Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 38

Sponsored Links

Karfe 5:00am tana kwance tana bacci yana tsaye akanta hannunshi rike da karamin bucket cike da ruwa ahannunshi dagawa yayi ya kwarara mata daga sama har kasa afirgice ta tashi tana salati four eyes sukayi ” kitashi aibakiga ta bacci ba kiyi sallah kisameni a bedroom dina” to kawai tace mishi ta tashi tacire bedsheet din da suka jike da ruwa takai toilet ta tasasu a drying machine itama tayi wanka tayi alwala tacanza kaya.

Bayan ta idar da sallah tanufi bedroom dinshi samunshi tayi yana zaune yana pressing din system idonshi sanye da farin glass daga gani wani aiki yakeyi me mahimmanci muryanta ahankali tace ” Mr azaad gani” batare da yakalli inda takeba yace kishiga kiwanke toilet dina da jikin toilet din sannan akwai kaya acikin washing machine kifito dasu ki wanke su tass inkin gama kuma banason inga dirty ko kwallin zarrah acikin part din nan and try to finish it before 9″ batace komai ba tashiga toilet din tabude washing machine ganin tulin kaya aciki kuma dukkansu wankakkune agoge wasuma baa taba sasu ba sunfi set 50 haka tafito dasu tafara wankewa tuntanayi ta dadin rai hartaji gaba daya tagaji bayanta har rikewa yakeyi. Ba ita tagama komai ba se wajajen 11:30am ko ina tayi kall dashi jiri take gani saboda gajiyan datayi ga yunwa bataci komai ba.
Lallabawa tayi tashiga kitchen tadafa indomie da tea tagama ci kenan tadan mike akan kujera har baccin wahala yafara daukanta yadawo tsayawa yayi akanta yana binta da eyes fridge yaje yadauko bottle water yabude yazuba mata afuska dasauri ta mike ganin shine tafashe da kuka ” shhhhh yimin shuru dukanki nayi ko zaginki nayi kitashi yanzu muje ” yafadin haka yayi gaba babu yanda ta iya haka tabi bayanshi wata kofa taga yashiga bata taba sanin akwai wani bedroom aciki ba seyau shiga ciki sukayi. Sake baki tayi ganin wani room and falon ne aciki sede alamu yanuna kamar yadade duk yayi mugun kura sosai wanda ko mutane uku ne sesunsha wahala kafin sugama gyarawa , tana cikin wannan tunanin taji yace ” oya ki gyara side din nan dan zuwa gobe nan zandawo ” fita yayi yabarta aciki tunani tafarayi shin ta ina zata fara gyara nan ,neman tsintsiya tayi tashare ko Ina sannan tafara mopping haka tabirkice kamar ba itaba babu abinda yake tsayar da ita se sallah.
Har karfe 9 nadare bata gama ba. Hango jakadiya abashiyya nayi da khairatyyy suna tsaye duk wani movement dinta suna wajan gabaki daya ransu abace yanzu sarauniyarsu ake aizabtarwa haka . Khairatyyy tace ” shugaba meze hana mudauki mataki akanshi ” girgiza kai abashiyya tayi tace ” ah ah khairatyyy wannan bangaren rayuwar sarauniya ne shidin mijinta ne mukuma babu ruwanmu da shiga tsakaninsu, domin tsakanin mata da miji se Allah amma abu daya ne nasani shine zeyi matukar dana sani arayuwarshi seyaji yatsani kanshi jizeyi komai na duniya bayamai dadi”

Yinin yau curr su ummi basuji dúriyan fanan ba harsun fara tunanin ko wani abune yasameta , fitowan Mr azaad zasuje masallaci ne yasa suka tambayeshi lafiya kuwa fanan shuru sece musu yayi tana nan lafiya kawai yau batajin fitowane zeenat ne tace ” to bari inje intayata hira” mugun kallo yawatsa mata yace koda wasa kar wanda yashigamin part yayi gaba abinshi.

Shigowa yayi bedroom dinta yasamu bata nan side din dayace tagyara yashiga anan yasameta akwance akan tiles ta dukun kune waje daya tana baccin wahala duk tagama aikin dayasata sa hannu yayi yadauketa yanufi bedroom dinshi da ita ajiyeta agan bed tashi tayi tana murza ido kallon ta yakeyi sosai can yace ” bace min da gani ” atsorace tabar dakin nashi dan ita yanzu tafarajin tsoronshi , batare data cire kayan jikinta ba ta fada toilet tasakarwa kanta shower warm water seda tadau 30mint kafin tafito daure da towel ajikinta duk tagaji batare data shirya cikin sleeping dress ba takwanta dakyar ta iyayin adduah tasamu tayi bacci, haka takwanta batare dataci komai ba.

Yau tun 5:00 ta tashi tafara nafila kafin aka kira asuba tanajin motsinshi lokacin daya tafi masallaci, yau ko komawa bacci batayi ba tafara aikace_aikace koda yadawo yasameta tanayi bece mata komai ba yashiga bedroom dinshi yakwanta , haka tasha aiki se 8:30 tagama komai tahada breakfast taci sannan tashiga tayi wanka tasa riga da wando tazura hijab dinta sadaf_sadaf take tafiya tanason taje gunsu ummi suyi sallama dantasan tsaff zece ze hanata fita tunda yanzu yasata agaba, kamar daga sama taji daddadar muryanshi yana fadin ” karki yarda kifita a part din nan kijira tukun ” ko waigowa batayi ba haka bata koma tazauna ba fitowa yayi yana sanye da farar jallabiya yabude suka fita.
Kowa ya hallara suka dai kawai ake jira sufito jinsu shuru ne yasa ummi tacewa zeenat taje ta kirasu kila basu tashi bane har zeenat tafara tafiya se gasu nan sun sauko sunkuyawa tayi tagaidasu, suka amsa suna tambayarta ko lafiya jiya bata fito ba satan kallon Mr azaad tayi ganin yakafeta da ido yanason yaji mezatace yasa tace ” ummi jiyan ne nadan tashi bana wani jin dadi sosai shine Mr azaad yasamomin magani” sannu suka dinga mata. Ahaka suka fito motoci guda 10 ne yakejiransu banda na securities, rungumeta zeenat tayi tana ” anty zanyi missing dinki” ” zanyi missing dinki nima sosai zee” cewar fanan, zuwa fanan tayi tarungume ummi, murmushi ummi tayi tace” my feena ba dadewa zamuyi ba kinji take care of yourself in son yamiki wani abu kifadamin” tom ummina, haka abba yasake jawa Mr azaad kunne akan yakula da fanan kamar gaske yace ” to” sosai tamusu adduah Allah yakiyaye hanya yakaisu lafiya yadawo dasu lafiya, sunjidadin addu’arta sosai.
Haka suka shiga motar zuwa airport suna musu bye-bye fanan kam jitayi kamar tayi kuka antafi anbarta da Mr azaad dakyar inzasu dawo susameta araye cewarta.
Haka yafinciki hannunta suka koma cikin gidan.

Tundaga wannan ranar fanan bata Kara sanin meye farin ciki ba duk wani hanyar dazata huta taji dadi Mr azaad yadatseshi gaba daya tafita ahayyacinta azabtar da ita kawai yakeyi da aiyuka masu matukar wahala duk tabi tarame tadanyi duhu abun tausayi ko kyakyawar bacci batayi yayi nasarar jefa mata tsoronshi aranta ko muryanshi taji jikinta daukan rawa yakeyi , kuma duk wahalar daze bata baya barinta da yunwa.

Yauma kamar kullum tunda garin Allah yawaye take faman wanke mishi wankakkun kaya da lafiyarsu kalau babu abinda yasamesu haka take tawanki kamar baiwa kwala mata kira yayi da ” keee ” naman jikinta ne yafara bari tsabajin tsoro haka tafito atsorace tace ” Mr azaad gani” cike da izza da gadara yace hadamin black tea ” dasauri tafice tashiga kitchen 3mint yadauke tagama tafito dashi hannunta narawa taza mika mishi yadan zuba ajikinshi wani gigitaccen mari yazabga mata a kumatu wanda seda tadena ganin komai nakusan minti uku kawai jinshi tayi yana” ke wacce irin mahaukaciya ce dazaki kona ni da hot tea” hawayen daya wanke mata fuska tagoge tana bashi hakuri dan tasan inya fusata yanzu ze kara mata wani marin daukan cup din tayi takai dustbin dan yadan fashe, tagoge wajan tana danne kukan daya ciyota kiranshi yaseer yayi yasanar mai yana falo.

Hira sukeyi da yaseer tashigo hannunta dauke dasu drinks takawo mishi tunda tashigo yaseer yake kallonta da mamaki ganin lokaci daya tayi wani rama kamar wacce tayi jinya fuskanta asake tace ” ya yaseer ina wuni ” amsawa yayi yana kare mata kallo dole akwai abinda yake faruwa , harzata juya cikin tsawa azaad yace ” ke zonan ” jikinta har bari yakeyi itaduk a tunaninta wani laifin takarayi nan da nan hawaye yafara zuba a idonta, kallonta yayi kafin yace ” meye nafada miki dangane da falon nan ?” Tana share hawaye tace ” kace karna kara shigowa ” ” okay yanzun renine yasa kika shigo ” cewar Mr azaad ja da baya tayi tana” kayi hakuri Mr azaad bazan sake ba”
Inbanda salati babu abinda yaseer yakeyi aranshi dama abinda azaad yake aikatawa yarinyar nan kenan tabbas yasan azaad ze aikata haka koma abinda yafi haka amma dayaji shuru yayi tunanin yarungumi matarshi ne suna zaman lafiya ashe bahaka bane, kallon fanan yaseer yayi yace ” zeki abinki” dagudu tashige cikin bedroom dinta dan gani takeyi kamar zebiyota yadaketa.
_____ Maida kallonsa kan Mr azaad yayi dake danna wayarsa ko ajikinshi gyara zama yayi yace ” yanzu dude abinda kake aikatawa dedene? dan Allah wallahi baka rike amana ba wannan karamar yarinyar inka azabtar da ita meye ribarka ” kallon yaseer yayi yace” dama aina nace nakarbi amanarta? Laifi tamin shisa nake hukuntata tana gama karban punishment dinta kuma zan saketa ” girgiza kai yaseer yayi yace” karkayi haka azaad wallahi fanan ba kamar sauran mata bace ! Koma me take maka kamata yayi kayi hakuri ko kamanta lokaci kadan yarage mata dazatama barmana duniyarmu takoma inda ake bukatarta haba dude kaji tausayinta mana zata tafi tabar kowa nata amma dukda haka kana wulakanta ta wallahi insu ummi sukaji bazasuji dadi ba” daga kafada sama yayi alamar I don’t care kafin yace” tafiyanta dakuma rashin tafiyanta nifa duk bedameni ba tatafi har yaumu takumu karta dawo dan nima ba kaunar ganinta nakeyi ba cos she’s like a burden to me! Abinda nasani shine intamin laifi zan hukuntata ” yaseer gani yayi inya biyewa azaad yanzu zasu iyayin fada yasa yatashi yatafi abinshi.

Yau Kwanan su Abba 5 da tafiya kullum insuka cewa Mr azaad yabawa fanan waya sugaisa ceyata basu uzuri, ummi de tanaji ajikinta kamar akwai abinda yake faruwa gashi wayarta yana hannunshi.

” Mr azaad dan Allah kabarni yau inje gidanmu ko kuma kayi hakuri kakiramin mama awaya ” idonshi alumshe kamar bayajinta tunani tafarayi kode bacci yakeyi sake nanatawa tayi nanma yayi banza da ita haka taci gaba da mishi magana harta gaji be kulataba yasa takoma bedroom dinta takwanta tana kukan halin data shiga , daga hannunta sama tayi tana adduah ” yah Allah ina rokonka kakawo karshen zamana da wannan bawan naka dayake kuntatawa rayuwata ! Allah kabashi ikon rubutamin takardar saki yau zuwa gobe ” haka tadinga adduah tana kuka……

 

Tom se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy

Masu comment damin adduah nagode sosai Allah yasaka da alkhari, kukuma da sede ku karanta kuyi shuru ba sannu bare Allah ya isa kallonku kawai nakeyi kowa yayi dede yasani .

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & Written by
MRS ISHAM

 

Back to top button