Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 58

Sponsored Links

Page 5️⃣8️⃣

 

Yana barin garden din part din mommy yanufa kofofin part din arufe knocking yayi , mommy dake kuka taji ana knocking yasata goge fuskanta tazo ta bude kofar ganin Mr azaad ne yasa tadaure fuska tamau ta ce ” kai lafiya zakazo kana bugamin kofa da wannar uwar Daren?” miskilin murmushi Mr azaad yayi yadan hadiye bacin ranshi ya ce ” ehhh to lafiya ba lafiya ba zan iya shigowa ?” shima yajefa mata tambaya ganin taki motsawa daga inda take tsaye ne yasa ya kutsa kai cikin part din nata direct kan kujera yaje yazauna yana ciro wayarsa yakira layin abba, ” hello abba sorry natasheka abacci banason kadawo ka ji labarin na kashe maka mata shisa nace bari in sanar dakai tukun” tunda abba yaji abinda Mr azaad yafada yagane kancewa yagano komai hamdala yayi dominshi yasan komai akanta amma shi sun rufe mishi baki Koda yayi kokarin sanar da wasu seya gagara , gyara murya abba yayi ya ce ” karka mata komai tukun 4:00am zan biyo flight din safe just make sure bata gudu ba ” jinjina kai Mr azaad yayi ya datse kiran.
ganin ya shige mata falo ne yabarta tsaye acan bakin kofa , shigowa falon itama tayi taga ya zauna be da niyar tafiya kuma shi be fada mata abinda yakawoshi wajanta ba ya sa ta ce ” katashi ka fita kabani guri ” afusace yatashi dan dama haushinta yakeji kamar yakasheta lokaci daya kowa ya huta , ya mata mugun shaqa fiffitowa idon mommy yayi waje taji damkar maza kakari tafarayi idonta yajuya jaa tana kokarin shekewa domin shaqar da Mr azaad yamata bana wasa bane ya daka mata tsawa lokaci da ya yacanza fuskan nan tayi ja tsaban bacin rai ” kimin shuru ko kuma kiyi dana sani” mit mommy tayi ganin ya hayayyako gashi yaki sakinta cillar da ita yayi ta kifu akasa tana rike wuyanta hade da nishin wahala ga idonta yayi ja , dakyar ta rarrafa tazauna akan kujera tana tunani iri_iri shi meyasa Mr azaad zeyi mata haka yaron da ma zata iya kirga sau nawa magana yataba hadasu tunda aka haifeshi be taba shiga part dinta ba sede in yanason hira da anty zainab da anty shayida ya kirasu suzo part din ummi ko a garden.

Tanzarzar na kallon abinda yake faruwa ta mudubin tsafi nan yagane asirin mommy yatonu kuma inde taji bakar azaba zata iya tonawa sauran yan kungiya asiri hakan yasa yamata magana ta cikin madubin ” hafsat kisan hanyar dazakiyi ki tsere musu domin yarigada yasan komai akanki ” jin abinda tanzarzar yafada mata yasa taji wani irin fargaba yakamata bawai dan na asirinta yatonu ba sedan tasan muddin ta fadi wata kalma dangane da yan kungiya to tabbas nata yakare, dago kai mommy tayi ta kalli Mr azaad dashima firgitattun idonshi na kanta , wuff tamike zata da ki kasa domin ta bace kenan , sarauniya ta damki dantsen hannunta ta baya , wurgi da ita kasa sarauniya tayi tana binta da muguwar kallo da idanunta masu firgita abokan gaba fuskan nan babu alamun sassauci ko rangwama atare da ita. Mamaki ne yakama Mr azaad ya akayi fanan tasan da yana nan Kuma ga abinda yakawoshi, laakari da irin shigar dake jikinta dayayine yagane ba fanan bace sarauniya fadima ce , sarauniyar nasminaya, hakan yasa yamike yatsaya yana kallonta ganin ko inda yake tsaye bata kallaba bare yasa ran zatamai magana. abinda yayi laakari dashi shine duk sanda ta bayyana a asalin sarauniyarta tofa wasu dabi’un ta kamar bata sansu ba wata zuciyar ta ce mai ” karfin jaaazana ne yasa hakan domin inta bayyana, sarauniya ce bawai fanan ba ” gabanshi ne yatsinke lokaci daya, da ya tuna kenan fanan intabar nasu duniyar mantawa zatayi dasu gabaki daya kenan bazama tasan da zamansu ba balle tayi tunanin dawuwa wajan ahalinta, dafe kai yayi dayaji yana juyawa.
daga inda sarauniya take tsaye ta daga hannunta tayi pointing mommy dake yashe akasa , kyasta yatsunta guda biyu tayi nan take igiyoyi suka fara daure mommy dauri bana wasa ba suka mata tamau yanda ko numfashi dakyar take iya fitarwa. tana gama daure mommy kuwa ta bace tabarshi tsaye awajan.

barin part din Mr azaad yayi yasa securities su tsaya akanta kar subarta tayi koda motsine dukda adaure take
. yakoma garden yazauna yana kada kafa har asuba , yayi alwala duk a garden din yanufi hanyar fita a gidan dan zuwa masallaci yaga su fawwaz da areef sunfito su ma. jerawa sukayi sukaje suka gabatar da sallah suka dawo be fadawa kowa abinda ke faruwa ba haka zalika be fada musu abba yataso ba yawuce part dinshi samun fanan yayi tana zaune tana azkar zama yayi akan kujera yana facing dinta harta idar ya ce ” morning wifey” ta ce ” habiby katashi lafiya ?” ya lumshe idanu kawai. ta ce ” habiby ina kaje daren jiya natashi naga baka nan amma naganka amarfakina a part din mommy” ” eh naje part dinta ne ” daga haka yakawar da zancen ta hanyan dauko wata maganar daban ya ce ” gobe zamu tafi yau zankaiki kije kiyiwa su mama sallama yau ” cike da murna taji zataje gida ya ce ” to Allah yakaimu” bata koma bacci ba ta cire babban hijab din jikinta yarage daga ita se wandon falazo da vest ajikinta tafara gyaran part dinsu tayata shima yayi suka gama , atare suka shiga kitchen sukayi breakfast dan wake tamusu tunda tafara kwaba dan waken da digawa Mr azaad yaketa yamutsa fuska yana ” nide bazanci wannan abun ba abu kamar wani kwallo_kwallo ” dariya tayi tasan be taba ci ba gashi itakuma shi takeson ci yau din nan gama danwaken tayi ta dafa kwai ta baresu sannan tayanka vegetables salad , tomato, ta yanyanka kwai din a bowl daban taki saka albasa aciki saboda yanzu seyasa bakin mutum yafara warin albasa, plate ta dauko tazuba danwaken dayawa sannan tasaka mai din data soya yaji albasa ta zambada yaji zaro ido waje Mr azaad yayi ya ce ” yanzu da wannan pepper zakici baby” murmushi tayi ta ce ” kadingayin jam’i zamuci zakace yau zan koya maka yanda akecin danwake” haka taci gaba da saka salad da tomato din da ta yanka tasa kwai din. ( bakaramin daukan hankalina danwaken nan yayi ba lokaci daya naji yawuna ya tsinke, kunsan ni , akwai ni akwai kaunar dan wake sosai. gashi ban Isa ince zanci ba yanzu se Mr azaad yayi kasa_kasa dani ) haka ta dauko plate din taje tsakiyar falo ta ajiyeshi akan carpet takoma taje tadauko bottle water da glass cup ta ajiye ta zauna zama shima yayi dan yaga yau tayi niyar kumburar mishi da ciki ne . sa hannunta tayi tafaraci tana santi babu yanda ya iya haka shima yasa hannu yayi yanda tayi yakai baki, ai ba arziki yafurzar dashi waje idonshi harseda ya kadà murya na rawa ya ce ” is to spicy kiban ruwa ” zuba ruwa tayi a glass cup ta mika mishi yasha yanata shishitan yaji, sannu tamishi sannan tasa hannu dede ta gabanshi ta kwashe yajin yarage dan kadan takara maggi ta gauraya mishi ta ce ” to nacire yajin kaci ka ji ” make kafada yayi kamar yanda take mishi a shagwabe ya ce ” nide bazan iya cin wannan abun ba is to spicy” dariya tayi ganin yanda yake mata shagwaba hakan ya kayatar . diba tayi ta bashi abaki dakyar ya iya cinyewa dukda babu yajin sosai wannan karan, haka suka cinye danwaken tas daga ya ce yakoshi setace ah ah yakara kadan de haka ta mishi wayo tadinga feeding dinshi harsuka cinye ,sunaci suna shishitan yaji kamar wayanda akama dole, sukasha ruwa hancinshi har wani ja yayi dan wahala gaba daya yazama wani kala dukda yaji dadin danwaken amma ya ji ya azabtar dashi .

Karfe 10:00am dede abba yashigo gombe yasauka agida part dinshi yayi , wanka yayi ya kimtsa babu wanda yasan da zuwanshi saboda babu wanda yasani se Mr azaad . Kiran yayanshi yayi awaya yasanar musu yanason ganinsu yanzu yanzu batare da bata lokaci ba , wannan kiran gaggawan da abba yamusu ya tayar musu da hankali yasa babu wacce tabata lokaci kowa suka hallara a main falo harta su Mr azaad da fanan duk babu wanda bezo ba duk suna zaune ,m afalo sukaji sallamarshi , zama yayi akan kujera fuska babu yabo ba fallasa. shan jinin jikinsu sukayi kowa yasake shiga rigar nutsuwa, suka fara gaisheshi.

bude taro yayi da adduah sannan yafara magana ” na taraku anan ne bandan komai ba sedan fayyace muku gaskiya” zuba mishi ido sukayi sunason suji meye ze fada , bin kowannesu yayi da kallo.

ya ce ” kamar yanda dukkanku kuka sani hafsat itace matata ta farko ! yar wazirin gombe ce tun kafin in kammala karatuna muka fara soyayya da hafsat , amma mahaifiyata wato marigayiya ammi , bata bada goyon baya ba saboda hafsat batada kunya bata son mutane kullum ako da yaushe adaki ake samun hafsat bata mu’amula da kowa seni sekuma yan gidansu ga ta da tsiwa ga shegen rashin kunya, amma dukda wannan dabi’ar nata take sona kuma nima inasanta, me martaba da waziri sunyi farin ciki sosai da kasantuwar wannan al amarin bayan na kammala karatu aka mana aure , me martaba yace tunda yanzu na kammala karatuna kuma nayi aure ni zan karbi sarautar gombe , hankalina yatashi domin ni bantaba kaunar zama sarki ba hasalima abubuwan sarauta baya burgeni ni babban burina shine inzama business man, shisa na ki kuma fulani ta goyamin baya , haka me martaba yakyaleni nayi abinda nakeso .
dede da rana daya ammi bata ta ba son hafsat ba in an tambayeta dalili setace jikinta nabata akwai wani mugun abu atare da hafsat tana ganinta amafarkinta. babu wanda yataba daukan maganar ammi serious kowa gani yakeyi kawai dan ta tsaneta ne yasa take fadar haka. bayan aurenmu da wata daya ammi ta rasu sanadiyar bugawar zuciya haka akayi zaman makoki aka watse tundaga nan ne hafsat ta fara nunamin mugayen dabi’un ta, bata sallah , ba karatun addini ko adduah bantabaji tayi ba,bata kaunar kowa ya rabeni , sannan kullum tana daki yanda na fita nabarta haka zandawo in sameta bata, bantaba sanin ya kalar test din girkin hafsat ba har yau danake muku wannan maganar sede masu aiki suyi mana abinci. bata rayuwarta da kowa tun ina mata fada harna hakura nazuba mata ido domin daga zaran nafarayi mata fada itama zata hayayyakomin kamar zata dakeni nikuma bazan iya sa’in sa da mace ba yasa se inbar mata part din se dare in dawo haka har tasamu cikin zainab ta haifeta, tunda nake arayuwata bantaba ganin macen da ta tsani abinda tahaifa ba se akan hafsat ta tsani zainab har kamata natabayi tashaqe ta tana kokarin kasheta dakyar nakarbi zainab ahannunta jaririya dabatasan komai ba se zabga kuka takeyi . daukan zainab nayi nakaiwa fulani nafada mata abinda yake faruwa hannu biyu ta karbeta renon zainab yakoma gun fulani. mukaci gaba da zaman doya da manja nida hafsat yau lafiya gobe kuma fada da tashin hankali ahaka harta fara fita araina dan nagaji da mugayen dabi’un ta. zainab nada shekara uku hafsat tasake samun wani cikin bata nuna bataso ba wannan karon har ina murna gata iya gata na nuna mata amma tana haihuwar shayida komai yasake dagulewa tsantsan tsana shayida tagani kamar ba ita tasha wahala tahaifeta ba harta abinci bata ba ta haka zata wuni da yunwa se na dawo gida tunku mukecin abinci abin nata da ya isheni ne yasa nafada mata muddin taci gaba da gallazawa shayida to nikuma zan saketa hakan ne yasa tayi sanyi domin tanasona sosai , akan abinda takewa shayida tarage kashi 20 acikin 100 gashi Zainab bata isa tazo part dinta ba seta mata mugun duka , lamarin ya isheni yasa nasaketa saki daya ta tafi gida nikuma nadauki shayida itama namikata gun fulani.
zuwana dubai gabatar da wani meeting da babban Company na A.A AZAAD, bayan mungama meeting kanin sarki azaad me suna arash ya gayyaceni gidansu cin abincin dare dukda inada wani uzuri haka na amsa gayyatarshi naje babban gidan sarautar dubai sunada matukar mutunci da karrama bako yanda suke haba_haba dani hakan yamin dukda nima dan sarki ne . muna zaune munacin abinci sarki azaad ya gabatar min da ahalinshi da matar kannenshi , matar arash dakuma matar asaad, sekuma matarshi wato mahaifiyar umminku aysha kenan se yaransu dasuka kasance dukkansu maza rai 9 jinjina kai nayi nace ” Masha Allah,Allah ya azurtaku da yara maza Allah yarayasu” suka amsa da ameen sarki azaad ya ce” ai sunada kanwa guda daya rak ita kadaice mace agidan nan ” murmushi kawai nayi bance komai ba , kiran sunanta sarki azaad yayi ” Aysha” fitowa tayi tana tafiya cikin nutsuwa yarinyace dabazata wuce shekara 15 ba aduniya kyakyawar balarabiya sanye da doguwar riga baka kanta rufe da mayafi tunda tafito idona akanta yake lokaci daya naji nakamu da santa, gabatar min da ita sarki azaad yayi, fuskanta dauke da murmushi tagaisheni amsawa nayi iname yaba hankalinta komawa ciki tayi duk matan wajan suka bamu waje , harga Allah tunda naga aysha naji inasonta kuma so na aure bazan iya barin dubai batare danayiwa iyayenta magana ba , ban boye musu komai ba na fayyace musu abinda ke raina nahada da fada musu inada mata da yaya biyu. banyi tsammanin zasu amincemin ba cikin ruwan sanyi ba kawai naga sun amince domin ba kowani balarabe ko farin fata bane yakeson hada jini da bakar fata ba sukace in turo iyayena da full confidence dina nabar masarautar zuwa masaukina dukda sunyi sunyi inzauna na ki. haka nadawo nigeria da farin ciki naje nasamu me martaba nasanar mishi shima ya amince da lamarin saboda suna shiri sosai da sarki azaad haka suka nemamin auren aysha, tunda hafsat taji labarin zan kara aure ta dami waziri da sede yanemeni zata koma gidanta haka waziri yanemeni yarokeni da inmaida auren haka kuwa akayi namayar da auren . hafsat takoma gidanta mukaci gaba da rayuwa balaifi dukda bakamar da ba , har a wannan lokacin bansake haduwa da aysha ba saboda a al adarsu inde yarinya zatayi aure bazata sake ganin mijin ba ko jin muryanshi ba se randa aka daura musu aure. Bayan nagama gina wannan gidan ne aka daura aurena da aysha saboda nafison zama awajen masarauta, hafsat itace uwar gidana yasa nabata zabi tazabi part din da takeso haka tazaba , aka kawomin aysha gidana yan uwanta mutane hudu ne suka rakota bayan anyi shagalin biki anwatse , natarasu a part dina dan musu nasiha dukda aysha batajin hausa daga larabci se turanci haka namusu fada sannan naraba musu kwana , hafsat bata nunamin komai ba ta tashi ta tafi abunta , haka rayuwa taci gaba da tafiya nan ne nafara samun kwanciyar hankali. takuramin aysha tayi akan lallai sede indawo da shayida da zainab wajanta haka nakarbosu daga wajan fulani na damka mata su aikuwa suna ganin gata sosai kamar ita ta haifesu ana haka aysha tasamu ciki tayi laulayi sosai fulani na yawan zuwa dubata kuma kullum ita take mata abinda takeso ta bada akawo mata. bayan wata tara tahaifi ya mace akasamata suna amina wato sunan kakarku ammi kenan ,haka tahada yaran dukkansu uku taci gaba da kula dasu tunda aysha ta haihu har akayi suna tayi arba’in ko kafa hafsat bata taka a part dinta ba nayi maganar harna gaji , amina nada shekara hudu aysha tasake haihuwa ta haifi da namiji yaci sunan kakanshi wato azaad sosai yaro yaga gata nan ne kadai hafsat tazo suna daga nan batakara zuwa ba amma aysha tana zuwa mata ta gaisheta lokaci zuwa lokaci , daga nan ne hafsat ta tayar da bori sede abata yayanta gudun masifarta yasa na kwashi yaran nakai matasu duk tunanina tacanza halayenta ashe bahaka bane ta karbesu ne dan ta kashesu , bazan taba mantawa wata rana inazaune a office meyi mata aiki takirani aboye tana sanar dani hafsat ta bawa shayida da zainab guba ba shiri nadawo gida tare da motar ambulance aka kwashesu akayi asibiti dasu dakyar aka ceto rayuwarsu saboda guban bedau lokaci ajikinsu ba , haushi kamar ya kashe hafsat raina abace nadawo idona yarufe bansan lokacin da na dinga zabga mata maruka ba tsabar taurin rai irin na hafsat ta kalli idona tacemin inde yaran nan ne seta kashesu domin bazata taba sonsu ba har duniya ta nade, banyi mamaki ba dan yanzu nasan hafsat bata sansu haka naje wajan aysha dabatasan abinda yake faruwa ba nace ta shirya muje asibiti duba su zainab hankalinta yatashi jin abinda hafsat ta aikata musu anan ne tasan bata sansu tayi kuka sosai dakyar na iya lallashinta, tadauki azaad da ake goyo muka tafi asibitin satin su biyu aka sallamesu ko da wasa banyi gigin kaisu part dinta ba nabarsu awajan aysha tacigaba da kula dasu . Haka shekaru sukata ja sosai aysha tasake haihuwa ta haifi fawwaz dakuma areef a time din duk suna makaranta duk sun girma , hafsat bata sake haihuwa ba. su shayida da sungama karatu har akayi auren zainab daga baya akayi na shayida , Allah yabawa zainab haihuwa ta haifi dan ta namiji akamin takwara Muhammad wanda yanzu yake Russian yana karatu, nan ne hafsat tasake samun ciki zuba ido nayi inason inga wannan karon ma zata tsani abinda zata haifane da iKon Allah tahaifi namiji aka samishi Mansoor soyayya, gata, kulawa babu wanda mansoor be gani ba tasoshi sosai kamar ranta , Mansoor nada shekara daya Aysha tahaifi zeenat kusan atare suka taso Wanda nasan kunsan hakan yanzu bari infada muku ainihin dalilin dayasa nataraku anan.

Ranar wata lahadi yakasance kwanar hafsat ne nadawo daga dubai sena sauka a part dinta, nashiga har bedroom dinta bansameta ba senayi tunanin ko tana toilet haka nazauna nayita jiranta shuru_shuru bata fito ba sena je jikin toilet din nayi knock naji ba alamar mutum yasa nabude naga wayam tunani nafara to ina ta shiga saukowa downstairs nayi naduba dakin mansoor nasameshi yana bacci , fitowa nayi har nazo zanfita naji kamar ana magana awani dakin saukan ba ki da hafsat ta hana kowa shiga acewarta intayi ba ki anan suke sauka kuma ni bana ganin kowa yana zuwa wajanta hatta danginta tamusu iyaka da gidan kuma bata zuwa se ta bushi iska , tsayawa nayi ajikin kofar na kasa kunne na dakyau wasu irin sambatu ne ke tashi wanda baze fadu ba kuma bana mutum daya ba . ahankali nabude kofar natsaya abakin kofar mummunar gani idona yayi da har yau inna kulle idona inaganin wannan bakar ranar , sauka idona yayi akan hafsat da wasu mutane kusan mutum uku da ita na hudu cikin wata suffa nadaban me ban tsoro jikinsu duk gashi babu kaya ajikinsu tsirara haihuwar uwarsu , sun sa namomin mutane agaba sunaci hade da shan jini hankalina yakai kololuwar tashi narasa meyakamata inyi in fitane ko in tsaya , yanda nake kallon su haka su ma suke kallona. bacewa sauran sukayi yarage daga ni se hafsat adakin nan take takoma ainihin suffar mutane, matsowa kusa dani tayi ta ce kai mijina ne kuma inasonka amma yanzu yazama dole in kasheka kokuma kahaukace amma kafin nan bari indan baka takaitaccen labarina tafada tana yar murmushi tafara magana , nakasance tun ina yar karama dani nake shaawar son cin naman mutane domin ko a labarai haka ake fada wai naman mutum yafi kowace nama gardi dakuma dadi hakan yasa nadauki son duniya na daurawa naman mutum, wata rana naje makaranta ina primary 5 naje toilet yin fitsari naga yarinya karama yar nursery 3 tafito daga toilet din tanata wasanta dubawa nayi naga babu kowa awajan ganin wannan babban damane agareni inna barshi subucemin zeyi yasa nakirata na mata wayo nakaita toilet din dukda banida wani isheshen karfi haka nayita kokarin murde mata wuya harnayi nasara na kasheta zama nayi dirshen akasan toilet din nasa hakori nafara fincikar namanta inaci senaji wani bankwarakwai saboda shine karo na nafarko amma hakan nadingaci seda nayi nisa acin naman sannan nafarajin dadi nakaimin har tsakiyar kaina haka nacinye yarinyar nan tas yayi saura kasusuwanta, tarkatasu nayi nazuba acikin dustbin nawanke toilet din yanda babu wanda zeyi zargin wani abu daga nan nakoma aji nadauki jakata nakoma gida kwanciya nayi cike da nishadi nafara bacci , abaccin ne naganni awani dokan daji me matukar girma sosai ga mutane sanye da bakaken kaya fuskokinsu arufe, sunatamin barka da zuwa cikinsu banji wani tsoro ba lokacin da suka sanar dani nazama daya daga cikin yan kungiya kuma zansamu duk abinda nakeso daga kudi duk wani abun duniya ga cin nama da shan jini sosai nayi farin ciki shisa duk wayanda sukace inkawo ayi sadaukarwa nake kaiwa , ganin mutane danakeyi ne yasa koda yaushe nake shiga cikin bukatuwa da cin nama idan kuma haka yaci gaba da faruwa to tabbas zaa ganoni shisa nake kebe kaina ni kadai bana shiga harkan kowa wanda kuwa yayi kuskuren takalata senaga bayanshi hankalina yake kwanciya , ana haka Allah yadoramin sanka kuma naji bazan iya cutar dakai ba harmukayi aure dalilin dayasa natsani shayida da zainab kuwa tunda nasamu cikinsu nabayar dasu ga kungiya akan insunzo duniya zaayi sadaukarwa dasu amma kwata_kwata hakan ya gagara akwai tsari ajikinsu domin me martaba yanason jikokinshi shisa tun ranar da sukazo duniya yake basu maganin tsari daga dukan sharrin mugaye acikin ruwan zam_zam , shisa na tsanesu tunda sungagara biyamin bukata , sekuma kadaukesu ka kaiwa matarka su wacce duk duniya babu wayanda natsana sama da ita da yayanta kuma nice nan ajalinsu sena kashesu musamman wannan dan nata azaad. haka tadinga fadamin asalin kalarta kwakwaran motsi nakasa ji nayi duk duniya babu wacce natsana sama da ita dakyar na iya bude bakina nace mata sena tona miki asiri kowa seyasan kedin wacece muguwa azzaluma macuciya kawai bari kiji na sakeki saki uku babu ni babu ke har abada , anan ne tayi kokarin kasheni da tsafi nadinga adduo’i bakina yaki shuru , hakan yasa tayi kokarin haukatani nan ma Allah bebasu saa akaina ba umarni shugabansu yabata kawai suka rubemin baki koda inasan infadawa mutane halin da ake ciki amma se inkasa , na matukar shiga damuwa seda nadanyi rashin lafiya aysha koda yaushe tanakan tambayata meyake damuna sede ince mata babu komai haka rayuwa taci gaba har lokacin da azaad yahadu da muguwar hatsari wanda ita da alh Ibrahim tijjani suka hada hannu dan kasheshi duk nasani amma ba halinyin magana , wato abinda yafaru jiya shine jiya harna fara bacci azaad yakirani yake shaidamin zekasheta kafin indawo inajin hakan nagano yasan komai hakan yamin dadi shisa nazo na warware muku komai ” in banda koke_koke ba abinda ke tashi afalon musamman na anty shayida da anty zainab jin wacece uwarsu dakuma irin tsanar da ta musu sosai ummi take kuka lamarin ya girgiza duk wani wanda yake cikin falon domin mommy ta gurbata rayuwarta dakuma cutar da rayuka mara adadi wayanda hakkinsu kadai sun isheta saboda tazabi duniya tayi son kai da son zuciya , kifa kai fanan tayi ajikin Mr azaad tana kuka domin al amarin kamar a film , dukda kasancewar ita tun farkon haduwarta da mommy tasan akwai wani abu ashe macijiyar sari ka noke ce , haka zeenat ma tana rungume da ummi tana kuka , mazan kuwa idanunsu yayi ja jijiyoyin kansu yatashi jisukeyi kamar su kamo mommy su kasheta kowa yahuta musamman Mr azaad barinma inya tuna yanda ta tsani yan uwanshi da ita tahaifesu shuru kawai yayi dan inya bude baki zeyi magana yasan kawai kalmar kashe mommy ne kawai ze fito daga bakinshi, kuma muddin yatashi tom nan ma seya kasheta shisa kawai yayi shuru dan yaga shi yafi alkhari yana lallashin fanan dake kuka .

Abba ne yadaga waya yakira securities yace su kunce mommy sukawo ta , shigowa sukayi da ita duk tafita a hayyacinta domin igiyar da sarauniya ta daureta dasu kamar na dalma ne azaba kadai takeji ga shi duk wani karfin tsafinta yabar jikinta dungurata sukayi a tsakiyar falon ta fadi da kallo kawai suke binta anty shayida ce ta ce ” mommy Meye zesa ? Mommy me muka Miki ? Meyasa kika jefa rayuwarki a irin mugun halin me kika nema kika rasa? Mommy bakya tuna haduwarki da Ubangijinki ? meye ribarki yanzu meyasa za ki mana haka bakya tunanin ya rayuwarmu zata kasance ?” muryanta dake fita dakyar ta ce ” tsanar dana muku baze taba canzawa ba kuma yanda na kudurta aniyar ganin bayanku tofa sena aiwatar, tsabar tsanar dana miki shisa daga zaran kinsamu ciki nake cinyewa tunkafin kusan da hakan tunda ke kinfi karfin kungiya ai abinda ke cikin be fi karfi ba sau takwas kina samun ciki ina cinyewa haka kema zainab naso in miki se kuma banyi nasara ba kai kuma ” tafada tana kallon abba” tunda na fuskanci ammi ta tsaneni yasa nakasheta domin yanda ta tsaneni nima haka na tsaneta, se kai azaad dan iskan yaro duk wata hanyar da zanbi wajan kasheka nabi amma hakan beyuba amma sena kasheka din ” daura hannu akai anty shayida tayi tamike tana kuka tana maganganu kamar wata mahaukaciya Jin abinda uwar da ta haifeta tayi mata ashe ita ba juya bace, mahaifiyartace take cinye mata ciki ganin zata iya zaucewane yasa abba yarikota yarungumeta yana lallashinta yana jin ciwon abinda hafsat ta aikata mishi wato ita takashe ammi tabbas dole yadau mataki akan mommy domin ta cutar dasu da yawa , tsananin tashin hankali kam yau sunjishi ,yau itace bakar rana agaresu haka mommy tadinga confessing abubuwan datayi , tsuma kawai da rawa jikin Mr azaad yakeyi mikewa yayi da niyar damko mommy abba yamishi alama da ido komawa yayi yazauna barin falon areef da fawwaz sukayi dan insuna kallon mommy jisukeyi kamar su mata mummunar kisa hakan yasa suka wuce part dinsu zuciyarsu na tafasa.
Ana cikin wannan mugun yanayin mommy ta fashe da wata muguwar dariya tana sambatu da kuma fade_fade nan take tafara fincike gashin kanta tana zubarwa akasa lokaci daya ta haukace, hauka tuburan babu wanda ya kalli inda take domin itadin baabin atausayawa bace mikewa tayi da gudu tafita afalon baba me gadi na bandaki tabude yar karamar kofar gate din tayi waje bin bayanta securities din gidan sukayi , Ina tariga da ta musu nisa tahaukan titi wata katuwar tankan ruwa ne yabi takanta ya takata haka namanta yayi piecing akan titi harta kanta seda yatarwatse kwakwalwarwa awaje haka mommy tayi mutuwar wulakanci atozarce gaba daya jikin securities din yayi sanyi haka wasu daga cikinsu yashiga gida yasamesu afalon yasanar dasu abinda yafaru haka Abba,ummi, zeenat,anty zainab,anty amina dakuma anty shayida dake atare da abba tana kuka suka fita Mr azaad kuwa ko ajikinshi yadauki fanan suka haura part dinshi .

Tunda suka kusa isowa inda tanka yayi kaca_kaca da mommy suka fara ganin namar jikinta daya tarwatse ga dandazon al’umma dake tsaye awajen, sa hand gloves securities din sukayi suka fara hada naman mommy waje daya aka samo leda zasu kwashe kenan wuta yatashi akan namar haka wuta yacinye naman nan tas yayi saura toka kowa nata tofa albarkacin bakinshi da yin tir da mommy haka suka diba tokar akasa aledar. jiri ummi tafara ganin tana kokarin faduwa anty zainab da anty amina suka riketa suka koma cikin gida suka zauna suna jimamin wannan bakar rayuwar duk sunyi shuru lokaci daya sabon tsoron Allah yasake shigansu ganin irin mutuwar wulakanci da mommy tayi daga fitarta da zuwa fada musu da securities sukayi befi minti biyar ba amma har rai yayi halinshi sosai sukeyi mata adduah samun rahaman Allah . dakyar aka samu siraran mutane dabasu fi 10 ba suka sallaci mommy ciki kuwa harda Abba shikadai domin daya kira waziri yasanar dashi ma kawai cewa yayi baze samu zuwaba Allah yajikanta yakatse kiran, yakirasu fawwaz da areef suma kin fitowa sukayi haka Mr azaad dayaga Kiran Abba ma kashe wayarshi yayi gaba daya haka aka je aka binne tokar nata a makabarta suna mata adduah.

zaayi zaman makoki abba ya ce baa gidanshi ba haka sukaci gaba da zama kowa jikinshi lakwas ba karfi anty shayida kuwa zazzabi ne me zafi yarufeta anty amina takira doctor safiya tazo tasamata drip abun tausayi . tunda Mr azaad da fanan suka koma part dinsu basu sake fitowa ba se karfe 3 , suka fito cikin shiri nazuwa anguwa babu yanda fanan batayi dashi akan abar maganar tafiyar gobe ba amma yaki haka dole yasata tashirya zuwa gida tasanya hijab dinta shima yasha half jumfa sunyi matukar kyau haka suka fito ba kowa afalon se zeenat kallonta fanan tayi ta ce ” zee hafiz ya farka ne ?” amsa zeenat tabata ” eh yafarka Kuma cikin nutsuwa babu wani damuwa atare dashi yayi wanka ummi tabashi abinci yaci yanzu hakama bacci yakoma ” murmushi sukayi atare ita da Mr azaad daman jiran farkawarshi sukeyi suga reaction dinshi Kuma ga shi alhamdulillah. zeenat ta ce ” anty fanan ina zakuje?” ta ce ” zamuje gida ne yi musu sallama gobe zamu tafi ” dama zeenat yau setaji gidan badadi bawani annashuwa kowa yana cikin damuwa saboda abinda yafaru hakan yasa tacewa fanan ” zan biku bari indauko gyale ” tafada tana haurawa part din ummi dasauri dan tasan halin Mr azaad inde tabata mishi lokaci yanzu zata dawo tasamu baya nan , tafito tasamesu a packing space duk suna cikin motar shiga back seat tayi ya tada motar suka tafi .

Kamar wasu kurame tunda suka fara tafiya babu wanda yace wani abu har suka isa yayi packing abakin gate , fitowa sukayi daga motar suka shiga gidan bakinsu dauke da sallama mama ce kadai agida kuma tana bacci adakinta, auta da hairah da ya usman sunfita dan yace zekaisu yawo ,zama sukayi akan kujera fanan takawo musu drinks da ruwa hade da snacks dan mama batayi girki ba saboda batasan da zuwansu ba kuma ita dayace agida dakin mama fanan tashiga tasameta tana bacci tashinta tayi ta hanyar kwanciya ajikinta tashi mama tayi ta ce ” dama nasan seke din ai tunda auta bata nan ! yaushe kukazo?” Mama ta tambaya tana daura dankwali akanta , ta ce ” bamu dade da zuwa ba suna falo ” daukan hijabi mama tayi tasa tafito tabar fanan a dakin. murmushi tayi ta ce ” sannunku da zuwa ?” gaisheta Mr azaad yayi sannan zeenat tagaisheta ta amsa zama tayi tana tambayarsu mutanen gida suka amsa da kowa lafiya haka suke hira sama_sama dan mama najin kunyar Mr azaad amatsayinshi na sirkinta , fitowa fanan tayi da liffaya ahannunta ta ce ” mama wannan na waye ?” kallonta mama tayi ta girgiza Kai ta ce ” na wa ne jiya babanku yakawomin meyafaru” yar murmushi fanan tayi ta ce” bakomai naganshi acikin leda ne shine nace bari intambayeki ” dariya mama tayi dan tagano fanan wato yamata kyau shine taketa wannan kauce_kaucen ta ce” to kuma seki mayar ko ” turo baki tayi ta ce” tom ” dariya taso bawa Mr azaad danshima ya harbo jirgin nata . Dawuwa falon tayi tazauna sukaci gaba da hira ganin kamar su Mr azaad basu sanarwa mama anyi rasuwa bane yasa ta ce ” mama anyi rasuwa a gida ” ta kasan ido Mr azaad yawatsa mata harara dauke ido tayi kamar bata ganshi ba , mama ta ce ” Allah sarki waye yarasu ” ta ce ” mamansu anty shayida ce ” sosai mama tayi musu taaziya dukda Mr azaad bece komai ba se jinjina kai da yakeyi zeenat da fanan kawai suka amsa , ya ce ” mama dama munzo muku sallama ne zamu tafi USA gobe in sha Allah ” adduah Allah yatsare hanya mama tayi musu bata sake cewa komai ba . tashiga kitchen domin hada musu abinci bin bayanta fanan tayi ta tayata sukayi komai tare jollof din dankalin turawa sukayi dayasha vegetables da nama ta shirya musu a food flask tajera a tray ta bawa fanan takawo falo .

Daki mama tashiga dan tabarsu suci abinci , , serving din Mr azaad tayi a plate hade da sa mishi ruwa a glass cup da drinks din ta jera mishi komai agabanshi sannan tasa musu nasu itada zeenat tamike takai musu dakinta da ruwa ta ce zeenat muje ciki , shiga dakin zeenat tayi fanan na kokarin tafiya Mr azaad yariko hannunta yajawota kan kujeran ya ce ” inazakije kuma?” ” zamuci abinci ne nida zeenat ” cewar fanan, rike habarta yayi yana kallon cikin idonta ya ce ” nikuma dawa zanci abinci in kika tafi ” zaro ido waje tayi ta ce” ka lan mama tafito taganni ina cin abinci tare da kai ah ah gaskiya ” bata fuska yayi” to shikenan tashi kije kici keda zeenat din nibazanci abincin ba hakan yamiki ina ” ya karishe maganar yana kwantar da kanshi ajikin kujeran ya lumshe ido haka bayanda ta iya ganin ranshi yabaci dantace zasuci tare da zeenat yasa tadibo hadaddiyar jallof din dankalin takai mishi baki, bude ido yayi yasaukesu akanta bece mata komai taci gaba da bashi abinci se lumshe sexy eyes dinshi yakeyi tsabar yanda girkin ya mishi dadi , takawo mishi spoon dede bakinshi kenan yasa hannu yarike spoon din yakarba yakai mata baki , haka sukata feeding din juna har suka koshi sukasha ruwa da drinks.
abangaren zeenat kuma gajiya tayi da jiran fanan yasa tafito dan kiranta taga sunacin abinci ita da Mr azaad, komawa ciki tayi ta zauna tana “lallai matar nan shine zata sani jiranta tasan da mijinta zataci nima de Kwanan nan zanyi mijin yauwa ” ita kadai take wayan nan magana tanacin abincin . Kwashe komai fanan tayi takai kitchen tadawo gun Mr azaad din bata dade dazama ba sega auta tashigo da gudu tayo wajan Mr azaad, ganin tanufo wajanshi yasa yabude mata hannu tarungumeshi tana ” oyoyo Yaya balarabe, ai ina ganin car awaje nace it must be you ashe kaine ” tafada tana haki dan dama gashi sun gaji ga gudun datayi ya ce ” cutie Ina kikaje haka ?” ta ce ” ya usman ne yakaimu yawo nida anty hairah kasan ina da ina mukaje ?” girgiza kai kawai yayi tacigaba ” munje ice cream planet bayan mungama shan ice cream mukaje makay shawarma daga nan ya usman yakaimu shaf’an sekuma yakaimu G_connect nayi lilo ” fanan kam bin auta kawai takeyi da ido ganin yanda intana magana bata tsayawa kamar suhaima ta ce” sannu fa auta tunda ba magana ko ganina ne bakiyi ba ?” ” Laaah anty fanan kece nadauka ai Yaya balarabe ne kawai yazo ” yanda take fitar da magana kamar wata uwar mata , shuru kawai fanan tamata . dariya Mr azaad yayi ya ce” ah gaskiya kunsha Lilo kam ” yana rufe bakinshi ya usman suka shigo shida hairah tsugunawa hairah tayi ta gaishesu suka amsa fuska asake, musabaha ya usman da Mr azaad sukayi nanma fanan tafadawa ya usman anyi rasuwa, taaziya yayi musu . Seda sukayi sallar la’asar fanan da hairah suka dawo falo suka zauna tana tambayarta ya karatu , Zeenat dake daki fitowa tayi ta gaishe da ya usman da basu dade da shigowa ba daga masallaci shida Mr azaad. kallon fanan tayi ta ce” bari in shiga gidansu amira! hairah zoki rakani ” tashi hairah ta ce ” tom ” dakin mama tashiga tafada mata zata raka zeenat gidansu amira mama tace sekun dawo fitowa tayi tasamu zeenat najiranta ta ce” anty zeenat muje ” harsun kusa bakin kofa fanan ta ce” ku tsaya ” sannan ta kalli Mr azaad murya kasa_kasa ta ce” habiby ayyah inje gidansu amira?” ” Eh ” yace aikuwa dasauri ta mike tayi gaba tabarsu abaya, dariya ya usman yayi ya ce ” to sannu iyah ! sun jiraki shine ke kina zuwa kikayi gaba kika barsu ” dariya kawai tayi batace komai ba , tafiya sukeyi suna har hira harsuka isa gidansu amiran afalo suka sameta tana waya da ya al ameen se zuba mishi shagwaba takeyi tana ganinsu ta taso tarungume fanan ” oyoyo my bestie” ” oyoyo bestyna kuma antyna ” cewar fanan ya al ameen yanajinsu yayi dariya kawai yakashe wayar. dakin Amira suka shiga suka yada zangon hira hairah de jinsu kawai takeyi batace komai ba saboda duk sun girmeta babu yanda zatayi tasa musu baki a magana basu sa ko ta ba aciki , lura da hakan dasukayi ne yasa suke hiran harda ita , takuwa sake jiki dasu sunata hira drinks Amira takawo musu sukaci gaba da hira. Agidan sukayi sallar mangrib sannan suka fito suka shiga dakin hajiyarsu suka gaisheta da fara’a ta amsa musu fanan tafada mata anyi musu rasuwa hade da gobe zasuyi tafiya tazo musu sallama taaziya hajiya tayi musu da adduah Allah yakiyaye hanya , sannan suka wuce gida sunko dawo adede baba yadawo yana gida gaidashi sukayi yayi musu taaziya domin mama da ya usman sun sanar dashi kuma sun sanar mishi da gobe zasuyi tafiya hakan yasa yabukaci ganin su , su biyun adakinshi , shinfida sallaya fanan tayi akan carpet din suka zauna adakin baba , ganin yanzu sun dedeta kansu ne yayi wa baba dadi nasiha me ratsa zuciya da kashe jiki yamusu yahada da musu fada , daga karshe yamusu Allah yatsare hanya,suka fito akunne Mr azaad ya rada mata ku shirya kuzo mutafi saboda zamu tsaya agidan maman junior tace mai to tasanar da zeenat kintsawa sukayi . Suka fito zasu tafi mama ce tafito hannunta rike da fashion bags guda uku tabawa fanan daya tabawa zeenat daya sannan tabawa amira daya godiya suka mata takoma ciki duk suka rakasu har bakin mota suka tafi hade da kewarsu Amira ta wuce gidansu tana me musu seda safe .

Shiga gida ya usman, hairah da auta sukayi dakin baba ya usman yayi sallama izinin shigowa baba yabashi zama ya usman yayi akan sallayar yana sunnar dakai kasa, tunda yashigo baba ya lura dashi yasan akwai magana abakinshi ya ce ” kazo kamin shuru kode babu abinda zaka fada ne usman?” Ya tambayeshi yana kallonshi sosa wuyanshi ya usman yayi ya ce ” am dama baba maganar hairah ne” sekuma yayi shuru , murmushinsu irin na manya baba yayi domin kuwa ya ganoshi seya nuna kamar besan meyake nufi ba ya ce ” tofa! meyasami ita hairah ?” yasake jefo mishi wata tambayar. Ya usman ganin baba yakasa gano inda ya dosa ne ya ce ” dama inason a tambayamin aurenta ne ” gyara zama baba yayi ya ce ” to shikenan tunda naga kazo da wannar maganar nasan kun gama dedeta kanku kai da ita hairah in sha Allah zaa tambaya maka aurenta inyaso se a hada auren nakun dana sauran yan uwan naka ! se anjuma tashi ka tafi bacci zanyi ” dariya ya usman yayi dan ya lura yau baba naji da barkwanci ya ce ” nagode sosai baba Allah yakara girma ” ya amsa da” ameen” sannan yafita da farin ciki aranshi kamar yazuba ruwa akasa yasha dan jindadi . Kiran Abba baba yayi yamishi taaziya.

Wasa takeyi da junior dake kan cinyarta se dariya yakeyi ga anty firdausi akusa da ita daddyn junior Kuma sunje sallah masallaci shida Mr azaad basu dawo ba.

Ina jiran comments dinku.

Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy .
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & written by ✍️
MRS ISHAM
(* Yar lelen Jarumai*)

 

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

⚜️ J. W.A ️

 

 

Gargadi…..
Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin.

 

 

 

Back to top button