Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

Kawali Ne 1

Sponsored Links

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*1*

 

*Abuja Nigeria*

 

A hankali motar ƙirar lexus 2023 fara rufe da baƙin glass,ke gangarowa harabar gun da aka tanada domin adana motoci,watakan parking space.
Ta jima da tsayawa kamin abuɗe ƙofar motar afito da ƙafa ɗaya waje wanda haka yabani tabbacin namijine acikinta duba da takalmin Gucci dake ƙafarsa daya laƙume milyoyin kuɗi.

Fitowa yayi,subuhanallah,Tsarki ya tabbata ga sarkin daya kyautata surarsa,dan Allah yayi halitta agurin.

Farine sosai,me murɗaɗɗen jiki,fuskarsa nada ɗan faɗi ba sosaiba ɗauke da saje me kyan tsari,gashin kansa nada yawa,sannan yaɗan mummurɗe,

Tracksuit ne ajikinsa farare na kamfanin Gucci,rigar armless ce hakanne yaba damatsan hannunsa damar fitowa.

Idanunsa masu kama da mejin bacci yana yawan lumshesu,kai takoina fa ya haɗu.

A hankali yataka zuwa bakin get ɗin daya baro,ga mamakina yana isa gun tsohon dake gadin gidan durƙusawa yayi har ƙasa ya cire glass ɗin fuskarsa yace a tausashe cikin muryarsa me daɗi”baba barka da warhaka,mun sameku lafiya?”

Faraace ta bayyana afuskar tsohon dake nuna jin daɗinsa yace”lafiya lau raihan,ya hanya kadawo lafiya?”

“Lafiya lau baba”ya faɗi yana murmushi.

“Allah yay maka albarka raihan ya baka mace tagari”cewar baba megadi.

Murmushi yayi ya miƙe cike dajin kunya ya nufi cikin gidan nasu.

Baba megadi bin bayanshi yayi da kallo,yana yaba kyawawan halayen Raihan ɗin,duk da kasancewarshi megadin gidansu amma yana mutuntashi,tamkar mahaifinsa.

Da sallamarsa ya tura ƙofar falon ya shiga,fuska ɗaure tamau bame cewa shine yagama yiwa megadi murmushi yanzu.

Mutane uku yasamu afalon,Mahaifiyarsa,ƙanwarta,se kuma ƙanwarsa,sanaya.

Can kusa da mahaifiyarsa yaje ya zauna a ƙasa kusa da ƙafarta,yaɗan rusuna yagaishesu.

“babana idonka kenan ko,tun yaushe nacema kazo hajiya rabi tazo dan ku gaisa amma kaƙi zuwa seyau”cewar mahaifiyarsa fuskarta ɗauke da faraa.

Ɗan gyara zama yayi yace”mummy ayyukane sukai yawa,in na saki na taho ban kammalaba ɓaci zasuyi shiyasa kikaga banzoba wancan satin”

“To agogo,nidama zuwa nayi inji ina aka kwana kan zancan auranka da nabeela,inyana nan ayi inbabu kar atakura kowa cikinku”cewar hajiya rabi ƙanwar mahaifiyarshi tana murmushi.

Ƙasa yayi dakai alamun kunya,yace yana sosa ƙeya”mummy Ni wlh ba yanzu zanyu aureba kawai abata damar auran wanda takeso”

Duka takai masa na wasa tana dariya tace”shaƙiyyi ay dama nasan zaa rina shiyasa kadena shigowa kano dan karma ku haɗu ko”?

“Aa mummy aykinane be bi tacan ba”ya faɗi yana murmushi dan yanzu yasaki fuskar dan zatonshi tilastashi auran nabeelar zaayi

Sun jima suna ɗan hirar sama sama kamin ya miƙe ya nufi ɗakinshi yana amsa waya.

Yana shiga ya kulle ƙofar ɗakin sannan ya wuce cikin bedroom ya zauna gefen gado yana faɗin”jabeer da gaske kakemin Farhana ta diro nigeria?”

Dagacan ɓangaren jabeer yace”wallahi raihan gatanan na ɗaukota daga airport zamu masauki.”

“Look jabeer farhana kadarace me tsada dan Allah karka taɓa kabari indawo,sabida asan sashin da za’a turata ta jawo kaya pls”

Dariya jabeer yayi irin ta ƴan bariki yace”banyi alƙawariba malam dan wallahi wannan kadarar daga kallo ma kawai baa hau gadoba zaa yi releasing”

Wata ƙara raihan yayi yace”dankutumar ubanka ganinan zan biyo jirgi yanzu wallahi tunda baka da amana”

Dariya jabeer yake masa kamar cikinsa zeyi ciwo,ya kashe wayar.

Miƙewa Raihan yayi da sauri ya fice yana duba agogo,afalo yasami su mummy suna ganin yadda yake sauri sunsan ba lau ba,tun kan suyi magana yarigasu da cewa”mummy container kayanmune tazo yanzu kuma costom na ƙoƙarin ƙwaceta shine zanyi sauri inje ayi clearance ɗinta”

“To Allah yatsare raihan ka dinga kulawa sosai don Allah”cewar hajiya rabi.

Mahaifiyarsa ma fatan alkhairi taimasa yafice daga gidan,baba megadi namasa fatan isa lafiya.

Koda yaje airport be jimaba jirgin tafiya lagoa yazama ready dan haka ya bada ajiyar motarsa a inda aka tanada domin hakan,ya hau jirgi zuwa lagos wanda yake ganin sam vaya sauri,ya ƙosa ya dira kamin jabeer ya masa illa.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Back to top button