Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 13

Sponsored Links

page 1⃣3⃣

 

Abbah gyaran murya yayi sannan yace maganar barin gida duk bata tasoba a yanzu muma mungane kuskurenmu tabbas duk abinda mutum yashuka shi zai gir6a wlh banga laifinkuba tabbas bamu dace da mukasance iyayenkuba, Abbah girgiza kai yayi yace kaicona da nabari son abun duniya yarud’eni har nawatsar da tarbiyar yarana alhali ni iyayena bahaka sukayi min ba, son zuciya da kwad’ayine suka ja mana dan Allah kuyi hak’uri da mummunar d’abi’ar da muka d’auraku akanta, wannan ya zama darasi a garemu ayi hak’uri a yafi juna.

mama cikin kuka tace dan Allah kuyafe mana insha Allahu yanzu zamu gyara tsarin gidanmu da komai zakuyi alfahari da mu.

Zarah ce tace bakomai wlh mun yafe muku duniya da lahira muma kuyafe mana.
kallonta tamaida ga su Rauda da basu da niyar yin magana tace yaya Rauda dan Allah kuyafe ma su mama tunda sun gane kuskurensu.

Rauda da Aysha cikin kuka sukace shikenan mun yafe musu Allah yayafe mana gaba d’ayanmu.

gaba d’aya suka amsa da Ameen.

sannan Abbah yace toh Alhmdllh da Allah yataimakemu muka farka tun kafin lokaci yak’ure mana naji dad’in hakan, insha Allahu zanyi k’ok’ari duk wani hak’inku da yarataya kaina inga na safke muku shi, saidai matsala d’aya yanzu cikin da yake jikin Rauda bansan ya zamuyi da Shiba.

Mama ma tayi nisa sannan tace mezai hana azubar da shi?

Zarah da sauri tagirgiza kai tace a’a mama bai dace azubar da shi ba karfa mumanta shi fa d’an baida alhakin kowa sai ma su da yakeda alhaki akansu da suka samesa ba ta hanyar halak ba, ga laifin zina ga na kisan kai ai k’ara tahak’ura tafauwala ma Allah lamurranta saboda Allah yana sane da halin da take ciki kuma komai rubutaccene ya riga ya tsara ma kowa yadda rayuwarsa zata kasance, shin baku tsoron wajen zubar da cikin tarasa rayuwarta? idan taje me zatace ma ubangijinta ranar gobe k’iyama? Shin kunsan yadda rayuwa zata kasance a nan gaba ko kuna tunanin nan gaba zata k’ara haihuwa? yakamata mumik’a lamurranmu ga Allah ubangijinmu mucigaba da rok’onsa tare da neman gafararsa Allahu gafurur rahim ne.

Dukkansu jinjina kai sukayi alamun gamsuwa da bayanin Zarah, Abbah yace tabbas Zarah nagamsu da bayaninki Allah yayafe mana kuskurenmu wlh ke d’iyar kirkice, kekuma Rauda Allah yasafkeki lafiya.

Gaba d’ayansu sukace Ameen, mama tace Allah yayi muku albarka Allah yaraya mana ku.
cike da jin dad’i sukace Ameen mamanmu,
muma muna alfahari da ku Allah yabar mana ku.

daga nan suka shiga tsara yadda zasu tafiyar da rayuwarsu, Aysha da Rauda ‘yan kud’in da suke hannunsune suka tattara suka ba iyayen nasu sukace asiyo kayan abinci,

tun daga ranar suka rabu da samarinsu gidan yagyaru, inda Aysha takoma islamiyya suna zuwa tare da Zarah, Rauda kuma tacigaba da rainon cikinta, a gida Zarah takeyi masu k’arin karatunsu Rauda da Mama.

cikin ikon Allah Abbah yasamu d’an aikin da ake biyansa duk wata da taimakon Allah yake samu yana rik’e gidansa gwalgwadon k’arfinsa,

su kansu a yanzu suna jin dad’in sauyawar da suka samu ta rayuwa.

_______________

Yarima Suhail yau tunda yatashi jinsa yake wani iri ga tsananin buk’atar sumayya da yakeyi daurewa kawai yake tsawon wata biyu kenan rabonsa da ita.

yau bayan yadawo wajen aiki yayi wanka ya shirya cikin shigarsa ta alfarma fitowa yayi yanufi part d’in sumayya domin yau ji yake hak’urinsa ya k’are baya iya cigaba da daurewa

 

Yarima d’akinn sumayya yashiga lokacin sumayya tana zaune a parlour tsakiyar kuyanginta suna ta mata hidima.

ganinsa yasa dukansu suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baibi ta kansuba yashige bedroom d’in sumayya, da harara sumayya tabisa sannan tamik’e tabi bayansa.

tana shiga ta tarar da shi zaune saman gado batare da ta tanka masaba taje tazauna itama kusa da shi nan wajen yad’au shuru.

ganin baida niyar yin magana yasa sumayya tace lafiya?

Harara yarima yawurga mata tare da cewa lafiyar kenan, hak’ina nazo kibani.

‘yar dariya gimbiya sumayya tayi sannan tace sai a yau za’a waiwayeni? ai nad’auka anrufe shafina, ko ka mance lokacin da nazo d’akinka kakoreni? ai nad’auka nagama amfani a wajenka ashe ina da sauran amfani.

 

yarima suhail wata muguwar harara yawurga mata cikin 6acin rai yace sumayya da ace akwai yadda zanyi inguje ma kusantarki da nayi domin nima ba dan nasoba nake nemanki domin kwatakwata ke ba ajina bace dandai *K’ADDARA CE* kawai tasa na amince ma aurenki, wlh kikiyayi ranar da zaki kaini k’arshe domin zan d’auki mummunan mataki akanki.

Sumayya ta6e baki tayi cikin rashin damuwa tace kai fa matsalata da kai bakasan arzik’iba sai kanaso ataimaka maka maimakon kalalla6ani shine kakemin fad’a da gori. wlh nima ashirye nake nakad’auki kowane irin mataki nasan dai duk abinka ba zaka ta6a k’ara aureba dan su dada ma nazasu amince ba.

 

yarima har ya bud’e baki zaiyi magana nan wayansa tafara ringing ganin ummi ce yasa yasaita nutsuwarsa sannan yayi picking tare da yin sallama.

chan 6angaren sultana sadiya ta amsa masa tare da cewa yarima kazo kasameni inason ganinka.

yarima suhail cike da ladabi yace ummi lafiya dai ko?

Ummi tace lafiya lou kawai inaso mutattauna ne akan kayan da kace aware akai gidan marayu da gajiyayyu.

yarima shuru yayi nad’an lokaci sannan yace toh ummi ganinan zuwa, nan yakashe wayar tare da mik’ewa ko inda sumayya take bai k’ara kalloba yaficce yabar d’akin.

 

sumayya haushi yakamata saboda ba haka tasoba taso ace sai tagama ja masa rai sannan zata amince masa domin itama buk’ace take da shi kawai dai tana daurewane domin tanuna masa kuskurensa na wulak’antata da yayi, tsaki taja tare da mik’ewa tsaye tace nasan dai dole zai dawo gareni.

 

 

yarima ko da yafita direct turakar iyayensa yaje a parlour yatarar da k’anwarsa Gimbiya Rahma a tsakiyar kuyangi sun zagayeta suna mata fifita da tausa inda ita kuma take waya.

 

ganinsa yasa gaba d’ayansu suka zube k’asa suna kwasar gaisuwa, Rahma ma dasauri tamik’e tsaye tare da d’an rissinawa cike da girmamawa tace barka da shigowa.

Yarima batare da ya tanka musuba yayi musu nuni da k’ofa alamun sufita.

gaba d’ayansu suka mik’e suka fita daga d’akin, Rahma ma har zata fita yace ke dawo.

Rahma dawowa tayi tazauna kujerar da take opposite d’in wadda yake zaune, kallon yayan nata take taga baida niyar yin magana gashi duk ya canza, ahankali tace yaya suhail bakada lafiya ne?

Yarima suhail ahankali yamaido kallonsa gareta kamar ba zaiyi magana ba sai kuma can yace tashi kije kihad’o min ruwan lipton da lemun tsami kar kizuba komai ciki.

Rahma mik’ewa tayi tare da d’an rissinawa sannan taffice daga d’akin.

Yarima jingine kansa yayi akan kujerar da yake zaune tare da lumshe idonsa shi kad’ai yasan abinda yake ji.

 

ummi tana fitowa daga d’akinta ganin yarima a haka yasa tayi tsaye tana kallon d’an nata ahankali tace suhail daman ka shigo shine baka fad’a min ba?

Yarima suhail ahankali yabud’e idanuwansa da suka rikid’a suka koma launin ja yasafkesu akan fuskar ummi tare da yin d’an guntun murmushi yace sorry ummi ban dad’e da shigowaba.

ummi tsaye tayi tana kallon d’an nata yanayinsa yasa saida gabanta yafad’i a rud’e tace suhail me yake damunkane bakada lafiya?

Yarima murmushi yayi yace lafiya ta lau ummi.

ummi kasa cewa komai tayi saidai binsa take da kallo tana nan tsaye Rahma tashigo da wani plate d’auke da ruwan lipton da lemon a gefe, gaban ummi ne yashiga fad’uwa ganin Rahma ta aje gaban yarima tare da duk’awa tana matsa lemon d’in cikin cup d’in,

tausayin d’antane yakamata domin tabbas tasan abinda take tunani shi yakasance, ahankali taga yarima suhail yad’auki cup d’in yana sha yana yamitsa fuska duk Wanda yagani yasan ba dan dad’i yake sha ba kawai dai dan ba yadda ya iya.

ganin haka yasa ummi tawuce tana jin wani iri a cikin ranta bata zarce ko’inaba sai turakar mijinta bata damu da gaisuwar da akeyi mataba domin kwatakwata ma hankalinta ba anan yakeba.

ko da tashiga lokacin yana zaune saman gado hannunsa rik’e da newspaper yana dubawa, jin anbud’e d’akin yasa yamaida kallonsa ga k’ofa, yanayin yadda yaga matar tasa ta shigo yasa ya aje newspaper d’in da take hannunsa yazuba mata ido.

Sultana bilkisu itama tsaye tayi tana kallonsa ta bud’e baki zatayi magana kenan sai hawaye suka fara zuba daga idonta, Sultan Ahmad cike da rud’ewa yamik’e yanufo inda matar tasa take yace bilkisu lafiya me yake faruwane?

Sultana Bilkisu fashewa tayi da kuka tace ranka yadad’e kagafarceni akan abinda zan fad’a domin hak’urina ya k’are ace d’ana tunda yayi aure baida kwanciyar hankali kaduba kaga duk mulki, sarauta, kyau, dukiya babu wanda *YARIMA SUHAIL* yarasa saidai abu d’aya shine kwanciyar hankali.

Sultan Ahmad zuba ma matar tasa ido yayi yana kallonta domin yasanta akwai hak’uri duk abinda za’ayi mata batanuna 6acin ranta saidai idan ankaita bangone, Sultana bilkisu cigaba tayi da cewa tun lokacin da d’ana yayi aure baida kwanciyar hankali domin kwatakwata bai samun nutsuwa, kula da tattali a wajen matarsa Sumayya, ba wai shi yafad’a minba kawai dai nafahimci haka kaduba kaga yadda yarame koda yarima baya fad’in matsalarsa saboda zurfin cikinsa ammah yanayinsa kawai zaka kallah kagane yana cikin matsala, girgiza kai tayi tace ya za’ayi ace da matarsa ammah yana shan ruwan lipton da lemon, ranka yadad’e ina tsoron ranar da d’ana zai kasa jurewa har yafara neman mata, bawai fata nakeyi masaba kawai dai ina tsoron hakan domin shima mutum ne kamar kowa,
rik’o hannun sultan Ahmad tayi tare da durk’usawa k’asa tace ranka yadad’e idan maganganuna sun 6ata maka rai kayi hak’uri ammah ina tausayin halin da d’ana yake ciki, Sultana Bilkisu tana kaiwa nan tasake fashewa da wani sabon kukan.

Sultan Ahmad cike da tausayi yarik’o hannun matar tasa yamik’ar da ita tsaye yarungumeta yace Bilkisu nima ina lura da lamurran Suhail narasa ya zanyi ne domin ko bakomai d’iyar d’an uwana yake aure narasa ya zanyi in magance matsalarnan domin ina tsoron abinda zai samo min matsala ni da d’an uwana.

Gimbiya Bilkisu d’ago kanta tayi tana kallon mijin nata tace ammah shi d’anka fa kaduba kaga matsalar da take shirin 6ullomasa dan Allah kataimaka kaduba lamarin yarima Suhail domin yana buk’atar taimakonmu.

Sultan Ahmad rik’o hannun matarsa yayi sukaje bakin gado suka zauna yace Bilkisu nima inajin Suhail sosai a cikin raina kikwantar da hankalinki zanyi shawara muga yadda zamu 6ulloma lamarin cikin ruwan sanyi kema inaso kije kiyi tunani a kai kidaina sanya damuwa a ranki kinji.

Sultana Bilkisu cike da gamsuwa da maganar mijin nata ta jinjina kai tare da yin murmushin jin dad’i, shima Sultan Ahmad murmushin yayi sannan yashiga goge mata hawayen da suke fuskarta.

godia tayi masa tare da mik’ewa tsaye, kallonta yayi yace Bilkisu ina kuma zakije? ai nad’auka zuwa kikayi kitayani hira?

murmushi tayi tace kayi hak’uri d’ana yana parlour yana jirana bari inje insallamesa sai indawo.

Sultan Ahmad shima murmushi yayi yace toh shikenan sai kin dawo.

Sultana Bilkisu d’an rissinawa tayi cike da girmamawa tace nabarka lafiya sannan tajuya tafita tabar d’akin,

Yarima Suhail ko da yagama shan lipton d’in komawa yayi yajingine kansa da kujerar da yake zaune yana jiran mahaifiyartasa tafito anan bacci yafara d’aukesa.

Sultana Bilkisu ko da tashigo ganin d’an nata yana bacci yasa tazauna gefensa tare da d’aura kansa saman cinyarta.

ahankali suhail yabud’e idonsa sanin mahaifiyarsa yasa yasakarmata murmushi tare da maida idanuwansa yalumshe,

itama sultana Bilkisu murmushin tayi nan tashiga shafa gashin kan d’an nata cike da so da k’aunarsa, a gefe guda na zuciyarta tausayinsace ta baibayeta.

**** **** *****

mama ce da su zarah zaune tsakar gida suna k’ulla zo6o da kunun aya suna fira cike da nishad’i, Aysha ce takalli zarah tace wai yaya zarah yaushene ma zakuyi walimar saukarku ta alk’ur’ani?

Murmushi zarah tayi tace kedai Aysha kin cika zumud’i sai fa nan da sati biyu kinga ai da d’an sauran lokaci.

Mama tace kud’in ma da kikace kina buk’ata suna nan ajiye tun jiya Abbanku yabani inbaki idan kin tashi tafiya islamiyya sai kituna min inbaki kikai dan kar ma inta6asu.

Zarah cike da jin dad’i tace nagode sosai Allah yak’ara girma da rufin asiri.

gaba d’ayansu sukace Ameen, Rauda tace toh anko d’in da zakuyi fa?

Zarah murmushi tayi tace bazanyi wannan ba yaya Rauda domin bazan matsa ma kaina ba abinda nakeda hali shi zanyi saidai in naje suhanani shiga taron.

Mama tace a’a zarah baridai muga abinda hali zaiyi idan da hali ai sai ayi miki.

zarah tace a’a mama kar kud’aura ma kanku d’awainiya abarsa kawai.

Mama tace zarah kibari dai muga abinda hali zaiyi idan da rabo ai za’ayi.

Aysha tayi karaf tace aikam dai dole ayi anko d’innan dan walima zamuyi sosai, nima zan bada gudumuwata.

Dariya Rauda tayi tace jarin sana’arki zaki bamu ko?

Aysha tace sosai ma ai har nafara tari ribar nake zubawa asusu.

dariya suka sanya mata zarah tace gaskiya nagode sosai ‘yar uwata da k’aunar da kike nunamin.

Aysha murmushi tayi tace wannan kuma halinkine domin ke kike nuna mana k’auna ta gaskiya.

 

A islamiyya zarah ce da k’awarta zaune suna d’an ta6a hira kafin malam bello yashigo, khairy kallonta tayi tace wai k’awata me kike shirya mana na walimar nan?

murmushi zarah tayi tace abinda hali yabani domin ba zan matsa ma kainaba abinda nake da halinsa shi zanyi dan ni ko ankoma bana tunanin yinsa.

Khairy zaro ido tayi tace kai zarah dan Allah kiyi anko d’in kinga kowa fa zaiyi ya za’ayi ace kekad’aice ba zakiyiba.

zarah murmushi tayi tace ba zan damuba domin kowa da bazarsa yake taka rawa, abinda Allah yahoremin shi zanyi.

Khairy jinjina kai tayi cike da gamsuwa da maganar k’awartata sannan tace toh Allah yashige mana gaba.

zarah tace Ameen ya rabb, shigowar malam bello ne yasa ajin aka nutsu daga nan aka fara darasi.

bayan angama anyi addu’a antashi zarah tace muje khairy inkai ma malam kud’in walimana,

a office suka samu malam hambali bayan sun gaishesa ya amsa musu, zarah tace malam ga kud’in walimata,

malam hambali yace zarah banda kud’in da kika biya ko k’arine muka samu?

zarah da mamaki take kallonsa tace ni kuma nabiya kud’i? da yaushe?

murmushi malam hambali yayi yace Malam bello yazo yakawo kud’inki.

Zarah da khairy kallon Juna sukayi sannan sukayi ma malam hambali sallama suka fita daga office d’in.

A wajen islamiyya suka hango malam bello tsaye ya zuba ma k’ofa ido da alamu zarah yake jira yaga fitowarta,

zarah saida suka d’anyi gaba sannan tad’auko wayarta takira malam bello tace gamu muna jiranka.

suna gama wayar malam bello yazo yasamesu fuskarsa d’auke da murmushi yayi musu sallama nan suka amsa masa tare da k’ara gaishesa.

zarah tace malam naje biyan kud’in walima shine aka shaida min ka biya nagode sosai ammah gaskiya bazanso kadinga matsama kankaba tunda kaga kaima karatu kake dan haka ga kud’inka na maido maka.

malam Bello yace a’a zarah ni dan Allah nayi miki dan haka bazan kar6aba, kuma kidaina maganar karatu nake koma me nakeyi ai dan ina da halin yi miki da ace banda su ai da bazan mikiba.

zarah tace hakane saidai ina tsoro kar asamu matsala aurenmu yak’i yuwuwa, malam Bello murmushi yayi yace kar kidamu ko da ace ban aurekiba wannan nasan *K’ADDARA CE* kuma wani baya auren matar wani dan haka kikwantar da hankalinki.

murmushi zarah tayi tace nagode sosai malam da taimakon da kakeyi min Allah yataimakake kamar yadda kake taimakona.

malam Bello yace kar kidamu ai yi ma kaine, yanzu muje inrakaki gida naga magrib ta gabato kuma k’awarki ta tafi ta barki,

zarah murmushi kawai tayi nan suka jera da malam Bello suna tafiya suna hira har saida yarakata har k’ofar gida sannan sukayi sallama yatafi itakuma tashiga gida.

 

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

Back to top button