Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 40

Sponsored Links

40
Dakatawa daga dube duben dasukeyi kowanne cikin tashin hankali da firgici suka dawo da kallansu a Kansa gabaki dayansu.

Baki sake hande tace nashiga uku yau ina Shirin ganin baqar Rana,
Ciwon qwaqwalwa ka samu Ababan khairi??
Mutuwar sumayyahn ta taba ka hakane bansaniba?
Benazir ce fa a gabanka,
Gizo sumayyahn ke Yi Maka ne?
Qalu innalillahi.

Anne da benazir kuwa tsayawa sukai cikin mamaki da fargaban maganar hande kodai gizo sumayyahn ke Yi masa sbd wahalan dasuka Sha a hannunsa.

Shiru yayi musu Saida hande tagama tsoki burutsun zancenta ta saurara taba kallansa da mamakin ganin hankalinsa kwance Bai shiga tashin hankali ba.

Tattaro duka nutsuwa da hankalinsa yayi ya fara kallansu Daya bayan Daya yaga su dinma dukkaninsu hankalinsu na akansa.

Akan benazir ya tsaida idanuwansa yafara da cewa

“Ke kina son ‘yar hannunki kuwa?”

Shiru sukai hande na sake shiga mamaki hakama Anne dagowa tayi ta Dan kallesa ahankali sbd Jin tambayar abinda bama sai anyi tambayar ba sbd ansan amsar.

Shiru benazir tayi tana kasa ko motsawa bare iya magana Dan kuwa fadanma tana son babyn hannunta kaman ragewa Miya gishiri ne.

Tsuke fuska Ababa yayi Yana fara hasala a siqe yace

“Ba tambaya nayi bane?kuka tsaya mun kaman wasu gumaka.”

Ahankali benazir ta gyada Kai batareda ta dago kan ba.

“Bakinki Zaki Bude ki ban amsa kan na tashi na fasa bakin ki a gurin”

Cikin sanyi Kai tsaye ta Bude baki a natse tace

“Eh Ina kaunarta sosai.”

Wani zafaffen tsoki ya sake Yana Hana zuciyarsa fusatan da zata sanyashi tashi yayi mata dukan fita hayyaci sbd a ciki ‘yayan hudun kaf Bai qaru da komai dasu itace last hope dinsa Kuma itace wadda zata kasance mukullin samunsa Dan haka yake sake tausan zuciyarsa Yana Hana kansa Dora hannu akanta.

Bayason rufa rufa ko batawa Kai lokaci har Wani lissafin ya kunce masa Dan haka ya sake hade fuska sosai yace

“Dukkaninsu ku Bude kunnuwanku da hankalinku harma da nutsuwarku ku saurari Abinda zan fada sbd magana ce da fitarta ko bayyanar gaskiyarta daidai yake da masifar da mutum bazai iya dauka ba.,

Hande ya kalla datake kallansa a matse da son Jin meyake faruwa da Ababan ne yace

“Ki nitsu hande kijini da kyau,
Kema me ciwon qwaqwalwa ki nutsu ki Jini Kuma ki fahimceni dakyau Dan wlh kuna kaucewa magana zan dauki ‘yar Nan nakai Tasha na ajiye Wani ya tsinta.

Daga yau benazir itace uwar data Reni cikin wannan yar takuma haifeta.

Anne ce kawai ta Dan kallesa sbd wannan ai maganar dazu ce ya maimaita.

“Idan nace itace ta Rena cikin Kuma ta Haifa Ina nufin babu Wanda zaisan munama da sumayyah anan gidan bare haihuwarta,
Benazir ce kawai ‘yata Kuma itace wadda ta Haifawa Bilal kaante ‘ya gatanan a hannunta,
Babu Wanda ya Isa yasan gaskiyar maganar Nan har sai ranar Danaso.

Wannan Karan harda benazir cikin masu kallansa Dan ita har lokacin Bata fahimci meye ainihin Abinda yake nufi ba.

Shiru sukai babu Wanda yace “toh” ko Wani abin sbd har lokacin dai ita hande kallan ya tabu take masa Anne kuwa Kai tsaye tasan meyake Shirin aikatawa da wannan maganar tasa.

Benazir ta Maida idanuwanta ahankali ta kalla sbd idan har ta fahimci inda Ababa yake Shirin dosa da zancensa itama lokacin rabuwarsu ne yazo zata tafi ta barta shikenan,
Amma a bangarenta idan har zai cusawa dangin Bilal benazir a matsayin sumayyah su amsheta da ‘yarta to zuciyarta zata yarda da wannan shawarar Dari bisa dari sbd benazir taje ta samu rayuwa Mai kyau ta fita daga wannan rayuwar da saidai su mutu a wahala tinda duka ‘yayanta sun mutu a wahalar sun barta.

Da wannan tinanin Anne Bata tsaya nazarin komaiba itace ta fara dagowa ahankali tace

“Na amince da Hakan”.

Wata dariyar Jin dadi ya sake mara sauti Yana kallan Annen da mamaki yace

“Na buga a daidai notin hankalinki ya dawo kenan?.

Sake dariyar yayi Yana cigaba da cewa

“Kuma yaushe aka baki zabin da kike maganar kin amince?
Magana ce nayi da Wanda ya amince da Wanda Bai amince ba da Wanda ya fahimta da Wanda Bai fahimta ba duka a banza sbd magana ta zaunu babu Wanda ya Isa a cikinku ya dagata,
Ke benazir ki sakawa kanki da qwaqwalwanki kece uwa kece mahaifiyar ‘yarki gatanan,
Ni bansan wata sumayyah ba anan gidan bare haihuwarta.

Hande ya kalla Yana cewa

“Hande ko ke kinsani ne?
Kinsan sumayyah a gidan Nan me haihuwa?

Baki sake hande tace

“Sumayyah a Nan gidan Kuma?
Labarin ya shude ai Kuma,
Allah dai ya Daya Miki ‘yarki benazir.

Wata dariyar farin ciki ya sake Yana Maida kallansa kan Anne da jikinta gabaki yayi sanyi ya mace yace

“Kin sake fahimtar komai yanzu da kyau ko?.”

Ahankali ta gyada Kai tana rintse idanuwanta dake radadin zafin Kuka Amma bayama iya zuwan.

Benazir data fara fahimtar inda aka dosa hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ahankali ta zube qasa tana sake riqe ‘yar da kyau idanuwanta na sauyawa zuwa jajir itama tana kasa Kuka ko hawaye sbd tashin hankalin da Bata taba tsammani ba.

“Ki shirya kowane lokaci idan muka gama maganar manya daura Miki aure zanyi a satin Nan sbd bazan yarda a Rena yarinyar Nan ba a waje mutane su ringa sheganta min ‘yar jika ba”

Kalmar aure Daya fada ya saka Benazir qarasa zubewa qasa tana Neman fita hayyacinta hannuwanta na rawa sosai hakama duka jikinta.

Anne ce ta durqusa ta riqota tana karban babyn dake Neman subucewa daga hannunta tana hadasu ta rungumo jikinta idanuwanta na qanqancewa Amma ba kukan.

Ababa daidai lokacin hade fuskarsa yayi sosai ransa na Dan shiga Baci yace

“Wannan maganar tawa yankan wuqa ce nayi nagama ki sakawa kanki qarfin halin Hawa matsayin uwar ‘yar idan ba haka ba kuskure Daya kikayi akan wannan maganar wallahi tallahi dauke ‘yar zanyi har abada bazaku sake ganinta ba zaku rasata kaman yanda Kuka rasa uwarta.”

Rarrafowa benazir tayi koina jikinta na rawa zata zube gabansa tayi roqo Anne ta riqeta hannuwanta itama suna rawa duka zuciyoyinsu kaman zasu Fashe a tare da babban tashin hankalin dayake Neman dimauta benazir,
Tayaya zatayi aure tabar Anne a wannan masifar ita kadai,
Tayaya Anne zatayi rayuwa babu ko dayansu a cikin su hudun,
Annensu barin ta a gidan a hannun Ababa da hande gwara Susan hankalinta ya gushe Koda an cutatar da ita bazata ji komaiba.

Miqewa Ababa yayi tsaye yabar gurin batareda ya sake bi ta kansu ba ya fice gidan.

Hande ma miqewar tayi sbd itama lamarin yamata daidai gwara benazir tayita tafiya da ‘yar sudai Abar musu gidan da ita kafin a ankara da haihuwar.

Daki hande ta shige tabarsu tsakar gidan sai alokacin Benazir ta fashe da Wani irin Kuka Mai tsananin ciwo da radadin zuciya tana qanqame Annenta.

Annen daurewa takeyi tana Hana kukanta fasuwa sbd ta sadaqar gwara benazir da ‘yarta su tafi inda rayuwarsu zata inganta Dan haka dole ta danne tsananin qunci da ciwon rabuwa da benazir din Datake ji ta nuna jarumta Dan nunawa benazir zata iya zama ita daya a tsakanin Ababa da hande.

Irin Kukan da benazir keyi a tsakar gidan jikinta na jijjjiga duk Wani baqin ciki,qunci damuwa da tashin hankalin data jima tana boyewa suna bayyana sbd Bata taba kawo tinanin aure ko tafiya ta rabu da Annenta ba kaman yanda bazata iya rabuwa da ‘yar sumayyah ba har abadan da Ababan ya furta.

Rarrashinta Anne keyi da hannuwanta batareda ta iya Bude baki ta furta kalma ko Daya ba Dan tana Bude baki kukan Datake riqewa ne zai fashe mata ta sake daga hankalin benazir.

Sai da suka jima a gurin benazir na kukan daya kasa raqe mata nauyin Abinda takeji danne a kirjinta,

Kamata Anne tayi suka miqe ko tsayuwa Bata iya Yi a ahankali suka koma dakinsu suka shige ta zube qasa tana fatan kanta ya juye itama ko zata samu sassaucin ko yayane taji sauki.

Zaunawa Anne tayi gefenta tareda dora mata babyn a jikinta tana Bude baki cikin qarfin hali da dauriya murya a sanyaye tace

“Karkiyi Kukan baqin cikin Hakan kokuma tinanin bazaki iya Hakan ba,.
Zaki iya benazir,
Zaki iya,
Kiyi Hakan sbd ni sbd ‘yar uwarki Kuma sbd ‘yarki,
Kije benazir ki samu ingantacciyar rayuwa na yafe,
Na yafe Miki ki tafi kinji bena,
Ke kadaice sanyin idaniyata da zuciyata a yanzu,
Kije ki samu rayuwar da kowannenmu ya kasa samu Dan Allah,
Kiyi Hakan sbd ni da ‘yarki.,
Kafin zuwanku duniya ni kadaice a cikinsu Ababan Kuma na rayu wahala Bata kashe ni ba Kuma Dan Kun tafi dukkaninku zan rayu inshallah sai ranar da Allah yayi kwana na a duniya zai qare..

Maganganun Anne suka sake rusa zuciyan benazir ta fasa Wani sabon kukan Daya saka jikin Anne sake mutuwa da sanyi Amma bazata nuna rauni da qunci Mai tsananin dake dabaibaiye da ita a lokacin zata daure koma yayane.

Kuka babyn dake jikin benazir tafara ahankali tana motsawa.

Anne ce tayi saurin karbanta tana jijjigawa sbd ta Dena kallo da sauraren benazir data kusa karya mata dakewa da qarfin halinta.

Ita kanta benazir Bata iya dagowa ta Kalli Annen sbd tasan daurewa ce da jarumtan dole Annen keyi Amma Kuma ko suyi jarumta ko kada suyi bazasu iya kaucewa tabbatar maganar Ababa ba har dai a yanzu da batada zabi sai na bin Abinda yace tinda ko guduwa bazata iyayi tabar Annenta ba ga Kuma ‘yar da batajin zata iya rabuwa ma da ita Koda Ababa zai ringa yanka Naman jikinta.

Masu buqatan pages din da sukai Nisa join VIP ko arewabooks
09033181070
##MAMUH#
#AMNAH KAANTE
#BENA
#DD
#ABABA
#SAFNAH
#HOTROMANCE

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button