Banana Island Hausa NovelHausa Novels

Banana Island 7

Sponsored Links

.Sunana Mohammed Adnan J. Babana bafullatanin Yola mamana Baturiyar ƙasar…” katsesa Tayi da sauri

“Meye J. Ɗin”

“Jalaludden..” jinjina kai tayi “Nice one sunan yarona na fari kenan ,Jalal sunan ƴan gayu”

“Bakince ƴan biyu sau bakwai zakiyi ba ko kin fasa?”

“No!… Hassan da Hussaini sai su koma Jalil da Jalal ”

Jan Numfashi yayi “Hmm… Nayi Nursery zuwa primary 2 a 9ja Daganan sauyawar aiki ta maida babana Uganda anan na gama primary dina ,natafi turkey acan nayi secondary ɗina ,Daganan na wuce U.S.A nayi karatun degree ɗina na farko inda na karanci tuƙin jirgin sama,a degree ɗina na biyu na zama technician …”

“Yanzu ka iya tuƙa jirgin sama kuma ka iya gyara shi ?” jinjina mata kai yayi.

“Amma me yaja ra’ayinka na zama pilot despite all the scientific courses we have?”

“challenge!… I told you na tsani mota tun ina ɗan ƙaramina lokacin ina schooling a Nigeria ,daga ranar da mota ta lalace ban sake hawa mota ba har yau ,infact na tsani mota …wannan dalilin ya samun jin dole ne in koya tuƙa jirgi Kinji dalili….bayan nayi degree na farko I now come to think of business ,Amma banason kasuwancin da kowa yikeyi I believe on ka bauɗe a abunda mutane keyi zaka sanu…hakan ya sani shiga makarantar koyar da sana’a a ƙasar China ,na faɗa masu kalar business ɗin da nikeso suka sani a hanya ,babana kuma ya ƙarfafeni da jari na fara saida jirage da farko daga baya kuma har na kai matsayin da muke kai a yanzu.”

“Ku nawane a wajen iyayenku? ”

“Ni da ƙanwata tayi aure shekaru biyu da suka wuce tana da yaro daya da mijinta yanzu haka suna Spain da mijinta ”

Turo baki tayi cikin sigar shagwaɓa “Uhm baka iya bahaka wai ake bada labari?”

“Ya ya kamata in Yi?”

“keep doing shaaaa…baka faɗa mun ina iyayenka suke ba”

“ok Iyayena suna zaune a Asokoro garin Abuja a halin yanzu ,nan ne permanent gidan mu a Nigeria amma kinsan wanda suka saba da yawo so ina jin muna da gidaje a ƙasashe kusan 23 including Saudi,America,England ,India da Dubai saboda sune ƙasashen da mukafi zuwa…

Abun zai baki mamaki in Nace maki na taɓa aure…I mean nasha yin aure amma auren baya lasting yake rugujewa tsananin sa sati guda ,dalilin haka yasa na ɗebi aure na watsar ,na cigaba da Addu’a Allah ya kawo mun mata daidai Ni ,wannan dalilin yasa mutane da yawa suke ganin kamar bani da feelings ne wasu kuma suyi mun sharri suna cewa wai Ni ɗin ɗan luwadi ne (gay) shiyasa mace bata dameni ba…but in a real sense matanne ba type ɗina bane…tun Ina aure da sanin dangina yanzu ma na daina”

“Kaiko wani irin matsala kenan kake dashi”

“Sha’awa…jaraba….harijanci!”

Rufe fuskar ta tayi da sauri

“Ki buɗe fuskar ki magana muke na gaskiya da gaskiya ina fucking mace badly they use to undergo surgery Amma a banza last su da kansu suke demanding saki….ummata tanason Taga na yi aure na zauna da matata amma bata sanin dalilin rabuwar mu Ni kuma ban taba gaya mata ba”

“Allah ya kyauta Ubangiji ya baka mata daidai kai ”

“Ai na samu mata saidai kace Allah yasa matar nawa ta jure nauyina”

“wacece ita aina take zaune kuma ,a banana island? Unguwar ƴan gayu?”

“kinason banana island ko?”

Jinjina masa kai tayi kawai saboda wani abu mai suka da taji ya turnike mata rai me kamada kishi tunda ya furta mata yina da mata

“karki damu zaki iya rayuwar ki a banana island”

“Ni talaka ce bazan taɓa auren mijin da ya fito daga upper class ba,so ta Ina zan zauna a banana island? Wajen da ma zamushiga da mai keke ne mu cire ƙwarƙwatan ido aka hana mu shiga…” tayi maganar cikin rauni idonta ya ciko da ƙwalla

“Me ya sauya ki nan take? ”

“Babu komai wallahi…muje ka kaini wajen mamata ka maidani makaranta mun dade tare nasan daga yau bazamu sake haduwa ba ko? Matarka bazata yarda ba”

“hmm kishi”

“Kishi? Dawa zan kishi”

“Ni mana”

Girgiza masa kai tayi “A’ah”

“ok ya isa ,baki tambayeni me najeyi a garinku ba kuma ya akayi na dauko Ummanmu na kawo ta asibiti”

Tagumi tayi ta zuba masa idon da tara masa ƙwalla duk karsashinta ya tafi

“Tun da muka rabu dake a ranar farko na haduwarmu naji na kwadaitu da Son kasancewa dake kawai surarki ta burgeni komai naki mai kyau ne ,gashi na bukaci sanin wani abu a kanki Kinki bani haske sanadiyyar hakan ,naje school dinku aka bani bio-data dinki,naje har garinku ,ban taɓa sanin talauci ba sai a ranar ,naso a bani umma in Tafi da ita nearest Asibiti fafur en rugan suka ƙi .nikuma abun ya dameni don haka naje nayi magana da Sarkin Gombe wanda ya kasance Aminin babana,yazo har ruganku yayi masu magana a bani umma in Tafi da ita ,Nan suka fara jero mun tambayoyin tuhuma wane ne Ni? Nace saurayinki ne…naji Haushin yanda suke zaginki wai dama zaki aika Karuwanci a Lagos the thing pain me….hakan yasa banyi dogon shawara ba nace masu ai ke kikace inzo neman Aurenki shiyasa ma na kawo sarki ya zama waliyyina , basu wani yarda dani ba aka daura mana aure ,nidai duk burina a bani umma mu tafi amma sai suka ce bazasu iya bada ita gareni ba ,wai zan saida itane,saidai in Za’a tafi dasu duka….Yes i promised them on that na ɗebe su duka motar mocopolo guda muka shigo garin Gombe ,saidai ina ganin babbar doctor ɗin dake garin yace mun shawara in kawo umma India sune suke da ƙwararrun likitoci ,wannan yasa na damƙa ma PA dina ragamar tafiyarsu na koma wajen aikina,bayan sati guda akayi masu duk cuku cuku suka taho India ,yanzu haka mamanki da family dinki duka suna ƙasar nan sai mamanki ta warke zasu koma kuma Alhamdulillah likita yace tana samun sauki don tana magana tana motsa ƙafafuwarta inshort ana mata passive exercise”

Tunda yake magana ta zabga uban tagumi batace komai ba ganin duk maganar da yakeyi kawai mafarkine let her not to be foolish ta farka ta ganta a gadon hostel ,all her dreaming become vanished

Washe mata baki yayi gamida blowing Iskar bakinsa a kusa da fuskar ta wannan ya sata ɗan yin firgigit

“Yadai?”

“Humm ”

“I’m sorry na Aureki ba tare da consent dinki ba”

“Adnan wake me up from this foolish dream”

“ba mafarki bane gaskiya ne babe and na Aureki ne saboda kauna ba wai don tausaya wa ba

 

Oum Aphnan
09065990265️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_

Book 2
Page *C*

Na…
Oum Aphnan ✍

“`Littafin kuɗi ne ,in kika fitar mun dashi kin cutar dani“`

Back to top button