Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 54

Sponsored Links

PAGE* 5⃣4⃣

Ahaka yarima yaje wajen aiki ammah kwata-kwata baida kuzari, Dr khalil shi kansa saida yalura da yanayin yarima,,,,,ko da yatambayesa abinda yake damunsa yarima banza yayi dashi yak’yale, kan dole Dr khalil yaja bakinsa yayi shuru dan ya san kome zaiyi toh bazai samu amsar tambayarsaba.

Zarah koda tashige bedbroom d’inta saman bed d’inta tafad’a tashiga tacigaba da kukanta wani irin son yarima ne yake fizgarta daga gefe guda kuma haushinsa takeji,,, ahaka tasha kukanta saida taji yunwa tana niyar yi mata illah sannan tamik’e taje wanko fuskarta tafita tad’auki coffeenta tasha.

 

Sumayya koda yarima yakoreta daga part d’insa bata wani damuba sosai cikin ranta cewa tayi na zan hanyar da zan 6ullo maka,,,,daga nan wucewa tayi tatafi turakar iyayenta.

Tana shiga a parlour ta tarar da sultana sadiya kishingid’e tsakiyan kuyanginta suna ta yi mata hidima, ganin sumayya yasa suka zube gabad’ayansu suna kwasar gaisu sumayya ko kallon inda suke batayiba ganin haka yasa cikin sauri suka ficce daga parlourn gudun kar suyi laifi.

Sultana sadiya tana ganin sumayya ta shigo nan tahad’e fuska babu alamun fara’a ko kad’an a tare da ita.

Sumayya jiki ba k’wari tazo tazauna gefenta ahankali tace ummana.

Sultana sadiya batare da ta kalletaba tace me yakawoki wajena.

Sumayya fashewa tayi da kuka tare da fad’awa jikin sultana sadiya, shuru sultana tayi tak’yaleta.

Cikin kuka sumayya tace ummah dan Allah kiyi hak’uri wlh na daina.

Sultana sadiya sai a lokacin ta kalleta tace sumayya kikyaleni kawai tunda bakyajjn magana kije kawai na sallamaki wajen wad’anda kike jin maganarsu.

Sumayya Cikin kuka tashiga girgiza kai ahankali tace ummah wlh ina jin maganarki akasine kawai aka samu kuma insha Allahu na daina bazan k’araba, dan Allah kiyafe min wlh duk na zubar da pills d’in.

 

Sultana sadiya cike da tausayin d’iyartata tashiga d’an bubbuga mata bayanta kad’an cikin sigar lallashi tace toh shikenan sumayya na hak’ura ammah dan Allah kidaina irin haka kinsan idan labari yajema su dada bazakiji da kyauba ke kinsan ko mahaifinki yaji sai kashinki ya bushe.

Sumayya share hawayen fuskarta tayi cikin jin dad’i tace insha Allahu ummah ba zan sakeba.

Murmushi sultana sadiya tayi tace yauwa d’iyata, yanzu sai kije kisamu kilallashi wanchan miskilin mijin naki ko shima ya safko, Allah yaimiki albarka.

Ameen ummana, insha Allahu zan k’ara bashi hak’uri….nan tazauna sukasha hira da ummah cike da jin dad’i sannan daga baya tayi mata sallama tafito tanufi turakarsu dada dan tagaisheta.

koda tashiga fuskarta d’auke da murmushi taduk’a tagaishe da dada,

Cikin jin dad’i dada ta amsa mata nan sumayya tazauna gefen dada tana murmushi tace ‘yar tsohuwa me kika ajemin?

Ido dada tazuba mata tace me fa zan aje miki bayan gakinan kinyi 6ul-6ul da ke kin koma d’imemiya wai mi wanchan miskilin yake d’irka miki?

Dariya sumayya tayi tace wlh dada hutune kawai,,,dada cikin rashin yarda tace kodai mun samu k’aruwane?

Girgiza kai sumayya tayi tace wlh dada banda komai.

Rik’e ha6a dada tayi tace sumayya kodai zakije asibiti aduba lafiyanki, tunda shi wanchan miskilin bai damu da hakanba.

Dada na je ance lafiya ta lau fa kawai dai lokacine baiyiba.

Ajiyar zuciya dada tasafke sannan tace toh Allah yanuna mana lokacin, Allah yasa ina da rabon ganin d’an cikinki.

Dariya sumayya tayi tace Ameen dada.

Ho ‘yar nema ko kunyata bakyaji….cewar dada.

Dariya sumayya tashiga yi tace kunya ai ya wa-ne yanzu.

Dak’uwa dada tayi mata tace gidanku sumayya, ja ira kawai.

Sumayya tsagaitawa tayi da Dariya da take tace afuwan ranki yadad’e na daina.

Murmushi dada tayi tace toh ya wajen ‘yar uwartaki ina fata tana lafiya.

Ta6e baki sumayya tayi tace inaji lafiya lou take.

Sakin baki dada tayi tana kallonta tace sumayya ban fahimcekiba? Kar dai kicemin baku zaman lafiya.

Sumayya k’wallah ce tacika mata ido tace toh dada ya zanyi yarinyar da bata k’aunata kullum batada aiki sai had’ani da mijina, ni me natsare mata da zata dinga min haka.

Dada da mamaki take kallon sumayya tace sumayya yanzu yarinyar nan da nake gani kamar babu ruwanta itace takeyi miki haka?

Hmm dada kenan kawai dai abar maganar dan in kikaji wasu abubuwanma da takeyi sai kinyi mamaki, ni yanzu babbar matsalata fushin da yarima yakeyi da ni kusan kullum sai ta had’amu.

Dada salallami tashiga yi tace na shiga ukku ni Asma’u, yanzu saboda Allah yarinya tazo tararar da ke gidan mijinki sannan tace zatayi miki irin haka?

Toh kibarni da yariman yadawo zan gansa idan shi bazai iya d’aukan matakiba a kai toh ni zan d’auka ko inhad’asa da memartaba tunda shi yana jin maganarsa.

Cikin jin dad’i sumayya tace yauwa Dadata ammah dan Allah kar kifad’ama yarima ni nafad’a miki dan wlh zai iya kakkaryani.

Cike da tausayin jikartata dada tace kar kidamu sumayya insha Allahu bazan ceba, kuma ko na ce ai bai isa yata6akiba dan ko dole inrama miki.

Cikin jin dad’i sumayya tace kibarsa kawai Dada ni zaman biyayya da hak’uri kawai nake da shi, duk abinda yayi min dan kansa, dan na ma fi ganin laifin wacchan munafukar matar tasa mai mugun hali.

Tsaki Dada taja tace kibarni da su kawai,

haka sumayya tazauna tayi ta 6ata zarah a wajen dada nan Dada tahau tazauna tana ta jimamin halin zarah.

 

 

Yarima koda yadawo wanka yayi yashirya sannan yad’anci lunch kad’an, yana gamawa fita yayi yanufi part d’in zarah dan kwata-kwata yanzu wani iri yakeji game da ita rashin zuwanta part d’insa ba k’aramin d’aga mai hankali yakeba.

Yana shiga bedroom d’inta daidai lokacin tafito wanka d’aure take da towel tana tsaye gaban dreesing mirror tana yin shafa.

‘Dago kai tayi takallesa nan suna had’a ido tajanye fuskarta daga kallonsa, yarima tsaye yayi yana kallonta batare da yayi maganaba.

Tana gamawa tawuce tanufi wajen wardrobe d’inta tabud’e tad’auko kayanta, juyowar da zatayi sai ganin mutum tayi bayanta tsaye, k’ara d’aure fuska tayi ta ra6a ta gefensa zata wuce yarima jawota yayi tafad’o jikinsa yarungumeta,

K’ok’arin turesa tashiga yi nan yak’ara matseta a jikinsa ahankali yace wai ke meyasa kike min haka?

Harararsa zarah tayi tace wani abu kaga na yi maka?

Zuba mata ido yayi yana kallonta da mamaki sannan yace dan kinga ina lalla6aki saisa kike min yadda kikaga dama
Ta6e baki zarah tayi tace kar ma kalalla6ani indai nice na gama shiga sabgarku tunda daman sai kunga na shiga sannan zaku sami daman wulak’antani,,,,fashewa tayi da kuka tace ni duk abinda sumayya takemin me nata6a cewa shine ni kamar jira ake ko banyi mata wani abuba sai ace na yi toh ya kukeso inyi!!! tak’arashe maganar cikin d’aga murya.

Yarima shuru yayi yakasa magana sai chan yarungumeta a k’irjinsa tare da runtse idonsa yana jin wani iri a ransa,,,ahankali kamar me rad’a yace ix owk zarah, insha Allahu hakan ba zai k’ara faruwaba,

Zarah janye jikinta tayi daga nasa tawuce zatabar wajen, kallonta yarima yayi yace wai ke dan kin samu ina lalla6aki shine kike min haka?

Zarah juyowa tayi takallesa sannan tace toh ni me kaji na ce maka?

Yarima har ya bud’e baki zaiyi magana nan wayarsa tafara ringing,,,d’aukowa yayi yaduba ganin me kiransa yasa yayi picking tare da yin sallama.

Daga chan 6angaren dada amsa mashi tayi sannan tace toh dodo kazo yanzu ina son ganinka.

Yarima kallon agogon hannunsa yayi sannan yace yanzu kuma?

Cikin fad’a dada tace eh, inkuma bazakazoba saboda ka rainani toh sai infad’ama ubanka shi sai yasa kazo.

Yarima shuru yayi baice komaiba.

Jin ya yi shuru yasa dada tace ko bakaji abinda naceba?

Cikin k’osawa da maganar yace ganinan,,,,yana fad’in haka yakashe wayar ko inda zarah take bai kallaba yawuce yafita yabar d’akin

 

Zarah da ido tabisa har yatafi sannan tad’auki kayanta tasaka, cikin ranta ji take daman batayi ma yarima hakaba.

 

Yarima koda ya isa turakar su dada a parlour yasameta zaune tana jiransa, ko da yayi sallama ciki-ciki ta amsa masa, saman d’aya daga cikin kujerun yazauna cikin girmamawa yagaisheta.

Amsa masa dada tayi daganan d’akin yad’au shuru ba wanda yak’ara magana, ganin baida niyar yin magana yasa dada tace toh d’an nema watau shine kayi zaune baka ma jin zaka iya tambayata dalilin kiran da nakeyi maka.

Murmushi kawai yarima yayi batare da ya yi maganaba.

Dada gyara zamanta tayi ta fuskanci yarima sosai sannan tace suhail na ji abinda kakeyi ma ‘yar uwarka kuma na gode ba ita kayimawa ba ni kayimawa.

Da mamaki yarima yake kallonta har saida takai aya sannan yace ranki yadad’e wani abu tace na yi mata?

Harararsa dada tayi tace kai kar kamaidani k’aramar yarinya ko ka d’auka duk abinda kukeyi mata kai da matarka bai dawowa a kunnena?

Yarima har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa nan yacigaba da dannar wayarsa da take hannunsa.

Nan dada tacigaba da cewa Toh bari kaji ko kaso ko kak’i sumayya ‘yar uwarkace kuma za6inmu ce sannan wannan aure naku mutuwa kawai zai raba, ita wacchan matar dan kaga za6inka ce saisa kake ma ‘yar uwarka wulak’anci son ranka kuma inaso kasani ciki Allah yake bayarwa kuma itama sumayya in da rabo zata haihu.

Yarima banza yayi mata kamar ba da shi take maganaba,,,dada k’ulewa tayi ganin baida niyar yin magana tace watau ga sakarya tana magana bakaji ma zaka iya tankamin.

Saida yarima yayi Kusan minti biyu sannan yad’ago yakalli dada da tatsaresa da ita, murmushi yayi sannan yace toh ranki yadad’e na ji.

ta6a hannu dada tashigayi tace na shiga ukku yanzu saboda Allah suhail ni kake ma haka? Ko mahaifinka bai isa yayimin hakaba sai kai?

Shuru yarima yayi yakyaleta nan dada tayita masifarta daga k’arshe jingine kansa yayi da kujerar da yake zaune yamaida idanunsa yalumshe.

Dada tsura masa ido tayi takasa cigaba da fad’an dan gabad’aya yarima ya gama kashe mata baki, cike da takaici tanuna k’ofa tace tashi kafita kabani waje.

Yarima bud’e idonsa yayi tare da d’aukan wayansa yace na barki lafiya.

 

Dada binsa tayi da kallo har yaficce takaici yacikata saisa batason wani abu yahad’ata da yarima dan takaici kawai take kwasa, cikin ranta kuma tana jinijna ma halinsa, ahankali tace wannan mutumin halinsa sai shi, ina amfanin miskilanci irin haka, lallai matansa da suke zaune da shi suna k’ok’ari.

Yarima koda yafita daga nan 6angaren iyayensa yawuce, ko da yashiga parlour ummi batanan, bakowa ciki, dan haka yasamu waje yazauna tare da dafe kansa dan shi gabad’aya anhad’a masa zafi dayawa tsaki yaja yace ta ko’ina ba sauk’i.

 

Sultana bilkisu da tafito daga bedroom tsaye tayi tana kallon d’an nata da gabad’aya hankalinsa baya a jikinsa, cike da tausayinsa tataka ta isa inda yake daga gefensa tazauna, Sai a lokacin yarima yad’ago yakalleta nan yasakarmata murmushi.

Sultana bilkisu ma maida masa martani tayi sannan tace my son lafiya naganka nan zaune?

Yarima duk’ar da kansa yayi yace ummina barka da rana.

Ido tazuba mai tace dafatan kuna lafiya?
Lafiya lou ummi.
Toh ya wajensu sumayya da zarah.
saida yajingine kansa da kujera sannan yace duk suna lafiya.

Toh ya d’iyartawa da jiki?
Yarima d’an sosa kai yayi alamun jin kunya sannan yace ummi dasauki.
Toh masha Allah, Allah yaraba lafiya.
Shuru Yarima yayi baice komai ba.

Sultana bilkisu rik’o hannunsa tayi tace my son me yake damunka?

Yarima kallonta yayi yana murmushi yace bakomai ranki yadad’e.

Sultana bilkisu batayi mamakin jin hakan daga garesaba dan ta san halin d’an nata, murmushi tayi tace shikenan ammah dan Allah kadinga hak’uri ka san ganinka cikin irin wannan yanayi ba k’aramin d’agamin hankali yakeba.

Yarima kwantar da kansa yayi saman cinyar ummi yace kar kidamu ummina babu abinda yake damuna kawai dai ji nayi inaso inzo inganki.

Cikin jin dad’i sultana bilkisu tashiga shafa gashin kansa tace Allah yaimaka albarka my son.

Ameen ummina….nan Yarima yamaida idanunsa yalumshe, sultana bilkisu tazuba mai ido tana kallon d’an nata cike da so da k’auna.

 

Tun daga lokacin Yarima yadaina shiga harkar kowa dan yanzu tun safe idan yafita baya dawowa sai wajen 9pm saboda meeting da suke zama, kuma idan yadawo sai ya gargad’i guards d’insa akan kar subar kowa yashigo masa hutawa yakeson yi.
ba zarah ba hatta ita kanta sumayya saida tad’an shiga damuwa.

 

 

_*After one week later*_

Yau yarima kasancewar bai fitaba zaune yake d’akinsa a parlour yana kallo zarah ce tashigo da sallamarta.

Yarima batare da ya juyo ya kalletaba ya amsa, zarah wani irin sanyi taji a ranta da tagansa, takawa tayi ta isa inda yake zaune da mamakinsa sai gani yayi ta zauna saman cinyarsa,

Sai a lokacin yarima yakalleta shi kansa wani irin sanyi yaji a ransa, zarah k’irjinsa tashige tare da fashewa da kuka.

Runtse idonsa yarima yayi yana jin kukan nata har cikin ransa, rungumeta yayi muryarsa tana rawa yace zarah me yake samunki?

Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace akwai abinda yake samuna bayan wanda kayi min?

Ido yarima yazuba mata batare da ya ce komai ba,

cikin sheshek’ar kuka tace shine kagujemin kadaina shiga sabgata gabad’ayama kadaina zaman gidan.

Yarima tallabo fuskarta yayi yace toh ya kukeso inyi muku naga kamar kinfison hakan, kefa kikace kin daina shiga sabgata saisa nabarki kihuta.

Zarah rungumesa tayi tace hakan da kayi ba k’aramin d’agamin hankali yayiba dan Allah kayi hak’uri na daina.

Yarima kallon cikin idonta yayi sannan yace meyasa bakison cin abinci?

Zarah turo baki tayi tace taya zanci abinci bayan babynka yana matsamin ina tunanin missing d’in daddynsa yayi……tak’arashe maganar tare da kashe mashi ido d’aya,

Yarima hannunsa yakai cikin rigarta yana shafar cikinta, zarah maida idanuwanta tayi talumshe tana jin dad’in hakan da yakeyi mata.

Gabad’ayansu shuru sukayi ba wanda yak’ara magana, ahankali taji hannunsa suna yawo cikin rigarta,

Chan kuma sai ya janye hannunsa daga cikin rigarta yace tashi muje kici abinci,

Zarah d’ago kai tayi takallesa tare da turo baki tace nifa na k’oshi.

Yarima zuba mata ido yayi sannan yace ammah ai ga shedanan yau bakici abinciba.

Zarah kamar zatayi kuka tace ni ice cream nakeson sha,

Jan hancin yarima yayi sannan yace toh kije kici abinci zan bayar asiyo miki,

Zarah mik’ewa tayi tana gyara rigarta sannan tace toh ammah fa kad’an zan ci.

‘Daga kai kawai yarima yayi batare da ya yi maganaba.

Juyawa Zarah tayi tafita tabar d’akin, nan yarima yakoma saman 3 seater yakwanta yana ci gaba da kallonsa yana jin wani irin nishad’i a ransa.

Daga k’arshe yamik’e yazari key d’in motarsa yaficce yabar gidan.

 

Zarah koda takoma part d’inta kad’an taci abincin nan tazauna zaman jiran yarima yakawo mata ice cream d’in ammah shuru, zuwanta biyu part d’insa ammah baya nan.

Ahaka har akayi sallar isha’i taje tayi wanka tai shirin baccinta,,,,tana cikin saka night gown d’inta sai ga kiran yarima ya shigo wayanta cikin jin dad’i tayi picking kamar zatayi kuka tace shine kabarni ina ta jiranka.

Daga Chan 6angaren yarima cemata yayi tazo ta amsa gashinan.

Cikin jin dad’i Zarah tace toh.

Cikin sauri ta ida shirinta tafito tanufi part d’in yarima.
Tana shiga ganin baya parlour yasa tawuce bedroom d’insa ahankali tatura k’ofan tashiga, saman gadonsa tahangosa zaune yana ta waya hannunsa rik’e da paper da biro yana rubutu.

Takowa tayi ta iso bakin gadon, d’ago kai yarima yayi yakalleta sannan yai mata nuni da ledar da take aje k’asa.

Cikin jin dad’i zarah taje tad’auki ledar, a nan k’asa tazauna tabud’e tad’auko d’aya sannan tatashi tasaka sauran cikin freezer d’insa.

Dawowa tayi tad’auki wanda ta aje taje gefensa tazauna tabud’e tana sha.

Har a lokacin yarima yana ta ‘yan rubuce-rubucensa, zarah ahaka tashanye sannan taje toilet d’insa tawanke bakinta.

k’arshen gadon taje takwanta tana kallonsa yana ta wayansa, daga k’arshe da taga wayar batada niyar k’arewa dan haka tamik’e takoma gefensa tazauna, marairaicewa tayi ahankali tace wai wayar ba a gamata hakanan dare fa ya yi.

Kallonta yarima yayi nan zarah tad’aga mai gira,
idanuwansa yamaida ga agogon da take manne ga bangon d’akin ganin har 11pm ta yi yasa yayi sallama yakashe wayar.

Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido sannan yace bazaki kwantaba?

Zarah batare da tayi magana ba tamik’e taje takwanta, yarima kashe gloves d’in d’akin yayi sannan shima yahau gadon daga gefen zarah yakwanta.

Zarah tana ganin ya kwanta nan tamaida kanta saman k’irjinsa, yarima kamar daman jira yake nan yarungumota jikinsa tare da k’ok’arin rabata da rigar jikinta, yana cirewa Zarah tazame jikinta takoma gefe,

numfashi yarima yaja, cikin kasalalliyar muryarsa yace ya dai?

Zarah cikin tsokana tace ni bacci nakeji.

Yarima matsawa yayi gab da ita sannan yace tun d’azu me yahanaki baccin?.

Zarah turo baki tayi har ta bud’e baki zatayi magana sai ji tayi yarima ya had’e bakinsu waje guda yafara kissing d’inta cikin k’warewa,

Zarah gabad’aya tafita hayyacinta inda kowane 6angare na jikinta yake kar6an sak’onsa, k’ara rungumesa tayi jikinta ita kanta ta san ta yi missing d’insa.

nan yashiga sarrafata son ransa, har tagaji ammah yak’i barinta daga k’arshe kuka tasa mashi ammah Yarima baima san tana yiba dan gabad’aya hankalinsa baya tare da shi.

Saida yagaji dan kansa sannan yabarta zarah chan gefe takoma takwanta tana sheshek’an kuka.

Yarima duk sai yaji ba dad’i dan haka yajanyota jikinsa batare da ya yi maganaba yashiga d’an bubbugamata baya alamun lallashi.

nan zarah tarage sautin kukan nata daga k’arshe bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima na jin ta yi bacci yajanyeta daga jikinsa yalullu6eta da blanket sannan yatashi yanufi toilet dan yayi wanka.

Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yahau gadon yakwanta tare da jawo zarah jikinsa yarungume yana shafar cikinta d’an wata biyar, a haka bacci yad’aukesa

 

Da asuba saida yayo alwallah sannan yatayar da zarah yawuce masallaci.

jikinta duk ciwo yake haka tajanyo kayanta tasaka tafita takoma part d’inta, a chan tayi wanka tad’auro alwallah tai sallah bayan ta gama tahaye saman gadonta takoma bacci.

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

Back to top button