Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 11

Sponsored Links

1️⃣1️⃣

Gabaɗaya matsin gadon da na bango ya sanya ya takura sosai, saboda wajen ya masa kaɗan akwai ƙunci sosai hakan ya sanya yake nishi dakyar. Ihu da kururuwar da Inna ke yi wanda ya tashi Hassan da Husaini bayan tashin Sadiya da ta yi cewa take.

“Innalillahi yau na ga ta kaina tsofai-tsofai da ni a ce an kawo min farmaki, mutane basa tsoron Allah ko kaɗan yo ban da lalacewa ma ina mamora a jikina jiki duk yaba” Cewar Inna tana rusa kuka kamar wata ƙaramar yarinyar da aka yiwa dukan kawo wuƙa.

“Haba Inna wai dan Allah ya kike so mu yi da ranmu ne, ke abin magana baya yawa a wurinki yanzu tsakani da Allah cikin daren nan ki tashi kike rasga kuka kina wasu maganganu marar kan gado” Cewar Sadiya tana miƙa hannu ta ɗakko duka yaran daga gadonsu ta ɗora su a kan cinyarta.

“Lallai Sa’adiyya baki da imani, to wallahi ta Allah ba taki ba maimakon ki tambayeni dalili sai ki rufe ni da faɗa kamar dai ke ce uwata mai daddawa?”

“Tambayar me zan miki Inna bayan kin tasheni kin tashi yaran nan, gashi kina ta faman yi da bakin ki sai kin tashi mai gidan”

“Waye me gida? Na ce waye me gida?Me gida ko dai me gira, ai sai dai a kira mijinki me gira mutumin da ya kwanta yana sheƙa bacci kamar matacce har aka samu wani garsamemen ƙato ya tsallakeshi a falo ya shigo nan zai haikemin, ban da jaraba irin ta ƴaƴan zamani me za a ji a jikin tsohuwa”

“Wai Inna ni fa ban gane ina maganarki ta dosa ba?”

“Na faɗa miki wato sangamemen ƙato ne ya zo ya shiga cikin bargona, dan wulaƙanci ya ƙanƙameni, wata irin ƙanƙama da ya mini wallahi ke kya ce wutar lantarki ce ta kama jikin mutum, bai tsaya iya nan ba sai da ya min ta turawa” Ta faɗa tana sakin kukan takaicin abin da aka mata.

Imran da ke tsakanin gado da bango ya sauke wata ajiyar zuciya jin Inna bata gane shi ba, ta ɗauka wani ne ya shigo gidan.

“Ya Allah ka ɗora mana abin da za mu iya, dama baka ɗorawa bayinka abin da ba za su iya ba, ni ma na fi kowa da na tsaya kike bani labarin da duka shiruftu ne kawai na tsufa” Sadiya ta faɗa tana kwantar da Husaini da ya sha nonon ya koma bacci.

“Uwaki Rakiya ce take shiruftun tsufa, na ce uwaki Rakindaɓo ita ce mai shiruftun tsufa, yo Allah na tuba har a nunawa na kwance farin wata, ras nake ina sane da komai ba wani tsufa ”

“To Inna in ba tsufa ba menene kin ce wai an miki ta turawa dan Allah hankali zai ɗauki wannan wa ma zai gane meye kike nufi bayan ke kan ki baki san me kike nufi ba”

“Babu mai fahimta kam sai mahaukaci, tun da labarin ƙanzan kurege ne nake baki, wato ga mahaukaciya tana bada labarin da mahaukaci ne kaɗai zai gane”

“Allah baki haƙuri, ni dai ki faɗa min wallahi bacci ne a idona” Cewar Sadiya tana kwantar da Hassan da ta gama bashi nono. Wani numfashi Inna ta sauke ganin giftawar da Hassan Sadiya ta yi da shi zuwa gadonta sosai gabanta ya bada rass.

“Na faɗa miki garda’u ne ya shigo ya shiga bargona ya ƙanƙameni har da min ta turawa”

“Mafarki dai kike amma babu wani mai sunan wannan da ya shigo hasalima mu kaɗai ne”

“Bari dai na miki gwari-gwari tun da na ga ke kan kwakwa gareki to ƙwarto ne ya shigo, ya shiga cikin bargona, ya rungume ni har kiris ya min(kiss) wato ya haɗe bakinsa da bakina mai zunzurutun sauran gooron da na ci na kwanta”

“Subhanallahi! Kwarto kuma Inna, haba Inna wai dan Allah meye damuwarki ne, har waye zai shigo gidan nan in har gaske kwartanci ya zo yana gani na ya j…

Imran da ke matse gefen gado ji ya yi kamar ya fito ya rufe Sadiya da duka jin ta ce wai kwarto ya barta ya nemi Inna amma ba hali dan yanzu idan ya fito ya yau sai ta Allah.

“Rufe min baki dan Allah, ƙarya zan miki kenan?” Inna ta katse ta tana jan wani dogon tsaki haushi ya sa ta tashi ta sakko daga kan gadon ta nufi makunnar fitilar za ta kunna.

Imran da ke ganin abin da Inna ke shirin yi ne ya shiga tashin hnkali dan ya san tana kunna fitilar asiri zai tonu, kuma ya san matsawar Inna ta ganshi kashinsa ya bushe. Aikuwa bata yu wata-wata ba ta kunna fitilar Imran saurin sadda kan sa ƙasa ya yi yana fatan kar Allah ya s Inna ta hangoshi. Inna tana kunna fitila idanunta suka sauka a kan Imran dake laɓe kansa sunkuye.

“La’ilaha illallahu muhammdur rasulullahi S.A.W ” Cewar Inna cikin karaɗi tana tafa hannuwa.

“Menene Inna” Cewar Sadiya tana kallon Inna.

“Sakko Halima maza-maza ga kwarton nan a ɗakin shege be dai bai samu damar guduwa ba, taso Imirana ku taho da taɓarya da madokai yau sai mun masa dukan kawo wuƙa, hatta mazaƙutarsa (al’aurarsa) Sai mun kwankwatseta mu ga gaba da abin da zai je kwartanci gidan matan mutane”

Imran hawaye kawai yake zubarwa yau ina zai kai wannna abin kunya.

Da sauri Sadiya ta diro daga gadon gabanta na dukan uku-uku wai kwarto.

“Subhanallahi! Kwarto kuma Inna, haba Inna wai dan Allah meye damuwarki ne, har waye zai shigo gidan nan in har gaske kwartanci ya zo yana gani na ya j…

Imran da ke matse gefen gado ji ya yi kamar y fito ya rufe Sadiya da duka jin ta ce wai kwarto ya barta ya nemi Inna amma ba hali dan yanzu idan ya fito ya yau sai ta Allah.

“Rufe min baki dan Allah, ƙarya zan miki kenan?” Inna ta katse ta tana jan wani dogon tsaki haushi ya sa ta tashi ta sakko daga kan gadon ta nufi makunnar fitilar za ta kunna.

Imran da ke ganin abin da Inna ke shirin yi ne ya shiga tashin hnkali dan ya san tana kunna fitilar asiri zai tonu, kuma ya san matsawar Inna ta ganshi kashinsa ya bushe. Aikuwa bata yu wata-wata ba ta kunna fitilar Imran saurin sadda kan sa ƙasa ya yi yana fatan kar Allah ya sa Inna ta hangoshi. Inna tana kunna fitila idanunta suka sauka a kan Imran dake laɓe kansa sunkuye.

“La’ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W ” Cewar Inna cikin karaɗi tana tafa hannuwa.

“Menene Inna” Cewar Sadiya tana kallon Inna.

“Sakko Halima maza-maza ga kwarton nan a ɗakin shege be dai bai samu damar guduwa ba, taso Imirana ku taho da taɓarya da madokai yau sai masa dukan kawo wuƙa, hatta mazaƙutarsa (al’aurarsa) Sai mun kwankwatseta mu ga gaba da abin da zai nemi matan mutane”

Imran hawaye kawai yake zubarwa yau ina zai kai wannna abin kunya.

Da sauri Sadiya ta diro daga gadon gabanta na dukan uku-uku wai kwarto.

ne yau a gidanta a ɗakinta taɓɗi.

“Lallai yau idan Abban twins ya kama mutumin nan sai dai uwarsa ta haifi wani” Cewar Sadiya.

Imran kuwa a ransa cewa yake

“Sadiya ni ne ma yau na san babu mai fahimtar da Inna cewa ba wajenta na zo ba ke ma da kike halalina tana sanya min ido a kn ki bare kuma ita ai cewa za ta yi dan kin haihu ne na je wurinta saboda jarabata” Ya faɗa a ransa yana zubar hawaye ga matsin da yake ciki na gadon ga kuma tashin hankali.

Waige Inna ta fara aikuwa ya hango kwalbar humra ƙatuwa a kan madubi da sauri ta sungumota tana cewa.

“Yi maza Halima taso mijinki kar kwarton nan ya shammacemu ya tsere ni bari in fara da wannan bata yi wata-wata ba ta ɗaga kwalbar ta rotsa a kan Imran. Wani uban ƙara ya saki da ya sanya Sadiya da Inna gane shi.

A zabure Imran da ke kwance falo a ya tashi zaune gabansa na faɗuwa hannu ya sanya ya dafe kansa da ya yi mafarkin an rotsa masa kwalba, jin babu danshin jini ya tabbatar da mafarki yake, sai huci yake yana sauke numfashi da sauri gabansa kwa bai bar faɗuwa ba ga wani gumi da ke sarto masa duk sanyin da ake amma shi gumi yake.

Kallon falon yake duk da ba haske amma yana so dai ya tabbatar duk abubuwam da suka faru a mafarki ne, ƙaran saukar munsharin Inna da yake jiyo wa daga cikin ɗaki shi ya sanya ya ƙara tabbatarwa mafarki yake, jaɓas ya koma ya kwanta yana sauke numfashi, tuno da yadda ya haɗa bakinsa da na Inna a mafarki hakan ya sa ya ji zuciyarsa na bala’in tashi har wani amai na neman taho masa hannu ya kai kam harshensa ya taɓa yana so ya ji goron nan na Inna a bakinsa amma jin babu komai bai sa ya daina jin tsantsani da tashin zuciya ba da sauri ya tashi zaune ya miƙe ya kunna fitilar ya sheƙa waje da gudu jin aman na neman zubowa, amai yake kwarawa tun ƙarfinsa, ƙaran ƙolon amansa ne ya farkar da Inna daga baccin da take, tashi ta yi ta kunna fitilar ɗakin, kallon Sadiya dake bacci cikin mamakin ganin fitilar falo kunne ya sa ta nufi falon tana son tabbatar da Imran ne ke amai, ganin baya falon kuwa ta tabbatar shi ne san ta san sheɗanin aljanin nan da ta gani jiya zai iya yin komai, fitowarta tsakar gidan ya yi dai dai da wani irin murɗawa d cikinta ya yi, dama tun kan ta kwanta take jin cikinta na wani iri babu daɗi.

Ganin Imran na sheƙa amai ta sanya takalminta ta nufi wurinsa tana cewa.

“Imirana lafiyarka kuwa kake ta sheƙa amai da talatainin daren nan ko laulayin ciki kake?”

Jin muryar Inna ya sanya Imran jin wani tashin zuciyar hakan ya sanya ya cigaba da ƙwaƙulo wani aman”

“Kai dai ka san jarabar da ka ci kake amai” Ta faɗa tana surar buta ta shige bayi ta ɗan kara ƙofar jin gudawa na neman zubo mata, ga tsoron aljanin jiya a ranta ga kuma gudawa da bata da haƙuri ko jinkirin fitowa.

Ƙaran yadda Inna ke sakin kashi ya sanya Imran jin gabaɗaya duniyar ta masa zafi, haka ya kunna famfo ya wanke fuskarsa da bakinsa ya kora aman ya kashe fanfon ya lallaɓo a hankali ya dawo ɗaki dan gabaɗaya ji ya yi ya galabaita da aman da ya yi, haka ya dawo falo ya kwanta, amma daga ya rufe idonsa bakinsa yake gani cike da goron bakin Inna haushi da takaici ya ishe sa. Bare da ya ki ta shige bayi ta daddage tana sakin gudawa ko ƙaƙƙautawa babu ƙaran kashin sai amsa kuwwa yake masa a kunnuwansa. Inna kuwa jin bata jin ƙaran aman Imran hakan ya bata tabbacin ya bar wurin, cikin sauri ta yi tsarki, ta ɗauki ruwa a cikin kwantainer da ake ajiyewa a bayi ta yi floshing ta fito tana jan ƙafa dakyar. Falo ta shigo ta zauna daɓas a kan kujera, Imran yana jin shigowarta, ya runtse idanunsa da ƙarfi dan ba ma ya son ganinta bare ya tuna mafarkinsa da ita.

“Imirana, Imirana, Imirana? Ta kira sunansa sau uku amma bai amsa ba kuma bai buɗe idon ba.

“Kai dai wannan yaro da mugun hali kake wallahi, kana ji ina kiranka amma ka ƙyale ni, dama maganin gudawa zan ce ka bani idan kuna da akwai a gidan” Banza ya mata.

“To ta Allah ba taka wallahi Imirana, ace ina maka magana amma ka ƙyale ni dama kana sheƙa amai ma dana maka magana ka ƙyale ni … Kafin Inna ta gama magana ta ƙara jin cikinta ya bada wani ƙululuuu da hanzari ta tashi ta fita ta sanya takalmi a baibai ƙafar dama a ta hagu ta hagu a ta dama ta nufi bayi duk da tana jin tsoron aljani amma kashin da ua matso ta ba zai ruƙu ba kuma dai ganin Imran idonsa biyu ya rage mata tsoron.

Sai da ta kwashe mintina sannan ta dawo tana zuwa za ta cire takalmi ta ga yadda ta sa a juye.

“Kai Allah raba bawa da wahala gauro a teburin mai shayi, ni Azumi matar Malam yau na ga takaina wallahi, tsabar ruɗewar da na ji cikina ya yi ashe takalmin ma baibai na sa”Ta faɗa tana zaunawa a kan kujerar falon.

“Kai dai wannan yaro baka da imani kana ganin yadda nake sawu wani kan wani zuwa bayi amma ba za ka iya ce min sannu Inna ba” Ta faɗa tana kallon Imran da ke zaune ya dafe kai. Kafin ya bata amsa ta ji cikin ya murɗa alamar gudawar ta taho aikuwa ta matse ƙafafuta ta zauna ta ce

“Kai ina dalili hallaw wani kashin ne ke shirin fitowa to babu inda zani kuma ciki ka gaji da ƙuginka ka barni, yo daga dawowata ace wani kashin ya taho bayan yanzu kafin in dawo sai da na tsaya na tsage shi tas, na tabbatar na gama babu wani saura” Ta faɗa tana ƙara matse ƙafafunta tare da zaunawa daram tana danna saitin mazaunanta a kujerar dan kashin ya koma sai wani gaba take tana baya kamar wacce take kan lilo wai duk dan kashin ya koma.

Amma da yake gudawa ne ko alamar komawa bai yi ba, haƙori ta sanya ta danne harshenta da ƙarfi sosai idanunta suka firfito , ai babu shiri Imran sai ganin Inna ya yi ta yi bakin ƙofa a sukwane, takalmin ma a hannu ta ɗauka dan kashin dab yake da zubowa.

Imran dariya ya fara har da ƙyaƙatawa yadda ya ga Inna ta fita da gudu-gudu tamkar an biyo ta.

“Wa ya faɗa miki barno gabas take, ai faɗa da mahaukaci ba daɗi, wallahi ba dai ni kika rufe a ɗaki da miciji ba na miki magiyar duniyar nan kika ƙi buɗewa har sai da na gama galabaita da shiga tashin hankali sannan kika buɗe ni kak rinƙa min dariyar na yi fitsari a zaune wai na rakuɓe a jikin bango kamar ƙadangare, son matata ta raina ni, ai dama na sha alwashin sai na rama dan bashi kika ci gashi nan yanzu kina karɓar sakamako” Imran ya faɗa yana dariya tare da tuna muguntar da ya yiwa Inna da dare wacce ta sanya ta gudawa.

Yadda Imran ya yi ya sanya Inna ta samu ruɗewar ciki. Kafin su kwanta da daddare bayan kowa ya watse lokacin da Imran ya dawo sai ya tarar da Inna zaune a falo da kwanon furarsa a gabanta za ta sha, wani haushi da takaici ne ya sanya ya kasa cewa komai dama ga haushinta da ya wuni yana ji ta rufeshi da miciji a ɗaki yana ta tunanin hanyar da zai bi ya rama sai ji ya yi ta ce.

“Imirana har an dawo kai wai baka da aiki sai zaman gida kamar mace, baka je ɗan yawo ba cikin abokai ku ɗan zanta, kai kullum a gida, haba ina dalili kai ɗan zaman majalissar nan ma na maza baka yi, daga an yi sallar isha’i sai a ganka ka shigo gida zunƙwai-zunƙwai ka kama ƙofa ka garƙame, ina ga masu barka ma da suke zuwa da dare gidan suke samu a rufe” Ta faɗa tana tashi ta fita.

Shi dai bai ce komai ba, kallonta kawai yake yana ji kamar ya rufeta da duka har sai ta daina motsi. Tana fita wata dabara ta faɗo masa da sauri ya buɗe hannun frige inda ake ajiye magunguna, ya ɗakko wani magani da aka rubuta masa kwanaki da ya kasa tsugunno (Ya kasa kashi) Shi ne likita ya rubuta masa da ya sha sai cikin ya saka ya samu ya yi kashin, murmushi kawai yake ganin ya samo hanyar da zai rama abin da Inna ta masa da sauri ya ɗauki maganin guda huɗu ya zuba mata a cikin furar ya gauraya ya mayar da maganin da sauri ya koma kan kujera ya zauna yana latsa waya kamar bai tashi daga wurin ba duk wannan abin da ake Sadiya tana bayi bata ma san Inna ta buɗe frige ta ɗauki furar Imran ba.

Ana jimawa sai ga Inna ta dawo riƙe da kofi ta kalli Imran da ke danna waya ta taɓe baki ta zauna ta ƙara ruwa a furar t gauraya ta shiga shan abinta ba tare da ta san ami Imran ya zuba a ciki ba. Sai da ta sha sama da luday bakwai ta ɗago kai ta kalli Imran da ke latsa waya bata san ba yana ganinta ta gefen ido ba yana dariyar ƙeta a ransa.

“Imirana dan Allah zan baka shawara amma kar fa aka ce santin fura ne ya sa na faɗa, ka daure ka gine wancan filin na tsakar gida kai ma ka yi turaka irin ta maza amma ina dalili kana ɗaki ɗaya da matarka kuma ko yanzu ka zauna ina shan fura kana zaune hakan bai kamata ba” Ta faɗa tana ƙara cika ludan ta sha.

Wani kallo Imran ya jefa mata, ya cigaba da abin da yake.

“Ka huta tun da ba zaka gina ba, to wallahi idan Halima ta sake haihuwa na zo ZAMAN WANKA baka yi turakar ka ba kana shigowa gidan nan zan fara maka waƙa in ke cewa ɗan cikin mata baki ya koshiye ya ci tuwon mata gumba yake jira ɗan karannana wa zai baka” Ta faɗa tana rausaya kai kamar ƙadangaruwa.

“Za ki san duk wannan abin idan cikin ki ya ruɗe kika ringa zuwa bayi ” Ya faɗa a ransa. Tana cikin shan furar ne Sadiya ta fito daga bayin wata kunya ta rufeta ganin Inna na shan furar Imran amma haka ta dake ta ƙyaleta gudun magana dan ta san yanzu idan ta yi magana sai cibi ya zama ƙari. Da wannan cakwakiyar suka kwanta to shi ne Imran ya yi mafarkin ya shiga bargon Inna shi ne da ya tashi yake kwara amai ita kuma hakan ya yi daidai da lokacin da maganin da ta sha a cikin fura ya fara aiki shi ne ta fara gudawa.

Yana dariya jin ƙaran tafiyarta ya yi shiru ya dake, haka ta shigo falon tana tafoya dakyar kamar ƙwai ya fashe mata a ciki.

“Wash kai mai za a yi da cutar kashi, haba ka rinƙa tsugunno babu ƙaƙƙautawa” Ta faɗa tana durƙuwasa a tsakiyar falon dan ji ta yi ƙarfinta ya ƙare, durƙusawa ta yi irin durƙuson masu naƙuda gwiwoyinta a ƙasa ta shiga ƙwalawa Sadiya kira dan duk abin nan da ake Sadiya tana ta shigar bacci.

Sadiya da ta fara jin kiran Inna sama-sama haka ta daure ta buɗe idonta ganin ƙwan ɗakin a kunne Inna bata kan gadon sai ta tashi zaune.

“Wayyo Sadiya ba kya zo ba in baki wasiyya dan ni na san lokaci ya yi, mu kuma haka Allah ya yi da cutar kashi za mu mutu, mu tashi a lahira muna ta tsula kashi, yo na ji an ce kowa da abin da ya mutu yana yi zai tashi a lahira yana yi, mu kuma haka za mu yi ta keta mutane a filin ƙiyama muna ɗoyi “Inna ta faɗa tana sakin kuka jin cikinta ya sake kiran ƙululuuu. Haka Sadiya ta taso ta fito a ranta tana jin haushi wannan ZAMAN WANKA ko jaraba ace bala’in safe da ban na rana da ban da daren ma ba a barka ka huta ba.

Amma kuma ganin Inna a durƙushe cikin wani yanayi sai ta nufe ta da sauri.

“Inna lafiya dai?”

“Ke ma dai Sadiya da shegantaka kike wallahi, yo ke da kika ganni na yi durƙuson naƙuda ma har kya tambaya lafiya, rabona da in yi durƙuson naƙuda tun lokacin hainuwar ubanki, amma yau cutar kashi ta sanya na kasa zama da ɗuwaiwukana sai durƙuso” Ta faɗa tana dafe ƙasa da hannuwanta.

“Subhanallahi! Inna me kika ci haka ya ɓata miki ciki?”

“Haba Sa’adiyya har kya tambaya ma menene zai ɓata min ciki ni da bani da ɓataccen ciki gareni ba, ni ai cikina sunansa komai da ruwanka dan komai na bashi karɓa yake, amma yau dai kin ga an saɓa lamba dan kuwa kashi nake ratatata, amma Imirana kin ganshi nan magana ma ta gagara”

“Sannu Inna “Cewar Imran .

“Riƙe abinka in dai duniya ce yau naka gobe ma ɗan uwanka kaima wani abun zai sameka ai”

“Babu abin da zai same ni”

“Imirana… Ƙaran da cikin Inna ya sake saki ne ya hanata ƙarasa maganar tata,

“Halima riƙeni kar in ɓata miki ɗaki dan ba zan iya tafiya ba ma, haka Sadiya ta kamata ta kaita bayin ta jirata da ta fito a ƙofar bayin ma ta watsar da takalman nata haka Sadiya ta kamata ta mayar da ita, frige ta buɗe ta ɗakko maganin gudawa ta bata cikin ikon Allah sai kashin ya tsaya haka suka koma suka kwanta baccin wahala ya ɗauke Inna. Kafin baccin ua ɗauketa take ta tunanin abin da ta ci ya ɓata mata ciki haka, a nan tunanin furar da ta sha ya faɗo mata nan kuwa ta tuna ta tafi ɗakko ruwa ta bar furar a wurin hakan ya sanya ta yi shakku a kan gudawar tata haka kawai ta ji bata yadda da Imran ba “Tabbas Imran ne ya min wannan abun” Ta faɗa lokacin da ta ke kwance kafin baccin ya ɗauketa,

“Wallahi Imirana sai na rama wannan abin da ka min dan wallahi sai ka san Azumi ka yiwa hakan…

Duk wacce ta san san ta fitar min littafi ta siya ta mn mgn in bata kuɗinta,

Masu son a tallata musu hajarsu
mmn afrah 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: “`Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

DAN ALLAH KAR WACCE TA SAYI LITTAFINA DAN TA FITAR MINI,IDAN DAN KI FITAR ZA KI SIYA KI RIƘE KUƊINKI HAJIYA BANA BUƘATA.“`

 

Back to top button