Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 15

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect writers)_

 

*GARIN DAƊI……!*

 

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

 

PAID BOOK

*15*

 

~~~Buɗe kyawawan idanuwansa yayi a kanta bakinsa ɗauke da kalaman godiya,

“zan iya mallaka maka gidan nan gaba ɗayanshi Hashim…….. Ka saki jikinka dani kawai”

“nagode Ranki ya daɗe tabbas haɗuwata dake alkhairi ne, ban ma san irin godiyar da zan yi miki ba, haƙiƙa kin sauya rayuwa ta cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kin mayar dani mai daraja a idon duniya……”

Lumshe idanuwanta tayi ta buɗesu cikin muryar hutu da rangwaɗa tace,

” Don’t mention it….. ”

Bin bayanta yayi suka ciga da zagaya gidan tana sake nuna masa sauran ɓangarorin gidan, bayan sun gama tare suka rankaya suka koma cikin gari bayan ya ajiye jakar kayanshi.
**

Kamar yadda muka shirya da anty washe gari da naje wurin aiki hutu na rubuta ina dawowa gida na sanar mata cewa na ɗauki hutun, a ranar ta turo min kuɗin jirgi na biya online,

Har lokacin a cikin damuwa da ƙuncin rayuwa nake babu abin da ya canja, addu’a ta a kullum dai Allah ya tafiyar min da ɓacin ran nan ya sanya farin ciki ko bai kai na da ba,

Ranar Friday na tafi Abuja wurin anty bayan nayi sallama da su Annie da ƙawalli, Anty da kanta taje ta taho dani saboda ban wani san gari ba, dan in banda Anty ta dawo nan ni banda kowa a Abuja yaya Faisal ne ma da yake cewa zamu zauna anan lokacin da ana maganar auren mu. Tun a hanya anty ta fara nuna min rashin jin daɗinta duba da irin yadda na rame na lalace na fiffige, kallo na ta sake yi a karo na ba adadi sannan ta mayar da hankalinta kan driving ɗin da take yi,

“Gaskiya ban ji daɗin yanda na ganki ba Widat…. Meke damunki haka?”

Murmushi nayi mai kama da yaƙe,

“Anty babu komai fa….”

“Haba Widat….. Ai ko ɗan ƙaramin yaro ya ganki ya san akwai abin da yake damunki sai dai idan ba zaki faɗa ba”

Murmushi nayi kawai ba tare da nace wani abu ba da haka har muka ƙarasa gida, baza ido kawai nayi ina kallon gidan anty mai kama da aljannar duniya, komai yaji ko ina gwanin sha’awa,

“Anty kice a aljannar duniya kike…. Wannan ƙaton gida”

“Naki ai sai yafi wannan Widat…. Nima tsohuwa na samu wannan bare ke”

Dariya nayi na bi bayanta ina sake bin gidan da kallo,bedroom ɗin ta tace in saka kayana amma naƙi na saka a ɗakin yaranta wato Islam, Aslam da Sultan. Da daddare muna zaune muna hira anty take ƙara tambaya ta dangane da damuwata sake cemata nayi babu komai,

“Amma babu komai Munatu kika bi kika lalace haka? Barin damuwa a rai dai baya magani bari in faɗa miki, problem shared problem solved”

Ajiyar zuciya na saki sannan nace,

“Anty ai aikin gama ya gama abin da ya faru ya riga da ya faru harma ya wuce sai dai labari……..” abinda ya faru tsakanina da Hashim tun farkon haɗuwarmu na kwashe na faɗawa anty, har na gama bata ce komai ba sai bayan da na gama sannan naji tayi ajiyar zuciya,

” Hmm to in banda abin ki Widat menene abin damuwa anan har da zaki bari ɓacin rai yayi tasiri akan ki? Godewa Allah fa ya kamata kiyi da yasa kika gane tun yanzu akan sai bayan kunyi aure sannan ya fito miki da halinsa kinga time ɗin is too late to cry…. Amma yanzu kina da options kina da damar da zaki fita daga rayuwar sa fita ta har abada…. Ke in banda abin ki ma wannan abin da Hashim yayi miki ai minor abune compared to butulcin da maza ke yi wa matayensu…… Widat zaki sha mamaki idan na fara baki irin cases da mata ke kawo mana akan mazajensu wallahi ke sai ki godewa Allah domin naki da sauƙi…… Sauƙin naki shine bai riga da ya zama mijin ki ba amma su yawanci mazajensu ne wasu harda yara biyar shida ko bakwai….. Ki godewa Allah kawai ki mance dashi dama taimako dan Allah kika yi to ladan ki yana gareshi, kuma insha Allah zaki samu mai sonki so na gaskiya wanda zai iya sadaukar da nasa farin cikin akan naki,wanda zai ƙaunaceki ya kula dake sannan ya baki dukkanin gata ”

” Hmmmmm to anty insha Allah zan manta da komai ” na faɗa bayan naja doguwar ajiyar zuciya dan gani nake kamar wannan lokacin ba zai zo ba, gani nake kamar farin cikina ya tafi kenan har abada zai yi wahala kuma ya sake dawowa. Har 12 muka kai muna hira da anty tana bani labarai kala kala dangane da butulci irin na ɗa namiji wanda ita ganau ce ba wai jiyau ba dan wasu cases ɗinma itace tayi handling ɗin su, ni kam na cika fam da mamaki domin wasu labaran tamkar a shirin wasan kwaikwayo wasu kuma kamar a littafin hausa lallai in dai hakane to wannan duniyar tamu cike take da butulu masu manta alkhairi, ganin 12 na neman wucewa yasa nayi wa anty sallama na shiga ɗaki, ɗakin yaran da girman sa yana ɗauke da ƙananan gadajensu guda uku sai wardrobe da mirror da toilet ɗin su, dama tun kafin zuwa na sultan a wurin anty yake kwana dan haka gadon dake girke da sunan nashi na maye, bayan nayi addu’a na fara tuna labaran da anty ta babbani ɗazu, lallai anty tayi gaskiya da tace ni kamata yayi in godewa Allah da ya nuna min ainihin halayyar Hashim ba wai sai after munyi aure ba, insha Allah zanyi ƙokari in cire kowacce damuwa daga raina kamar yadda anty ta faɗa, da waɗannan tunane tunanen dai na samu nayi bacci na zuciya ta wasai babu damuwar komai.

Rayuwa ta a gidan Anty sai sam barka da godiyar ubangiji domin har na ɗan canja duk da cewa har yanzu akwai ɗan abun da ba a rasa ba amma yanzun dai an samu ci gaba ba kaɗan ba gashi anty babu takura duk abin da nake so shi zanyi haka idan tana gida zama za muyi mu wuni muna hira a haka har na samu kimanin sati uku lokacinne muka yi waya da yaya Faisal yace min zai kawo matar shi gidan anty mu gaisa, a ranar kuwa bayan sallar magrib sai gasu,

Abun mamaki da dariya matar sai taƙi amsa gaisuwa ta sai iya ta anty kaɗai, ko a jikina daga ƙarshe na shigewata ɗaki naje ina chaten da ƙawalli ta wadda take tsegunta min wai yaya Hakim ya tafi Ilorin zai yi wani aiki ita kuma shine har da kuka lokacin da zai tafi wai da cewa ma yayi zai fasa tafiyar, dariya nayi nace mata ai da ya fasa ɗin, ina nan kwance ina ta shan dariyar labarin ƙawalli anty ta leƙo take cemin wai baƙi zasu tafi,

“su gaida gida anty” na faɗa ina daga kwance,

“a’a Widat ba a haka, ki fito kiyi musu sallama ai saboda ke suka zo, ni tun yaushe nake garin amma kinga sun taɓa zuwa?”

Ajiye waya ta nayi na miƙe nabi bayan anty, iskesu nayi suna sallama da anty, nima nace su gaida gida na ɗan taka musu na juyowa ta cikin gida. Bayan kamar zuwan su da kwana biyar kawai ranar a WhatsApp sai naga dogon massage daga yaya Faisal wai dan Allah duk wata hanya ko kafa da chaten ko waya a tsakanin mu in yi haƙuri ya yanketa saboda hakan na neman haifar masa da matsala a gidan sa shi kuma yana son matarshi da zaman lafiyar su sannan bashi da niyyar ƙara aure yanzu, yana yimin fatan samun miji nagari wanda ya fi shi da komai kuma zai yi blocking ɗina, wannan abu yayi mutuƙar yimin ciwo dan har saida na zubar da hawaye, nan take nayi blocking ɗina nima na goge no ɗinsa raina na ƙuna, bayan anty ta dawo daga aiki nake faɗa mata, dariya naga tayi kafin tace,

“hmm ai dama nasan za arina, ai tunda naga wannan matar tashi tana shasshan ƙamshi na san za ayi haka”

“to amma Anty ni nake kiran yaya Faisal ko ni nake yi masa magana online? Wallahi shine yake kirana kuma shi yake yimin magana, daɗin abin ma nice na ƙishi tun farko ba shine ya ƙi ba bare su goranta min, idan ma shine yayi min wannan massage ɗin ko ita ce tayi duk damuwarsu kuma su ta matsewa…. ”

” Kowa dai yayi abinsa yagama insha Allah mijin ki na nan yana jiran ki wanda yasan darajarki da muhimmancinki, karma wannan abun ya dameki ”

Shiru nayi domin damuwa kuwa ta nawa, ƙarewar damuwa har kuka ma nayi. Sati na huɗu a gidan anty tace min in shirya zamu tafi Lagos tare da aminiyarta anty Salma wacce zata jagorance mu zuwa wannan training ɗin da tace min zamuyi na wani aiki wanda za muyi wanda ya shafi na’ura mai ƙwaƙwalwa, aikin ita ya dace tayi amma ganin yanda nake da naci da ƙoƙari akan computer yasanya tace ni inje in yi ta san zan iya, tare da ƙawarta Anty Salma zamu tafi zamu je muyi 1 month, kayana duk na gama shiryawa ranar Lahadi muka wuce Lagos domin ranar Monday za a fara training ɗin, wannan shine mafarin sauyawar rayuwa ta domin acanne labarin zai fara wanda yake cike da ƙalubale masu tarin yawa………… ✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*Ina mata ƴan ƙwalisa ƴan kwalliya masu son burge mazajensu da gyara kansu cikin sauƙi rahusa ga dama ta samu ku garzaya ko nemi maman Maryam domin huce takaici, zaku samu haɗaɗɗun ɗinkakkun Lagos lace cikin farashi mai sauƙi gefe guda kuma ga GHT product domin gyara ku, zaku iya tuntuɓarta ta wannan no 07047034063 kada ku manta nima Ummi Shatu da bazarta nake rawa dan siyan na gari maida kuɗi gida*

_*Ummi Shatu*_

Back to top button