Miskili Ne 23-24
❤ *MISKILI NE*❤
*23&24*
………wani irin mugun electric chock sheriff yaji Ajikinsa sakamakon rungumar da Amaan ta masa”kasancewar bbu macen daya tab’a bari hakan yafaru tsakaninsu in aka cire Ammi” tsaye kawai yayi k’ik’am awajen,yakasa tab’uka komai”yana jin yadda taketa sakin k’aramin kuka”gaba d’aya jin jikinsa yakeyi ya mutu murus”yakasa furta mata ko a…. Abokinah! yaji muryar mus’ab Abayansu”hakan yasaka yayi saurin janye Amaan daga jikinsa suka had’a Ido da ita”kansa kawai ya girgiza mata Alamar ta dena kuka,yana kuma kallon kayan dake jikinta”mini hijab ce da doguwar riga bak’a jallabiya Ajikinta”bece komai ba yanufi wajen mus’ab dake d’auke da Ahmed yana kuma rik’e da hannun bilkisu”ya d’auka Amaan zata biyosa sai yaga tayi tsaye tana kallon k’asa…….murya akasale shariff yace”bilkisu babu dai wata matsala basuyi muku komai ba ko?”Eh Alhmdllh basuyi mana komai ba”beyi mgn ba ya Amshi Ahmed d’an 3 yrs A hannun mus’ab”gaba d’aya suka nufi k’ofar fita daga lambun “sbd polices d’in tuni sun fice tare da wad’anda sukayi nassarar kamawa”kamar Ance mus’ab yaduba yaga ko Amaan ta biyosu ?”yana dubawa yaga babu ita,yana juyowa yaganta tsaye kanta ak’asa”wanda sarai shariff ya lura bata biyosu ba Amma miskilin yashareta yak’i yimata mgn….. Amaan zomu tafi mana”yafad’a yana kallon ta”ta d’ago kanta tana share hawayenta ta nufosu”shariff kuwa kallo bata isheshiba sukayi gaba”bayan sun fito daga cikin get d’in gidan”mus’ab shida family nasa suka shige motarsa”Amaan dai na tsaye tanata raba Ido”shariff najan tsaki cike da izzah yace”kina jiran saina miki mgn nace ki shiga mota mu wuce? ko kuwa shi mus’ab d’in zaki bi?”tunda gashi d’azun yace kizo ku tafi kin kuma zo…. yafad’a yanata y’an harare harare “Amaan dai batayi mgn ba ta nufi back sit zata shiga”wata uwar tsawa yadako mata yana fad’in waye driver d’inki?nanma batayi mgn ba tana dai tsaye”mus’ab ya fito daga cikin mota yana fad’in laifin me kuma tayi Abokinah?”tab’e baki shariff yayi yana fad’in gata nan saika tambayeta idan tasakanar maka sai kamun hukunci”in kuma binka zatayi ku tafi banida matsala da hakan”yak’are maganar cikin zafin rai yana bud’e k’ofar driver sit yashiga”mus’ab ya girgiza kansa yana nazarin shariff sbd zahiri kishin Amaan ya hango k’arara Acikin k’wayar idonsa”matsawa yayi da sauri yabud’e mata front sit yana fad’in zoki shiga”sbd yasan k’aramin Aikin shariff ne yatafi yabarta”jikinta Asanyaye tashiga”mus’ab yace”yanzun haka An kama Alh Isan yana hannu”shi Alh yahaya d’in zanyi waya atura police suje kabasu shi ko?”banza shariff yamasa sbd wani irin mugun haushinsa yaji yana ji”mus’ab yasaki wani irin shu’umin murmushi me wuyar fassara yarufe k’ofar”saida shariff yamula yasha iska sannan yatashi motar aguje yabar wajen”itadai Amaan batayi mgn ba tana dai satar kallon sa”ya kama fuska ya daure yanata jan k’aramin tsaki jifa jifa”yana kuma driving d’in Anutse “can ya d’an kalleta suka had’a Ido”yamutsa fuska yayi kamar Ammasa tilas yace”tayaya kikaje wajen su?”d’an shiru tayi can tace”dama na fito daga d’akin Ammi bbu kowa a parlourn sai Abban yashigo yace”nazo na Amshi sak’o na kaima Ammi”daya fad’i hakan saiya fita”shine sai na biyosa”yanata tafiya Ina binsa har bayan windows kawai saiya juyo ya fesamun wani abu Afuskata”daga nan na farka na ganni Anan wajensu…..Allah ya kyauta! daga yau duk wanda baki sani ba yace”kizo irin haka karki koma zuwa”Ahankali tace to”can kuma tace”hamma dan Allah kafad’amun Abinda bakaso saina dena”d’an kallonta yayi ya tab’e baki yak’iyin mgn”har suka iso gidan bbu wanda yakoma mgn”sai k’amshin turarensa ketashi Ajikinta sbd hugging nasa datayi d’azun”tun kafin ya gama yin parking Amaan ke k’ok’arin fitowa”shi kuwa dayake yana son kaita mak’ura sai yayi lock d’in k’ofar”bayan yagama parking d’in yayi zaune cikin motar yana danna waya….ita kuma tanata k’ok’arin bud’e k’ofar Amma tak’i bud’uwa”hamma nika bud’emun mana”ta fad’a cikin shagwab’a”banza yamata ,kamarma badashi take ba”can ta fashe masa da kuka tanata jijjigar k’ofar”da mamaki yazuba mata manyan idanuwansa yana kallon ta….kinsan Allah kikamun b’anna saikin sani”naga Ai sauri kikeyi ki fita ko?”to bazan bud’e miki ba sai naga kinyi kukan jini tukum”yafad’a yana gallah mata harara “shiru tayi tana share hawayenta bata koma rok’arsa yabud’e ba”saida yagama shan k’amshinsa sannan yabud’e “itama ta bud’e Ada Aguje zatabar wajen Amma jin yace”ko kiyi tafiya cikin nutsuwa kona tattakaki”hakan yasa batayi gudu ba”saima juyowa tayi ta masa gwalo ta wuce da sauri batare data yi gudun ba”me makon yaji haushi sai yaji murmushi yasub’uce masa wanda be shirya yinsaba”kawai saiya basar yabiyo bayanta”kusan atare suka shigo cikin parlourn”Ammi na ganin Amaan ta mik’e tsaye tana fad’in Alhmdllh y’ata tadawo”Amaan Aguje taje ta rungumeta”shariff dai na tsaye yana kallonsu shida Abdallah dake zaune a parlourn “Allah ubangiji yatsare gaba”sai kije kiyi wanka ki kwanta ki huta ko?”kanta Amaan ta gyad’a mata”Shariff ya k’araso ya zauna suna tattaunah maganar da Ammi “yayinda Amaan ta wuce d’aki batare data tanka Abdallah dake mata jaje ba……sai bayan police sunzo sun Amshi Alh yahaya sannan shariff yabar gidan yanufi office….. Abin mamaki yasami fareedah da nadiya na zaman jiran isowarsa”had’e rai yayi daya hangosu”kai tsaye yanufi wajen ma’aikatan daketa kok’arin ganin an gyara wajen sbd gobarar da Akayi jiya….tun kafin ya musu mgn yaji muryar fareedah Abayansa tana fad’in yallab’ai dan Allah inason mgn dakai”afusace yajuyo ya nuna mata hanyar waje da hannu kafin cikin kakkausar murya yace”wacece ke dakike son mgn dani?”koda zanyi mgn da wata saimai tarbiya da kunya had’e da mutunci zanyi”duk ranar dakika koma zuwa nan kika koma ganina kika nuna kinsanni saina wulak’antaki…. yak’are maganar yana jan tsaki had’e da yamutsa fuska “tsabar mamakinsa kuka fareedah tasaka”Nadiya tazo ta janyeta tana rarrashinta… fareedah na kuka tace “ya cuceni Nadiya! ya kumaci Amana ta dayayi dubaran had’a kai dani sbd yacuci mahaifina….shiru fareedah tayi sbd ganin wasu police na kok’arin yimusu koran kare”hakan yasa suka nufi mota suka shiga zuciyar fareedah na tafarfasa…..sharif kuwa tsaki yaja yana duba Agogon dake daure a damtsan hannunsa”k’arfe 1:11 pm hakan yasa ya wuce masjeed….bayan sallar Azahar Amaan na kwance kan cinyar Ammi tana yimata tsifar kalbar kanta sunata fira har Amaan d’in nayin dariya…. Ahaka shariff yashigo cikin parlourn “tana jin Amon tattausan muryansa sai tayi gum da baki bata koma mgn ba”ya zauna kan kujerah yana yiwa Ammi barka da gida”ta Amsa tana kallon ledojin hannunsa”wanda kayan daya badama Amaan ne d’inki Aciki”Amaan tashi ki d’aura d’an kwali ki kama yayanku ruwa”dato ta Amsa”shariff yayi saurin cewa bana buk’atar komai Ammi tabarsa”yafad’a yana satar kallon Amaan d’in “suna had’a Ido ya tab’e baki ya a sakar mata harara”ta d’auke kanta kawai”mik’ewa tsaye yayi yamatsa ya mik’ama Ammi ledojinsa hannunsa beyi mgn ba yabar wajen”dan gaba d’aya haushin Abinda Amaan ta masa ne Aransa”wato sbd ta tsanesa shine tana dariya dan ya shigo saita d’aure fuska”dama Ance mata yana buk’atar ganin dariyarta ne?”duk ya Ayyana Aransa yana hayewa samansa”kasancewar jiya be samu baccin kirkiba yasaka ya kwanta bacci”sai gab da sallar la’asar yatashi yayi wanka da sallah”k’ananun kaya yasaka ya aza suwaita Asama yasaki hular Abaya”fuskarsa Ad’aure yasakko k’asan “idanuwansa sun rage ja”yayi masifar kyau “Amaan dake zaune tana ganinsa tayi saurin tashi zatabar wajen”Ak’ule shariff yace”ke zonan! dan Allah kayi hak’uri”koma hassalashi tayi ,yana tunanin me yarinyar nan ta mayar dashi wai?”wata zuciyar tace”mugu! bazaki zoba ne?”dama d’an kwali zanje na d’akko”tsaki yaja yana nufar dining area yace”kika sake kika guda zakiyi mamakin Abinda zai biyo baya game da hakan”daga haka yaja kujerah ya zauna”kasancewar k’a’idarsace ba’a seving nasa shine ke zuba ma kansa komai”hakan yasa yazuba Abinda yakeso”be jima da fara cin Abincin ba Amaan ta fito da sabuwar doguwar rigar orange d’in shadda Ajikinta”wacce akayima Aiki da b’akin zare “sosai shaddar ta haska farar fatar jikinta”ta d’aura d’an kwalin saku saku irin d’aurin ture kaga tsiya d’in nan” sai mayafi bak’i data rataya gefen kafad’arta”d’an matsowa gab da dining area d’in tayi Ahankali tace”hamma! k’in kallonta yayi yana cigaba dacin Abincin sa”hamma kayi mgn mana”beyi maganar ba saidai kallonta kawai yayi”saidai wannan karon kallon dayake mata yasha babban da sauran irin kallon daya saba yimata Abaya”be tab’a tsayawa ya kalleta sosaiba kamar irin yau ba”menene?”k’asa tayi da kanta tace “Ammi ta Aikeni bakin get na kira Abdallah”saikin dawo”shine Abinda yafad’a yana bin bayanta da kallo”yana jin bugun zuciyarsa na tsananta bugawa…. Amaan na kawowa zata fita Ibtihal na kok’arin shigowa tadawo daga skul”bata san duk Abinda yafaru ba”kusan banga zar juna sukayi”Amaan ce tayi saurin jaa da baya tana hararar ta batayi mgn ba”bakida hankaline ko kuwa bakya ganine??” cewar Ibtihal tana binta da kallon banza”k’asan zuciyarta tana jin zafin baiwar kyawun halittar da ubangiji yayima Amaan “ita kuwa Amaan tsintar kanta tayi da fincikota tana kai mata mari had’e da cewa”kinga Alamar banida hankalin ko?”saita turata da k’arfi “kutumar ubancan”cewar Ibtihal cikin masifa tana kok’arin nufar Amaan”ita kuwa Amaan saita juya Aguje tana yimata gwalo da nufin tabar wajen…..ji kawai tayi taci karo da mutum”gabanta yafad’i sbd jin k’amshin turaren hamman ta”tana d’ago kanta idanuwanta suka sark’e da nashi”tsaye kawai yayi fuska Ad’aure yana kallon ta….. kasancewar tunda suka fara fad’an yagani hakan yasaka yataso yanufosu”yayi mamakin Amaan data mareta…ke kin Isa ki dakeni kici bulus ne?cewar Ibtihal tana matsowa gefen Amaan”da sauri ta b’uya bayan shariff tana rirrik’e gefen rigarsa tace”hamma ka ganta ko?”ita kuwa Ibtihal bata yadda ta kallesaba danma karya mata kwarjini,tana kuma jin Amaan bata Isa ta mareta ta k’yaleta ba,hakan yasa ta nufi bayan nasa da nufin ta rama……idan kika sake kika tab’a koda hannunta ne sai kinyi nadamar dabaki tab’a yiba Arayuwarki”na baki nan da mintina goma ki kwashe inaki inaki ki bar mana gida”Ayanzun mahaifinki beda wata Alak’a da gidan nan”yafad’a murya Akausashe”kasa mgn Ibtihal tayi gabanta na fad’uwa ta nufi bed d’in Ammi “shariff yadaka mata wata rikitacciyar tsawa yana fad’in ubanme zakije kiyi ne Anan?”batace komai ba ta nufi hanyar d’akinta”yaja tsaki yana juyowa suka had’a Ido da Amaan “hararara yasakar mata yana fad’in waye ya koya miki fad’a da mutane??”Toba itace tafara jana ba hamma”bece komai ba yaduk’a ya d’auki d’an kwalinta daya fad’i k’asa ya mik’a mata”sai tak’i Amsa ta harari d’an kwalin ta yafa mayafin saman kanta”shi kuwa cikin parlourn yanufa ya zauna kan kujerah yana rik’e da d’an kwalin nata”yana k’ok’arin zaro wayarsa Amaan tazo kusa dashi ta zauna tace”hamma wankin kai zaka kaini kokuma Abdallah zai kaini? kuma ni Ina jin sanyi….shiru yayi yak’i mgn “kukan shagwab’a tasaka”can ya girgiza kansa Anutse yace”Amaan kinaso na b’ata miki rai ko?”da yake yanzun kinaso ki Amfana dani ai dole kimun wata shagwab’ar gulma”d’azun kina ganin na shigo kina dariya shine kika dena sbd ga mugu ya shigo ko?”to kayi hak’uri hamma nah”kullum fa zan dinga yimaka komai kake so”ni bana so kana yawan fushi dani dayimun tsawa ko?”shiru yayi yana danna waya”ita kuma tanata kallonsa”abu biyu ke d’aukar hankalinta Asaman kyakykyawar fuskarsa”daga karan hancinsa sai sajensa…Ahaka Abdallah ya shigo da sallama”Amaan ta Amsa tana fad’in yanzun Ammi tace na kiraka”tana Ina ?”tana d’aki”bece komai ba ya kalli shariff yace” my sweet yaya nah sannu da hutawa”d’ago kansa yayi ya maka masa harara”dan har yanzun be Ida hucewa ba”uhmm yaya Amun Afuwa”kunyi kyau kaida Anty Amaan ko Anguwa zakuje ne?”Amaan ta kallesa zatayi mgn shariff yayi saurin take mata k’afarta dake kusa da tashi da takalmisa sawu ciki”hakan yasa ta rintse Ido tana kallon farar lallausan k’afar tata”kafin tayi mgn Abdallah yayi gaba….. idanuwanta har sun kawo k’wallah”shariff ya janye k’afarsa fuska Ad’aure yace “kinaso nace bbu ruwana dake?”girgiza kanta tayi”tashi kije ki d’aura d’an kwalin kizo muje na kaiki saloon d’in”saura idan munje ki dameni da surutu”to hamma sanyi nakeji kabani suwaitar nan na saka mana”ya d’auki kusan second 5 kafin yace”wacce kikeso?wannan ta jikinka mana”tafada cikin shagwab’a tana nuna suwaitar da hannunta”hakan yayi daidai da fitowar Ibtihal rik’e da troley d’in ta tanaja fuskarta bbu walwala ta fita…..✍️
sharhi
wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba