Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 66

Sponsored Links

6⃣6⃣

A chan 6angaren memartaba koda yana a kwance ammah har a lokacin maganarsa d’ayace shidai yarima, ahaka yasa aka ware kud’i masu yawa yace agyara ma suhail d’insa part d’insa dan yana ji a jikinsa zai dawo garesa, kowa ya d’auka magagin ciwone har anshare maganar saida sukaga ran memartaba yana shirin 6aci sannan akasa akafara yi masa gyara.

Yanzu mulkin hannun waziri suka damk’asa dan bawani mai kwanciyar hankali a cikin ‘ya’yansa, gabad’aya family d’in abubuwa goma da ishirin sun had’u sun cakud’e musu, kullum maganar d’ayace shine memartaba ya amince aje ayi scanning d’in ammah ya k’i saidai ruwan addu’o’i da malamai suke aiko masa da shi ake bashi yana sha, masallatai ko duk sallah sai sunyi ma sarkinsu addu’a dafatan Allah yatashi kafad’unsa.

Yau ma kamar kullum ‘ya’yansa ne zagaye da shi daga gefensa dada ce, cike da damuwa sultan ahmad yaruk’o hannun mahaifin nasa yace ranka yadad’e kataimaka ka amince muje ayi scanning d’innan kaga gabad’aya hankalinmu atashe yake babu sauran mekwanciyar hankali dukkanmu nan a k’ark’ashinka muke burinmu d’aya shine muga kasamu sauk’i.

Murmushin k’arfin hali memartaba yayi sannan ahankali muryarsa tana fita dakyar yace Ahmad kucigaba da yi min addu’a in da rabon intashi toh zan tashi domin waraka ta ubangiji ce.

Dada fashewa tayi da kuka tace hakane ranka yadad’e ammah ai ubangiji bai safkar da cutaba saida yasafkar da maganinta dan Allah kataimaka aje asibitin kaga bamu kad’aiba hatta sauran mutane hankalinsu atashe yake.

Cikin dauriyar ciwo memartaba yace shikenan na amince muje ammah ubangiji ya gama tsara komai akan lamarinsa.

Cike da jin dad’i tare da neman gasgata kalmar da kunnuwansu suka jiye musu nan suka shiga kallon juna suna murmushi.

Sultan Abbas ne yace dagaske ya amince muje?
Shima sultan ahmad murmushi yayi yace nima kusan abinda kunnuwana suka juyo min kenan.

Dada share hawayen fuskarta tayi tace Alhmdllh yanzu kuje kusa ashirya motocin da zamu tafi da shi, asibitin suhail kawai zamuje.

Cikin jin dad’i sukaje sukasa aka shirya motoci nan aka fito da memartaba aka shigar da shi motar da aka tanada dominsa Dada kawai tashiga cikinta.

Su kuma cikin d’ayar motar suka shiga ahankali ake tuk’in duk inda aka wuce talakkawa d’aga masu hannu suke suna ma shugabansu fatan samun lafiya.

Koda suka isa Prince.S hospital, cikin gaugawa akazo aka tarbesu dan motocin kawai da suka gani yasa sukagane daga inda suke,

Dr khalil da sauran manyan likitocine tsaye akan memartaba a cikin wani k’ayataccen room suna ta bincike bayan anyi masa scanning d’in, inda shi kuma yake ta baccinsa.

Gabad’aya hankalinsu ya tashi saboda basusan yadda zasuyi sushawo kan matsalar ba nan sukayi ‘yan maganganunsu.

Dr khalil ne yafito jiki ba k’wari yanufi inda su dada suke zaune, ganinsa yasa gabad’ayansu suka mik’e suna tambayarsa jikin memartaba.

Murmushin k’arfin hali yayi yace Alhmdllh dasauk’i sannan yasamu waje yazauna, ya umurcesu da suma suzauna bayan sun zauna, kallonsu Dr khalil yayi sannan yace Alhmdllh mun gano abinda yayi causing d’in ciwon cikin ba komai bane face ‘yan hanjinsane da wasu suka nad’e,

Gabad’ayansu saida gabansu yafad’i sukace ‘yan hanjinsa sun nad’e?

Ganin yadda hankalinsu yatashi yasa Dr khalil yad’anyi murmushi yace kar kudamu ba wata babbar matsala bace tunda daman ana samun masu shiga wannan condition d’in kuma suna rayuwa saidai ta hanya d’aya za’a bi.

Gabad’aya suka had’a baki wajen cewa ta wace hanya kenan?

Ajiyar zuciya yasafke sannan yace ta hanyar yin theatre.

Sultan abbas ne yace toh Dr indai ta hakan za’a samu sauk’i toh mu relatives d’insa mun amince ayi masa kawai.

Jinjina kai Dr khalil yayi yace abbah saidai wani hanzari ba guduba jinin memartaba ya hau sosai babu yadda zamuyi mu iya yin wannan aikin batare da jininsa ya d’an yi low ba.

Salati suka sanya cike da tashin hankali, dada kuka tasaka tace yanzu khalil babu yadda za’ayi a iya yin komai?

Cike da jin tausayinta yace ranki yadad’e kar kidamu zamu duba mugani.
Yauwa Dr dan Allah kubincika sosai.
Dr khalil yace kar kidamu ranki yadad’e zamuyi iya bakin k’ok’arinmu.
Yafuto sultan Ahmad yayi da ido sannan yamik’e yace ina zuwa.

Saida yafita sannan sultan Ahmad yamik’e yabi bayansa.

A office d’insa suka je, bayan sun zauna Dr khalil kallonsa yayi cike da damuwa yace daddy adai cigaba da yi masa addu’a dan jininsa ya hau over, kuma a wannan condition d’in da yake ciki baikamata ad’au lokaciba batare da anyi masa aikinba, ammah a yanzu zamu d’aurasa akan wasu drugs tsawon kwana ukku idan har jinin baiyi low ba toh saidai afitar da shi abroad.

Innalillahi wa’innah ilaihiraji’un daddy yashiga nanatawa cike da damuwa.

Dafe kai Dr khalil yayi kamar mai tunani sannan yace yauwa akwai wani mai irin wannan condition d’in da aka kawo mana bamuyi aikinba sai dagabaya akace mana ankaisa a wani gari wani likitane yayi masa aikin saidai ban tambayi wane gari bane ammah gaskiya ance yanzu haka mutumin yana nan lafiya lau ya warke.

Cike da damuwa sultan ahmad yace dan Allah khalil kataimaika kagano wane garine inyaso sai muje.

Murmushi Dr khalil yayi yace insha Allahu daddy zan bincika yanzu dai bari inje infara kawo drugs d’in da zai fara amfani da su mugani, Indai har akayi kwana ukkun bai safkaba sai kutafi chan.

Jinjina kai daddy yayi cike da gamsuwa da maganar Dr khalil yace Allah yashige mana gaba.

Ameen,,cewar Dr.
Sannan suka tashi suka fito tare inda sultan ahmad yakoma wajensu dada yai musu bayanin rik’esu da za’ayi tsawon kwana ukku ad’aurashi akan magani, ammah bai fad’a musu sauran bayaninba gudun kar hankalin tsohuwar tasu yatashi sosai.

 

Haka Dr khalil yaje yakawo drugs d’in, tun daga wajen d’akin dogarawane aka zuba suna gadinsa, sultan ahmad ne yace zai dinga kwana da mahaifin nasa ahaka su dada suka amince suka koma gida.

Kulawa sosai memartaba yake samu daga ma’aikatan asibitin ba a awa d’aya batare da anzo anduba lafiyarsaba, abinci dakyar ake samu yana d’an ci kad’an kafin yasha magani, su dada kullum suna hanyar asibitin sai dare suke komawa.

Mutanensa dadama sunzo dubasa dan ma ana hanasu shiga wajensa saboda ba aso ana damunsa dayawa.

*BAYAN KWANA UKKU*

Nan likitoci suka k’ara taruwa akan memartaba aka k’ara bincikawa ammah har a lokacin jinin nasa bai yi wani low ba saidai d’an ragewa da yayi kad’an.

Gabad’ayansu hankalinsu ya tashi, nan Dr khalil yakira sultan ahmad da sultan abbas cikin damuwa yasanar da su,

Su dukansu hankalinsu ya tashi, ganin haka yasa yace ammah Alhmdllh na binciko garin da kwararren doctor d’in yake ance min garin Abuja saidai sunce bazasu iya tuna sunansaba ammah yana aiki a babbar asibitin garin, insha Allahu inaji a jikina za’a dace idan akaje chan.

Cike da gamsuwa suka ce insha Allahu zuwa gobe zasusa ayi masu komai sukama hanya dan yanzu ma dare ne kuma sunaso suyi shirye-shirye saisa bazasujeba a lokacin.

Dr khalil yace Allah yasa adace.

Nan sukaje suka sanar ma dada akan batun zuwansu jihar abuja, saida ta jinjina ma lamarin sannan tace toh shikenan Allah yakaimu goben yanzu muzo mutafi gida muyi ‘yan shirye-shiryenmu.

 

Koda suka koma gida kayansu suka shirya nan sultan abbas yaje yayankar musu ticket, su sultana bilkisu da sultana sadiya sunso subi aje dasu dada tace a’a subari sai daga baya sai suzo ammah yanzu in suma sunbi wa za’a barma gidan.

Haka suka hak’ura suka zauna tare da yin fatan Allah yasa adace.

Da dare koda waziri yashigo duba jikin memartaba, rik’o hannunsa memartaba yayi cikin muryarsa da bata fita sosai saboda zafin ciwo yace ga amanar gari da talakkawana nan na damk’a maka.

Rik’e hannunsa waziri yayi kwallah duk tacika masa ido yace na amsa ranka yadad’e Allah yabani ikon cikawa kaikuma Allah yabaka lafiya.

Cikin jin dad’i memartaba yayi murmushi tare da maida idanunsa yalumshe.

 

Wanshe kare tun dasafe motoci kusan guda goma sukayi layi suna jiran fitowar su memartaba, wajen k’arfe goma suka fito, inda su sultana bilkisu sukayi musu rakiya har airport, inda dandozon mutane suke tsaye ahaka suka shige jirgin mutane na d’ago musu hannu tare da addu’an Allah yaba shugaban nasu lafiya, saida sukaga tashinsu sannan kowa yakoma gida.

*GARIN ABUJA*
Suna isa garin nan sukatarar da motoci da shi kansa sarkin garin tsaye suna jiran isowarsu, kasancewar daman tun jiya sun sanar da shi akan zuwan da zasuyi.

Cikin karamci da jin dad’i suka tarbesu daga nan suka d’unguma wani k’ayataccen gida da aka tanadar masu dan suzauna a ciki, sunso sufara wucewa asibitin ammah sarkin garin yace sufara zuwa su huta sannan.

Haka suka hak’ura saida sukaje suka kimtsa suka ci abinci sannan sukafito suka shiga motocin da sarkin ya aje musu aka jasu zuwa asibitin.

Koda suka isa yanayinsu kawai aka gani da motocin da suke ciki yasa aka gane daga inda suka fito, koda daman sarki kabir ya kirasu ya sanar da su akan zuwan sarkin gazban.

Tarbarsu akayi sosai inda aka wuce da memartaba a amenity, nan suka duba history taken d’in da ke cikin folder d’insa na chan garin, saida suka k’ara yi masa scanning d’in dan tabbatarwa nan kowa yai shuru.

Sultan Ahmad ne yasanar da su abinda Dr Khalil yafad’a musu akan wani mai irin condition d’in da aka ta6a yi ma theatre kuma BP d’insa yayi high.

Jinjina kai MD Dr Muhammad bashir yayi sannan yace shikenan zanje intuntu6i Dr S domin nasan shine kawai zai iya hakan.

Cikin jin dad’i sukayi masa godia nan yatashi yanufi office d’in Dr suhail da baisan wainar da ake toyawaba.

Lokacin da M-D yashiga zaune yatarar da shi yana research a cikin system d’insa.

Nan yamik’a masa hannu suka gaisa, bayan sun gaisa nan yake sanar da shi akan zuwan wasu da irin condition d’in da patient d’in yake ciki.

Shuru Dr suhail yayi na d’an Lokaci sannan yace zan iya ganin file d’in patient d’in?

Nan Dr muhammad bashir yayi waya, ba a wani dad’eba saiga wani Dr hannunsa rik’e da file nan yabud’o yamik’a ma Dr suhail, saida gaban Dr suhail yafad’i ammah yadake yana karanta history taken batare da ya duba sunan me file d’inba.

Saida yagama karantawa nan gabansa yai wani irin fad’uwa lokacin da yaga sign d’in Dr khalil, cikin sauri yajuya bayan folder d’in, baisan lokacin da saki folder d’inba lokacin da yaga sunan da yake jikinsa, nan gabansa yacigaba da dukan ukku-ukku tashin hankali yabayyana k’arara a fuskarsa.

Bai san MD yana masa magana ba saida Dr muhammad bashir yata6osa tare da cewa Dr S lafiya.

Ajiyar zuciya suhail yasafke cike da damuwa yace ba zan iyaba kusami wani yayi.

Kallonsa Dr muhammad bashir yayi cike da damuwa yace ammah ai an tabbatar min da cewa kaine kata6a yi ma wani mai irin condition d’in.

Dafe kansa yarima yayi yace ni ba zan iyaba kakyaleni.

Cikin d’aga murya Dr muhammad bashir yace haba Dr suhail baidace kace haka ba bayan aikinka ne kuma inaji a jikina zaka iya.

Mik’ewa suhail yayi tare da kife system d’insa yace bazan iyaba nafad’a maka!.

Cikin jin haushi shima yamik’e yace zaka iya man, dan haka umurni nabaka a matsayina na shugabanka dole kacika umurni na.

Wani irin kallo suhail yawurga masa yace shugaba kuma?

Murmushi Dr muhammad bashir yayi yace eh shugaba kaga indai kanaso kacigaba da aiki a k’ark’ashina dole sai ka bi umurni na.

Cikin d’aga murya suhail yace ank’i abi umurnin naka, kai bari kaji baka isa kasanyani abinda banyi niyaba, kuma dayake kaga su masu haline saisa kake rawar k’afa a kansu, ammah talakkawa wane irin wulak’ancine bakayi musu?

Cike da k’ulewa yace suhail ni kake fad’a ma magana haka?

An fad’a maka, shin ko ka mance lokacin da me irin case d’in yazo wulak’ancin da kayi ma relatives d’insa kafin ka amince? Ko ka mance da yadda ka wulak’antasu a lokacin da kud’insu bai cikaba? Ko ka mance da nayi musu aikin yadda kadinga nuna hakan bai burgekaba.
Matsowa suhail yayi kusa da shi yace idan ka mance toh ni ban mance ba kuma ni wajena da talakka da mekud’i duk d’ayane, dan haka a yanzu idan kai zaka iya yi saikaje kayi.

Dafe goshinsa Dr muhammad bashir yayi yace wai kai suhail maganar me kakeyi haka, kuma kasan ni ba cadre ta bane, ni doctor ne iyaka induba marassa lafiya kawai, kaiko har theater kanayi.

Key d’in motarsa yad’auka yace sai kasan yadda zakayi,,,yana fad’in haka yajuya zai fita.

Cikin d’aga murya Dr muhammad bashir yace suhail kar kasaki kafita daga hospital d’innan inkuma ba hakaba zaka fuskanci hukunci daga gareni.

Juyowa suhail yayi yakallesa a wulak’ance yace indai kana tak’ama da matsayin medical director da aka bakane toh daga yau kakoreni kaga idan zan daina numfashi kuma idan kana tunanin ina cin kud’ine a wannan aikin da nake toh nabaka satar amsa kaje katambaya kaji nawa nake kar6a, inaso kasani babu abinda zaku bani kawai dai ina wannan aikin ne saboda Allah,,,yana fad’in haka yajuya yaficce yabar Dr muhammad bashir tsaye.

Cike da mamaki Dr muhammad yakebin k’ofar da kallo sannan daga k’arshe yaficce yanufi office d’in Dr mu’az.

 

Yarima koda yafita motarsa yashiga yai mata key dagudu yafita yabar asibitin cikin k’ank’anin lokaci ya isa gida, lokacin da ya isa zarah tana bedroom dan haka yai kwanciyarsa saman 3 seater, jin kansa yake yana wani irin sara masa, ahaka yamaida idanunsa yalumshe zuciyarsa tana masa wani irin zafi.

Zarah da tafito daga bedroom tsaye tayi da mamaki tana kallonsa dan batasan dawowarsaba, takowa tayi ta iso inda yake daga gefen da yake kwance tad’an zauna tace ashe ka dawo.

Shuru yayi yakyaleta,
Am ko bacci zakayi? Cewar zarah.
Batare da ya bud’e idanunsa ba ahankali yace please kibarni banason damu.

Marairaicewa tayi tace toh bakada lafiya ne?

Bud’e idanunsa yayi da suka canza launin ja yai mata wani irin kallo da yasa zarah tamik’e ba shiri dan sak yarima suhail d’insa yakoma mata, maida idanunsa yayi yalumshe.

Juyawa zarah tayi takoma bedroom tana mamakin canjin da yarima yayi mata cikin k’ank’anin lokaci tunani tashigayi toh ita me tayi masa? Ko dai wani ya6ata masa a wajen aiki? daga k’arshe sharewa tayi tacigaba da hidimunta.

 

Dr muhammad Bashir ba ko sallama yashiga office d’in Dr mu’az kujerar da take opposite d’insa ce yaja yazauna fuskarsa ba alamun fara’a yace Dr wane irin marar kunyane kakawo mana muka d’auka aiki har yake ik’irarin fad’amin magana.

Cike da mamaki Dr mu’az yace ranka yadad’e wa kenan nakawo muku?

Cikin d’aga murya yace akwai wani bayan wanchan Dr suhail d’in.

Cike da mamaki yace suhail kuma anya shine zai maka rashin kunya?

Toh wa kake tunani bayansa duk matsayina a hospital d’innan ammah har zansa shi yayi theater yak’i bayan kuma abinda yazoyi kenan aikin, toh wlh kafad’a masa idan baiyi wasaba zan sa akoresa, su daman ‘ya’yan talakkawa basu iya samun wajeba daga ya samu ana biyansa albashi mai tsoka shine har yai bakin da zai fad’amin magana ko yana tunani daidai yake da ni? Daman tunda naga take-takensa nasan bazamu zauna lafiya da shi ba dan ya cika jin kai.

Dr mu’az baki yasaki yana kallonsa har yakai aya sannan yace Dr suhail d’in da kansa?

Tsaki yaja cike da k’ulewa yace kai wai ma shi d’an gidan uban wanene a garin nan? Wlh in dai har baizo yayi abinda nasa shiba toh zanyi sanadiyar barin aikinsa.

Mik’ewa Dr mu’az yayi yana murmushi tare da jinjina kai yace ranka yadad’e kayi hak’uri saidai ina tunanin bakasan waye prince suhail ba.

Da mamaki Dr muhammad Bashir yake kallonsa yace prince suhail kuma? Wanene kuma haka.

Murmushi Dr mu’az yayi a karo na biyu sannan yace prince suhail tun daga zubinsa da yanayinsa da komai nasa yaci ace ka gane babu talauci a tare da shi dan ko hanyar talauci bai saniba, d’an sarautane gaba da baya dan shine zai kasance magajin garinsu, saidai nasan kanka zai d’aure da kaga ya zo yana aiki a k’ark’ashinka.
shuru yayi nad’an lokaci sannan yace prince yana da babban hospital wanda yake mallakinsa ne, kuma kud’in da yake rik’ewa per month ko rabinsu ba a biyanka, ko salary d’in da ake biyansa a nan ba shi yake cinsuba yana raba ma talakkawa mabuk’ata, girgiza kai mu’az yayi yace idan prince yaso takarda kawai zai rubuta ba kai ba hatta ni zai iya yin silar barin aikinmu, dan de bai d’au kansa komai ba saisa bai bayyanar da kansaba ga sarkin garin nan.

Dr muhammad Bashir zare ido yake cike da tsoro dan gabad’aya maganganun Dr mu’az sun firgitasa, shi kansa ya yarda da maganar saboda yanayin yarima kawai zaka kallah kagane cewa kud’i sun zauna masa.
kuma nasan prince yana da dalilinsa da yasa yak’i yin aikin, ammah prince mutum ne mai tausayi.

Ajiyar zuciya Dr muhammad Bashir yayi tare da mik’ewa yashiga zagaye office d’in sai chan yace mu’az meyasa tun farko bakaimin bayani akansaba?

Murmushi Dr mu’az yayi yace ranka yadad’e ai shine bayaso ana bayyanasa yanzu ma nafad’a makane dan naga kana da buk’atar sani tun kan katafka babban kuskure.

Jinjina kai Dr muhammad yayi yace tabbas ka taimaka min kuma nagode, ammah akwai wani taimakon da yarage kayi dan Allah kataimaka kaje kalallashesa yazo yayi wannan aikin yaceci rai wlh wannan shima daga royal family yafito duk ga danginsa chan suna jirana kuma sarkin garin nan yakirani yafad’amin zuwansu.

ajiyar zuciya yasafke yace shikenan zan kwatanta yanzu bari inje office d’in nasamesa.

Ai baya office d’in ina tunani ya tafi.
ohk bari inje gida ina tunani yana chan.

Dr muhammad yace dan Allah kataimaka kashawo kansa.
kar kadamu Dr zanyi iya k’ok’arina.
jinjina kai yayi yace Allah yataimaka.
Ameen Dr mu’az yace,,,nan suka fita a tare.

 

Tunda yayi horn aka bud’e masa gate d’in gidan a chan parking space yahango motar yarima, murmushi yayi sannan yaje ya aje tashi koda yafito cikin sauri yashiga gida, bai ko je part d’insuba direct yawuce na su yarima.

Knocking yayi zarah da take cikin bedroom ita tafito da mamaki taga yarima yananan inda yake nan tawuce taje tabud’e, ganin Dr mu’az yasa tayi murmushi tare da gaishesa.

Amsa matayayi sannan yace prince fa?
Juyowa tayi takalli yarima da baida alamar motsawa sannan tace gashinan, bismillah kashigo.

Da sallamarsa yashigo nan zarah tashige bedroom tabasu waje.
Kujerar da take kusa da yarima yaje yazauna tare da fuskantarsa yace prince ba dai bacci kakeba ko?

Yarima batare da ya bud’e idanunsaba yace ya dai?

Murmushi Dr mu’az yayi yace ranka yadad’e da ka taimaka ka tashi sai muyi maganar

Banza yarima yayi yakyalesa
Ganin baida niyar tashi yasa yace prince dan Allah kayi hak’uri da abinda yafaru tsakaninku da MD kataima kayi ma patient d’innan theater d’in domin yana buk’atar taimakonka.

Ahankali yarima yabud’e idanunsa yasafkesu akan Dr mu’az murmushin k’arfin hali yace shikenan ka gama?

Girgiza kai Dr mu’az yayi yace kayi hak’uri ranka yadad’e ban gamaba kawai dai ina neman alfarma ne koda banga patient d’inba bansan irin condition d’in da yake cikiba shi kansa MD a yanzu ya yi nadama akan abinda yayi maka.

Ta6e baki yarima yayi yace wannan matsalarsa ce dan ni banda lokacinsa, kuma da kake maganar patient wannan ba matsalarku bace kuma ga surgeons nan mezai hana kunemi wani tunda bani kad’ai bane.

Haba prince bansanka da hakaba please kataimaka ka…..
‘Daga masa hannu yarima yayi yace please mu’az kana cikani da surutu kabarni zanyi nazari akai.

Jinjina kai mu’az yayi yace angama ranka yadad’e Allah yasa muji alkhairi ahuta lafiya.

Yarima batare da yayi magana ba yamaida idanunsa yalumshe, ganin haka yasa Dr mu’az yamik’e yafita yabar d’akin.

koda yafita kiran Dr muhammad Bashir yayi yashaida masa yadda sukayi, ajiyar zuciya MD yayi yace toh Alhmdllh zamu sauraresa,,,,bayan sun gama wayar zuwa yayi yasamu su sultan ahmad da suke jiransa cike da girmamawa yace kuyi hak’uri na tsaidaku.

cikin zak’uwa sultan abbas yace ya kukayi da Dr d’in da zaiyi theatre d’in?
Ajiyar zuciya yasafke yace ranka yadad’e kuyi hak’uri yanzu haka shi muke jira muji daga garesa.
Dr ahmad ne cikin sanyin jiki yace toh ko zaka rakamu wajensa muje mu dakanmu murok’esa.

Kar kudamu kukwantar da hankalinku insha Allahu munasa ran zai zo yayi masa domin Dr d’in baida matsala.

jinjina kai sukayi cike da gamsuwa da maganarsa sannan sukace Allah yasa.

Bayan Dr mu’az ya fita yarima wayarsa yad’auko yakira wani doctor da yake k’ark’ashin yarima nan sukayi magana.

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu:

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Sak’on gaisuwa agareku Mamar rumaissa nd khadija mekano ina ji da ku irin sosai d’innan_

❤❤❤

_*Mum chubad’o muhammad a kullum ina alfahari da ke har cikin zuciyata Allah yabarmu tare*_

Back to top button