Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 58

Sponsored Links

PAGE* 5⃣8⃣

Koda yayi parking kallon yarima yayi yace ranka yadad’e mun fa iso.

‘Daga kai kawai yarima yayi, nan Dr khalil yakalli zarah ta mirror yace gimbiya bismillah mun iso, murmushi zarah tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace toh.

Gabad’ayansu suka bud’e motar suka fito, yarima kallon zarah yayi da take taku dak’yar yace ko intaimaka miki?

Zarah batare da ta kallesaba tagirgiza kai, nan Dr mu’az da yarima sukayi gaba tana bayansu har suka shiga a main parlour suka tarar da matar gidan zaune ganinsu yasa tamik’e fuskarta d’auke da fara’a tace oyoyo ga manyan bak’i,
Dr mu’az ne yayi murmushi yace dear yau fa ga prince a gidan namu,
Murnushin jin dad’i tayi tace yau muntaki sa’a gaskiya,

Saman kujerun da suke d’akin suka zauna nan matar dr mu’az tad’an russuna cikin girmamawa tagaishe da yarima.

Murmushi yarima yayi sannan ya amsa mata,
Wajen zarah tanufa tana murmushi tace gimbiya sannu da zuwa ina wuni?

Murmushi itama zarah tayi sannan tace ina wuni.

Bayan sun gama gaisawa, Dr mu’az yace ranka yadad’e ga d’an akurkin gidan namu ina fata zaku iya rayuwa a cikinsa.

Harararsa yarima yayi yace kai fa tsiyata da kai ka iya tsokana.

Dariya Dr mu’az yayi yace ai gaskiya ce nafad’a,
Kallon matarsa yayi yace jamila gashinan prince yau wani irin farin ciki nakeji da naganni tare da shi, abokina ne tun daga primary har secondary tun lokacin banda komai muke tare da shi, shine silar yin karatuna dan a lokacin iyayena basuda komai mu talakkawane sosai da taimakonsa nayi karatu har nakai wannan matsayin da nake da shi kinga ko taya zan iya mance prince?

Jinjina kai matarsa tayi tace tabbas hakane bazaka ta6a mancewa da halacci da yayi makaba, saisa a kullum yana cikin addu’anmu.

Kallonta yarima yayi yace madam kema kin biye ma wannan mijin naki sarkin tsokana.

Murmushi Dr mu’az yayi yace prince kenan kaima kasan gaskiya nafad’a saidai idan kanason 6oyetane.

Shuru yarima yayi baice komai ba.

Zarah dai tana zaune tana saurarensu ita dai burinta takwanta tahuta.

Matar mu’az mik’ewa tayi tace bari akawo muku ruwa kusha kafin agama abinci.

Bayan ta fita Dr mu’az kallon yarima yayi yace ranka yadad’e muje kuza6i part d’in da yayi muku a cikin gidan nan.

Girgiza kai yarima yayi yace no ba sai mun za6aba duk wanda aka bamu munaso yanzu magrib ta gabato muna buk’atar kimtsawa ga madam babu lafiya ina so asamo min drip zansa mata,,,yak’arashe maganar tare da kallon zarah.

Dr mu’az yace ayya Allah yasauk’e bari inje insa asamo daga nan ashigo muku da kayanku, yana fad’in haka yamik’e yafita yabar d’akin.

Yarima kallon zarah yayi da ta jingine kanta a kujerar da take yana shirin yin magana sai ga Matar mu’az ta shigo dan haka yafasa.

A gabansu ta aje k’aton tray d’in da yake d’auke da kayan marmari nan tatsiyaya musu drinks a cups ta aje ma kowa gabansa sannan tace kuyi hak’uri abincin ya kusan zama ready.

Murmushin k’arfin hali zarah tayi tace bakomai Aunty hakan ma mun gode, nan tad’auki cup d’in tafara shan drink d’in.

Nan Dr mu’az yashigo bayansa megadine janye da trollies d’in su yarima d’aya daga cikin rooms d’inne Dr mu’az yasa aka shigar da kayan sannan yakalli yarima yace ranka yadad’e kuduba kuga idan part d’in baiyi mukuba sai a canza.

Murmushi yarima yayi yace kar kadamu yayi mana, kallon zarah yayi yace muje kisamu kihuta.

Jamila cike da tausayi takalli zarah tace sannu gimbiya, Allah yabaki lfy.

Cikin Jin kunya zarah tace Ameen Aunty nagode, nan tamik’e tabi bayan yarima.

Wani makeken d’akine mai d’auke da room nd bedroom ya tsaru sosai komai na cikinsa mai kyau da tsada ne, angyara ko’ina fes, suna shiga bedroom zarah saman gadon tafad’a takwanta agajiye, kallonta yarima yayi sannan yawuce yashige bathroom dan yawatsa ruwa.

Bayan ya fito kallon zarah yayi da take kwance yace kitashi kije kiwatsa ruwan ko kinji k’arfin jikinki.

Zarah kallonsa tayi ganinsa d’aure da towel yasa tad’auke kanta, batare da ta k’ara kallonsaba tamik’e tanufi wajen kayansu wardrobe d’in tabud’e saida tagogeta sannan tabud’e trollies d’insu duk tajere musu kayansu, Bayan ta gama ta gefen yarima taratsa taje tashige bathroom, cikin sauri yarima yad’auko kayansa yasaka sannan yatayar da sallar magrib a gida, dan a lokacin ana gab da sallame sallah a masallaci.

Yana saman darduma zarah tafito d’aure da towel tawuce wajen wardrobe d’in tad’auko gown tasaka sannan tayi sallah.

Koda yarima yagama saman gado yakoma yazauna nan yajanyo wayoyinsa yacire dukkan sim d’insa yakashe wayar ya aje.

Dafe kansa yayi yana jin wani iri a ransa dan baisan halin da umminsa zata shigaba dan gabad’aya itace damuwarsa, abubuwan da suka faru nan suka fara dawo masa a rai.

Zarah da take tsaye tana kallonsa wani irin tausayin mijin nata takeji, ita kanta zuciyanta zafi take musamman ma da tasan ta dalilinta yarima yafad’a wannan matsalar, hawayene suka fara fita daga idanunta, ahankali tataka ta isa inda yake daga gefensa tazauna,
‘Dago kai yarima yayi yakalleta ganin tana hawaye yasa yace zarah meyake samunki ko jikin ne?
Girgiza kai tayi tace banso karabu da kowa nakaba saboda ni, da ace ni karabu da ni inyaso koda bayan na haihu ne sai ka amshi babynka.

wani irin abu yaji ya tokare masa zuciya akan maganar da tayi, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace zarah ba zan miki doleba indai kinsan bazaki iya zama da ni ba toh kifad’amin insha Allahu zan baki takardarki dan zan iya rayuwa ni kad’ai koda ace banda kowa,

Jikinsa tafad’a tare da fashewa da kuka tace kayi hak’uri ni ba haka nake nufiba wlh zan iya zama da kai a kowane hali.

Wani irin sanyi yaji a ransa,
Knocking d’in da akayine yasa yajanyeta daga jikinsa tare da mik’ewa yawuce yaje yabud’e.

Dr mu’az ne yana murmushi yace ranka yadad’e ga fa dinner chan a dining yana jiranku inkuma nan za’a kawo muku toh.

Yarima murmushi yayi yace ohk, gamunan zuwa nan yamik’a mai ledar hannunsa yace ga sak’on ansamo.

Kar6a yarima yayi yace nagode.

Koda yajuyo kallon zarah yayi da take kuka, itama d’ago kai tayi takalleshi, ahankali yace kukan fa?

Zarah turo baki tayi tace bakai bane kake fushi da ni.

Yarima wucewa yayi ya aje ledar saman bedside batare da ya kalletaba yace tashi muje kiyi dinner inyaso sai insanya miki drip d’in daga baya.

girgiza kai zarah tayi tace ni na k’oshi.

Kallonta Yarima yayi yace me kikaci da kika k’oshi?
Shuru tayi batace komai ba dan haka yarima yace oya tashi muje.

Mik’ewa zarah tayi taje tad’auko hijab d’inta tasaka sannan tabi bayan yarima suka fito.

A main parlour suka tarar da su zaune suna jiransu ganinsu yasa suka mik’e suka nufi dining.

Jamila ita tayi serving d’in kowa, zarah tunda tarik’e spoon d’in kallon plate d’in kawai take.

Yarima ahankali yad’ebo yaci idanunsa suna kan zarah, d’ago kan da zatayi ne suka had’a ido cikin sauri tad’ebo taci,

bawani dayawa yaciba nan yatsare zarah da ido har saida yaga ta d’an ci na kirki sannan yamik’e yakalli Dr mu’az da shima yake kallonsa yace Dr ba dai har ka k’oshiba.

Murmushi yarima yayi yace am ohk.

Jamila ce tace ranka yadad’e ko dai girkin ne baiyi makaba acanza maka wani?

No madam girkin ya yi min dad’i sosai kawai k’oshine nayi.

Zarah ma ganin zai bar wajen yasa tamik’e, kallonta jamila tayi tace gimbiya kodai kema abincin baiyi mikiba.

Girgiza kai tayi tace wlh Aunty jamila yai min dad’i sosai sai ma nazo kin koyamin.

Dariya jamila tayi tare da kallon mijinta tace sweet kana jin gimbiya tana tsokanata.

Dr mu’az murmushi yayi yace kibarsu na lura kamar abincin baiyi musu ba.

No kawai dai a gajiye muke muna buk’atar hutune….cewar yarima.

Ohk doctor ahuta lafiya, nan sukayi musu sallama suka koma masaukinsu, zarah wajen wardrobe tanufa dan tacire kayan jikinta dubawa tayi ammah ba sleeping dress ko kala d’aya, juyowa tayi takalli yarima kamar zatayi kuka tace baka sakomin kayan bacciba.

Kallonta yarima yayi batare da yayi magana ba, ganin haka yasa zarah tace ni kuma ban iya bacci da na jikina.

Toh ya kikeso inyi ina zan je yanzu insamo miki sleeping dress a yanzu, kibari zuwa gobe insha Allahu zan samo miki, yanzu kizo insa miki drip d’in.

Zarah turo baki tayi taje tahau gadon takwanta nan yarima yahad’a drip d’in yasa mata, bayan ya gama daga gefenta yayi zaune yazuba ma waje d’aya ido,

Zarah kallonsa take cike da tausayinsa dan ko ba a fad’aba yanayin yarima kawai zaka kallah kasan yana cikin damuwa kawai dai daurewa yakeyi baya nunawa.

maida idanuwanta tayi talumshe tana ji kamar tarungumo mijinta talallashesa ko ya rage damuwar da take tare da shi.

Wajen k’arfe tara yarima yatashi yaje yashiga wanka, lokacin da yafito daidai lokacin ruwan yak’are nan yacire mata sannan yawuce wajen wardrobe yafiddo kaya.

Zarah mik’ewa tayi itama tashiga toilet dan tawatsa ruwa.

Lokacin da tafito tsaye take d’aure da towel tana kallon yarima da yake zaune bakin gado ya dafe kansa, ahankali tataka ta isa inda yake, janye hannuwansa tayi da yadafe kan, nan yarima yad’ago yakalleta damuwa k’arara a fuskarsa.

Cike da rashin damuwa zarah tazauna saman cinyarsa nan idanunta suka cika da k’wallah ahankali tace meyasa kake shiga damuwa? Bakasan ganinka cikin irin wannan yanayin yana d’agamin hankali ba? Taya ni hankalina zai kwanta alhali kai gabad’aya naka hankalin a tashe yake, dan Allah kadaina shiga damuwa wlh ni ina tare da kai a kowane lokaci,,,,tak’arashe maganar tare da fashewa da kuka.

Yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri akan kukan da takeyi rungumeta yayi a k’irjinsa nan zarah ta narke mashi tacigaba da wani irin kuka
Cikin wata irin murya yace please zarah kukan ya isa haka.
Cigaba tayi da kukanta, nan yarima yacigaba da lallashinta ammah tak’i daina kukan, tallabo fuskarta yayi yana kallonta yace wai zarah ya kikeso inyi ne? Nima kinaso inyi kukan ne?

Cikin sauri zarah tagirgiza kai tare da rage sautin kukanta.
Da mamakinta sai gani tayi yarima ya sa harshenta yana lashe hawayen fuskarta, ai nan sai kukan yatsaya tacigaba da binsa da kallo, daga karshe yatura bakinsa cikin nata yana mata tsotsar lolli pop, kamar daman zarah jira take nan tabiye masa suka cigaba da kissing d’in juna, tana ji lokacin da yazare mata towel d’in da yake a jikinta nan yacigaba da yawo da hannuwansa a jikinta, zarah ma hannuwanta tad’aura tana shafar lallausan gashin da yake kwance a k’irjinsa cikin wani irin siga.

Sun dad’e a haka sannan daga k’arshe yarima yad’auketa suka haye gado nan zarah ta dage sosai wajen ganin mijinta ya samu nutsuwa duk yadda takejin batada lafiya ammah haka tadaure taba yarima kanta, shi kansa ahankali yadinga bi da ita saboda ya san batada lafiya kawai dan ba yarda zaiyi da sai yahak’ura yabarta.

Bayan komai ya lafa yarima rungumeta yayi a k’irjinsa yana shafar gashin kanta, zarah ko cikin jikinsa talafe idanuwanta a lumshe tana numfashi ahankali.

kallon agogo yayi ganin lokaci ya ja yasa nan yajanyeta daga jikinsa yamik’e.

Zarah batare da ta bud’e idanunta ba tayi saurin rik’o hannunsa, yarima juyowa yayi yakalleta yace ya dai?

Cikin shagwa6a zarah tace nima ina son wankan.

Batare da ya yi magana ba nan yaduk’a yad’auketa yanufi toilet da ita saida yatara ruwa sannan yasafketa ciki, zarah sai a lokacin tabud’e idanunta ganin baida niyar shigowa yasa tace please kashigo muyi wankan.

Shuru yarima yayi.
Ganin baida niyar yin magana yasa tajingine kanta tare da runtse idanunta, da mamakinta sai ji tayi ya shigo cikin ruwan bud’e idanunta tayi tare da komawa jikinsa.

Ganin batada niyar yin wankan yasa yarima yayi mata sannan shima yayi nasa, wankan tsarkine kawai tayi da kanta bayan sun gama shagwa6a tasa mashi kan dole yad’auketa suka baro toilet d’in.

A saman gadon yadireta nan shima yakwanta tare da jawo blanket yalullu6esu, zarah jikinsa takoma takwanta nan yarungumeta ahaka har tayi bacci ammah yarima bai samu yarintsaba sai wajen k’arfe ukkun dare.

Da asuba sun so sumakara sallah, dan saida gari yad’an fara haske sannan suka tashi.

Bayan sunyi sallah baccinsu suka koma, basu suka farka ba sai wajen 11am.

Yarima yafara shiga yai wanka lokacin da yafito zarah ta gyara ko’ina k’amshi kawai yake tashi.

Bayan ya fito itama taje tashiga lokacin da tafito yarima har ya gama shirinsa cikin dakakkiyar shaddarsa ya yi gwanin kyau, gaban dreesing mirror zarah tatsaya nan tafara shafa lotion, tana ganin yarima ta cikin mirror d’in yadda yatsareta da ido, karaf suka had’a ido.
‘Daga masa gira zarah tayi alamun ya dai?
Janye idanunsa yayi daga kallonta.
zarah tana cikin shafa takallesa kamar zatayi kuka tace wayana fa tana chan na baro ban zo da itaba.

Shuru yarima yai mata, ganin haka yasa tacigaba da shirinta nan tawuce tabud’e wardrobe tad’auko atamfa d’inkin riga da skirt nan tasaka sannan taje gaban mirror tamurza d’aurin kallabinta tare da feshe jikinta da turaruka, juyowar da zatayi nan suka had’a ido da yarima murmushi tasakar mashi tace nayi kyau?

Janye idanunsa yayi daga kallonta sannan yace ba laifi.

Matsowa zarah tayi kusa da shi kamar zatayi kuka tace kana nufin dai banyi kyau ba toh bari inje incanza kayan,,,juyawa tayi kamar da gaske.

Ruk’o hannunta yarima yayi baisan lokacin da yace kinyi kyau ba.

Juyowa zarah tayi tana murmushi tace kaima kayi kyau sosai k’albina.

Kallonta yarima yayi yanaso yagaskaka kalmar da tafito daga bakinta.

Kashe masa ido tayi tare da janyo hannunsa tad’aura saman cikinta tace babynka fa yunwa yakeji.

Janye hannunsa yayi daga cikinta yace muje kiyi breakfast.

Zarah tana rik’e da hannunsa suka tafo har zasu fita nan yarima yatsaya, kallonsa zarah tayi tace ya dai naga ka tsaya?

Shima kallonta yayi sannan yace haka zaki fita ba mayafi.

Oh sorry dear wlh mancewa nayi, nan tawuce taje tabud’e wardrobe tad’auko veil d’inta tayafa sannan tazo suka fita a jere.

Zaune suka tarar da mu’az da matarsa a main parlour suna hira, ganin su yarima yasa suka fad’ad’a fara’arsu mu’az ne yace sannunku da fitowa, hannu yarima yamik’a mashi sukayi masabaha sannan suka samu waje suka zauna

Jamila ce cikin girmamawa tagaishe da yarima nan ya amsa mata.

Zarah ma saida ta gaishe da mu’az sannan tagaishe da jamila.

yarimane yace ashe baka fita aikiba?

Taya zan fita bayan ina da manyan bak’i, ai yau ina tare da kai kwana zamuyi muna hira jiya ma dan naga agajiye kuke saisa nabarku,

Murmushi kawai yarima yayi batare da ya yi magana ba.

Jamila ce tamik’e tace muje kuyi breakfast gashichan tun d’azun yake jiranku.

Gabad’ayansu suka mik’e suka nufi dining nan jamila tayi serving d’in mijinta.
inda zarah itama tayi serving d’in yarima, ruwan lipton kawai zarah tazuba ma kanta tafara sha.

Kallonta jamila tayi tace gimbiya menene wannan zakisha?

Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido sannan tamaida kallonta ga jamila saida tasakar mata murmushi sannan tace Aunty jamila banaso da madara nafi jin dad’insa a haka.

Ayyah Allah sarki ammah ai hakan baya maganin yunwa.

Murmushi Zarah tayi tace kar kidamu lafiya lou nake jina idan nasha.

Haka suka cigaba da breakfast d’in duk d’agowar da zatayi sai sun had’a ido da yarima,
Ganin batada niyar cin chips d’in yasa yarima yace ya za’ayi ruwan lipton kad’ai yarik’eki kici chips d’in mana.

Zarah yamutsa fuska tayi tace na k’oshi.

Mu’az ne yace toh in batasonsa dear ko kije kigirka mata wani abun taci.

murmushi Zarah tayi tace a’a abarsa kawai nafi jin dad’in hakan kawai.

Nan kowa yacigaba da breakfast d’insa, bayan sun gama Zarah taimaka ma jamila tayi suka kwashe kwanukan suka kai kitchen sannan suka dawo nan suka tarar da su yarima a parlour suna ta hira koda rabin hiran duk mu’az ne yakeyinta dan yarima daga uhm sai uhm-uhm sai in tabada amsace shine zaiyi magana, ganin haka yasa jamila taja Zarah sukaje parlournta suka zauna suna hira.

Zarah kallon wani pic d’in wata yarinya tayi da yake manne a bangon d’akin tace Aunty jamila wannan fa babynki ce?

Jamila kallon pic d’in da Zarah take kallo tayi sannan tace eh itace d’iyan da nahaifa tana da 2yrs tarasu tun daga kanta har yau ban k’ara ko 6atan wataba.

Cike da tausayi Zarah take kallonta tace Allah sarki, Allah yakawo masu albarka.

Cikin jin dad’i jamila tace Ameen gimbiya nagode sosai.

nan sukayi shuru nad’an lokaci sannan jamila takalli Zarah cike da sha’awa tace Allah yasafke mana ke lafiya musha suna.

Cikin jin kunya zarah tace lah Aunty jamila banda fa komai

Dariya jamila tayi tace gimbiya kenan ai saidai kifad’a ma wani ba dai ni ba dan daga ganin yanayinki ya nuna cikine da ke gaskiya kinyi sa’a da kika samu yarima a matsayin mijinki dan ina jin labarinsa sosai wajen mijina yarima mutumin kirkine.

Murmushi Zarah tayi sannan tace Aunty jamila kema ai kuna da kirki sosai.

jamila tana shirin yin magana sai ga Dr mu’az ya shigo kallonsu yayi yace a’ah kuna nan kuna ta hira.

Kallon juna sukayi sukai murmushi sai jamila tace eh mun baku wajene kud’an labarta, muma sai mukazo nan muyi namu dan kar mu matsa muku.

Dariya mu’az yayi yace eh kun kyauta gaskiya, yanzu ma fita zamuyi saisa nalek’o, kallon zarah yayi yace gimbiya kije prince yana son ganinko.

Ahankali tace toh sannan tamik’e tafita takoma masaukinsu, a bedroom tasami yarima zaune yana jiranta.

Daga gefensa taje tazauna, kallonta yarima yayi yace bakyajin magana ko? Na yi miki magana akan zama da yunwa ammah kink’i dainawa.

Zarah saman kafad’ansa tad’aura kanta cikin siririyar muryarta tace kayi hak’uri wlh idan naci amai zanyi.
Cike da tausayinta yace ammah ai sai kija su mama sud’auka bana kula da ke.
d’ago kanta tayi takalleshi sannan tace babu wanda zai ce baka kula da ni saidai wanda baisan wanene yarima ba,,,tak’arashe maganar tare da kashe mai ido d’aya.
Yarima jan hancinta yayi yace bakijin magana ko?
K’irjinshi takwantar da kanta cikin shagwa6a tace ina ji man, inshirya muje tare?
Rungumeta yayi sannan yace ina zamuje tare?
Turo baki tayi tace inda zakaje man.
No kar kidamu kiyi zamanki ba wani dad’ewa zanyi ba, kifad’i abinda kikeso insiyo miki.
Murmushi zarah tayi tace duk abinda kasiyo min inaso.
kallonta yarima yayi yace kidai fad’a kar insiyo abinda baiyi mikiba.
Wani irin fari tayi mashi da ido sannan tace za6in mijina shine nawa indai ya yi maka toh nima zaiyi min kar kadamu my prince.

Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yace shikenan, mik’ewa yayi nan zarah itama tamik’e tabi bayansa har suka fito main parlour lokacin mu’az yana zaune yana jiransa ganin yarima yasa yamik’e.

Jamila da zarah har wajen k’ofa suka rakasu sukai musu Allah yakiyaye hanya sannan suka dawo suka zauna suna hira.

 

 

 

 

_Comment_
*Nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Wishing an amazing day and many great things to come to a wonder person. *Happy Birthday my dear umm abideen*_

 

Back to top button