Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 61

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*61*

Zee ta baje a falo tuni an jera mata abincin da aka kawo daga gidansu tare da matar da zatana tayata aiki saboda cikinta ya tsufa Ummeey na gefe tana Shan watermelon zee ta kalleta tace ” Ina shegiyar aminiyar taki ”
“tana nan dazu muka rabu ta koma gida, ke anty wai mijin nata Ina yake aikine bayan kamfanin da yake dashi ”
” Ke dallah mutum nada companies guda nawa kike zancen Wani aiki, Yana da Wani a can Saudi fah yanzu maganan da nake Miki Yana Shirin Bude banki tare da wasu larabawa ai Ayman ya haye iswear badai kudi ba sai dai Wani abu daban, kinsan from day one shi na fara cewa Ina so Allah Baiyi shi zan aura ba da yanzu nice nake fantamawa ” Ummeey ta jinjina Kai tace ” no wonder..Kinga motoci kala kala Wanda ake Kai besty school dashi kuwa ” “kina magana..dazu fah aka masa clearing Lamborghini guda biyu da ya Siya daga UK ” ware Ido Ummeey tayi ” Lamborghini fah anty ..ke kinsan kudin Lambo kuwa ”
“Don ubanki ni zaki fadawa kudin Lambo …ke ni duk ba wannan ba dama maganan da yasa na kiraki kenan matso nan kiji abinda nake so daga gareki ” magana ta fara mata kasa kasa tamkar mara gaskiya sun share minti 20 zee na mata bayani daga baya tace ” amana …bance ki fadawa kowa ba ko momy ce bana son ta sani sai Abu ya kankama kinsan halinta ”
gyada Kai Ummeey tayi tana murmushi haka suka cigaba da hira kafin zee ta Ciro mata tsaraba.

kwanciya tayi bisa carpet sanyin AC ya mamaye falon ga Kuma qamshin turaren wuta ta kashe fitilu ta sauke curtains bacci takeson Yi yayi sallama ya shigo, yanayin falon ya burgesa matuka lumshe Ido yayi ya karasa inda take kwance ” bacci ne my baby ” “uhmm..
” Yaushe zakuyi exams da Ina son next week muje Sudan ki gaisa da sultan” gyara kwanciya tayi tana kallonsa” jibi zamu fara C.A sai next month zamu fara exams din insha Allah”
“Good..idan kin gama test sai muje ba dadewa zamuyi ba dama ”
“Owk..Allah ya kaimu”
“Ameen..ga motoci a waje sai kin tashi kije ki duba ki zabi Wanda ya Miki ” tashi tayi ta zauna
“Allah ya Kara lafiya da arziki Allah ya saka da alheri nagode sosai ”
Murmushin Jin dadi yayi

“Ameen love aduar ki nake bukata a kullum,ki tayani da adua akwai abinda nasa a gaba Allah yasa alheri ne”
“Allah ya tabbatar da alheri ya Bada sa’a”
“ameen thank you so much, yau me zaki dafa mana kinsan yau kece da girki ” ware Ido tayi
“Har ta gama girkin kenan?”
“Yes..ba ku kuka zabi kwana daidai bah , so just kwana d’aya ne Kuma yau turn naki ne”
“Hmm.. gaskiya nidai A’a na bar mata girkina ”
“Baki Isa bah ni ban yarda ba ” shiru tayi ya kura mata idanu, tabe Baki tayi wannan wace irin jaraba ce kwana d’aya juya idanu tayi” ok me kake so na dafa Maka?” Yaji dadin wannan tambaya
” Tuwon shinkafa da miyar edikang kinsan miyar? Murmushi tayi
” Nasan miyan da ganyen kabewa Ake ”
“Oho..nidai a Lagos na Saba cinsa Kuma Yana min dadi Ina son miyan sosai, yanzu me dame za’a Siya sai na tura Fauzan yaje ya Nemo kafin ki tashi daga bacci”
“Uhmm…ganyen kabewa da water leaf sai crayfish ,sai kuma kpomo Muna da kifi da nama already sai Kuma ya Kara pepper ”
“Ok angama ranki shi dade ” murmushi take ya tashi ya fita. ta koma ta kwanta tana lumshe Ido baccin takeji da gaske nan da nan kuwa baccin yayi gaba da ita ya dan Dade kafin ya dawo ya samu tana bacci ya kashe TV tare da ja mata kofa ya koma part nasa.

Bayan sallar ishah sun hallara cin abinci a bangaren Hajjo meenal na makale da Babanta Failuzaa kuwa anci kwalliya kamar me Shirin zuwa biki hajjo kuwa dogon jilbab ta saka har kasa saboda kananan kayane a jikinta , ta zuba masa komai sannan ta juya wajen Failuzaa ta tura mata a gaba tana cewa ” kar na zuba kadan kice na Miki rowa ”
Murmushin karfin Hali tayi don Gani take tamkar da gangan hajjo taki zuba mata abincin tace ” lah..ai Babu komai bashi kika ci zan rama ne ” Ayman dai ya fara cin abincinsa meenal tace bazata ci ba Failuzaa kadan ta zuba tana cewa
“Yau kin tuna mana Lagos kenan, Qalbee yaushe zamuje Hutu ne Ina missing din beach wallahi ” “idan na samu lokaci sai muje ” daga haka Bai sake magana ba Yana cin tuwon ya masa dad’i sosai ya cinye wanda ta zuba masa sannan yasha ruwa ya dauki y’arsa suka koma falon suna kallon Sunnah TV, Failuzaa tace ” kinje Kinga motarki kuwa, ni har na shiga nawa wallahi motocin sunyi ba karya sai a tayani godiya wajen ango ”
“Ke da mijinki maman meenal idan ba Neman magana ba ni a suwa ” tana Jin dad’in yadda Hajjo ke nuna Halin ko in kula ga mijin nasu dama haka take so ,dariya tayi
“Kinsan mutumin namu sai s slow ni nasan Halin kayana Yana da murdeden haline in fada Miki ”
“Toh ni Ina zan sani nida nazo jiya Kuma Babu Wani shakuwa tsakaninmu ” ” ke kinsan Allah nifa har yau na rasa dalilin aurenki da yayi duk wand ana tambaya sai yace baisani ba , da dai nasan Aman ke nemanki kawai ranar aure na samu labari lokaci d’aya hankalina ya tashi ba kadan ba ”
Murmushi hajjo tayi” Nima har yau Babu Wanda ya gayamin”
“iKon Allah…wato dai rabon zaki shigo rayuwrmu kenan koh, toh Allah yasa dai ki samu ki haihu a gidan ” sai Kuma ta wayance ta kama dariya hajjo tana kallonta kasa kasa lallai dole tayi taka tsantsan da wannan matar me take nufi da Allah yasa ta samu ta haihu a gidan? Haka dai suka ci abincin har suka gama Failuzaa na son gwadawa hajjo wayo tana buga cikinta hajjo kuwa ta nuna mata Baki Isa bah, shiru falon yayi Babu me magana cikinsu meenal tayi bacci bayan baban ya hada mata tea Tasha ya Kalli Failuzaa yace” kije ki kwantar da yarinyar nan”
“Kai Qalbee korata zakayi wato ka gaji damu koh, yanzu zamu Baku wuri a Sha love ” dariya ta kyalkyale dashi tana daukan meenal hajjo dai Wani lokaci tana ganin tamkar matar na da matsalar brain a tunaninta Niko nace bakisan sharrin kishiya bane wannan dariyar da wata a kasa.
Babu Wanda yayi magana ta dauki y’ar ta sabe a kafada tana musu sai da safe Hajjo kadai ta amsa shi gogan ko kallonta Baiyi ba, wayarsa tayi ringing ya dauka ya fara magana da turanci da abokan business nasa yake waya yafi minti 30 hajjo dai d’aki ta shige taje tayi brush ta sake gyara jikinta cire hijabin tayi ta fesa turaruka sannan ta sake fitowa falon baya ciki ta haye 3 seater ta kwanta.
Har 11 Yana gaban system Yana video call Wani zoom meeting suka hada akan sabon bankin da suke Shirin budewa investors din ne sukayi meeting din tare, sai bayan Wani lokaci suka gama yaje ya watsa ruwa ya fito singlet ya saka da 3 quarter off white pants ya fesa turarukansa ya gama Shirin bacci ya Duba time 11:40 wato wannan yarinyar ta nuna sai dai yayi ta bin ta zuwa part nata kenan, silifas ya saka ya wuce part nata idonta biyu tana kallon Wani love film da ya tafi da ita ta amsa sallamar tasa ya dawo kusa da ita ya kwanta ya matseta , turo Baki tayi ” amma dai kasan wannan kujerar ya mana kadan koh ”
“Punishment ne meyasa Baki sameni part dina bah ” ni..ni kallo nake ”
“Tashi muje mu kwanta is late ”
“Film din ya kusa karewa fah ” ” I insist”
“Okay… zata tashi ya jawota ta koma ta fada jikinsa suna kallon juna yasa hannu Yana shafa kitson nata Yana murmusawa juya idanu tayi bazata jure wannan killer smile din nasa ba , jawo kan nata yayi ya maso dashi dab da fuskarsa hancinsu na gugan juna suna shakar numfashin juna , bugun zuciyoyinsu ya karu kowa da abinda yake cikin zuciyarsa sun share 10 minutes cikin wannan yanayin a hankali ya tura lips nasa bisa nata ya zura harshensa cikin bak’inta ya fara tsotsa a hankali tamkar Yana tsoro, numfashin hajjo ya fara sarkewa saboda yadda yake sarrafa harshensa cikin bak’inta it’s so breathtaking…
Ya cigaba da wasa da harshensa cikin Wani salon da batasan dashi ba ya dade Yana Abu guda kafin ta tsinci hannunsa bisa hips nata ya musu Wani irin riko cikin Wani style ya juyo da ita ba tare da ya raba bakunansu ba ya Maida ita kasa shi Yana sama ya cigaba da abunda yake kafin a hankali ya fara zame harshen nasa ya dawo kan lips nata Yana tsotsa a hankali daga nan ya gangara habarta ya koma wuya nan ne tayi Wani irin Mika saboda gaba d’aya tsigar jikinta ya mimmike Yana latsan wuyan nata cikin Wani salon da shi kansa baisan ya iya Hakan ba, hannunsa d’aya ya dora bisa kafadunta ya fara mata tafiyan tsutsa ya dawo dai dai kirjinta nan ne Wani tsoro ya shigeta ta fusge kanta tace ” please ya… Ayman..”
Cak! ya tsaya da abinda yake tana Maida numfashi ya juya ya mirgino ya koma bisa kafet yabar mata kujerar ta runtse Ido har yanzu tana Jin tamkar suna tare gaba d’aya jikinta sai Wani y’ar..yake mata numfashi sama sama take fitarwa , Ayman kuwa gaba d’aya hankalinsa ya gama tashi bazai iya jure rashin wata kusa dashi ba a wannan lokacin don ya fara Nisa cikin system din, idanunsa a rine ya juya ya kalleta Yana Jin Wani irin radadin cikin zuciyarsa shin meyasa ta kasa yadda dashi duk irin kulawar da yake Bata meyasa… Juya masa baya tayi don bazata iya kallonsa ta kulle Ido hoton abin na mata yawo cikin zuci karar rufe kofa taji a nan ta Bude Ido ya tafi kenan baya cikin falon, ya Salam ba dai fushi yayi bah ya Allah ka yafemin…ta furta kamar zatayi kuka ita Batasan dalilin dayasa take gudunsa ba bayan wani bangare na zuciyarta ya aminta dashi ga Kuma irin kyautatawar da yake mata,
Yanzu idan ya tafi wajen matarsa Kuma ya zatayi kenan? Wani hawaye me dumi ya fara gangarowa nace hajjo ga kishi ga iya shirme masu kishiyoyi haka kuke wannan hauka da wawanci koh… gida biyu maganin gobara a kafta, ta rasa me zatayi ita dai bazata iya zuwa part nasa ba Gani take zai rainata haka ta cigaba da Juyi bacci ya kaurace mata alamar shigowar text taji a wayarta ta sauri ta dauka tana dubawa ko Yana jiranta ne sai Kuma bugun zuciyarta ya tsananta sabanin abunda ta karanta cikin text din kamar haka
” Sorry baby girl I have to go to Failuzaa cos kin latsamin zuma a Baki kin barni na kasa controlling din kaina am sorry dafatan zaki yafe mana wannan daren night…”
Wani kuka ne ya kwace mata ta cillar da wayar gefe Bata fado ko Ina ba sai bisa tiles a wannan lokacin screen din ta tsage hajjo Bata bi kan wayar ba sai kuka take ta kankame jikinta waje d’aya tana hawaye.

Back to top button