Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

kawali Ne 19

Sponsored Links

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*19*

Awanni biyu aka kwashe akanta sannan Allah ya sauketa lafiya ta haifo ƴaƴanta kyawawa masu kamanni biyu shiyasa ba ta yadda zaka kallesu kai tsaye kace ga da wanda suke kama.

Sin ɗauko kamannin mahaifansu duka,shiyasa sukai wani irinbsihirtancan kyau dake ɗaukar hankalin maabota kallonsu.

Hajiya da husna murna suke bada wasa ba dan ji suke ƴaƴan kamar nasune.

Itama maijego tana kallonsu taji tausayi da sonsu alokaci guda na shiga zuciyarta,haka ta rungumesu tana hawaye tana musu addua.

Sai washe gari da rana aka sallamosu daga asibitin,suna zuwa gida hajiya tasa ruwa me zafi ta wanke mejego,ta gasheta tsaf,sannan ta wanke yaran.

Kawu se godiya yakewa hajiya harda hawayensa,inda ta nuna masa bakomai ɗa na kowane karya damu.

Da kanshi ya kira mama yasanar da ita batun haihuwar na rayhana,mama jin ta haihu lafiya sosai taji daɗin hakan,sannan tausayin yaran yakamata duba data hanyar da aka samesu ba hanya bace me daɗin ji.

Siyama ma anata ɓangaren ta taya ƴar uwarta murnar sauka lafiya,amma ga yaran addua take Allah ƙarɓi rayuwarsu kowa ya huta.

*********

“Wanne irin wulaƙancine nusaiba nace kituro aɗaukeni ina airport amma har yanzu shiru baki turoba”cewar rayhan lokacin daya sauka a Abuja.

“babe ba kowa a direbobin ni kuma kasan hannuna be faɗaba,kawai kayi bolt”ta bashi amsa a shagwaɓe.

Tsaki yayi ya kashe wayar tashi,dan yasan badan ita yadawo nigeria yanzuba yadawone kawai dan yasamu damar ganin rayhana,tuno hakan da yayine yasa yabar ajiyar kayansa a airport ɗin ya yanki ticket zuwa kano,dan yaje ya ganota yasamu sauƙi azuciyarshi.

Ya iso kano da laasat inda yayi bolt zuwa garin na kaita.

Besha wiyar gane gidan nasuba,dan haka har ƙofar gida yaje yasamu yaro ya ayka yay masa sallama da rayhana.

Siyama na zaune a tsakar gida taji yaro na shaida mata ana sallama da ita.

Tsayawa tayi sororo saida mama tace”maza kije kigano mana ko waye kika sani ko addua tace ta amsu mijin nakine yazo”

Dariya tayi tace tana sa hijab”kai mama daga zuwa tunma kan asan ko waye shi’ta ƙarasa maganat tana fita daga gidan.

Lokacin datai arba da rayhan agabanta tsorata tayi taja baya dafe da ƙirji.

Da ike acikin soron gidan na farko ya tsaya,yana ganin yadda tayi yayi maza ya zube akan guiwowinsa yace “nasani rayhana zaki tsorata da ganina kiyi haƙuri nazo gareki neman yafiyarki rayhana na gaza samun sukuni tun lokacin danai miki haka,don Allah ki yafemin kuma ki amincemin in aureki wallahi ina miki son da ko kaina banawa ki rausayamin”ya faɗi hawaye na biyo idanunsa.

Siyama rasa wanne zatayi aciki tayi,murnar tsuntsu daga sama gasasshe zatayi koko takaicin rayhana yakeso ba itaba,to faɗa mishi gaskiya zatayi ko ƙaƙa.

Shin inta faɗa masa gaskiyar ze yarda in ya yarda ya makomar soyayyar datake masa.

Wainnan sune tarin jerin gwanon tambayoyin dake yawo akanta.

“ko zaginane rayhana kiyi don Allah inde xuciyarki zatayi sanyi karki hukuntani dayin shurunki”yasake faɗi araunane.

Wasu hawayene ke biyo idanun siyama wanda batasan kona meyeba,amma tafi alaƙantasu da kishi.

Gyara tsayuwarta tayi sannan tace cikin salon kwaikwayon muryar rayhanar”kayiwa zucita da rayuwata giɓi me girman gaske,kwana kusa banajin zan iya gafarta maka rayhan”ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Ƙara marairaicewa yayi yana bata haƙuri,wanda ko kusa be ɗauka nanda shekara guda ma zata yafe masa ba amma kawai ga mamakinsa se ji yayi tace.

“na yafe maka komai ya wuce Allah tsare gaba,haka Allah ya ƙaddaro tsakaninmu”

Cike da farinciki ya ɗago yana mata godita itako se sinne kai take ita ala dole game kunya.

 

Rayhan be gama cika da mamakiba seda yaga rayhana ɗauke da darduma ta shimfiɗa masa gamida gabatar masa da abinci da abun sha.

Abunka da soyayya tagama rufe masa ido ga kuma dama yatara yunwa gaka yazage ya kwashi girki yana mata santi.

Sun ɗan taɓa hira inda yake bata labarin ya haɗu da siyama adubai kuma tanuna zata dawo nigeria.

Gyata zama tayi tace atausashe”wallahi ta dawo sede abu beyi daɗiba dan da ciki ta dawo ita kuma mama taga bazata iyaba ta turata can habuja gun ɗanuwan vabanmu ta haihu dan bazata iya da abun kunyar ƙauyan nanba.

“shidama kaucewa hanyar Allah ba abinda besawa Aɗlah ya yafe mana muma amin”

Daga haka suka ɗan cigaba da hira daga bisani ya buƙaci tai masa iso gurin mama.

Koda ya buƙaci zuwa yaba mama haƙuri hanashi tayi tace ya bari zatai mata bayani dan ta ɗau zafi.

Be kawo komaiba ya yarda da abinda tace dan Yana sonta bada wasa ba.

Sai gefin magriba ya barota bayan sunyi musayar number waya,daƙyar ya iYa barinta,itama haka.

Koda yahawo jirgi zuwa abuja cike yake da mamakin sauƙin kai irin na rayhanar lallai tana da haƙuri da wannan tunanin ya shigo birnin tarayya,gidan mahaifiyarsa ya kira aka turo masa driver,ya ɗaueshi direct gidan nasu ya nufa dan ya gana da hajiyarshi,cike yake da kewarta.

 

 

 

 

*Ku hanzarta siya 500 ne kawai dan vama ayi komaiba awannan labari*

COMPLETE ƊINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Back to top button