Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 48

Sponsored Links

48
Kukan Baby Amnah ne ya sakasa Dora fararen idanuwansa a gurinsu Zeenah din ya saukar dasu kan Amnah dake jikin benazir tana sake Kai madarar bakinta fuskarta a sanyaye da rashin sanin me zatayi Amnah ta Dena rigiman sbd rigiman Amnah daga rikitar da ita yakeyi Sam Bata San Abinda zai saka Amnah din Kuka.

Qarasowa yayi cikin palon har lokacin idanuwansa akan Amnah batareda ya Kalli wadda ke riqe da Amnah din ba.

Umme kuwa nata idanuwan akan dagayen fararen lafiyayyun qafafuwansa dake bayyane sike duk da tasan sune best kayan dayafi sakawa idan Yana gida Sam baya wahalarda Kansa da kaya masu nauyi ko takura.

Zaunawa yayi gefen ummen a hankali cikin nutsuwarsa ya gaidata batareda wainda ke palon sunji maganarsa sbd rashin daga muryan.

Zeenah dake kokarin gaidasa ne cikin farin cikin ganinsa maganarsa ta katseta kaman daga sama Benazir taji magana daga bayanta cikin sautin kamewa da nutsuwar murya.

“Baby Amnah ce??”

Benazir da maganar ta daketa Kai tsaye sbd Bata lura da shigowar kowa ba hannuwanta rawa suka fara ahankali batareda ta juyoba Dan Bata ma gane meya fada ba sbd nutsuwan muryan.

Zeenah ce ta daga baby Amnah din tana goge mata baki da lallaunsa pink baby hanky ta taso ta nufosa tana cewa

“Sannu da dawowa Yaya DD.”

Babyn yake kalla harta iso gabansa tana sake cewa

“Baby Amnah ga daddy ya dawo ki Dena rigiman haka.”

Sai alokacin ya juyo ya Kalli ummensa da idanuwansa dasukai Wani Dan shigewa da alaman “da gaske Amnah ce wanna?”

Murmush Mai yalwa Umme ta saki tana karban Amnah din daga hannun Zeenah tana sake goge mata Dan qaramin bakinta na mahaifinta data dauko Zak da Zak ta gyada masa Kai tana cewa

“Eh Amnah ce,gatanan duk ta ruda mummynta sbd rigimanta.”

Numfashi ya sauke a hankali mara sauti Yana kallanta daga hannun ummen Yana son daukanta Amma Bai San ya zai daukota ba sbd shi ba maabocin daukan Yara bane,
Bayama daukan Yara Sam Amma Kuma wannan tasa ce Yana Jin buqatan daukanta kaman yanda kowane Uba yake daukan ‘dansa idan an Haifa masa.

Dariya Umme ke masa da Zeenah lokacinda Umme ke kokarin Dora masa Amnah a hannuwansa Dayake Jin kaman zaa Dora masa farin cikin rayuwarsa ne kaf.

Ita kanta Amnah din kaman tasan gurin waye zata je dan haka tayi shiru idanuwanta a Bude.

Lokacin da Umme ta gama Dora masa ita ta janye hannuwanta suka barsa da ita ajiyan zuciya ya sake saukewa a Karo na biyu yanajin tsaftatacciyar kaunarta me qarfi da sanyi na sake kama zuciyansa,.

Yanzu shine uban wannan kyakyawan babyn ta hannunsa,
Daman haka feeling na zama Uba yake da sanyin nutsuwa?

Meyafi wannan kyakyawan babyn ta hannunsa a rayuwarsa yanzu??

Dagota yayi ahankali ya Karanto mata addua a natse cikin qaramin sautin da babu Wanda yaji tukuna ya miqe tsaye da ita a kafadansa ya fice zuwa palon dad kaante yana tafiya kaman bayason jijjigata hakama Bai Wani iya riqeta sosai ba sbd Bai iya dinba.

Yana fita Benazir data kasa motsi bare juyowa ta miqe tsaye a hankali cikin nutsuwa ta dauki kayan madarar tayi kitchen ta miqawa Nafisat Dan da tsaftacesu ita Kuma ta nufi daki hannuwanta na rawa bugun zuciyarta Datake ta riqewa sbd bugawan Dayake da qarfi Yana qaruwa.

Bedroom dinta ta nufa ta shige tareda qarasawa kan sofa ta zauna ahankali tana damqe hannuwanta dake Dan rawa.

Babu Wani tinanin Dayake ranta bayan na firgicin data shiga duk da tanada dauriya da nutsuwan danne firgicinta.

Zaunawa tayi a dakin shiru Bata fita ba tanata daidaita kanta Daga tsoro da fargaban data shiga har tsawon lokaci kafin ta tashi ta fada toilet tayo alwala ta tayarda sallar ishai tayi ta gama.

Tana tashi daga dadduman sallah mayarwa tayi ta nufi toilet Dan Yin wanka.

Tana shiga Bata Wani jima ba ta fito ta shafa Mai sama sama tayi duk Abinda zatayi ta saka doguwan Slianche free gown black da fari kadan a ciko har qasa tana kokarin daukan wayanta tagani ko zata samu magana da Anne Nafisat ta shigo ta sanar da ita lokacin dinner yayi.

Sauke numfashi Mai dumi tayi ahankali tareda ajiye wayar
Jikinta na mutuwa kafin ta miqe ta fito.

Tana fitowa Zeenah na fitowa daga nata bedroom din sanye cikin Riga da wandon Fendi masu Dan kauri ta shaqi qamshin Benazir din Mai sanyi Dayake Dan tashi jikinta tace

“Muci abinci muje mu duba dd babba tareda masa barka da dawowa.”

Gyada Kai benazir din tayi tana qarawa da cewa to.

Suna doso dining din Yana sake shigowa palon a Karo na biyu rungume da Amnah datai bacci a jikinsa.

Da nutsuwa yace

“Zeenah karbeta I think ta gaji or may be she’s hungry or something tana son farkawa kaman.”

Benazir data kasa gaba ko baya ta tsaya bayan Zeenah kanta a sunkuye shikuwa Yana bawa Zeenah Amnah ya nufi dining gurin ummensa.

Qarasawan da Benazir bataiba kenan ta juya dauketa Amnah Takoma daki batareda itama ta iya Koda tsautsayi daga Kai ta kallesa ba kaman yanda shi bai ma yi noticing nata ba.

A daki taci abincinta bayan tagama shirya Amnah tayi bacci sai tabarwa Nafisat ita suka fita zuwa sashen dd babba.

Dan mayafin Dayake kanta yasakata kakkame jikinta sbd gabaki Daya babu mayafin kirki a kayan da aka Siya mata Tin daga kan na lefe har Wanda aka sake sissiya mata bayan auren.

Da sallama suka shigo Zeenah ce a gaba sai Benazir din bayanta kaman yau aka kawota gidan.

Idanuwan dd babba akan Benazir tin shigowansu Kuma acikin mintina qalilan ya Karanto nutsuwa a tattare da ita Kai tsaye Dan haka ajiyar zuciya ya sake saukewa a Karo na biyu tareda amsa gaisuwar datai masa kanta qasa cikin tsananin girmamawa da ladabi.

Numfashi ya sauke tareda sakar mata a fuska cikin kauna da kulawa ya tambayeta Yaya baquncin sabon guri.

Kanta ta sake yin qasa dashi cikin sanyin murya da nutsuwa tace lafiya kalau.

Amnah ya tambaya itama tace lafiyan kalau.

Cikin hikima da nutsuwa yayita yan mata tambayoyi har akan karatunta yaji inda ta tsaya take ya yanke shawarar zata koma makarantarta tinda ashema hutun ya qare tin last 3 weeks.

Tariga ta cire tsammani daga komawa makaranta Dan haka tana Jin zancen nasa ta dago ahankali Amma Bata iya kallansa ba tayi godia cikin sanyin jikin yanda zatayi karatu da Amnah,
Kwatsam mutane su ganta da haihuwa ba aure.

Dd babba hanata tafiya yayi Saida yayi mata tambayoyin Daya gamsu da tafara samun sabo da kwanciyar hankali a Kaantes Dan haka ya sallameta ta tafi.

A Karan farko itama data samu nutsuwa da sanyin kwanciyar hankali da Wani Kai tsaye a cikin Kaantes din bayan Zeenah da Umme.

Jin tayi kaman ta samu Wani sabuwar nutsuwa da yanda dd babba ya mata nasiha tareda Bata tabbacin ta Kwantar da hankalinta a qarqashinsa babu Wani Abu dazai sameta ko Annenta duk da Bai fito ya nuna mata yasan komai ba.

Tana dawowa tini Zeenah ta shige hakama umme Bata ma sashen tana gurin dad kaante Dan haka itama shigewa tayi tayi Shirin bacci ta sallami Nafisat ta tafi sashen masu aiki ita Kuma ta shige bargo da Amnah dake bacci sosai har lokacin.

Washe gari suna cikin breakfast hajar me aikin Umme ta shigo har dining room ta sanar dasu Abbakar ya Aiko cewan Bena ta shirya za’a kaita makaranta.

Daga Umme har Zeenah sosai sukai farin ciki da Hakan Dan haka sama sama ta qarasa breakfast din ta miqe taje ta shiryo ta fito cikin wata Kuwait jallabiya me tsadan gaske maroon Bada mayafi bare hijab Dan haka dole kaman yanda Zeenah ta fada mayafin rigar ta Tayata nadowa suka fito gabanta na tsananta duka sbd yanda zataje school da ‘ya Amma Kuma hankalinta zai rabu biyu bazata taba samun nutsuwan karatun ba matiqar ba da Amnah taje ba Dan haka tini ta shiryata fes cikin designer kayan babies masu taushi da rashin ado aka nadota a pink shawl sai qamshi takeyi suka fito Nafisat na bayanta dauke da baby bag dinsu ta kayan Madara da komai na buqata da amfanin Amnah din.

Daga takalmin qafarta har chanel handbag din Dayake hannunta batasan kudinsaba Amma a yanda nutsuwarta yake Zaka dauka komai na jikinta ta San kudinsa Jan ajine takeyi Amma ha Hakan bane.

Bayan kwallin cikin fararen idanuwanta babu komai a fuskarta sai facemask Wanda Zeenah ta Koya mata amfani dashi ko acikin gida wasu lokutan,
Ita kuma Zeenah ta dauki dabi’an ne Daya yayan nata da babu inda zashi Bai sakasa sbd baya San ana yawan kallansa sai gashi Allah yayi masa wata irin haiba da kwarjinin da duk inda yaje zaa kallesa din sbd Wani nutsatsan kyau da ajin kamewa ne dashi.

Har mota Zeenah ta Rakata Driver ne sabo aka kawo yau din sbd kawai Kai Bena makaranta Kuma a Daya daga cikin motocin dd babba ya ware mata Dan kaita kawai da daukota.

Driver na ganin isowarsu ya fito da sauri ya budewa benazir din mota Yana mata barka da fitowa.

A mutunce cikin fargaba da tsoro ta amsa har Saida Zeenah a ta Bata qwarin gwiwa ita fa kaante ce yanzu ba buqatan Jin fargaba ko Jin nauyin girman da zaa ringa Bata.

Nafisat a gaba ta zauna Dan haka benazir din ce kawai a baya ita kadai sai Amnah dake jikinta.

Wayarta ta fidda tana son Kiran wayar Anne Amma tasan wayar na hannun Ababa lokacin Amma tinda ance driver ya biya da ita ta dauki takardun makarantar Datake ganin tana buqata wainda duka ta baro gida sai takejin gabanta na tsananta faduwa duk suka qara kusanci da Isa gidan.

Tsoro ne da rawa hannuwanta keyi sosai na Ababa Daya dasa musu a cikin ransu da har abada bazasu iya goge wannan tsoron ba.

Id card dinta kawai take buqata daga takardun makarantar data bari gidan Amma zuwan nata Sam Badan Id card din zatayisa ba sbd buqatan ganin Annenta ne da suka Dade Basu ga juna ba saidai a waya.

A kofar gidansu lafiyayyar motar tayi parking sai Data sauke ajiyan zuciya da numfashi a Jere kusan ba adadi zuciyarta na bugawa da qarfi cikin tsananin tsoro da shiga tashin hankali.

Tana cikin wannan firgicin ne Driver ya Bude mata kofa bata ma saniba Saida ya kira sunanta cikin girmamawa da a nutse.

Fitowa tayi qafafunta na Dan rawa tana damqe hannuwanta dake rungume da Amnah.

Kai tsaye kofar shiga ta nufa Nafisat na bayanta kaman jela dauke da jakar kayan madarar Amnah.
#MAMUH#
#ROMANCE
#LOVE
#HOT
#DBENA
#AMNAH
#BABY MAMAH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button