Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 56

Sponsored Links

PAGE* 5⃣6⃣

Cikin zafin nama yarima yatura k’ofan, abinda yaganine yafirgitasa a kid’ime yafara furta innalillahi wa’inna ilaihiraji’un.

Sumayya da zinat da suke manne da juna basu ma san shigowarsaba dan gabad’aya basu cikin hayyacinsu saida sukaji yana salati sannan sukayi saurin rabuwa da Juna, cikin sauri zinat tajanyo bedsheet tarufe jikinta.

Sumayya wata irin razanannar k’ara tasaki tare da furta na shiga ukku na bani na lalace dan Allah yarima kayi hak’uri ba laifina bane sharrin shaid’anne.

Yarima da yake tsaye jikin k’ofa ya runtse idonsa innalillahi kawai yake nanatawa dan samun sauk’in abinda yakeji a ransa inba hakaba ya san zai iya abinda za’azo ana da na sani.

Cikin sauri zinat tajanyo zanenta tad’aura tana zare ido saboda a tsorace take, Sumayya ko bedsheet d’in tayaye tarufe jikinta da shi har a lokacin kuka take tana jin abun kamar a mafarki.

Ahankali yarima yabud’e idanuwansa da suka koma launin ja saboda tsananin 6acin rai, murmushin takaici yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace Sumayya ban ta6a sanin ke dabba bace sai a yau, ke ko dabba ma ta fiki k’wak’walwa mai kyau, ace a matsayinki na mace kina aiwatar da wannan mummunan halayyar, wlh a yau na tsaneki Sumayya bana fatan k’ara sakaki a idona, na yi da nasanin amincewa da nayi na aureki.

kallon zinat yayi yace kekuma har da tako min gida kika daki matata sannan kuka aikata masha’a a cikin gidana!

Sumayya cikin kuka tace dan Allah yarima kayi hak’uri wlh nabi ka nai maka alk’awali bazan k’araba dan Allah kar katona min asiri.

Zinay had’e hannuwanta tayi waje guda tana kuka tace dan Allah ranka yadad’e kayi hak’uri wlh tsautsayine yakawoni.

Yarima maida d’akin yayi yarufe sannan yace da fari zan fara rama ma matata dukan da kukayi mata,,,wucewa yayi yajanyo adaptor irin mai kaurin nan yatsige kan yad’auki wire d’in, wajen da suke yanufa daga bakin gadon yatsaya yafara shaud’a musu, ihu suke suna kuka nan tacigaba da had’awa da mari daga k’arshe k’asa yajanyosu yacigaba da duka da harbi da k’afa, ihu suke suna kuka ammah yarima bai k’yalesuba saida yaga ya had’a musu jini da majina basu iya kotsin kirki sannan yabarsu,

Jikinsu duk sahun bulala ya kwanta duk saida sukayi da sun sani akan ta6a zarah da sukayi.

Yarima kallon Sumayya yayi da take kuka yace wannan ramama matata nayi, sannan kuma ada nazo da niyar inyi miki saki d’aya ammah ganin abinda kike aikatawa ya sa zan miki….cikin sauri Sumayya tace dan Allah yarima kar kasakeni please kacigaba da dukana kar kafurta kalmar.

Wani irin kallo yarima yai mata mai tattare da tsana sannan yace kije na sakeki saki ukku dan bana buk’atarki a cikin rayuwata.

Wata razanannar k’ara Sumayya tasaki tare da rarrafowa ta iso inda yarima yake cikin kuka tace dan Allah kabarmin saki d’ayan wlh shi kad’ai ma ya isheni please ka janye biyun tafad’i haka tare da ruk’o rigarsa.

Yarima fizge rigarsa yayi yace kar kik’ara ta6ani da wannan hannun naki mai najasa, wucewa yayi yabud’e bedside d’inta yad’auko paper da biro nan yarubuta mata saki ukku ya cilla mata sannan yace na baki nan da awa d’aya kitattara komatsenki kifita kibarmin gida inko ba hakaba zan sa6a miki.

Sumayya dafe kanta tayi tare da k’ara sautin kukanta tace na bani na lalace yau ni ya zanyi da rayuwata,,,,kallon zinat tayi da take raku6e waje guda fuskarta duk ta kumbura tace shikenan zinat kinja min yau nima aurena ya mutu yau ni nashiga ukku ina zansa rayuwata.

Yarima a fusace yace na dai fad’a miki kar kibari indawo in tarar da ke,,, yana fad’in haka yajuya yabud’e d’akin yafita.

Sumayya tana ta k’wala mai kira yai mata banza, nan tacigaba da kukanta.

Zinat na ganin ya fita ta rarrafa tajanyo rigarta da veil d’inta tasaka, dakyar tamik’e tsaye, sumayya ganin zata fita yasa cikin kuka tace zinat ina kuma zaki tafi kibarni kina ganin matsalar da kika jefani.

Zinat jakkarta tad’auka batare da ta kalli sumayya ba tace tafiya zanyi tun kan yarima yadawo ya6allani koma me kenan nidai sai munyi waya dan haka kinga ma tafiyata kisan yadda zakiyi kikare kanki,,,zinat na gama fad’in haka tabud’e k’ofan taficce cikin sauri, gudu-gudu haka tasamu tafita daga masarautar bata tsaya jiran abun hawaba tacigaba da sauri sai da tayi nisa sannan tasamu tahau abuabun hawa.

Sumayya na ganin zinat ta fita nan ma k’ara fashewa da sabon kuka tayi tace na bani ni yanzu ya zanyi da kaina wai nice yarima yasaka wlh ba zan yardaba sai anmaida aurenmu,,,,rarrafawa tayi tajanyo wayarta tana kuka tai dialing d’in number d’in ummanta.

Ummah tana yin picking taji kukan sumayya yana tashi, ahankali tace ya salam sumayya me kuma kike ma kuka kedai inba kukaba ba abinda kika iya.

Cikin kuka sumayya tace ummah ya sakeni.

Ummah da take kishingid’e zumbur tamik’e tsaye tace me kikace sumayya saki?

Eh ummah.
Innalillahi wa’innah ilaihiraji’un garin ya haka yakasance sumayya? Nashiga ukku ni halima, dan ubanki kifad’amin me kikayi yasakeki.

Sumayya cikin sheshek’ar kuka tace ummah daga na daki matarsa shine yasakeni.
Dan Allah asashi yamaida ni

Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kin tabbata abinda kika fad’amin gaskiya ne?
Eh ummah.
Toh shikenan yanzu yi maza kije wajen su dada kisanar da su, nima ganinan zuwa ai dole kikoma d’akinki.
Sumayya cikin kuka tace Toh ummah,,,nan takashe wayar tare da mik’ewa tajanyo kayanta tasaka.

A firgice tafito cikin sauri tanufi turakar su memartaba, tana shiga parlour dada ce kawai nan sumayya taduk’e k’asa tare da fashewa da sabon kuka.

Dada rud’ewa tayi tace lafiya sumayya me yake faruwane? Bakida lafiya ne?

Sumayya girgiza mata kai tayi tace kod’aya dada, yarima ne yasakeki.

Dada dafe k’irji tayi tace Innalillahi wa’innah ilaihiraji’un, saki fa kikace?

Memartaba da yake ciki yana shirin fita jin hayaniya yasa yafito yana cewa hayaniyar me nakeji haka?

Sumayya duk’awa tayi tagaishesa cikin girmamawa,
Saida memartaba yazauna sannan ya amsa mata tare da cewa lafiya sumayya kike kuka?

Dada girgiza kai tashiga yi tace ranka yadad’e wlh yarima baya da mutunci yanzu saboda Allah ace ya saki ‘yar uwarsa?

Memartaba cikin d’aga murya yace saki kuma? Anya kuwa sakinta yayi dan bana tunanin yarima zai zartas da wannan hukuncin batare da na saniba.

Dada tallabe ha6a tayi tace wlh indai yarima ne zai aika.

Memartaba kallon sumayya yayi yace ke kallanni nan fad’amin me kikayi masa yasakeki?

Sumayya rage sautin kukanta tayi sannan tace banyi masa komai ba daga matarsa ta ja ni fad’a har da cemin juya marar haihuwa, shine nikuma nabiye mata nan mukayi fad’a shine yakamani yai min duka,tafad’i hakan tare da d’age hijab d’inta su memartaba salati suka shiga yi da suka ga kwanciyar bulala a jikinta.
Cikin sheshek’ar kuka tace bayan ya gama dukana shine yasakeni.

haushine yacika memartaba yace banyi tunanin hakan daga wajen yarima ba banta6a tunanin zai iya min cin mutunci irin hakaba ammah bari inkira iyayenku suzo asan yadda za’a 6ullo ma lamarin.

Memartaba wayarsa yad’auka yakira mahaifin yarima da na sumayya yace duk suzo da iyalansu susamesa.

Bayan kamar minti goma sai gasu su duka sunzo harda Aunty husna da rahma da suke gidan basu koma gidajensuba,

Lokacin su memartaba suna zaune suna tattauna al’amarin gabad’ayansu suka duk’a suka gaishesu, kowa da mamaki yake kallon sumayya.

Bayan su memartaba sun amsa gaisuwa, gyaran murya yayi yace wani ya aika akira min yarima dan na kira wayansa a kashe.

Abban sumayya ne yace toh ranka yadad’e nan yamik’e yaje ya aiki wani dogari yace yaje yakirasa.

 

Yarima bayan ya baro part d’in sumayya nan yakoma 6angaren zarah yanayinsa kawai zaka kallah kasan ba k’aramin tashin hankali yake cikinsaba, kallon zarah yayi da take kwance ta zuba ma waje d’aya ido tana kallo, daga gefen gadon yazauna tare da dafe kansa yana tunanin lamarin sumayya dan gabad’aya ta gama ficce masa a rai, wayoyinsa yakashe gabad’aya dan ya san dole sai memartaba ya nemesa dan dama gudun kar amaido masa aurenta yasa yaimata saki ukkun.

Zarah ruk’o hannunsa tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace tunanin me kakeyi?

Kallonta yarima yayi cike da tausayi yace in kaiki asibiti adubaki ko?

Girgiza kai zarah tayi tace babynka lafiyarsa lau dan basu samu sun ta6asa ba nikuma ciwon jikine kuma nasan zan warke insha Allahu.

Yarima d’aura hannunsa yayi saman fuskarta sannan yace ammah kina buk’atar asa miki drip kuma jikinki akwai zazza6i.

Zarah maida idonta tayi talumshe, yarima zuba mata ido yayi yana kallonta.

Knocking d’in k’ofan da akayine yasa yamik’e yaje yabud’e kuyangar zarah ce cikin sauri taduk’a tagaishesa, yarima batare da ya amsa mataba yace ya dai.

Jikinta yana rawa tace ranka yadad’e daman dogari ne aka aiko daga turakar sarki yace yana son ganinka.

Yarima baiyi mamakin hakaba, dawowa yayi yakalli zarah da take kwance ta ji duk maganarsu, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace bari indawo sai muje hospital.

‘Daga mai kai kawai zarah tayi, nan yarima yajuya yafita yanufi turakar memartaba.

Lokacin da ya isa baiyi mamakin ganin family d’insa da suka hallaraba, bayan ya yi sallama, waje yasamu k’asa chan gefen Aunty husna yazauna, cikin rashin damuwa yagaishe da su memartaba.

Ciki-ciki memartaba ya amsa masa nan d’akin yad’au shuru kowa saurare yake yaji memartaba ya fara magana.

Gyaran murya memartaba yayi sannan yakalli yarima da kansa yake sunkuye k’asa yace wannan taron ba dan kowa nayisaba sai dan kai yarima.
suhail ka bani kunya ban ta6a tunanin hakan daga garekaba koma menene ai ana son sasacin a cikin aure, wace irin zuciyace ta d’ibeka har kasaki matarka.

Gabad’aya ‘yan d’akin sukace saki!! Nan aka fara kallon kallo.

Memartaba nuna sumayya yayi da take kuka har Lokacin Sannan yace toh gatanan dai ya saketa, ke kifad’a musu dalilin sakin suma suji.

Sumayya saida takalli yarima da kansa yake sunkuye sannan tamaimaita abinda tafad’a ma su memartaba.

Da mamaki yarima yad’ago yakalleta jin k’aryar da tadage tana shararawa, wata uwar harara yawurga mata nan Sumayya tafara dabarbarcewa.

Yana hararanta karaf a idon dada cikin fushi tace kikwantar da hankalinki kiyi bayaninki dan babu abinda ya isa yayi miki tunda kina a gabanku,
Nan Sumayya tacigaba da bayani.

Bayan ta gama d’akin yad’au shuru kowa yana jimami a cikin ransa, dadyn yarima ko kunyace takamasa ganin abinda d’ansa ya aikata ma d’iyar d’an uwansa, ummi ma jin abun take wani iri dan bata ta6a tunanin hakan daga garesaba.

Gyaran murya memartaba yayi yace kunji jawabinta, kunga abin kunyar da yarima ya aikata kan bare yarabu da ‘yar uwarsa, toh yanzu ba sai anja maganar da nisaba na umurceka kamayar da ita d’akinta.

Sai a Lokacin yarima yad’ago yakalli memartaba cike da girmamawa yace ranka yadad’e kagafarceni, bata fad’a muku saki nawa nayi mataba? Ko daman idan anyi saki ukku ana komawa.

Nan d’akin yarikice da salati memartaba yace da hankalinka zakayi ma matarka saki ukku yarima? Sakin da ubangiji bayaso ana yi, ina iliminka da tuninka suke.

Yarima har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Memartaba yace inji a lokaci guda kayi sakin?

Sumayya tayi karaf tace eh ranka yadad’e gabad’aya yayimin.

Toh Alhmdllh tunda gabad’ayane kuma cikin fushine zamu iya d’aukansa a matsayin saki d’aya kaga sai kamaidata d’akinta yanzu….cewar memartaba

Yarima k’ara duk’ar da kansa yayi sannan yace kagafarceni ranka yadad’e na riga da na haramta ma kaina k’ara auren Sumayya,

A firgice kowa na d’akin yakalli yarima, nan Sumayya tafashe da kuka tace na shiga ukku dan Allah kutaimaka min yamaidani d’akina.

Memartaba kallon yarima yayi yana jinjina kai dan ya ma rasa abinda zai ce masa,

Dada ce tashare kwallar da tazubo mata saboda tausayin Sumayya sannan tace ranka yadad’e ka gani ko? Lokacin da nake fad’a maka wulak’ancin da yarima yake ma Sumayya ba ka yarda, duk wulak’anci da cin mutuncin da matarsa takeyi mata bai ta6a tankawaba sai ita da suka d’an samu sa6ani shine yadank’ara mata har saki ukku.

Ummi kallon yarima tayi kallon mamaki, yarima cike da jin kunyar ummi yaduk’ar da kansa k’asa.

abban Sumayya ne yai k’arfin halin cewa kuyi hak’uri yanzu haka wani haukan ne Sumayya tayi masa kuma ba a ji daga garesaba.

Memartaba murmushin takaici yayi sannan yace bana buk’atar jin komai daga garesa, nagode sosai suhail ni kawulak’anta tunda ni na aura maka Sumayya yanzu ka maido min abuna ka ce ban isa inyi maka abinda bakasoba,
Saboda ganin kamar ban kyauta makaba yasa nabarka kaje ka auro za6inka bayan shekara d’aya da aurenku da Sumayya, duk labarin da ake bani akan abinda kake ma Sumayya ban ta6a yardaba sai gashi yau na gane ma idona abinda zai d’aga min hankali abinda d’ana nacikina bai aikataba sai gashi jikana namiji tilo d’aya ya aikata ma ‘yar uwarsa.

Yarima d’ago kai yayi yakalli memartaba yace kagafarceni ranka yadad’e nima ba a son raina na aikata hakanba, wlh Sumayya ba gaskiya tafad’a mukuba.

Memartaba d’aga masa hannu yayi yace dakata bana buk’atar jin komai daga wajenka abinda idona yagane min ya isheni.

Daddyn yarima kallon yarima yayi cike da takaici yace suhail ka ban kunya kana gani yadda nake zaune da d’an uwana lafiya ammah karintse ido kakarta min rashin mutunci har haka, yanzu da wane ido kakeso ink’ara kallonsa.

Girgiza kai yarima yashiga yayi yace kayi hak’uri daddy wlh nima ba a son raina hakan takasanceba.

Memartaba a hankali yafurta innalillahi wa’innah ilaihiraji’un, kallon kowa yayi d’aya bayan d’aya sannan yamaida kallonsa ga dada yace kin gani ko? Ni yanzu banma san wane hukunci zan yanke masaba ko zan samu d’an sauk’i a raina.

Dada kallon yarima tayi sannan tace ma memartaba ranka yadad’e kaga ita tagaban goshin tasa tana chan tana hutawa babu abinda yadameta bata ma san wainar da ake toyawaba ita ga ‘yar gaban goshi me ciki.

Jinjina kai memartaba yayi sannan yace nasan abinda zanyi, kallon Rahma yayi da take kuka yace ke jeki kisamo min takarda da biro, mik’ewa Rahma tayi tafita.

Nan kowa yayi jugum yana jira yaji hukuncin da memartaba zai yanke.

Bayan kamar minti biyar sai ga Rahma ta dawo rik’e da takarda da biro, tsugunnawa tayi gaban memartaba tamik’a mai,

Kar6a memartaba yayi yace yauwa, sannan yakalli yarima da yake zaune har Lokacin bai d’ago kansa mik’a masa memartaba yayi yace kar6a.

‘Dago kai yarima yayi yakalli takardar sannan yamaida kallonsa ga me martaba, a karo na biyu memartaba yace kar6a mana.

Hannu yarima yamik’a yakar6a tare da tsare memartaba da ido yana jira yaji abinda zai ce.

Shima memartaba kallonsa yake sannan yace inaso karubuta ma wacchan matar taka itama saki ukku.

Gabad’aya d’akin d’agowa akayi aka kalli memartaba cike da mamakin kalmar sakin da ya ambata.

yarima ko gabansane yayi wani irin fad’uwa saida biron takubce daga hannunsa, tashin hankaline k’arara yabayya a fuskarsa.

har a lokacin memartaba kallonsa yake fuskarsa ba alamun wasa yace indai kana son cigaba da zama a gidannan toh dole kasaketa saboda hakan shi zaifi dacewa karabu da kowace d’aya daga cikinsu.

Dada gyad’a kai tayi tace tabbas ranka yadad’e ka kawo shawara mai kyau inma cikin da yake jikintane yake ma rawar kai toh taje gidansu da abinda tacigaba da raino zamu dinga aika mata da duk abinda take buk’ata har sai ta haihu, intaso tashayar da abunta inkuma batasoba tabamu abunmu a haka zamu sami wacce zata kular mana da shi.

Ummi ita kanta saida gabanta yafad’i dan ita jin abun take kamar a mafarki tabbas ta san d’anta akwai dalilin da yasa ya saki sumayya saidai miskilanci da zurfin jikinsa bazasu ta6a barinsa yafad’aba.

 

Abban sumauya ne yaduk’ar da kansa yace ranka yadad’e ataimaka a sassauta ma yarima wannan hukuncin yai masa tsauri.

Sultana sadiya da take gefe takaici duk ya cikata tana ji kamar tashak’e yarima yamace kowa yahuta, jin maganar da mijinta yayi yasa tawurga masa harara, sai a lokacin tace ranka yadad’e tabbas wannan hukuncin da kayanke shine daidai dan yarima ya tozarta min d’iya,,,, d’aga mata hannu sultan abbas yayi yace ke banason hauka na san duk abinda yaima sumayya toh tana da laifi a ciki dan na san sumayya bata ji.

Sultan Ahmad ne yai k’arfin hali yace ma sultan Abbas kadaina cewa haka domin yarima bai kyautaba.

 

Memartaba gyaran murya yayi nan kowa yanutsu, sannan yace duk naji k’orafinku saidai inaso kusani babu wanda ya isa yasa incanza maganata dan ku kanku kunsani ni kaifi d’ayane bana magana biyu.

Duk’ar da kansu sukayi sukace Allah yaja da ran sarki me adalci.

Memartaba kallon yarima yayi da duk sanyin A-C d’in da take d’akin ammah bai hana yayi zufaba, murmushi Memartaba yayi sannan yace suhail ina saurarenka dan kaji abinda nafad’a.

Aunty husna ce tad’auki biro d’in da tafad’i tamik’a mashi.

Cikin sanyin jiki yarima yak’arfi biro d’in yad’aura saman paper, nan kowa yazuba mai ido ana jira yarubuta.

Ido yazuba ma paper tare da d’aura biro d’in kamar zaiyi rubutu nan gabansa yashiga dukan ukku-ukku jinsa yake wani iri gabad’aya komai ya kwance masa, yarasa cikin biyu wane zaiyi shin sakin zarah zaiyi ko kuma ya amince yarabu da family d’insa, runtse idanunsa yayi yana jin wani irin k’unci a ransa……..

 

 

_Shin yarima zai amince yasaki zarah?_

_Ko zai amince yarabu da family d’insa kamar yarda memartaba yafurta?_

 

_*Muje Zuwa dan jin yadda zai kasance*_

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*Nagode Sosai da kulawarku agareni masoya, gaskiya naji dad’i dan naga k’auna zallah daga gareku, banda abinda zanyi inbiyaku saidai ince Allah yabar k’auna da dank’on zumunci*_

 

Back to top button