Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

Kawali Ne 3

Sponsored Links

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*3*

“Siyama lokaci fa yayi daya kamata ace dik wannan shashancin kin denashi duba da ganin yadda rayuwarmu ketafe cike da ƙalubale,yakamata muji tausayin mahaifiyarmu kinga ba wadatacciyar lafiya gareta ba”cewar wata matashiyar budurwa wacce shekarunta zasukai sha takwas.

Wacce aka kira da siyama kyaɓe baki da fuska tayi sannan tace tana tura ɗankwalinta gaba”Rayhana,inaso kisani Allah yayi mu tagwaye,yayi mu talakawa futuk,se kuma ya kyautata surar mu maana yamana kyau fiye da duk inda ake hasashen kyau,yayimana diri irin wanda kowacce mace take fatan mallaka,Rayhana Allah fa be tsaya nan ba seda yasa mana farinjini kowa sonmu yake.da talauci kawai ya ragemu,shine kike so inzo in jubge komai ahijabi bazanje in nemi arziƙin da ƙirar da yay minba,naki wasane rayhana wallahi bariki ni banyi komaiba ma tunda har yanzu ban fara hulɗa da gomnoni da ministociba”

Tunda siyama ta fara magana hawaye kebiyo idanun rayhana,har ta kammala sannan rayhana tace”siyama wannan kyau da Allah yay mana shine babban iftilain daya haɗamu dashi,wanda in bamuyi takatsantsan ba zekaimu ga shiga wuta,kuma….”

Da sauri siyama takatseta da cewa”kece kika ɗauki kyan daya baki a iftilai,niko nawa a mazaunin jari na ɗaukeshi,tsanin dazan yi amfani dashi inhau sama”ta ƙarasa maganar tana jefa mata harara.

Murmushin ƙarfin hali rayhana tayi sannan tace,”amma kinsan halin da ummanmu ke ciki na hawan jini ko?”

“Setace miki ni na ɗora mata ko?”cewar siyama afusace dan rayhana tafara kaita bango.

“batace ba amma ay kinsan ranta beson wannan abinda kike”

“To kibata shawara ta koyawa ranta so”tana kaiwa nan ta miƙe ta gyara tsayuwar matsatstsan siket ɗin dake jikinta tasa kai tai ficewarta tana kaɗa mazaunai.

Bin bayanta rayhana tayi tana girgiza kai cike da takaicin halin da ƴar uwarta ke ciki.

Fitowar mahaifiyarsu daga ɗakine yasata saurin miƙewa ta ɗauko mata kujera ta zauna tana mata sannu.

“yauwa rayhana Allah yay miki albarka nagode,karki gaji kici gaba da faɗa mata insha Allahu wataran zata ɗauka”

“To mama zanci gaba amma siyama na buƙatar taki adduar ma Dan wlh tayi nisa mama”cewar rayhana hawaye na biyo idonta.

“Allah ze kawo sanadin shiryiwuwarta karki damu”cewar mahaifiyarsu tana shafa kan rayhanar.

Haka suka ci gaba da hira akan halayen siyamar gamida miƙa kukansu ga Allah.

*********

Siyama,Rayhana Abba takai tagwayene ƴan kimanin shekaru goma shatakwas aduniya.

Identical twins ne tayadda ko iyayensu a murya kawai suke banbancesu kasancewar Rayhana bata da harafin R abakinta,da haka kawai ake banbancesu,amma in bata hakaba basu da banbanci.

Haifaffun garin takai ne ta jihar kano,mahaifinsu malam Adamu wanda akafi sani da Malam Abba mutumne me ƙaramin ƙarfi wanda beda cin yau bara nagobe seya fita ya nemo.

Matarsa inna Rabi tun wajan haihuwar tagwayen nata tasamh matsala amahaifa bata ƙara haihuwaba,mace ce me haƙuri da kawaici da kauda kai akan komai na rayuwa.

Rayuwa suke ta rufin asiri ita da mijinta da ƴaƴan nata,

Kyawawane ajin farko fiye da duk yadda akw tsammani kyansu ya wuce nan,tun tasowarsu siyama nada ƙiriniya saɓanin rayhana,shiyasa kullum cikin ɗauko magana take.

Tunda suka girma suka kai matakin balaga siyama ta fara yawan banza inda intaga dama ma setaƙi kwana agidan takwana ɗakin saurayi.

Tun iyayen basu gano halin datake cikiba har suka gano.

kullum cikin addua da fatan Allah shiryeta suke sabida sunyi faɗan amma bataji.

Rayhana ko yarinyace me kamun kai da natsuwa,uwa uba gata da ilimin addini dan ita siyama tajima da cire kanta amakarantar islamiyyar.

Bata da hayaniya ko kaɗan,gata da biyayya,uwa uba girmama duk wanda tasan ya girmeta.

Shiyasa jamaar garinsu kowa yabonta yake saɓanin siyama da kowa ke turrr da ita ana tsine mata.

Mahaifinsu ya rasu shekaru biyu dasuka wuce shiyasa nauyin komai yadawo kan mahaifiyarsu,wacce ba isasshiyar lafiya gareta ba.

Hakanne ya ƙara ba siyama damar cin karanta babu babbaka dan dama shike taka mata burki to yanxu bayanan.

 

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Back to top button