Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 1

Sponsored Links

*1*

*_Bazanci gaba dasa number ba course masu fita dashi Allah ya isa kuma ban yafe ba duk wacce ta fitarmin da buk saboda bake kadai kika biya ba faqat_*

Da mugun gudu motar me qirar Ferrari ta shigo makarantar Adon Bayero University wadda suke Kira da new set birki ta taka da sauri tare da furta “ya Salam na bigeshi wlh na bigeshi rahama” tana fadin haka ta balle murfin motar ta fito da sauri wata kyakkyawar budurwa ce chocolate color wadda da gani babu tambaya kasan tanaji da kanta kuma tana tashen rashin kunya duba da yanayin shigarta.

 

Riga da wando ne farin jeans da jar riga three quarter ta hade gashinta na fulanin asali ta daure a baya ta dora wata hula me kamar nadin gammo a kanta tsakiyar kanta a waje ta zuba zobunan gold qafa da hanu sai daukar ido takeyi kamar walqiya duk wani lafiyayyen namiji idan yaganta a yanda take sai yaji yarr a jikinsa yanda take takawa duwaiwakanta na juyawa hips dinta yana daukan hankalin maza duk inda kyau yake Samha takai a kirata kyakkyawa.

 

Da dan sassarfarta ta qarasa ta tsuguna gaban kyakkyawan farin saurayin takai hanunta zata kamoshi ya kuwa daga hanu ya dauketa da wani lafiyayyen mari ta dafe gurin da sauri ta dago ta dubeshi bakinta yana rawa kafin tayi mgn ya sake dauketa da mari yace “ke wacce irin yar iska ce ki rinqa yiwa makaranta shigar isa saboda rashin tarbiyya dubeki waike kin waye jahila daqiqiya dake saboda kunfi qarfin kowa shiya aka kyaleku kuke abinda kukeso to wlh ba commusioner ko gwamna ne ubanki zan iya bi dake da abinda kike taqama dashi banza shashasha ballagaza kawai dubi shigarki waike qaramar yar iska mtssss”

 

Yaja tsaki tare da miqewa ya dingisa qafarsa dake zubar jini ya nufi wani teather dake kusa da gurin, wasu hawaye ne masu zafi suka zubowa Samha a idonta tunda take baa taba marinta ba ba marin ne yayi mata ciwo ba irin kalaman batancin daya fada Mata sune sukafi komai zafafa zuciyarta fitowa qawarta Rahmah tayi ta kamo hanunta tace “kinyi mugun bani kunya Samha kamar ki ki tsaya wannan qazamin dalubin ya mareki duk jin izzarki da isarki ni wlh tsoroma naji kar wannan daskararren hanun nasa yaji miki ciwo” ta fada tana shafa kuncin qawar tata.
Kawar dakai tayi ta furzar da wata iska me zafi ta taka a hankali zuwa inda motarta take ta zagaya wajen me zaman banza ta zauna tare da cillawa Ramsy key din taja suka qarasa.

 

Har Ramsy tayi parking Samha batasan sunzo ba sanya hanu Rams tayi ta janye mata tagumin tace “ki manta kawai mu ya tabo wlh Idan yayi wasa sai munsa anyi withdraw nasa a skull dinnan.
“Wayeshi a makarantar nan da baisan wace ni ba wayeshi da baisan matsayi na ba meye taqamarsa a school dinnan Rams meye taqamar guy dinnan daya jizgani haka?”

 

Bude mata motar Rams tayi tana riqe da jakarta tace “ki manta kawai dole ya girbi abinda ya shuka Samha….” Daga mata hanu tayi suka jero matasan dake gurin suka taso su uku suka rungume suna fadin Allah ya taimaki uwar dakin mu yaufa da haduwa a club.

 

Murmushi tayi na qarfin hali karo na farko data farayin danasanin shigar isar da takeyiwa makarantar tasu ta hanyar yin gudun wucce sa’a tare da buge duk wanda tsautsayi ya fada kansa.
Wasu yan matane su uku suka taso bayan matasan mazan sun gama shafeta daga sama har qasa dayan yayi kissing boobs dinta suma yammatan rungumeta sukayi suma murmushin yaqen tayi musu ta wuccesu ta nufi Hall din da zasuyu lecture ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

 

Shigowa sukayi suka zauna kusa da ita dukkansu fuskarsu dauke da damuwa da alamun Rams ta qyasa musu abinda ya faru Surayya ce ta ruqo hanunta tace “kiyi cooling mind dinki Samha babu wanda ya isa ya takaki a cikin mkrntar nan mu kyaleshi wlh saiya gane kurensa sai yasan ya tabo click din masifa da bala’i” Nadiyya ce ta cafe tace “kecema kika ba damu Samha da kinbi takan dan iska kin markadeshi kamar greater aida baiyi mana wannan cin mutuncin ba” Rams ce ta cafe zaren zancen da cewa “ni nama rasa me zance tun dazun wlh ni tun ranar dana ganshi naga yanda yake taqama da kyau da isa gaba daya naji na tsaneshi” Zainab da tunda aka fara mgnr take kallonsu tayi qwafa tace “uhm kune baku sanshi ba bakuda lbrnsa a haka jin kansa yake saboda yana da kai sosai Abdullah kenan duk faculty of law shayinsa sukeyi asalinsa dan sarautar Katsina ne amma da ganinsa a wahale suke sarautar ma wlh” dukkansu suka kwashe da dariya amma banda Samha data dora hanunta a kanta tace “oh sheet!”

 

Tsayawa sukayi suka zuba mata ido takart ta dauka ta fito da bututun shisher ta miqawa Rams da sauri ta karba ta dauki magic could ta kunna Mata a ciki ta zuba mata flavor din ta miqa mata ta sanya a bakinta ta zuqa ta fesar tana sauke ajiyar zuciya zuqarts biyu tayi jifa da ita ta dafe kanta tace “tention din kaina yafi qarfin wannan bude Jakarta ta kumayi ta dauko wasu qananun qwayoyi ta watsa a bakinta tabi dasu da ruwan ever din dake hanunta daidai lkcn malamin nasu ya shigo duk faculty of educational psychology ana tsoron malamin amma banda wannan click din sai ya kasance shine ma yake tsoronsu saboda tsagerancinsu dadinta daya shugabar tasu wato Samha tana gane darasin nasa sosai wanda ya sani bawai donta gane din take zama ba kawai brain dinta ce me saurin ganewa batare data nemi shawararta ba gyaran murya yayi yace “yau zamuyi lecture ne akan clinical psychology…”

 

Iyakar abinda Samha taji kenan harya gama ya fita kanta yana kife saman dext tana baccin qwaya sosai lamarin yarinyar yake bashi mamaki bata missing attending lectures amma kullum cikin maye take indai lkcn lecture dinsa ne ance talauci shine yake sanya lalacewar tarbiyya da shaye shaye to kuwa idan har gaskene da Samha Sa’ad Dandoki batayi ba saboda talaucin ma gudunsu yake saboda yasan uwarsa zaici harda ubansa a wannan family din.

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

Back to top button