareda daukar hijabin ta ta Mayar, zata wuce. “Wait my Hajiya ai muje a yimin wanka ki karasa ladanki tukuna.
Kokarin tafiya takeso tayi, khaleel yace “Yaya please let her go kafin mommy ta ankare. “Muje intayaka tafada kai tsaye, domin batasan meye matsalar shi na yimusu karan tsaye ba yanaso ya hanata sakewa a lokacin da ta samu damar ta,

“Toh munafuka Y’ar gidan masu kwana kan buzu, zoki fita shashasha, ko kunya an narkawa yarinya dukiya kinzo kin shige, zo ki wuce, kai kuma Ahmed idan ka wuce iyakata banyafe ba, kaima khaleel dakai ake haduwa anamin bita da kulli, kuzo ku shirya ku tafi daurin Aure, in mace ce matsalar ka Ahmed na zabo maka ta kece raini ba wannan Y’ar shilar ba, koma daka nayi baki. Da gudu ta fita while khaleel ya wuce Abinshi batareda ya tanka ba Ahmed ma haka ta karaci sababi tareda turo masu aiki su Kara gyara duk Abinda aka bata a turare shi.
Saida ta shaki kukanta ta tashi tayi wanka ta caba Ado wayar ta ta dakko taga sakonnin shi da basa taba rabuwa da wayar ta, “Am sorry matata idan muka dawo zankira ki mu fita shakatawa kinji. Dariya tayi kamar dagske yanzu mommy nace wa Ahmed zai sunne kai, “my gentle man. Tafada cikin nishadi, so hana ganin laifi,

Biki yayi biki ko Ina ba masaka tsinke a cikin babban birnin na kano a yau Auren yaran manyan mutane guda hudu at once, ga kuma Y’ar masu kasa Wato fauziya,
Daurin Aure ne Wanda ya jirkita garin ba kadan ba manyan baki ta ko Ina, kawu wakilin Angwaye Wanda baisan da zancen Auren Salifa ba sai ranar Auren, ya fara fada kamar zai Ari baki, har cikin gidan yazo ya kirata “Hajiya bilkisu halina na nan, yanzu saboda Allah yaro Aure wata biyu kisa ya karo Aure? Hajiya bilkisu kiji tsoron Allah. “Toh nidai bani nasa yaron nan Karin Aure ba ka kirashi ka tanbayeshi. “Koda bani na haifeshi ba jini nane nasan halin Ahmed nasan tirsasashi kikayi kuma Ina gargadinki da kibi a hankali. Shigowa Khaleel yayi ya zauna tareda gaida kawun yace “don Allah kasa baki ta bar yarinyar ta tare a part d’in ta kafin wata tazo kuma kawu ai itace uwar gida yakamata ace ita tafara shiga wancan gidan. “Yanzu kokarin kai karata kakeyi Ibrahim, Wato ya turoka kazo kasa kawunku ya yanke ni toh ka koma ka fadamai wallahi sai Salifa ta shiga Wannan gidan kafin Wannan Y’ar gidan malaman ehem. Tayi fuuu ta shige, ya so ya cire son zuciya ya agaji yayan shi amma mommy, Hmmm. “Khaleel ku shirya mu wuce ka Kira d’an uwan ka, mu ake jira,. Yafada domin lokaci natafiya kuma suntara manyan Kasa harda mai kano baki daya, kuma zai dawo mata idan komai ya natsa.

Andaura Auren fauziya da Khaleel sai kuma Salifa da Ahmed, Wanda akan sadaki mai matukar tsada akan miliyoyin kudi, domin gadarar mommy, Wanda Ana gama daurin Aure angwayen suka dawo dakunan su kowa kajishi shiru, ba wani motsi, lokacin da aka Kira mommy andaura ta rangada guda tareda kawayen ta, kannin mijinta ne suka iso suna Allah Sanya Alkhairi badon sun soba, babbar tace Ina uwar gidan Ahmed d’in? Tana nan zuwa anjima za akawo ta. Mommy tafada da gadara, “Hmmm Allah ya shiryeki bilkisu Wato harda yayan mu bai duniya baki canja bakin hali ba ko?, to wallahi sai Kinga sakamako idan kika cutarda Y’ar mutane. “Toh ku dama wayake taku dama ai duk kannin miji y’an bakin ciki ne don haka ni yau banda lokacin ku nayiwa ya’ya na AUREN GATA.
Taci gaba da guda, dakin Ahmed suka nema inda suka sameta zaune yan uwan ta sunzo tana ta walwalar ta ta fauwala wa Allah, Wanda ta mugun burgesu zama sukayi a dakin suka sake sosai sukasha hira anan suke fada mata su gwaggwnin mijinta ne, ta saki jiki ta kula dasu itama dasu Aunty Raliya sai hira sukeyi.
Damuwar ta kadan ce zuciyar ta na wurin Ahmed batasan halin da yake cikiba Wanda saida yakira likita ya dubashi yace “gaskiya Ahmed idan zuwa gobe bakaji sauki ba kazo Asibiti ayima xray saboda ciwo a kirji yanada matukar Matsala.
Godiya yayi yasha maganin shi ya kwanta yayi bacci sosai har magrib.

Taro ya ragu zuwa Karfe bakwai duk taron Naziya sun watse sai ita kadai, yau ta yabawa d’an gin Ahmed harda y’an gidan kawu gefenta suka tare sun share mommy da gayyar ta, yanzu bakajin komai sai kai da kawon su Aunty zarah iyayen ango,
Takwas aka kawo Amare Wanda kafin Wannan lokacin ba Wanda yasan inda angwayen suke.
Main house aka shigo dasu cikeda guda Wanda tanaji, a take wani kuka yazo mata, shikenan rayuwar da tafara mafarki watace zatayi da mijin ta, shikenan sun samu third party tunkafin su mori Auren su.
Saida suka gama feshe feshe kafin kai Amaren gefen su wainda kowacce cike take da tata salon rashin kunyar hade da rawar kai………. 🖊

*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus: 🌻🌻AUREN GADO🌻🌻

 

*Matar soja ce*

 

Daga marubuciyar
KUKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
Y’AY’AN GATA
And now AUREN GADO,

Ga masu son su biya ga account details dina, * NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* sai Ku min magana ta wannan number 09069200154

 

 

 

Back to top button