Ikraam 1
IKRAAM~ By Khaleesat Haiydar
1……
Da sauri har tana tuntube ta karaso kusa da wani Babban Grocery dake cikin kasuwan, bbu fruits din da bbu wajen, cikin rashin sa’a warce take sauri dominta har ta gama biyan kudin fruits din da ta siya ta sakale handbag dinta ta dauki manyan ledojinta tayi gaba, bata yi give up ba still ta bita da gudu tana cewa “Anty, Anty,” matar ta juya da sauri cikin rashin sa’a daya daga ledanta ya kubce kayan ciki suka xube kasa, fashions na dankunnaye da sarkuna ne sae takalma, da sauri yarinyar ta yarda itacen hannunta ta durkusa tace “lah ashe baki rike ledan da kyau ba,” snn ta shiga kwakkwashe mata su tana mayarwa cikin ledan, har ta gama, snn ta dauki ledar ta daura a ka tace “bar in taya ki rikewa Anty,” matar da ba haifanta ba har jika xata yi da ita tayi murmushi tana kallonta tace “ki bar shi kawae yan mata,” yarinyar ta bata rai tace “A’a ni Anty sae na taya ki,” matar tayi murmushi ta ajiye daya ledan hannunta snn ta bude karamar jakarta ta ciro dari biyar ta mika mata tace “to gashi yan mata, yi tafiyarki kawae,” yarinyar kmr xata yi kuka tace “Allah sae na taya ki” matar dariya tayi wnn karan snn tace “to mu je ‘ya ta,” tafiya suke amma kallon ledan fruits din hannunta kawae take, kuma shine babban dalilin da yasa ta taimaka ma matar, har suka fito daga babban kasuwar suka iso bakin titi matar sae sannu take mata, ita ta sauke mata kayan daga kanta snn tace “ya sunanki dota?” yarinyar tace “ni sunana Rabi’atu, amma Ikraam Ammi da Abba da yan anguwarmu suke kirana, Ammi tace kawu na lado ne yace a sa min Rabi’a wae sunan kanwarsa ce kuma ta mutu baxata dawo ba, Amma Ammi tace sunan mamarta da xa’a sa min, ni dama bana son wnn kawu na ladon don mugu ne ssae baya son Ammina da babana har ma dani, matarsa shatu ma muguwace, idan Ammi ta aikeni gidanta sae ta rankwasheni kafin na dawo gida, snn ga lukutar yarinyar nn shafa me dukana hka ma watarana….” da sauri matar ta katse ta tana dariya tace “kai ikraam sunanki fa nace ki gaya min,” Ikraam ta dan marairaice fuska tace “Ae nace maki sunana Rabi’a, Ammi da baba da yan unguwarmu suna kirana Ikraam, amma malamar bokonmu Rabi’a take ce min don tace a makaranta ba a boye sunan gskya, hka ma wata yarinya a ajinmu ranan…” dariya ssae matar take tana kallon Ikram tace “naji hka Ikram, maxa ki tafi gida kar a nemeki kin ji,” Ikram ta bata rae tana wasa da xariyar skirt dinta tace “to Anty baki bani Ayabar da na gani a ledan can ba,” matar tace “ayya ae ban san kina so ba Ikram,” wani ledan ta dauka ta shiga debar mata Bananan har ma da apples, sae washe fararen hakoranta take tace “Anty baki gaya min sunanki ba,” matar ta juya tana murmushi tace “sunana Hajiya Amina amma Mami ake ce min,” Ikram tace “nima knn baxan ce maki Hajiya Amina ba Mami xan ce maki,” matar ta dan yi murmushi tace “eh dota,” ta mika mata ledan fruits din tace “to me kika xo yi kasuwa Ikraam,” Ikram xata yi magana wayar matar ya ruri cikin jaka, ta ciro wayar ta danna snn ta kara a kunne, sae kallon matar Ikraam take a xuciyarta tana cewa xan ce ta bani katon wayar nn. Matar ta shiga cewa “ehh srry ka dan dawo baya na hango motarka ynxu, bn lura da wucewarka bne,” tace “ok” snn ta katse kiran tana kallon Ikraam tace “to dota maxa ki wuce gida Allah yyi maki albarka,” Ikraam tace “to ae baki tafi ba ke ma, ko in tsayar maki da mota,”matar tayi murmushi tana shafa kanta tace “ynxu xa’a xo a daukeni dota,” bata rufe baki ba wata lafiyayyar mota tayi parkn gabansu, Ikraam ta bude baki tace “wnn motar xaki shiga,” kan Mami tace komai aka bude driver sit ya fito yana kallonsu yace “sannu mami kina ta jira ko, wllh akwae holdup ne a hanya,” Mami tace “ae ban wani jira ba ynxun nn muka fito kasuwar,” ya karaso gabanta ya duka xae dauki ledan Ikram ta fixge tana kallon Mami tace “Anty waye wnn,” daga kai yyi yana kallonta, ita ko sae kallon Mami take tana jiran Amsa, Mami tayi dariya tace ” ‘da na ne,” Ikram ta gwalo ido ta rufe bakinta da hannu daya tace “lah wnn katon yaron” dariya ssae mami take, shi kam kallonta ya shiga yi daga sama xuwa kasa, wata kodaddiyar atamfa ce riga da skirt jikinta, amma sbda tsabar neatness dinsa ba ka ganin kodewar atamfar, hula ce baka a karkace a kanta sae bathroom slippers a kafarta, girgixa kai yyi hade da dauke kansa ya kwashe ledojin ya bude bayan mota ya saka su, ya juya xae ce da mami ta shiga su wuce yaci karo da Ikraam bayansa, tace “oucch, baka gani ne yaro,” tana shafa goshinta, xae yi magana tace “dan matsa, ina son in leka cikin motar ne,” barin wajen yyi ta tura kanta cikin motar snn ta fito tana dariya tace “ba irin ta kawu bala bane tasa kujerun duk sun yage kuma baya kamshi hka turare ake sa ma motar?,” mami na dariya ta shiga mota tace “maxa ki tafi gida ikraam,” ikram ta juya da gudu ta bar wajen, mami ta kirata da sauri, ta kuma dawowa, mami ta ciro dubu daya ta mika mata tana murmushi tace “daga nn ki wuce gida kin ji,” kai kawae Ikraam ta gyada mata tana washe hakora snn ta juya a guje ta bar wajen.