Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 8

Sponsored Links

Page8️⃣

 

Ahankali yace ya Isa please okay kawai tace mishi tabar wajan bin bayanta yayi da kallo Yana girgiza Kai wannan yarinyar daga gani zatafi zeenat rashinji juyawa tayi ahankali tanaso tasaci kallonshi karaff suka hada ido mugun kallo yawatsa mata murguda mishi Dan karamin bakinta tayi mikewa yayi aharxuke ganin datayi wajanta yanufo aikuwa tafara kokarin guduwa taku biyu yayi yacafko ta yaja hannunta har bakin gadonshi kafin yatsareta da ido ke wakike harara cikin fuskan shagwaba tace nifa bada Kai nakeyi ba to dawa kike inbadani kike ba nida wancan filon nakeyi juyawa yayi yakalli filon yace okay tunda ke karamar mahaukaciya ce maza bawa filon hakuri zaro manyan idonta tayi waje gyada Kai yayi yace yes bashi hakuri Kuma karki yarda kibari wajan nan se filon ya hakura. Kwanciya yayi abinshi itakuwa FANAN tafara bawa filo hakuri tun tanayi ta dadin Rai harta fara kuka idonshi alumshe Yana kallon duk wani motsinta juyowa tayi setaga alaman yayi bacci sanda tafarayi takarasa kusa dashi ahankali tace yauwa yayi bacci juyawa tazoyi zata gudu tsantsi yakwasheta tafada jikinsa kan faffadar kirjinshi cikin sauri tafara kokarin tashi zagayo da hannunsa yayi ya matse kugunta ajikinshi yar Kara tayi sbd tadanji zafin rikon dayamata matso da fuskanshi yayi gaff danata har sunajin saukar numfashin juna ahankali yabude Baki kamar bazeyi magana ba yace meyakawoki jikina kika kwanta dasauri takalleshi ganin yanason mata sharri hararanshi tayi tace mekuwa zanzoyi jikinka hannu yasa yamatse mata Baki yarinyar nan naga kamar kinaji da tashen balaga Amma karki damu kafin inbar asibitin nan sena gyara miki zama takasa magana kawai SE hawayen dakebin kuncinta kallon cikin kwayar idonta yakeyi kafin yamaida kallon nashi libs nata da take tacizewa ahankali tsabar azabar rikon dayamata kokarin tashi tafarayi da iya karfinta Amma ko motsi beyiba seda yatabbatar tagalabaita kafin yasaketa yace tashi kibarmin jiki mara kunya kawai mikewa tayi tana share hawaye ahankali taje tadauki hand back dinta tasa facemask ko kallon inda yake batayi ba tabar dakin sauri sauri take tafiya yau ko takan Kiran Amira batayi ba tawuce gida shigowa tayi da sallama abakinta bata samu kowa afalon ba tashige dakinta kawai tacire kayan jikinta tafada toilet tayi wanka tare da alwala tafito tana tuna abinda azaad yamata kwafa tayi kawai ta tada sallah bayan ta idar ne tafito tasamu kowa ya hallara afalo gaidasu tayi amsawa sukayi suna tambayarta ya aiki alhamdulillah kawai tace auta ce tazo kusa da ita tazauna anty Ina tsaraba na laaah wlh auta namanta Amma in sha Allah gobe zankawo miki ko tom shikenan anty, abinci suka fara ci bayan sun gamane baba yace yauwa namanta banfada muku ba su Al ameen gobe zasuzo gombe fah cikeda murna tace allah yakawosu lafiya tsabar farin ciki tarasa inda zatasa ranta domin kuwa ba karamin good time sukeyi da ya al Ameen dakuma suhaima kanwarsa, sudin yaran kanin baba ne. Ya usman ne yamikawa fanan wata leda me kyau da ita kayan cosmetics ne aciki sesu perfumes godiya tamishi aka cigaba da hira nan taji wayarta na ringing dubawa tayi taga wayene ganin my bestyne yasa tayi saurin daga kiran suka gaisa bestie ya akayi yau Baki jirani ba kokin koma gida dawurine eh kekam wlh inada wata uzurine shisa nadawo banbiyoki ba to shikenan bakomai SE gobe kigaida mama okay zataji, tashi fanan tayi tace musu seda safenku allah yatashemu lfy suka amsa shiga daki tayi tabude ledan Da ya Usman yabata powder ce mekyau dasauran kayan kwalliya lotion tafito dashi Shima mekyau SE Kuma turare masu dadin kamshi murmushi tayi tace allah sarki ya usman allah yakara budi jera kayan tayi agaban mirror gadon tahau tafara game din Angela.

 

Washe gari bata bar gida ba SE 11:30 ta tafi hospital shigowa tayi tasameshi Yana breakfast Ina kwana tace mishi ko kallonta beyiba balle tasaran ze amsa bakin desk Dake dakin taje ta dauki magungunansa ta mika mishi da ruwa karba yayi yasha SE asannan ne yadago Kai yakalleta jeki daukomin tissue ko kala batace mishi ba takawo mishi ta ajiye akan table din gabansa suna haka doctor ammar yashigo gaishesa FANAN tayi ya amsa yamata yamejiki kafin yaje yamikawa AZAAD hannu sukayi musabaha yamishi y jiki kafin yace AZAAD akwai yar matsala fa kallonsa yayi yace name kenan ummi ba lafiya jiya naje nadubata jininta yahau Amma yanzu dasauki mikewa yayi yafara tafiya dasauri Ammar yatsayar dashi karka tafi yanzu AZAAD karkayi wannan gangancin kasan rayuwarka tana cikin hatsari Kuma haryanzu baka gama komawa Dede ba cikin tsawa yace I don’t fuckin care ummi bata da lafiya sannan kanacemin intsaya mtsssw dogon tsaki yaja yafito yabar dakin dasauri Ammar yabi bayanshi Dan yasan halin azaad yanzu seyace zehau taxi shibesan yanda ake farautar rayuwarsa ba FANAN kam tunda yadakawa ammar tsawa tayi sumar tsaye domin aduniya tsawa Yana Daya daga cikin abinda yake birkita mata lissafi tana Daya daga cikin mutanen dabasa jure tsawa yanzu zatafita a hayyacinta. Dogon numfashi taja duba dakin tayi taga bataga kowa adakin ba yatabbatar mata dasun fita itama fita tayi taje addimission ward tana duba patient’s. A waje kuwa dakyar Ammar yayi nasaran dakatar dashi azaad kadakata kajini tsayawa yayi kashiga mota muje inkaika gida Amma is very dangerous kahau taxi shuru azaad yayi be tanka mishi ba Yana tsaye a inda yabarshi ammar yazo da motor shiga yayi suka kama hanya babu Wanda yacema Dan uwansa kala, cikin gra suka shiga anguwar dayake dauke da manya manyan gidaje nagani nafada wata Dan karerin gate naga hancin motarsu tanufa security ne da sojoji abakin gate din suna gadi kasancewar sunsan doctor ammar shisa suka wangale mishi gate shiga sukayi wata dankareriyar gidane wacce Tasha kudi tundaga Bakin gate zaka gane wanann gidan bana kana nan masu kudi bane domin anyi barnan dukiya kamar baa kaunarsu parking space yaje yayi packing din motarsa fitowa sukayi atare azaad nagaba Yana sanye da facemasks afuskanshi tafiya yakeyi cike da izza da takama falo yashiga da sallama abakinshi kasa kasa ya Salam nikam sumane kawai banyi ba ganin aljannar duniya kamar baa Nigeria ba falone na alfarma Wanda yaji kayan alatu komai na more rayuwa akwai sa aciki. Ganin dayayi bakowa a falone yasashi haurawa upstairs yanufi dakin ummi abakin kofa yatsaya Yana kallonta tana kwance akan gado idonta alumshe kyakyawar balarabiya ce Wanda kana ganinta kasan tabbas wannan itace tahaifi azaad ga kannenshi azagaye da ita harda first born dinsu itama tana zaune kusa da ummi hannunta acikin nata sunyi jugum shigo dakin yayi babu Wanda yalura dashi kama dayanda hannunta yayi ahankali yafurta ummi arazane dukkansu suka dago suna kallonshi cire facemask din fuskanshi yayi mikewa sukayi tsaye suna nunashi da hannu Banda ummi data kura mishi ido tana hawayen farin ciki rungumeta yayi yanadan bubbuga bayanta cikin rada yake fadin am sorry ummi am so sorry areef ne yayi karfin halin fadin ya azaad dama kana Raye baka mutu ba kafin fawwaz yace Yaya dama kullum ummi maganarta Daya ita tasan AZAAD dinta be mutu ba fadawa jikinshi zeenat tayi tana kuka…..

 

SE munsake haduwa
Muhadu a comment section

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by (MRS ISHAM )

 

Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

 

____________________________________________

Back to top button