Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 40

Sponsored Links

Khaleesat Haiydar 40….. Kallonta kawae Aliyu ke yi bae ce kmai ba, kmr xata yi kuka tace “yayana baxa ka min oyoyo ba” dauke kansa yyi, ya kashe laptop dinsa ya rufe, Ikram ta juya tana kalln Mami dake tsaye tana hararanta da sauri ta mike daga jikinsa a tsorace tace “wayyo Mami wllh na manta ashe na daina wasa da shi” siyama dae na tsaye sae kallnsu take, Mami ta karaso cikin falon tana kallon siyama tace “momynku fa siyama” siyama tace “tana sama Mami, wllh daxu muke ce ma ya Mujaheed ya kai mu gidanki yace mu bari gobe sunday ashe ma kina hanya” Mami tace “to sae ku xo goben ae bae baci ba, ina su saiham da Aisha” Siyama xata yi mgna Khaleel ya shigo gidan kmr mara gskya, ta wara ido tace “lah ya Khaleel” da gudu taje ta rungumesa, yyi murmushi yana kallnta yace “hw re yhu siyama” tace “wllh yaya baka da kirki ko kadan” hannu ya daura a bakinsa alamar tayi shiru, dariya tayi tace “wllh baxan yi ba” su saiham da Aisha ne suka sakko jin hayaniya downstairs, basu bi ta kan Mami ba duk suka yi gun Khaleel da gudu suka rungumesa cike da jin ddin gninsa, Ikram tayi kusa da Mami tace “Mami su waye wa ennan sun san yaya khaleel ne, amma gashi suna rungumesa baki yi masu mgna ba kuma ae shi namiji ne su kuma na mace ne” Mikewa Aliyu yyi ya dauki system dinsa yyi hanyar stairs Mami ta bisa da kallon mmki har ya haura, hka ma seeyama ganin bae gaida Mami ba, Momy ce ta sakko da fara’arta tana ma Mami sannu da xuwa, bude baki tayi ganin Khaleel tace “iyye yau xa ayi ruwan sama da kankara, Hajiya kice yau kin lallaba autanki ya biyo ki knn don nasan lallabasa kika yi” dariya Khaleel yyi ya gaisheta ta amsa tana dariya tace “Barrister Khaleel knn, bayan mamin ka baka san da Allah yyi ruwan kowa a duniyar nn ba, xumunci dae ba abun wasa bne” dukar da kansa kawae yyi yana Murmushi ya xauna Saiham taje ta dauko masa drinks a fridge, Mami tace “Hajiya fa” Momy tace “ina jin suna kitchen da Farida” Mami tayi hanyar kitchen din, Momy ta kama hannun Ikram tace “mu je sama bby” duk yan matan suka bi Ikram da kallo da ta juya sae taga kallnta suke, suna isa stairs ta murguda masu baki tana jujjuya masu ido har suka haura sama da momy, dariya suka shiga yi ssae Khaleel na kallonsu. ciki ciki Hajiya ta amsa ma mami kmr ko da yaushe Mami ta juya tayi hanyar stairs tana murmushi. Duk yan matan suka xagaye khaleel suna ta lbri suna dariya, a hka Hajiya da farida suka fito daga kitchen suka samesu, Khaleel ya gaida Hajiyar ta tsaya kallonsa snn ta tabe baki ta amsa tayi gaba abunta tana cewa “kai ka girma ynxu sae shekarar da ka ga dama kke xuwa gaida mutane, don baxan ce rana ba, sae ayi shekara ba a ganka ba duk ka tare gun uwarka” shi dae bae ce mata komai ba sae ma daure fuskarsa da yyi, ikram ce ta sauko kasa rike da can malt tayi gun Khaleel tace “yaya Khaleel Mami tace ka bude min” ya harareta yace “ni xan bude maki” kmr xata yi kuka tace “don Allah mana ina son in sha” karbewa yyi ya bude mata, sae da ya fara shan na sha snn ya mika mata ta fasa ihun da sae da gidan ya amsa tana kiran Mami, rikota yyi da sauri tana tsalle tsalle yace “ke baki san gidan mutane muke ba” cikin kuka tace “wllh sae ka biya min abu na” yace “to to bari in xuba maki nawa” ya bude drink dinsa da sauri ya xuba mata, ta karbe tana leka ciki ko gwangwanin ya cika, da sauri ya karasa cika mata ta share hawayenta tare da murguda masa baki ta yi hanyar stairs, su seeyama duk sakin baki su ka yi suna kallonta, Aisha tace “wae wacece wnn ya Khaleel” ya wara masu ido yace “nima ban sani ba ku tambayi Mami” bayan Magrib Mami tayi ma momy sallama xa su koma gida, Momy tace “kin ki cin abincin gidanmu Hajiya” Mami tayi murmushi tace ni dae a koshe nake suna fitowa corridor Mami ta bude kofar dakin Aliyu, yana kwance yana kallo tace “ina yini Aliyu” kallo daya yyi mata ya dauke kansa, snn can ciki ya gaidata, harararsa tayi tace “aa kadae amsamin gaisuwata, kuma me ya hanaka xuwa aiki wk din nn” ba tare da ya kalleta ba yace “nayi tafiya ne” tace gud, snn ta fice daga dakin, ikram ya gani durkushe gefensa tana kallonsa kmr xata yi kuka, ashe sae da tasan ynda tayi ta shigo dakin Mami na masa mgna, mikewa yyi da sauri ya dago ta ya rungumeta yace “bbyna ta ina kika shigo” tace “yayana ka daina xuwa gidanmu ni ina sn ka dinga xuwa” yyi murmushi ya dago kanta yace “Mami bata son ina xuwa gidanta Ikram” Muryar Mami taji tana kiranta alamar nemanta take, ta mike a tsorace shima ya mike ya dauko mata pack din chocolate ya mika mata snn ya manna mata kiss a kumatu a hankali yace “i love yhu Ikram” washe masa hakora tayi tana kallon chocolate din ya bude mata kofa ta fice tana daga masa hannu, har suka fito compound Mami bata daina harararta ba, Ikram ta rike hannun ya khaleel kmr xata yi kuka don bata son harara, wata mota ce ta shigo gidan suna shirin shiga tasu motar, drivern dake sanye da kayan soja ya fito da sauri ya bude sit din baya, yana rike da jarida ya fito daga cikin motar da gninsa ka ga Aliyu, khaleel ya juya da sauri yace “ya salam”
[2/25, 08:35] Zjy: ~

Back to top button