Miskili Ne 53-54
❤ *MISKILI NE*❤
*53&54*
……. Ahankali Amaan ta murd’a handle k’ofar ta shigo da sallama can ciki”shariff na zaune kan 2 seeter ya Aza k’afa d’aya kan d’aya yana danne danne Awaya”Amaan ta bishi da kallon so had’e da burgewa tana jingina bayanta Ajikin k’ofar “saida miskilin yad’ago kansa sannna ta janye idanuwanta daga barin kallonsa”cikin tattausan muryansa ya Amsa sallamar tata yanata kallonta yace”k’araso mana,ko nazo na d’aukeki ne?”yafad’a ko Ajikinsa “ita kuwa d’an murmushi tasaki tana mamakin meyasa beda kunya kuma baya b’oye Abinda ke ransa?…..bata gama wannan tunanin ba taji sautin takunsa da sanyayyan k’amshin turaren jikinsa”da sauri ta kallesa k’irjinta na bugawa….”kin d’auka wasa nakeyi ko?”girgiza kanta tayi tana d’an turo baki ta matsa sbd ganin yanufota gadan gadan “tab’e baki yayi yabiyota suka zauna kan kujerah”yana k’ok’arin yimata mgn wayarsa tayi ringing”d’auka yayi be Amsa sallamar sadeeq ba yace”kun shiga theater room d’in?”sai kuma yaja tsaki cikin fad’a yace”bance maka ba karku yimata Aikin?”tab’e baki yayi yana fad’in damuwarta ce”daga haka ya yanke wayar yana kallon mutuniyar tasa dake sauraren wayar tasu “yanzun kuma hijab Aka saka mun?”uhmm”wacece za’a yiwa Aiki?”tab’e baki yayi yana fad’in wata shed’aniya ce data Aikata sab’on Allah ! subahanallahi “nasan ke bazaki san taba”sunanta fareedah “y’ar lesbian ce ita”shine kyandir ya shige mata sukazo Asibintin sadeeq”Aka wuce da ita emergency theater”za’a shigane na kirashi yake sanarmun zasu shiga yiwa y’ar gidan marigayi isah tafashiya theater”shine na tambayesa sunanta yasanar mun….to hamma taya kasan meta Aikata?”labarin nada tsayi salfad “ni Allah saika sanar mun kona ce nafasa yin soyayyar dakai”ta fad’a cikin shagwab’a “murmushi yasaki yana fad’in wannan kuma ke baki isaba yarinya”sbd maganar farko itace sarki ke Amsa dama kowa gaba d’aya”to Ai yanzun ba’a gabansa muke ba”nidai Allah kafad’amun”to naji sai kinmun Alk’awarin baza kiyi fushi ba?”fushi kuma? Eh mana”to shikenan hamma Ai na yarda dakai”zamansa yagyara ya shiga sanar mata yadda ya had’a soyayyar k’arya da fareedah sbd yana son gano waye mahaifinta da Abinda yake Aikatawa??”har zuwa yadda aka saceta itada matar mus’ab duk mata bayani….”Allah ya kyauta ya shiryeta”Amma ni hamma banga laifin sadeeq ba tunda be saniba”fatanmu Allah yasa hakan yazama sanadin shiriyarta”tab’e baki yayi yak’iyin mgn “Ina yaya mus’ab?”yakoma masau kinmu ne sbd yabarni na wala na sanki da k’auyancin fulatanci na kunya”hmm! babu komai” toshi wannan marar mutuncinfa?”d’aure fuska yayi yak’i yin mgn “kayi hak’uri hamma dan Allah yaci darajan su daddy”banaso dangin mahaifina suga laifinka”ta fad’a kamar zatayi kuka”wato kina tausaya masa ko?ah ah wlh hasalima na tsanesa”bayan iyayena sai kai kawai nake tausayi… murmushi yasub’uce masa yabita da kallo yace”to ki fad’amun I love you too kuma kina kallonah”gaskiya bazan iyaba”meyasa?”toba kunya zanjiba”ni meyasa banji kunyar fad’a miki ba?”to ai kai ba….sai tayi shiru”banida kunya ko?”shikenan mubarsa A hakan, nan bada jumawa ba zaki gane hakan…dan Allah mekake nufi?”dariya yaka mayi yana haskata da wayarsa”ta kare fuskarta tana masa shagwab’a”shidai yama kasa mgn sbd idan tana masa hakan wani iri yakeji Ajikinsa be kuma son ta dena masa shagwab’ar….ilove you too salfad”da sauri ya Ajiye wayar saman cinyarsa yana matsowa dab da ita yafara tafa hannayensa yana fad’in inye salfad d’ina ta waye”yadda yayi Abin zaki d’auka irin yarone shi kamar Abdallah “Amaan ta kama yimasa dariya sbd ya burgeta Akwaita dason shirme”kinsan wani abu?”uhmm uhmm” idan An kamun ke gidana zamu dinga yin….nidai banace bana son maganar ba”to shikenan naji nadena”wacce kikeso Ayi?”nidai gobe kaje Amaka Aski sannan kazo kayi break fast saimu d’an fita ko?”Amaan d’ina rigima”Amasau kinmu zamuyi break fast banaso ki wahala idan nazo da safen saimu fita naga garin naku yaya yake ko?”uhmm” Amma 2days zakayi sannan ka tafi”to shikenan zamu gani idanda yuyuwar hakan”ni nafiki buk’atar kasancewa dake Amaan”dakin san k’uncin da zuciyata ta shiga na kewarki dakin tausayamun”Koda natafi dole duk week end nadinga zuwa na ganki ko?”to zaka dinga kwana idan kazo?”No! ta jirgi zan dinga zuwa na koma ta jirgi”niban yadda ba Allah “cikin wata iriyar murya yace”to fad’amun yakikeso Ayine tawan?”saida tad’an kallesa tayi k’asa dakai kafin ta turo baki cikin yarinta tace”nidai nafison kazo kayi kwana 2″shikenan idan naga da halin hakan babu damuwa zanyi salfad”yanzun k’arfe nawa daddy ke shigowa?”da k’arfe 9 ko tara da Rabi”wai kummaci Abincin?”munci baby nah dukda nasan bake bace kikayishi”hakane Amma gobe nice zan had’a muku break fast”to shikenan Allah yakaimu” ga Ammi nan zan kirata saiku gaisa ko?”haka nan yau ta tsintsi kanta dajin kunyar Ammin”shi kuwa duba time yayi yana kuma dealing d’in number d’in mus’ab “bugu ukku ya d’auka”Anutse yace”zaka iya zuwa yanzun sbd daddy yakusan dawowa “yana fad’in hakan ya yanke wayar yana kallon ta yad’age gira sama yana fad’in”itama Ammin kunyarta kikeji ne?”shiru tayi tak’i mgn”ya matso yaja karan hancinta “d’an matsawa nesa dashi tayi Ahankali tace”Ina wannan Ibtihal d’in take?”ita kika tuna kuma?”uhmm”tana can yawan banza dana shaye shanye Ayadda naji labari na kuma gani da idona”tab’e baki Amaan tayi sai kuma tasaki murmushi…kin tuna fad’an ku da itane?”Eh mana hamma”wlh kana ji dani sosai”ke kuma bakyaji dani ko?ko kuwa sai munyi Aure?”k’in mgn tayi ta sunkuyyar dakai”yanata kallonta yana kissima Abubuwa masu wuyar fad’a Azuciyarsa”shi sai yanzun yaji garama ya Auri k’aramar yarinya wacce sai yadda yayi da ita….hmm! kana mgn ta kaida zuciyarka ko?”meyasa kika gane da sauri haka?”zuciyata ce tasanar mun”hakane salfad”sau da dama nima zuciyata tana yawan sak’amun Abinda kikeyi idan na fad’a yazama daidai”Amma meyasa kike zuwamun a mafarki?”da mamaki Amaan ta kallesa tana k’ok’arin mgn mus’ab yamusu knocking”hakan yasa tayi shiru”shariff yabashi damar shigowa cikin parlourn “kafin ya tsura mata Ido yace”kira ko yusuf ne muji daddy yadawo ne?”yamafa dawo hamm….bance bana son hamma ba?”d’an murmushi tayi “Adaidai nan mus’ab yashigo”gaidashi tayi ta mik’e tsaye ta fita…. Abokinah kadena zama gab da y’ar mutane wlh” karkaje ka kama musu yarinya wl…shiru yayi sbd pillow d’in kujerar da shariff ya wurgo masa yana yatsina fuska yace”Angaya maka kowama irinkane jarababbe? da bakada Aiki kullum kana kan mace”dariya mus’ab yadin gayi yana fad’in lokaci zai nuna nida kai wayafi wani jarabar dakake fad’i “banza shariff yamasa yana danna waya”Ahaka daddy yashigo da sallama”suka Amsa suna sakkowa k’asa kan carpet suka zauna suka gaisa dashi”daddy yayi gyaran murya yana fad’in naji dad’in ziyararku shariff “sannan naji dad’in yadda ka d’auki mataki kan Nasir”Ina rok’a masa Alfarmar kayi hak’uri zuwa gobe da safe kasaka su sallamesa”kansa Ak’asa yace”to shikenan daddy “mus’ab yad’an muskuta yana k’ara sunkuyar da kai yace”dama daddy munzone harda dalilin shariff naso Abashi dama yaturo magabatansa sbd suna son juna da Amaan”to kuma Abinda yafaru d’azun yasaka yana neman Alfarmar in ka Amince gobe iyayensa zasu iso su kawo kud’in gaisuwa Asaka rana….shiru na kusan second 15 daddy yayi kafin ya sauke Ajiyar zuciya yace”Alhamdulillah! naji dad’in wannan mgn sosai mus’ab “na kuma yaba da tarbiyan shariff babu matsala zasu iya zuwa Allah ya tabbatar da Alkhairi”Salma ko nace wacce kukafi sani da Amaan ba wata babba bace yarinya ce ita”inaso ka rik’eta Amana dan Allah shariff”dukda dai muba wasu bane na Amince ne nabaka ita sbd nasan itama tana sonka…insha Allah daddy bazaka sameni da wata matsalaba”koda bance Ina son Amaan ba zumuncin daya had’amu nime rik’eta ne “hakane sharif”to Allah yayi muku Albarka “suka Amsa da Ameen”ya mik’e tsaye yafita”shariff ya sauke nauyayyar Ajiyar zuciya”mus’ab yakama dariya yana fad’in kaga goma saura katashi muje mu kwanta saika kira su Abban suzo ta jirgi”nafison zuwa 4 pm munbar garin nan Ango”Amma dai kasan dole sai nayi sallama da baby nah ko?”hmm! shariff kenan”wlh idan kana haka sai naga kamar bakai bane MISKILIN nan dana sani”d’age kafad’a yayi yana fad’in ko yanzun miskilanci nah yana nan”sbd Ance hali zanan dutse” Amaan d’ina ce kawai bana mawa”itama sadda kamata kayi mata”shiru yayi yamik’e tsaye yana k’ara wayarsa Akunne yanufi k’ofa “yana k’ok’arin fita ita kuma tana k’ok’arin shigowa”Aikuwa ta fad’o jikinsa….da sauri ta matsa k’irjinta na bugawa”shariff ya rik’e tafin hannunta guda cikin nasa….ji tayi kamar an zare mata duka lakkar jikinta”sakama kon canjin dataji Ajikinta”da k’yar tafara k’ok’arin k’wace hannun batare data yadda ta kallesaba”saidai yak’i cikawa yatsareta da narkakkun idanuwansa yanata binta da wani irin mayen kallon daya haifar mata da kasala da mutuwar jiki lokaci guda…”pls hamma kar su hamma yusuf su ganmu”bece komai ba yacika hannun nata”saidai tak’i yadda ta kallesa”Ahankali tace “dama saida safe nazo nayi maka”meyasa baraki bini ba kitayani kwanan?”ni kuma?”yana k’ok’arin mgn sukaji muryar mus’ab yana fad’in pls Akwai sanyi kazo mu wuce”kaje Ina zuwa”mus’ab ya kalleta yamata sallama ya wuce”ita dai kanta ak’asa tana jinta wani iri tunda ya rik’e mata hannu”salfad! uhmm”zan tafi”saida safen?”bashi nakeso ba”to me kakeso hamma nah?”shikenan kinmun Abinda nakeso”meke kenan?”shagwab’ar ki mana”rufe fuskarta tayi tana dariya ta wuce aguje”yabita da kallo yana murmushi “saida yadena hangota sannan ya juya yabar wajen…. mus’ab nata tsokanarsa har suka iso masaukinsu ko wane ya wuce d’akinsa “maimakon shariff yayi shirin kwanciya bacci ,ah ah,saiya kafa sabuwar waya da Amaan”basu dena wayar ba saida yace”wai idan tayi bacci tayi mafarkin yazo sun kwanta suna bacci”hakan yasa ta yanke wayar sbd kunya”lokacin karfe 11:12 pm”sai wajen 11:30 pm shariff ya kwanta”da Asuba kuma suka cigaba da wata wayar”bayan sun idar Amaan ta wuce kitchen “shi kuwa bacci yakoma”
k’arfe 9:17 sharif da mus’ab na tsaye bakin titi sun fito daga cikin hotel d’in da nufin su tafi gidansu Amaan”mutumin naku ya wanku cikin farar sabuwar shadda”wacce Akayima Aikin hannu da b’akin zare”ba k’aramin haskashi kayan sukayiba”mus’ab nata tsokanarsa da Ango Ango!!”shi kuma yanata Azalzalarsa yazo su wuce kar Amaan ta gaji da jira tayi fushi”suna Ahaka ta kirashi”yana d’auka tasaki kukan shagwab’a…..”kinga ya Isa haka my salfad” munafa kan hanya”wlh banci komai ba”girkinki kawai nakeda muradin naci”Ina fatan kinmun make up?”to zakiyi hugging d’ina?”murmushi yayi sbd jin ta yanke wayar “mus’ab yabishi da kallo yace”SO(book d’ina) yasaka ka canza”yanzun y’ar yarinya kamar Amaan kakema rantsuwa?”ban saniba d’an sa ido”yakama dariya yana fad’in da nine kaga nayi haka dana sha surutai wajenka”banza shariff yamasa aka bud’e masa back sit suka shiga”lokacin da suka iso gidan har 9:30am tayi”Amaan takasa zaune da tsaye”tana jin k’arar motoci ta fita da sauri mommy na tsaidata ta wuce Aguje “tana sanye da gownt d’in lace red ta yafa mayafi red saman gashin kanta data d’aure Abaya”wanda yasha gyara”lips nata sun k’awatu da red d’in lipstick “ba k’aramin kyau Amaan tayiba”tana isowa haraban gidan su sharif na shigowa “bata dena gudun ba dukda ba sosai takeyiba ta nufi gefensa”shi kuwa bud’e mata hannayensa yayi”mus’ab dai na tsaye yana kallonsu yana dariya”bata rungumesa ba saidai ta tsaya gefensa tana maida numfashi fuskarta shimfid’e da k’ayataccen murmushi Ahankali tace”hamma nah kayi kyau”b’ata fuska yayi yajuya mata baya”mus’ab ya kauda kai yana fad’in Amaan Ina kwana?”da sauri ta maida masa gaisuwar ya Amsa ya wuce ciki”ita kuwa gaban shariff ta dawo tana fad’in menene kuma salfad? koban maka kyau bane?”….kinyi kyau harkin gaji salfad”Asalima baki tab’a yimun kyau kamar na yauba”sai naji banso mus’ab ya kallekiba”kukan shagwab’a tasaka tana kwasar fili tana doddoka k’afafuwanta tace”shima kishi kakeyi dashi?yabita da kallo yana jin kamar ya mannata da jikinsa”murya can k’asa yace”ya Isa haka kinga karki b’ata kwalliyarki”bana kishi da mus’ab wasa nakeyi”da gaske?”eh mana”to ki kalleni mana”babu musu ta kallesa suka had’a Ido”Atare suka saki murmushi tace”Ina kwana?”lafiya qlau salfad”Ina fatan kinyi mafarkina Adaren?”kaiko salfad? hmm! kaje kuyi break fast d’in”ganinki yafimun naci komai Amaan”Ina sonki har bansan iyakaba”bana zaton ko su mommy zasu fini sonki”tayi murmushi tana danna wayarta ta shiga vedio tafara d’aukarsu”sai shige mata shariff yakeyi”ita kuma tana d’an dojewa”sunfi mintina 20 suna vedios yana biye mata sannan suka idar”Amaan ta kallesa salfad bakaji ko?”me kuma nayi ?”meyasa bakaje wajen Askin ba?”yanzun idan zamu fita saiki rakani ko? yakare maganar yana kallonta”uhmm”to jeki idan mun gama zan kiraki saiki fito mu wuce”nidai to muje na rakaka bakin k’ofar parlourn”yana murmushi yace”to”saida suka iso bakin k’ofar shiga parlourn sannan ta wuce cikin gidan”mus’ab na zaune yayi hani’an yana waya da matarsa be jira zaman jiran shigowar shariff ba”kallo d’aya shariff yamasa yanemi waje ya zauna….cikin nutsuwa shariff yayi break fast d’insa”Aransa yana yaba yadda Amaan da mommyn ta sukayi matuk’ar iya tsara girki”yana kammalawa yakira Amaan Akan ta fito su wuce…ita dashi ne a back sit zaune “sai driver da mus’ab a front sit”suna tafe suna fira irinta masoya wanda mus’ab bema jin me suke fad’a sbd yadda suke maganar k’asa k’asa…..sunsha yawo sosai”har wajen Askin saida sukaje shida ita da mus’ab suka shiga ta zauna Ana masa suna fira”wasu nata kallonsu”sai wajen k’arfe 2 pm suka dawo harda uban shopping daya mata”bayan sun sauke Amaan suka wuce masaukinsu ,
“Anan su Alh isya (yayan Ammi) da Alh lawal k’anin mahaifin su shariff suka samesu “sai suka had’u suka iso Atare gidan su Amaan “daddy da Abokansa guda biyu suka musu tarban mutunci”naira Millon 2 Aka kawo kud’in gaisuwa da kayan saka rana “tsakanin lemo, cartoon d’in biscuits, chiweengum,sweet,ruwa da sauransu “Ankawo kusan cartoon 100 aka jibge”daddy ya d’auki naira dubu d’ari biyar yace”sun Isa yabashi Amaan ne dan Allah da kuma sbd kyawawan halayensa”sosai su Alh lawal sukayi mamakin rashin son Abin duniya da daddy yanuna”sunso ya Amsa Amma yak’i ya Amsa”sosai sukayi murna domin haka yanuna cewa su surukan Arzik’i ne”shi kansa shariff ya yaba da karamcin daddy”Atake Aka saka ranar Auren Amaan da shariff wata ukku masu zuwa”sai wajen sallar la’asar gaba d’aya sukayi hararramin tafiya gida”kuma harda sharif zasu tafi, jirgin k’arfe 4 zasu hau”body quards nasa kuma su wuce gobe da safe ta mota…..bayan sun gama sallama da daddy shi yatsaya bakin get yakira Amaan yasanar mata tazo ta samesa bakin get”saidai bayan sun gama wayar yafara tunanin yadda zai rarrasheta ta yadda yatafi gida yau…..✍️
wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba