Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 28

Sponsored Links

Aliyu
yyi murmushi ya dafa ta yace “yauwa kanwata xo
muje ki fada min me dame Anty ta koya maki” ya
karbi jakarta suka nufi garden din tana gaya
masa menene bad habit kmr ynda taji Anty tace
yau. Ikram na xaune a falo ita da Jummai tana
cin abinci bayan Aliyu ya wuce Mami ta shigo
gidan taje ta rungumeta da gudu tana jin ddin
ganinta, Mami tace “dota kinyi karatu da kyau
yau ko” Ikram tace “eh mana yayana ya koya min
assignment dina kuma na iya bari in kawo in
maki ki ga” ba karamin mamaki Mami tayi ba
ganin ynda tayi solve din Bodmas da kanta, tace
“Ikram wa ya koya maki wnn” Ikram tace “wnn
yayana din nn mana shi ya koya min, har da
dayan ma na iya bari ki ga” Mami na kallon
Jummai tace “Khaleel ne ya koya mata?” Jumma
tace “A’a doctor ne ya koya mata” Mami ta dan
yi murmushi tace “to ya kyauta” da daddare xa
su kwanta Ikram ta ishi Mami wae ita gun
Amminta xata, Mami tasan kewar uwarta take
ssae don hka ta shiga kwantar mata da hankali
tace “kar ki damu dota ran sati xan kai ki kinji”
da kyar Ikram ta yrda don har da kukanta Mami
ta hadata da wayarta tana ta danne2 daga nn
bacci ya dauketa. Cikin sati dayan da Ikram tayi
tana xuwa sch ba karamin mmki ta ba Mami ba
don bata manta duk abinda aka koya mata, duk
da da kuka take barin gidan idan sch bus ya xo,
snn kuma da yamma Aliyu na assistn dinta ssae,
Mami ta shiga neman islamiyyar da xata sata na
yamma idan ta dawo daga sch in yaso sae lesson
din da Aliyu ke mata ya dawo da daddare, ko
kadan bata bari Ikram tayi kallo sae dae ta
hadata da wayrta tayi ta dannawa daga nn bacci
ya dauketa. Ranar asabar Mami ta shiryata cikin
kananan kaya da hijab dinta tayi kyau ssae, cikin
jin ddi tace “Mami ina xa mu” Mami tayi
murmushi tace wajen Amminki xamu dota, tsalle
Ikram ta shiga yi tana jin ddi Mami ta hade rae
tace ban hanaki wnn tsallen ba Ikram” khaleel ne
ya sauko rike da car key Mami tce “na fa ce mka
xamu fita son”

Back to top button