Matar So 5
Page.5*
Jikina na rawa na kwashe garin kuɓewar sama sama, na mayar cikin robar na rufe kallona umma tayi cike da mamaki yanda Allah ya ɗaura min tsoron jaraba, gashi na iya laifi amma cikina cike ya da tsoro, bani ɗaya ba harsu Rahilah haka muke da tsoron kata’i.
Da sauri nabar kitchen ɗin zuwa ɗakinmu, na ɗauko sakonta na fito kallonsu Rahilah nayi cikin nutsuwa nace.
“Jiranku nake kar lokaci ya kure.”
“Amma dai kya jira na gama sai mutafi ko?” tace min,
Ina zaune ina jiranta har ta wanke shinkafar tuwon, ta jika Rahima tana gurin Mama dan ba zata bimu ba,
Da sauri muka fito ni ina sanye da Nikk’af ita kuma taki sakawa, muna tafiya muna hira har muka fito daga unguwarmu, abin hawa muka tara muka faɗa mishi sunan unguwar da zai kaimu, ba tare da wani gardama ba ya kwashemu zuwa unguwar,
A kofar gidan aka saukemu, unguwar sabon gurine dan kamar manyan mutane ne, suka sayi filayen, tura get ɗin mukayi da sallama, mai gadin gidan ne ya mike gaisheshi mukayi, sannan nace.
“Malam hajiya tana gida kuwa?”
“Eh tana ciki,” ya bamu amsa a takaice.
Godiya muka mishi sannan muka shiga gidan da sallama abakinku, duk suna falo a zaune da murmushi ta amsa mana tana cewa.
“Yau nice da manyan baki haka? Malama Rahilah tare da Malama Maryam Sajida barkanku da zuwa.”
Ture kanshi tayi a cinyarta tace.
“Aman! Tashi bana son shirme kazo ka min bake bake akan cinya da Allah ya baka haihu ai da jikokina zan ɗauka tashi nayi bakine.”
Dakyar ya buɗe idanunshi tar akan Rahilah, gyara kwanciyarshi yayi ya sake lumshe idanunshi, wani bakon yanayi yake ji na daban.
“Ina wuni Hajiya, Ya gida” Na gaida hajiya falmata.
“Lafiya lau, ya Malama Hasina? Da jikin Malama Atika.”
“Alhamdulillah, humm dama aikinkine umma ta bani toh na manta ne dan tun safe ta bini na kawo miki, amma sai na lura kaman baki zo ba.” na faɗi haka a takaice,
“Eh wallahi mai gidane ya dawo, jiya toh kuma sauran Yan matan da nake bari suna makaranta shi ya hanani zuwa.”
Jinjina kaina nayi sannan na buɗe jakar makarantana na fito mata dashi, na mika mata tare da mikewa zamu bar gidan,
“A’a da wuri haka nagode, amma ga aikinta nakice mata inji Iyayen Zakiya, daga zari’a suna gayyatarta walimah auren zakiya naso da naje yau da kaina zan bata sakon, amma ki bata hakuri bikin saura sati biyu.”
Ture kanshi tayi akan cinyarta aikuwa ya tura bakin da cewa.
“Mami zata karya min wuya, tun bada ga jikokinta ba.”
Juyawa yayi ya tsare Rahilah da ido, itakan bata san yanayi ba dan game take a wayarta.
Ni kuwa mamakin yanda yake iya kallon mutune haka ya bani, basar da abin nayi na cigaba da leka game ɗin rahilah muna magana kasa kasa, tare da sake dariya.
Fitowarta yasa muka mike, mika mana wani jaka tayi, me ɗauke da tambarin Wani mall na dubai, sai ta sake bamu aikar umma shima a wani jaka daban tace.
“Wannan na farkon nakune ku uku, wannan kuma na Malama Hasina ita da Malama Atika, akwai katin bikin a ciki, idan nasami shigowa gobe zan mata bayani, ga wannan ku rike kuɗin napep.”
K’in karɓan kuɗin mukayi cike da kunya, Rahilah tace.
“A’a don Allah ki barshi faɗa umma zata mana, kiyi hakuri,”
“Lallai kuwa toh ku zauna babu inda zaku je tunda bazaku amsa ba.” ta faɗa mana hk.
Babu yanda mukayi haka muka karɓa kaman zamuyi kuka, godiya muka mata sannan muka bar gidan.
Sai a lokacin ya buɗe idanunshi ya gyara kwanciyarshi, yace.
“Mamie!”
Sai kuma yayi shiru bai kuma magana ba, tasan halinshi shi yasa tace.
“Yaran Malamarmu ne, ita mai nikk’af a fuska itace maryam Sajida, sai ita ɗayar Yar kishiyar malama ce, Rahilah”
Gyara kwanciyarshi yayi ya cigaba da lumshe idanunshi, sautin muryan Rahila na yawo a kunnenshi, juya bayanshi ya saka hannunshi a kunnensa yana yaki da zuciyarshi.
*Ina dukkansu ma yaudaranw basu san kome ba sai kyalkyale banza awaje da zaran sun shiga ciki su xama kaman jakuna*
Hira sukayi sama sama har Mahaifinshi ya shiga, Dr Mahmud Mandara, zama yayi cikin nutsuwa tare da zubawa Aman ido cikin harshen shuwa yake tambayar, Hajiya Falmata mike damunshi.
Dariya tayi tace.
“Hali a jikin rai, kazamar matarshi yake tunawa.”
Juyowa yayi cike da jin ba daɗi yace.
“Kaiii Mamie In-law ɗinki ce fa, itace kazama, toh ki nemo min mi tsafta.”
Dariya Dr Mandara yayi kamar me yace.
“Falmata kinji ba, yana kalubalartaki na kiran Hindu kazama, toh ni dai babu ruwa.”
Mikewa zai bar falon,
“Aman ashe cigaban da kuka samu kenan bamu sani ba, ɗazun Alhaji Muh’d Yunus yake faɗa min ds muka haɗu a fadar zazzau, wai gwnatin naija tabarku ku buɗe kamanin software.”
Murmushi Aman yayi cike da jin daɗi. Yace.
“Abba Nasaran ba tamu bace mu ɗaya, jigon Nasaran Mai Nasarane, Abba kaga kuɗin da ya narka ne, kashi 59% na shine kashi 20% nawa, 21% na Ahmad Zailani Bature, Abba da zuwanmu Dubai kome ya rigada ya tsara, babu abinda muka ɓatar namu, Ya Allah ka jagoranci al’amuran Yunus Mai Nasara,”
“Amin” Iyayenshi suka ce, nan yake warware musu halayar Mai Nasara,
Cike da jin daɗi sukayita samu su albarka.
****
Karfe uku, na rana ya isa garin katsina, a jirgi yan kasuwa dama drvn gidansu yasan da xuwanshi, ba tare da bata lokaci ba ya isa inda drvn yake, jikin drvn na rawa yazo ya buɗe mishi kofar motan, yana shiga ya koma gurinshi ya zauna yana cewa.
“Barka da zuwa Yallaɓai, ya hanya.”
“Alhamdulillah Malam Nuhu ya iyalanka.”
“Muna lafiya, barka da zuwa ashe karaman madam tasan zaka zo shine take ta murna.”
Murmushi Ahmad yayi har suka isa dutse tsafe quarts, inda gidan Ambasada Alhaji Zailani Bature,
Kunna kan motar yayi lokacin da aka buɗe tangamemen get ɗin gidan ya nausa hancin Motar ciki, tunds suka ga mai gadin basu ga kowa ba, mai gadin na rufe kofar shima yabar gurin,
A hankali suka fito ya kwashi wayoyinshi da jakar computer ɗinshi yayi cikin gidan.
Yana tura kofa, balloon na fashewa akanshi take wasu kananun abubuwa masu kyali suka zobo mishi,
Yana cikin mamakin haka suka shiga,wakar karin shekara suka shiga mishi, cike da mamaki yaga Yarshi rike da,cake yar kimanin shekara uku,.
“Happy Birth Day Dadda.”
Durkusawa yayi gabanta, ya hure wutar jikin cake ɗin sannan yace.
“Thank kyau My ChuChu.”
Yan uwanshi suka shiga murna da shewa, godiya yayi musu ya ɗaga kanshi step inda yake jin takun Mahaifiyarsu sanye take da doguwar rigar super wax, hannunta na dama rike da, casbi da 40 rabbana,
Takawa yayi har inda take, ya ɗaura kanshi a kafaɗarta, suka sauko tare.
Zama tayi a kujeran mai cin mutane uku, zuwanshi katsina yasashi manta wasu abubuwan ns ɓacin rai da ya kunso, a gurin Gimbiyarshi hafsat.
Sukayi kanenshi aka yanka cake, aka kaiwa masu aikin gidan da akayi murnan tare dasu, sai da suka nutsu ya kalle Mahaifiyarshi yace.
“Ummi !”
Zuba mishi ido tayi cikin nutsuwa tace.
“Ina jinka Deedat”
“Ummi auren zan kara.”
Yanda yayi magana a sanyayya ɗauka baida gaskiyane,
Tausayi da soyayyar ɗanta, suka mata diran mikiya, san bata son ta tursassashi, akan abinda Matarsa take musu dan a haka ma bashiri suke ba, ina kuma ina ta goya mishi baya yayi aure murmushi tayi irin tasu ta manyan tace.
“Idan babu damuwa kayi hakuri mana, duk abinda hakuri bai bada ba, toh rashinsa bazai bada ba ka mata uzuri har zuwa nan da wani lokaci, idan bata sauya ba kana da damar yin kome.”
Shiru yayi ya rasa yanda zai mata bayanin halin da yake ciki,musaman yanda rena danginshi da shi kanshi, rike chuchu yayi yana kallonta cike da tausayi kiran sallah yasasi zuwa masalacin dake jikin gidan.
****
“Toh Yau matarce a zaria, lallai abu yayi kyau, mi kika kawo na ɗaurenmu.”
Ware ido huda tayi tana dariya tace.
“Alhaji nice ma zan kawo maka, kayan auren taɓ na fasa.”
Dariya suka sannan ya kalleta yace.
“Kije gida ina zuwa, kinji.”
Haka Alhaji Muh’d ya turo Huda gida.
****
Fitowa Fareeda tayi daga tayi ta rike da wayarta, akunne waya take akan kayanta da suke da da shigowa daga, lagos.
“Allah Managa baxan baku ba ai wanca da na baku biyani kuɗina ba, taɓ kuyi hakuri kawai wannan karan nima kayan bazu zo min da sauki ba, balle na bada bashin da bazai fito ba.”
Tana gama faɗar haka ta kashe wayarta kallon Hasana tayi, tace.
“Sameer bangashi ya fito ba,”
“Ai tun ɗazun ya tashi yake tambayarmu ina Yayarshi shine muka ce mishi sun tafi zaria da alhaji shine ya koma ciki yana kuka.”
Tsaki Fareeda tayi cike da jin haushin tafiyar da Mai Nasara yayi da huda ba tare da Sameer ba ai ko babu kome, Sameer ɗin shine magajinshi na gaba, ba Y’a mace ba dan gidan wani zata.
D’akin yaran ta wucce ta sameshi yanawa Mufida rashin kunya dake itama bata da hakuri ta sauko ta make shi, tun daga bakin kofa take jin muryanshi da sauri, ta isa ɗakin tasami fuskarshi tayi ja.
Gashi bakinshi bai mutu ba, sai zagin mufidar yake, da cewa.
“Shegiya muguwa, jaka Allah ya isa min, azaluma.”
Ita kuwa da zuciya ya ciwota taje har gabanshi ta wanke mishi fuska da mari, sai akan idanun uwar “kam uba” inji Fareeda,
Ko ajikin Mufida, ta koma bakin gadonta ta zauna “keeee Uban mi yayi miki kike dukanshi kaman jaki dan uwarki.”
Mufida bata da kunya yar shekara goma amma rashin kunyarta ya fi karfinta dan tsabar ta haɗa abubuwa biyu daga iyayenta miskilanci daga uba mulki daga uwarta, ita a rayuwatar tana son bada oda kuma sau ɗaya take magana, na biyu dukkane idan kuma babbane toh duk maganar da ta sauka a harshenta shi take faɗa mishi, dan haka da fareeda ta zageta ɗago idanunta tayi farare kafin tace mata.
“Ki tambayi rashin tarbiya.”
Tana faɗa mata haka ta juya tayi kwanciyarta take ran Fareeda ya ɓaci ta fincikota ta tsinketa da mari, wanda yaja hancinta zubda jini dan tana haɓɓo.
“Dan Ubanki kika ce naje na tambayi rashin tarbiya dani dake waye bashi tarbiya.”
D’ago kanta tayi cikin nutsuwa ta share hancinta tace.
“Ki sake min rigana.”
Yanda tayi maganar kaɗai abin mamakine dan idanunta sunyi ja kamar wata babba, amma babu ko ɗigon hawaye asalima, hucci take tsabar ɓacin rai,
Fita tayi daga ɗakin zuwa sider ɗin Uwarta tana uwar ɗaka yanda Mai Nasara yabarta haka take a kwance,
Ba sallama ta shiga cikin kuka da batayi a ko ina ba sai a gaban uwar take faɗa mata abinda Yadikonta tayi mata,
Abin takaici ka ɗibo damuwarka kazo inda za’a share maka kwalla amma sai uwar ta kalleta ta gyara kwanciya sannan tace.
“Fita ki bani guri bacci nake ji.”
Zaro ido yarimyar tayi cike da bakin ciki ta suri wayar Uwar tafita da shi, tana ganinta amma tsabar mulki ya hanata magana, Mufida kuwa layin Uban ta kira, yana kwance a ɗakinshi na zaria ta tsalla mishi ihu da ya ɗauka tare da kururuwa tace.
“Daddy Maman Samee ta fasa min hancina, har yana jini sannan ta zageni wai Ubana mara zuciya, ko kai bazata ragawa ba kuma sai tasa ka daina sonmu, aimu Matane kafi son Samee akanmu, mu ɗin banza mu ɗin wofi dan baka sonmu.”
“Ya isa Mamana gani nan zuwa kinji.”..
Yace mata,
Kashe kiran tayi Laraba da Hasana suka kallon yanda Mufida ta haɗa bom lokaci guda.
Zuwa ɗakin uwar tayi ta ajiye mata wayarta sannan ta fita.
…….
Takarkacen shi ya haɗa yayo waje, ɗakin Mama kilishi ya leka yace.
“Mama zan tafi, munyi waya da Alhaji taso muje Huda.”
“Daddy lafiya? Zamu koma yau ba kace sai gobe ba.” inji huda kamar zatayi kuka,
“Eh toh muje Mufi takirani tana kuka, muje dai next week zan kawoki ki kwana biyu.”
Tana jin yace Mufi taji ranta ya ɓaci ɗakin hajiya kilishi ta shiga ta ɗauko kayanshi suka fito, lokacin Hajiyarshi ta fito har kasa ya durkusa ya faɗa mata tafiyar Allah ya kiyaye hanyan tace mishi,
Mikewa yayi suka bar cikin gidan da rakiyar Mama kilishi, mikawa Huda wani leda tayi me ɗauke da kayan kwalliya da tarkacen mata tace
“Mai Nasara karka kawota sai sati na sama, akwai bikin da zamuyi Yar gidan Yaya galadima zata auri muttak’an mai martaɓa, kaga sai taxo ayi bikin da ita dan har nasa a mata ankon fitar bikin.”
“Toh Mama.” ya ce mata a takaice.
Shafa kan huda tayi wacce tayi tace.
“Kishiya ki min dariya mana.”..
Murmushi Huda tayi tace.
“Nagode granMah, Allah yakara buɗi da lafiya ya kara soyayyarki da me farin gashinki.”
Dariya Hajiya tayu tana musu bye da hannunta, tunda suka bar gidan ta kauda kanta ta zubawa gefenta ido, yana sane fushi tayi amma tsabar baida lokacin rarrashinta ya kyaleta ya cigaba da tukinta.
Huda yarinyace karama amma tana da wani irin kaifin tunani, nazarin mahaifinsu da gidansu take, sam bai bai amshi sunanshi na magidanci ba, kowacce rayuwarta take tsullawa son ranta, dole asamu wcce zata sauya mishi alkibila dan duk cikinsu babu wacce zata iya wannan aikin, kwalla ne ya zuɓo mata tasa hannu zata goge ya mika mata tissue karɓa tayi ta goge, ahankali tace.
“Thanks.”
Sai yaji ba daɗi, riko kafaɗarta yayi, a hankali ya furta kalmar kaman baya son faɗar kalman yace.
“Sorry.”
D’ago kai tayi ta sakw murmushi wanda ya bayyana tsantsar kaman da take da Uban tace.
“Is ok.”
Basu shigo gida ba, sai da magrib masalaci ya wucce ita kuma ta kwashi kayanshi da taimakon drvn suka shiga dashi cikin gida,
Kallon Sameer da yake ta tsalle tsalle,akan kujeru tayi ta kauda kanta, ɗakinshi ta kai mishi kayanshi sannan ta wucce ɗakinsu, Mufida na zaune da kayan da jinin ya bata gana kan hancinta, da ta bushe kallo ɗaya sukawa juna kowacce ta basar,
Ban ɗaki Huda tashiga tayi wanka da alola, tazo ta gabatar da sallah.
…….
Bayan isha….
Zaune suke akan gurin cin abinci, baka jin kome sai karan cokala, suna gama cin abinci, kallesu dukkansu yace.
“Ina nimanku, Huda ki kira min Mufida.”
Tunda ya faɗi haka bai kuma bin takansu ba ya wucce gefenshi, Huda ta mike itama, sai matan kowacce ta koma gefenta ta kintsa sannan suka nufi falonshi yana kishingiɗe, sanye da farin wando yadin maza sai rigarshi itama faran har kana hango farin shimin da yasaka ta ciki,
Zama sukayi a kan kujera, Mufida na shigowa ta zauna a gabanshi, ɗago kanshi yayi ya kallesu, sannan ya kalli kafet ɗin, da yake malalle a falon, ko ba’a faɗa musu ba, sunsan mi yake nufi, sauka sukayi kowacce ranta a ɓace musaman Balkisu wacce take ganin kamar ya haɗata da sauran matanshine,
Manta da tasharsu yayi ya cigaba da aikin gabanshi, har kusan tara, Mufida tace.
“Daddy Barci nake ji”
“Ok mi ya faru da bana nan.”
Ya jefa mata tambayar, raurau tayi da idanunta, nan ta kwashe karya da gaskiya ta faɗa mishi, sannan har da shaidunta na an fasa mata hanci,
Buɗe baki fareeda tayi cike da mamakin yarinyar da aka haifeta a gabanta itace ta kula mata zarge,
“Tashi kije sai da safe Matar Alhajina” yace mata,
Tana fita ya juye musu kwandon bala’i dan akan yaranshi baida sauki, har yana ikirarin sake mata akan Yaranshi.
Abin da yabawa Balkisu haushi ta mike, cikin isa tace.
“Ai magana ya kare, suna gams hutu zasu koma bodin babu yar da zata sani ɓacin rai da ciwon kai.”
Fita tayi tabar musu falon cikin masifa Fareeda ta mike jikinta na tsuma, tace.
“Kace bamu da amfani.””
Bai saurarresu ba ya cigaba da aikinshi ila iyaka su hanashi hakkinshi dake kansu suje ya hakura dashi, dariya ke cikin cikin Aneesah dan itama Mufida ta taɓa haɗa mata makirci har tayi yaji, dan sai da mai nasara ya kifa mata mari biyu. Shi yasa idan ba huda ba, Aneesah bata shiga hidimar yaranshi, har sameer ɗin ba kunyane dashi ba ynx zai zage mutum.
Suna gama fita ya zubawa nauran gabanshi ido, shi baiga wani abu me muni ba, a hukuincin shi asalima, duk uba nagari irin haka zai yanke,
(A tunanin ka ba Yunus)
****
Muna komawa gida muka baje abinda Hajiya falmata ta bamu, turaruka da humra ga kayan kwalliya, kallon Rahila nayi cikin nutsuwa nace.
“A novel kowa ya iya, make ove ko?”
Dariya Rahimah tasaka har da rike cikinta tace.
“Wallahi ke muguwa ce, wato kin tarfo Rahil….”
Shiru tayi tare da kallon kofar shigowa Aunty Gausiya ne da goyonta, batsal batsal muna ganinta sai da gabanmu ya faɗi, mikewa mukayi, tana rike da Aiman a hannunta bakin cikin ganinta yasa muka tattara muka shige ɗakinmu,
Daga bakin kofa Malam Yace.
“Alhamdulillah kin kashe aurenki ba? Madalla zauna akwai ɗakin Yan mata ki kutsa kanki cikinsu, Hasina !!!Atika!!”
Da sauri suka fito kowacce hankalinta tashe, yace.
“Daga Yau kar wata ta kuma shiga madafi girki, sannan yan matan gidan kar wata ta kuma fitowa aiki, su kwanta su huta Allah ya kawo musu sauki, Duk wani aiki ya rataya a wuyar gausiya, da fatan kun fahimce ni.”
Gyaɗa kai sukayi, abin tausayi ɗan da kafi so shi ke wahalar da kai, juyawar da Mama Amarya zatayi sai zuɓewa tayi a gurin, “Wayyo Allah mama!”
Da gudu muka fito daga ɗakin Malam da Umma suka isa kanta, a hargitse Rahilah ta tureta cikin tashin hankali tace.
“Karki taɓa mana Uwa, muguwa azaluma, mara imani kin kasheta burinki ya cika, idan ma maita kika ciy…”
Kifeta da mari Umma tayi cikin zafin rai tace.
“Kiyi min shiru.”
“Bani ruwa Rahima?” malam yacewa Rahimah,
Har ture ture, muke nida Rahimah, muka kawo ruwan muna bashi ruwan ya shafa mata, a jiyar zuciya ta sauke, idanunta a rufe a hankali tace.
“Ku taimaka min na shiga ɗakina.”
Umma da Malam suka taimaka mata suka kaita ɗaki, aka shimfiɗata a gadonta zama mukayi muna mata fifita, sai ajiyar zuciya take saukewa,
D’akinmƴ Aunty gausiya ta zauna tana kuka, sai yanzun take dan danasanin kashe aurenta da tayi, gashi tun ba’a jekoina ba tafara kuka,
Tunda muka samu Mama Amarya tayi bacci, muka dawo ɗakinmu, ni da Rahilah muka koma ɗakin Umma Rahimah ta koma ɗakin Mama da zama haka muka mata watsewar zaɓi.
****,Aslinmu,
Mu yan kasar nijar ne, Malam da Umma, Asalin sunan Malam Omer Harzuka, ɗan asalin Damagarane bazabarme ne, Gidansu malamai ne, a damagaran wanda ake ji dasu malam yana da yan’uwan shi nacan,
Rigimar cikin gida ya haɗashi da Yan uwanshi, wanda haka yasashi yayi fushi yabar gida,
Malam shine babba a cikin gidan sai ya zamana a gidan ɗakuna ukune, akwai ɗakin Uwar gidan mahaifiyar Malam Mairama,sai Dakin Kyauta, sai dakin Halima wacce suke kira Hali dubu, Kakanmu malan Hayatu yana da yan kadarorinshi na kiwo, irinsu shanu, sai rakumai da tumakai,.
Gidansu suna yawa maza da mata,, ɗakinsu Malam yana da kane, guda biyu yan biyune suma,
Dakinsu basu da wani fitina kamar sauran ɗakunan, Hassana da Hussaina am musu aure acan nijar ɗin amma suna zuwa mana.
Dalilin barinshi gida ya farune bayan auren Umma yar abokin Babanshi, inda kakanmu ya ɗauki wasu daga cikin dabobinshi yabawa Malam, sai kanen suka tada rigima akan mi zai bada Omer su bai basu ba, faɗa yayi musu yace wannan kason da yabawa Omer yabashine dan rabonshine na kiwo da yake mishi.
Tunda suka ji haka sai sukayu shiru,dan Malam kaɗai ke masa kiwon dabobin.
Bayan anyi haka da kwana biyu, aka samu ɓullowar cutar amai da gudawa wanda yayi sanadin rasuwar kakanmu.
Bayan rasuwarsa yan uwan malam suka buɗe mishi wuta, akan sai ya bada dabobinshi araba bai damu ba dake yaba son fitina, sai ya mika musu da aka raba ya ɗauki Iya kakarmu da Umma suka bar nijar inda yazo maraɗi ya sai da dababinshi ya shiga motar katsina, daga sun zauna a katsina har na tsawon shekara, kafin ya dawo kaduna yazo ya kama haya, ya shiga makarantar markazi na malam mahmud gumi, dake yana da iliminshi tun can sai karatun bai bashi wahala ba.
A lokacine Umma tasami cikin Yaya Hayatu, cikin me matukar laulayi, ita da Iya sukayita fama har ta sauka lafiya,
Shagon saida litattafan addini ya buɗea kasuwar barci, kuma sai Allah yasaka mishi luɗifi a cikin shagon take ya bunkasa, Yaya nada shekara uku aka turashi madina yayi karatunshi acan,
Cike da farin ciki yazo ya faɗawa Umma da Iyarshi, aikuwa sukaita murna,, dake shi ɗaya zai tafi sai yabar shagonshi ga yaronshi yana cirewasu Umma kuɗin abinci da na haya,
Allah cikin ikonshi Naziru yarike su Umma da Amana har tsawon shekara biyar kafin malam ya dawo lokacin shagon ya kara bunkasa, Naziru ɗan nan kaduna ne, kuma maraya ne, amma mutune mai gaskiya da amana,
Bayan dawowar Malam ya maida Naziru makaranta dama bai gama scndry ba, dan yana aji biyu ya ajiye karatu gashi ynx yana niman shekaru ashirin, da buga buga malam ya turashi makaranta,
Dawowar malam aka sami cikin Aunty Shema’a, wacce cikinta baibawa umma wahala ba. Bayan haihuwar umma Malam ya fito da maganar karin aure Iya ce ta taushe Umma har aka kawo Mama Amarya,
Lokacin Aunty shema’u babu inda bata shiga, dan sai aka ɗauki shekara ɗaya da rabi kafin akayi auren, dukkansu malam ya kwashe ya zuba a makaranta high islamic,
Sun cire kishi a ransu sun rungume hidimar mijinsu, fiye da kima.
Watan Mama goma sha ɗaya ta haifi Aunty Asma’u wacce take aure, a Abia mijinta ma’aikacin banki ne,
Aunty Asmau watanta goma sha uku, sai ga cikin Aunty Hamdiya wanda lokacin Umma kama da tsohon cikin Ya kabir wanda yake bautar kasan shi a Edo,
Mama na fama da karamin cikinta, sosai suke fama da kansu ga Uwar mijinsu. Da ba lafiya watan guda tsakani Umma ta haifi ya kabiru, sati biyu da haihuwarshi Iya ta rasu, sun kaɗu sosai har na tsawon wata biyu, ana haka akayiwa malam tallar gida a tudun wada layin yan kosai, ba tare da wani damuwa ba yaje yasayi gidan me ɗauke da ɗauka bakwai ciki da falo da ban ɗaki guda uku, ciki ɗaya ɗaya, da ban ɗaki guda biyu sai ciki ɗaya babu ban ɗaki a cikinsu sai a haraba, nan malam ya ajiyewa yaranshi maza,
Ciki biyun da ban ɗaki na yara mata,
Bayan wani lokaci Mama ta haifi Hamdiya, lokaci Yaya kabir yayi kwari sosai, gidanmu ruwa biyune ɗakin Umma mu bakakene sai ɗakin Mama su kuma farare ne.
Sai da Aunty Hamdiya tayi shekara ɗaya da wata biyar aka sami cikin Aunty Gausiya, tunda Umma tasami cikinta ciwon Asthma ya shigeta da an ɗauka wank ciwo nadaban ne sai da aka tsananta bincike aka gano Asthma ce, dakyar dakyar cikin ya kai wata bakwai karshe tiyata aka mata, aka ciro babyn yar karama, umma ce ke hidima dasu har suka shekara dan Mama ciwo tayi sosai,.
Gashi gausiya ta tashi garau, sonda Mama ke nunawa Gausiya ya ɓaci tun bata da wayo har ta fahimci da zaran ta tsalla ihu Mama zata birkice, sai ta tsiro da fitina kala kala, ga faɗa da zagi haka Umma zata rufe ido ta zaneta, tun mama bata nuna bacin ranta har ta farawa Umma ba’a a wasa inda take cewa.
“Yaya da dai kin daina dukar zuciyar mamanta dan ji nake da ita kamar tsoka ɗaya a miya.”
Tunda ta faɗi haka umma ta kame hannunta a jikin yarinya amma kiri kiri, umma ta ware gausiya a cikin yara, tun malam bai fahimta ba har ya ɗago wariyar yayiwa Umma magana tace.
“Ita zata iya rike sauran yaran dan a hannunta aka haifesu ita kuma gausiya yar soce taje Uwarta ta riketa.”
Suna haka kwatsam Mama tasami cikin shkura shima tasha wuya dan har cirewa aka so yi Allah bai nufa, aka haifeta lafiya,
Bayan shekaru ashirin cif, yaran umma huɗu har dani da sai na mama Amarya shida, bayan shekaru aka sami cikinmu inda aka haifeni bakwaini, su Rahilah sai da suka cika wataninsu cif, ina da wata huɗu aka haifesu, mune kananu dan yayunmu duk sun girma har ana batun aurar da Aunty Shema’u Yaya Hayat yana karatu a ɗan fodio Uni.. Sokoto gausiya da shukra sune yan mata kananu,
Shema’u da Asma’u aka aurar dasu rana ɗaya, Aunty Shema tana auren wani ɗalibin Malam ne, sai mijin Asmau shima babanshi abokin malam ne,
Bayan shekara uku aka aurar da Hamdiya da iya kar yaran gidanmu scndry, daga nan magana ya kare,
Halayar gausiya ba daɗi, gashi sai rashin ɗa’a take a unguwarmu, yayinda shukra tafita.
Haka suma suka cigaba da karatu, har suka gama scndry shukra ta sami wani malamin jami’a anan kasu ya fito nimanta,
Gausiya wani yaro ta makalewa, ganin tana shirin lalacewa Malam ya hanata fita ga fitsara da rashin mutunci, babu me shiga shirginta har muma kanenta, ganin idan akace xa’a jirata ɓata lokacine akayi bikin Aunty Shukra.
Lokacin da Yaya Hayat ya gama karatunshi na likitanci, ya dawo gida nan ya gano gausiya na fita ya kamata yayi mata mugun duka,
Ranar malam na kasuwa Naziru yazo mishi, ya zama babba malami shima yana koyarwa a A.b.u, cikin farin ciki suka zo gida yaci abinci.
Nan yake faɗawa Malam ai zuwanshi hutu yayan Mamanshi daga Maiduguri yazo ya ɗaukeshi suka tafi can, dake suna da buɗi sai suka nima mishi takardu ya tafi sudan, har ya auri yar uwanshi bata jima da rasuwa ba gurin haihuwarta na uku, Malam ya tausaya mishi, ya tambaya Yaya hayat da shema’u anan malam ke faɗa mishi ai gidan ya cika, shigowa malam yayi ya faɗawa su Umma,
Komawa yayi gurinshi suka shigo gidan, inda farkon shigowarshi yayi tozali da Aunty gausiya,
Bayan anyi gaishe gaishe, akayi yaushe gamo, anan yake shaida musu Ai yaron shi babba sunan Malam ne ana kiranshi faruq, sai takwaran Iya Maryam,
Sosai malam yaji daɗi,, da zai tafi ya saukewa malam kayan masarufi,
Bayan sati biyu sai gashi nan yaxo ya gaida malam, wasa wasa ya maida gidanmu gurin zuwanshi, har karatun dare da na safiyar da ake, duk yana zuwa kai da yaga zai cutu ya fito ya faɗi abinda ke damunshi,
Malam yayi farin ciki, ya sami Umma da mana ya faɗa musu suma murna sukayi da aka faɗa mata katsaye tace.
“Lallai fa ni bana sonshi.”
Babu wanda ya saurareta, har aka fara maganar tayi karfi, sannan Baban faruq ya fara zuwa gurinta duk fitarta sai ta mishi rashin ɗa’a har akayi auren cin mutunci da wulakanci, cikin yaranta rabone kawai ya ratsa dan sai sun raba hali ya gwada mata karfi yake karɓan hakkinshi sai rabo ta ratsa,
Gashi Allah ya haɗata da munafukar makociya ita ke ɗaurata Kan kome, bayan aurenta akayi bikin yaya shida matarsa da suke zaune a doctors quarts anan kaduna, har da yaransu biyu Hasina wacce suke kira da Afren sai Atika wacce suke kira da Ihsan,
Tunda aka fara maganar auren Aunty ciwon Mama ke tashi har zuwa yanzun da ta kaso auren,
…….
Cikin tausayawa na share kwallar dake bin fuskana. Bayan sallar isha muka sake lekata tana bacci sannan muka koma ɗakin Umma.
****
Washi gari…
Muna tashi muka fito zamu fara aiki malam yace.
“Kuje mu kwanta, Gausiya ta fito.”
Jikinta na rawa tafito ya fara aiki, dakyar Umma tashawo kan malam ya barta tayi abin karyawa muka ci, bamu zauna ba sai makaranta.
Koda muka dawo an gama abinci, zama mukayi abinmu ko kulata bamuyi ba, muna gama cin abinci muka kai mata kwanon gurin wanke wanke muka shige ɗakin Mama , aka buɗe hira banu fito ba sai da azahar.
****
Kamar jiya yau ma shi yayi abin karyawa kuma ya cinye abinshi dan bata tashi, yana gamawa ya shiga ɗakin motse jikinshi yana idarwa Ahmad ya kirashi a kune ya saka wayar can kasa makoshi yace.
“Barka angon Hafsat.”
Yana sauke numfashi, dariya Ahmad yayi yace.
“Shege kana rage gajiyane na tsinke maka jin daɗinka toh idan kagama muna jiranka a officer.”
Katse kiran Ahmad yayi a gurguje ya shirya sanye da bakin jeans da farin shirt an rubuta Armania mai dogon hannun.
Yana isa officer din Ahmad ya sakashi a gaba da dariya……
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….
Dedicater To Hafsat Abubakar
_Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_