Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 15

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*NASARAR RAYUWATA*

*15*

Aman na kwance a bayan mota ya hango Ayman na fitowa daga snake farm ” wannan Kuma uban me yaje Yi a snake farm” tabe Baki yayi ya koma ya kwanta jikin lallausan kujerun ya cire idonsa daga bangaren Ayman tunanin Hajjo yake Yana son ganinta a yau din nan Amma ya rasa dabarar da zaiyiwa Ammi ya samu ya fita ba tare da tasan inda yaje ba, yanzu gaba taya ta Kara saka masa Ido duk shiga da fitarsa tasani ga uwa Uba wNnan mayyar yarinyar zee tabi ta takurawa rayuwarsa Bata da tarbiya ko kadan Bata da kunya, yanzu ne yasan lallai kunya ma Ado ce ga mace. Yinin ranar Ayman ya kasance ckn farincki da nishadi duk da cewa baisan matakin da inna zata dauka ba Amma Yana da yakinin cewa zatayi Naam da shawararsa saboda ya lura ita din macece Mai ilimi da sanin ya kamata donhaka ya barwa Allah zabi , kowane dakika fuskar Hajjo yake hangowa ckn zuciyarsa duk lokacin da tunaninta ya fado masa lumshe Ido yake Yana murmushi.

********

Inna ta gama magana da mmn Nana sun gama shawarwarinsu daga haka suka tare Abar Hawa zuwa maraba Kai tsaye heart plaza suka sauka inna tana son Siyan karamar waya karo na farko taji shaawar ta mallaki waya saboda tana Shirin rabuwa da sanyin idaniyarta ya zama dole ta nemi hanyar sadarwa Koda Basu tare. Ckn kudin da Ayman ya damkawa Hajjo suka cire suka Siya Tecno karama 7k daga nan suka shiga kasuwar maraba sukayo cefane sannan suka wuce gida, da dare inna ta karbo sabuwar wayarta daga gun chaji ta saka sim da komai ta kunna wayar zuciyarta na raya mata Kiran Wani Amma dayan bangaren na zuciyar na gargadinta haka ta kasance ckn waswasi daga karshe ta kasa Kiran ta ajiye wayar a gefe ta kwanta tana Mai tuna rayuwarta na baya da Wanda take burin Jin muryarsa akoda yaushe. Bacci ya fara daukanta mmn Nana ta shigo zata kwanta tace ” har kin kwanta ne malama halan kin manta Baki kira wannan yaron ba” tashi tayi ” subhanallah..Kinga har na manta wllhi hankli na ya tafi Wani waje daban, bari na dakko layin nasa Ina Hajjo da Nana suke basuzo sun kwanta ba” ” suna can farfada wai zafi yayi yawa” ” ai gara su dawo tunda kema kin shigo kenan” bara na kirasu Amma ki gama wayar kafin nan” tana fada ta juya ta fice, murmushi inna tayi Kai mmn Nana akwai sanin ya kamata nan ta tashi ta Bude purse nata ta Ciro katin ta saka lambobin bugu daya ya shiga ya fara ringing har ya katse baa d’aga ba ta sake kira a karo na biyu nan aka kashe sannan aka kirata back, ckn muryarsa Mai cike da Kamala yayi sallama ta amsa masa nan suka gaisa tana gabatar da kanta yace yagane muryarta, daga nan ta sanar dashi shawarar da ta Yanke yayi murmushi Mai sauti nan yake shaida mata akan gobe su shirya zaa zo a daukesu akaisu makarantar, cike da mamaki inna tace ” Amma gobe Baiyi sauri ba bamu shirya komai ba fah” kwantar da hankalnki mama insha Allah Babu wata matsala kedai ku shirya ku fito under bridge zamuyi waya inda zaa daukeku” ckn sanyin murya tace ” shikenan Allah ya saka da alheri Allah ya nuna mana goben ” Ameen mu kwana lfy mama” daga haka ya kashe waya, inna tayi jimm tana tunani Anya batayi kuskure bah, batasan Halin mutane ba tayi saurin yarda dasu zatayi wasa da rayuwar y’ar ta kwaya D’aya tilo. Mmn Nana ne ta shigo tare da sallama yaran na biye da ita a baya kowa ta nemi wajen kwanciyarta, numfashi inna ta sauke tace” Hajjo dawo nan magana zamuyi ” Hajjo ta dawo kusa da ita ta zauna ” Ina son ki bani aron hankalnki a nan” gyara zama tayi mmn Nana tana kallonsu cike da tausayawa , nan kuwa inna ta fara mata nasiha ” kiji tsoron Allah duk halinda kk tsinci kanki, ki rike ibada duk da nasan Baki da matsala Amma Ina son ki dage karkiyi wasa da sallah ki zauna matsayin da Allah ya ajiyeki Babu ruwanki da shiga tsabgar masu kudi, ki Maida hankali kan abunda kk je Yi Kuma ki rike mutuncinki Babu ruwanki da zuwa gun malamai ko kebewa da Wani namijin, kiyi taka tsantsan da mutane kibi komai a sannu Kuma kiyi hakuri duk halinda kk tsinci kanki ciki , …haka dai inna ta cigaba da mata nasiha Mai ratsa jiki Hajjo tace ” insha Allah zan kiyaye toh Amma inna inane zan tafi haka?” Murmushi tayi tace ” makaranta zaki tafi inda zakije ki cika burinki na rayuwa ki Maida hankali sosai banson wasa da karatu Ina son ki fito da sakamako Mai kyau ” insha Allah inna zan dage ko saboda ke da Baba nah” “Allah ya Miki albarka ya Baki nasara ya tsaremin ke” Ameen innata Amma tare zamu tafi koh” shafa gashinta tayi tace ” ah ah Hajjo zamu na Kai Miki ziyara Amma ke can zaki zauna sai anyi hutu” kwalla ya cika mata idanu nan inna ta danne nata hawayen tana rarrashinta haka man Nana ta saka Baki tana rarrashinta, haka suka kasance har zuwa Wani lokaci ckn kankanin lokaci bacci yayi awon gaba da Hajjo inna ta gyara mata kwanciya sannan ta fito tayi alwala ta kama nafilfilu tana rokawa y’arta Nasara a rayuwa tana Kai matsalolinta ga ubangiji.

Karfe 10:30am suna under bridge din maraba suna jiran Kiran Ayman suna nan tsaye sai ga wata mota fara Kal da ita tayi parking Ayman na gaban mota ya leko yace musu su shigo fauzan ke xaune maxaunin direba , inna ta Bude suka shiga fauzan ya ja suka kama hanyar ckn Abuja a nan suka gaisa Hajjo kuwa hankalinta na kan hanya tana kallon kyawawan gine ginen garin saboda wannan shine karo na farko da ta taba shiga ckn garin. Murmushi Ayman yake Yana kallonta ta ckn mirror mmn Nana kuwa a tsorace take don tana ganin tamkar sato su akayi inna kuwa hnkli kwance take kallon titi tana tuna abubuwa dayawa na rayuwarta saboda ba wannan ne karo na farko da ta fara shiga birnin tarayyan ba. Tafiya suke Babu Wanda ya sake magana cknsu har suka Kai A.Y.A fauzan ya Mike xuwa hanyar wuse Bai tsaya ko’ina ba sai women center nan yYi parking a dai dai katafaren building din Sahad stores, Ayman ya juya yace ” Bismillah mama zaku iya zuwa ki zaba mata abunda take bukata duk da ma school din suna Bada abinci Amma ki ɗauko mata duk abubuwan suka dace ” ” ah ah ba sai anyi haka ba abincin makarantar ya wadatar ” don Allah kada kiyi haka please ki daure ku shiga” Batason gardama donhaka ta Bude kofa ta fita Hajjo ta kawo Kai inna tace mata koma ki zauna mmn Nana taho muje” turo Baki tayi tana kunkuni don so take ta shiga wannan katafaren wajen daga Gani zai Hadu ga nan securities birjik ga mutane ana shiga ana fita, Kai tsaye inna ta kama hanyar xuwa cki tana tafiya ckn kwanciyar hnkli mmn Nana kuwa ta rikice don Bata taba shiga guri irin haka ba, shi Kansa fauzan yYi mamakin inna yadda take tafiya ckn confidence Babu tsoro Babu gidadanci haka yabi bayansu inna ce a gaba har suka Isa wajen entrance nan suka karasa cki, fauzan Bai Kara mamaki ba sai wajen hawan escalator yadda inna ta hau kadai zai tabbatar ma cewa ita din wayayyice mmn Nana ko sai raba Ido take hannunta na ckn hannun inna domin ba karamar drama aka Sha ba kafin ta yarda tahau wanga abin…
Bayan sun kammala duk wata siyayya akaje wajen biyan kudi inna ta fiddo kudi zata biya fauzan yace baisan da zancen ba haka ya Mika ATM card din ogan suka bi layin biyan kudin.

Al’amarin Hajjo da Ayman kuwa bayan tafiyan su inna Hajjo ta turo Baki ta Bata rai Ayman ya juya Yana kallonta Yana murmushi yace ” ba gaisuwa” kauda Kai gefe tayi tace ” Ina kwana” kullum sai na roka, haka zakiyi idan kika auri Aman?” da sauri ta d’aga Kai tana kallon” kodai Baki murnar zuwa makarantar, Aman ne fa yace Akai ki can” ” don Allah..da gaske? Abokine yace a kaini makarantar kwana?” Ckn kankanin lokaci fuskarta ya fadada da murmushi, Wani abu ya daki kirjin Ayman ya basar ya juya Yana gyara zama Yana Jin zuciyarsa na masa nauyi ” Ina Abokin nawa ya daina xuwa wajena me na masa?” shiru yYi kamar bazai kulata ba sai yace ” yayi tafiya ne idan ya dawo zai Kai Miki ziyara” murmushi tayi ta koma ta kwanta ckn kujerun tana karewa wajen kallo. ” Nan Ina ne? Wane garine wannan” “Abuja”
“Toh Amma ba garinda muke zama a can maraba ne Abuja ” murmushi yYi Bai sake mata magana ba har fitowar su fauzan daga haka aka shigar da kayan yaja mota suka tafi, mmn Nana dai tana bawa idonta abinci yau lallai kuwa yaune tasan ta shigo Abuja don wannan gidajen benayen sai dai a film take kallonsu dolene masu kudi kowa Abuja kowa Abuja tabbas Abuja gari ne, Kai tsaye airport road suka mike suka cigaba da tafiya can suka shiga Wani street sai gasu agaban Wani katafaren bene ko a ce benayen tunda ba Daya bane Wani katon gate ne a garkame a Saman an rubuta Future hope leaders academy Lugbe Abuja, horn ya danna Wani security ya leko sannan ya Bude gate din suka wuce tafiya Mai Nisa sukayi sannan suka tsaya bakin Wani gate Kuma daban nan ma securities ne birjik fauzan ya Bude booth suka Duba sannan ya wuce, ckn harabar makarantar yaje yYi parking dama can sungama komai donhaka Basu Sha wahala ba aka karbeta hannu biyu Ayman Yana ckn mota fauzan ne yayi komai ya gama sannan suka fito tare da inna da Hajjo da mmn Nana, senior boarding house mistress ta fito nan mamaki ya kashe fauzan da mmn Nana domin kuwa inna da ta fara magana da Wani kalan pure English Babu mix ko kadan very fluent har ta gama gaisawa da matar ta gabatar da kanta , cike da faraa ta rike hannun Hajjo tana tambayarta ya sunanta Hajjo tayi rau rau da Ido inna ta girgiza mata Kai tana rarrashinta a haka fauzan ya fito da kayanta dama makarantar ce zata Bada uniform kudi kawai zaka biya su zasu Bada komai har littafai. fauzan ya sake Bude booth wata karamar trolley Mai kyau ya kawo gabansu ya ajiye matar( Mrs julliet) tace a Bude saboda checking ta gama Duba kayan ciki su sabulai ne da toothpaste body spray body cream inner wears da sauran abubuwan inna dai mamakin wannan lamarin take har ynxu batasan manufan Ayman akan abubuwan da yake musu ba Amma ba komai da sannu zata sani, nan inna ta karbi number Mrs julliet akan idan akwai wata matsala a sanar da ita sauran siyayyan da suka mata a Sahad aka sake budewa kayan tea ne da sabulai dasu cornflakes golden morn da sauransu, orange house aka Bata daga haka sukayi sallama Hajjo na kuka inna ta sunkuyar da Kai ta juya mmn Nana tabi bayanta suka wuce mota direct, fauzan ya shigo ya ja motar suka fice.

Thanks for the prayers Allah barmu tare

Back to top button