Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 14

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*NASARAR RAYUWATA*

*14*

*Shin kin taba amfani da kayan ummu Dalil kuwa y’ar uwa?, Ina mata Yan kwalisa masu aji masu son gyaran fata da inganta lafiyar fatarsu? Maza ku garzaya ku nemi ummu Dalil tana da ingantattun kayan gyaran fata kamar su body scrub, body butter, lightening oil, beauty soap da half cast black soap Wanda ta hada da ingantattun kayan da ta gudanar da bincike akansu Kafin tayi amfani dasu domin inganta lafiyar fatarmu, mallaki naki ckn aminci insha Allah Muna aikawa kowane gari da izinin Allah sai kun zo*

Inna tare da mmn Nana suna d’aki suna tattaunawa ” kiyi hakuri mmn Nana bani da zabin da ya wuce Hakan saboda tsira da mutuncin mu , hukuncin da na Yanke shine yafi dacewa damu ” mmn Nana kamar zatayi kuka tace ” yanzu malama tafiya zakuyi ku barni ckn wannan gari bayan ke kike bani kwarin guiwa Kuma na Saba zama daku har nake ji kamar bazan iya rayuwa Babu ke bah” kiyi hakuri y’ar uwa ni kaina bahakan nake so mu rabu ba, kaddara ce tazo mana a Hakan nagode kwarai da halaccin da kika min hakika bazan manta Dake ba a tarihin rayuwata, ke din kina daga ckn mutanen da suka min halaccin…” Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar suka rungumi juna suna hawaye, Hajjo ta shigo d’akin da sallama turus ta tsaya ganin halinda suke ciki ” inna meke faruwa , waya mutu?” Mmn Nana ta d’aga jajayen idanunta tana kallon Hajjo take tausayin yarinyar ya kamata batayi wata wata ba ta jawota a jiki ta kankame ta cigaba da hawaye ” mmn Nana menene don Allah ki fadamin meyasa kk kuka ke da inna ?” Murmushin karfin Hali inna tayi tana share hawaye ” kije ki ci abinci kizo akwai inda zamuje ” Babu gardama ta juya ta fice, sauke numfashi inna tayi ita kanta Bata son barin unguwar saboda ansaba ga shakuwa tsakaninta da mmn Nana ga Kuma sana’arta. Shiru ne ya biyo baya can mmn Nana ta d’aga Kai tana kallon inna ” da dai kin canza shawara a Nemo Wani mafitan Banda wannan ” girgiza Kai tayi ” kedai ki mana adua da fatan alheri insha Allah idan komai ya daidaita zamu kawo Miki ziyara, ki min fatan nasara a wannan karon komai zai iya faruwa saboda shekaru sun ja rabona dasu, ni kaina bani da mafitane shiyasa ya zama lallai na koma garesu saboda tsira da mutuncin ya’ta, Ina guje mata shiga gararin rayuwa “.

*7:15am* suna tsaye ta tsallaken titi suna Neman abin Hawa da zai kaisu Tasha , Hajjo sai waige waige take kamar Mai Neman abu. Yana kwance a bayan mota idanunsa a lumshe suke kamar ance masa ya Bude nan kuwa ya saukesu a kanta damn…zuciyarsa ta Bada sauti “stop” ya furta da karfi har fauzan yayi mamaki domin Bai taba Jin ya d’aga murya haka ba, Wani wawan birki driver ya ja Bai Jira komai ba yasa hannu ya balle murfin motar ya fita fauzan ya Bude gidan gaba ya biyo bayansa , sauri yake kamar zai Fadi ckn kankanin lokaci ya iso gabansu tare da sallama ckn nutsuwa kamar yadda ya Saba , inna da mmn Nana ne suka amsa a yayinda Hajjo ta kure mishi idanun tana son tuna Ina tasan wannan fuskar ” Ina kwananku ” “lfy alhmdllh ya gida” lafiya, dama Ina wucewa ne ya hangoku a nan kamar Kuna Neman abin Hawa ” murmushi inna tayi tace ” Amma kamar naso na Gane ka” sunkuyar da Kai yayi ” ni Dan uwan Aman ne ” Aman?” Inna ta furta sunan tana son tunowa ” lokacin da tayi rashin lfy munkai mata ziyara asibiti” dam ..gaban inna ya Fadi ” oh..iKon Allah ya akayi bangane ka ba Yi hakuri don Allah ya wajen naku ” ” lfy alhmdllh, idan bazaki damu ba muje a rage muku hanya ” ah ah..kaga Yi tafiyarka mungode ” ” kiyi hakuri mama dama Ina son ganinki magana zamuyi ” sauke numfashi tayi tace ” kayi hakuri sauri muke kar mu rasa mota don tafiyace a gabanmu Kuma zamuyi Nisan zango ” koh kadan Hakan Bai dace ba, nasan Kuna Shirin barin garin ne saboda Aman Wanda a zahiri Bai dace ki katsewa y’arki karatu da komai na rayuwarta saboda Wani ba” mamaki ne ya bayyana a fuskar inna a yayinda mmn Nana ko Wani dadi ya ziyarci zuciyarta Allah yasa a fasa tafiyan saboda ko kadan batason suyi Nisa da ita. Hajjo kura mishi Ido tayi tana Yaba kyaunsa a ckn zuciyarta yafi Abokinta kyau nesa ba kusa ba kawai dai Aman zai nuna masa haske ne, ita gaba daya hankalnta baya kan maganganun da suke, ” don Allah mama ki bani lokacin ki mu tattauna Ina da mafita idan har zaki bani dama” shiru inna tayi tana nazari ” tsayuwarku akan titi Bai dace ba muje gida muyi magana” sauke numfashi inna tayi Bata da zabin da ya wuce ta saurareshi, da Ido yayiwa fauzan magana ya Gane meyake nufi nan ya sungumi sabuwar jakarsu ta Ghana most go ya wuce mota Ayman yYi gaba inna ta mara masa baya, mmn Nana ta rike hannun Nana ” kizo muje kin kafesa da idanu Babu gaisuwa ” turo Baki tayi ” toh ni nasan shi ne ” ckn tsigar wasa tace ” surukinki ne fah, yayan saurayin naki” cike da kunya tace ” nidai ba saurayi na bane , abokina ne” inna tana jinsu batayi magana ba, fauzan ya Bude musu gidan baya suka shiga, Ayman na Gabar tsakiya,wato jeep ce me gab’a uku na baya tsakiya sai gaba. driver ya ja mota suka fara tafiya fauzan ya juya ya waiwayi inda suke ” Ina zamu bi?” Inna ta Kalli mmn Nana ta rasa me zata fada saboda har ga Allah batason suje can unguwar tasu saboda magulmata, tamkar Ayman yasan tunanin da take yace ” just go to snake farm” fauzan ya fadawa driver nan suka cigaba da tafiya.
Snake farm Wani wajene na gidan gona Wanda aka maidashi kamar lambun shakatawa haka babban gidan gona ne Amma akwai macizai dayawa ana kiwonsu a wajen akwai Kuma kananun dabbobi ga Kuma korama sai rumfa Mai dauke da kujerun zama dayawa a takaice dai wajen Shan iskane mara hayaniya Wanda yake kan hanyar keffi idan ka fito Abuja hanyar makarantar su Ayman ne shiyasa yasan wajen , sau D’aya ya taba zuwa wajen Babu hayaniya ga Kuma kujerun zama Kuma akwai masu siyar da kayan makulashe, ya Duba agogon hannunsa *7:35am* Yana da lectures by 8.lumshe Ido yayi ya sake budesu Yana adua Allah yasa ta karbi shawarar da zai Bata don ko kadan bayason su bar garin suyi Nisa inda bazai Kara Jin labarinsu, yanzu ya Kara gaskata irin son da yakewa yarinyar rashin Jin muryarta Bai masa dadi ba Amma ganin fuskarta yasa ya dan samu kwanciyar hnkli game da halinda yake ciki, driver yYi parking a gefen titi Ayman ne ya fara fitowa ya Bude musu mota mmn Nana ce ta bakin kofa ta fara fitowa sai Hajjo sannan inna , bayansa suka bi ya biya kudin shiga daga bakin gate suka wuce ciki security na mamakin me zasuyi da safiyar Allah haka. Fauzan ya tsaya nesa dasu hakama mmn Nana ta rike hannun Nana suna kewaye wajen suna kallon dabbobin a yayinda Ayman da inna suke zaune bisa wasu kujerun suna fuskantar juna ” kiyi hakuri mama kada Kiga kamar na muku shishigi ckn rayuwar y’arki , tabbas na fahimci matsalarki bakison hulda da masu kudi …” da sauri inna ta d’aga Kai wannan Yana Bata mamaki ” kada kiyi mamaki mama na fahimci Hakan ne ta hanyar labarin da Aman yake bani na cewa y’arki tana da tarbiya Bata karban abun hannunsa, Amma Ina son ki Gane cewa y’arki batayi wayon da zata fahimci soyayya take da Aman ba ita ta dauki Hakan ne a matsayin shakuwa na abota saboda haka nake rokonki kada ki canza mata tsarin rayuwa akan Wani dalilin da batasan da zamanshi bah, kiyi hakuri ku cigaba da zama a nan garin kada ki ruguza mata buri da mafarkinta na rayuwa, ba Ina nufin idan kunbar garin burinta zai wargaje ba aa Amma…” Ban katse Maka hanzari ba Amma Ina son ka gane cewa Hajjo ba sarar auren Dan uwanka bane saboda mu talakawa ne bamu da komai sai wadatar zuci Kuma bamu ajiye komai ba sai abunda Allah ya bamu donhaka nakeson nisantar Hajjo da Dan uwanka saboda Basu dace da juna bah, bana son ta Saba dashi ta kamu da sonsa daga baya ya rabu da ita hakan bazai min dadi bah don ita kadai Allah ya bani itace sanyin idaniyata abin farin cikina , na rokeka kada ka fadawa Dan uwanka wannan labarin Amma barin garin nan shine kadai mafita ” numfashi Ayman ya sauke Yana Jin zuciyarsa Babu dadi idanunsa suka canza launi , karon farko a rayuwarsa yaji bazai iya boye damuwarsa ba ya zama dole yasan yadda zaiyi Hajjo ta kasance kusa dashi.
” Mama ga shawara, ” inna ta kura mishi Ido tana son karantar yanayinsa ” mama ni zan Sanya ta a makarantar boarding school ni zan dauki nauyin karatunta Amma bisa sharadi..” suna kallon juna inna tana mamakinsa ta kasa Gane inda ya dosa ” Ina Jin na cigaba… ” Sharadin shine bazaki taba fada mata cewa ni na dauki nauyin karatun ba Kuma bana son kowa yasan inda take har zuwa lokacin da zata kammala, bana son tazo gida sai ta gama Amma zaki iya zuwa duk karshen wata kina Duba ta” kyam..ta kafesa da idanu tana Jin maganganun nasa tamkar a mafarki ” Anya kana da adalci kuwa?” ta jefo masa tambayar ” Ina fada Maka itace sanyin idaniyata itace farin cikina sannan kana bani shawarar da zan mara nisantani da ita? Waye zai kulamin da ita, waye zai tarbiyantar da ita? idan tayi kuka wazai rarrasheta? Kasan irin son da nake mata kuwa? Bata da kowa Batasan kowa ba sai ni Amma kake son nayi Nisa da ita??” Lumshe Ido yYi baisan ya zai fahimtar da ita ba Amma ya zama dole ya mata filla filla Amma Yana tsoron hukuncin da zata Yanke fadan gaskiyar zai iya tsoratata ya Kara mata himman barin garin me abin yi? Shiru ya ziyarci wajen kowa da tunanin da yake ckn zuciyarsa, Wani bangare na zuciyar inna na Bata shawara akan ta amince da bukatarsa Wani bangare na gargadinta ta d’aga Kai suka hada Ido tace ” meyasa kake son taimaka mana, Meye ribarka Kuma menene a ranka?” Murmushi yYi yace ” bani da wata manufa ahakan kawai naga dacewar Hakan ne Kuma naga kina Shirin tauye hakkin y’ar ki akan Aman” sauke numfashi inna tayi tana kallon wani bangare tace “zanyi shawara” murmushi yYi Wanda ya bayyana jindadinsa ” mama don Allah kiyi tunani da kyau, rabuwa da ita na kankanin lokaci ne Kuma ynzu zaki ga yazo kamar yau din nan idan Muna raye,Kuma ko bayan raina zakiyi alfahari da hakan” kallonsa take tana mamakin kalamansa tana son ta karanci me a ckn zuciyarsa Amma ta kasa , ya Duba agogon hannunsa yace ” kiyi hakuri makaranta zan wuce Ina da lectures ga number wayata idan kika gama shawara, kuyi hakuri ku shiga abin Hawa nayi latti ” ya cire kati a aljihunsa Mai dauke da numbobinsa ya Mika mata . Ya Mike tsaye ya mata sallama ya juya ya tafi tabi bayansa da ido Yana ckn izza da Kamala Kai tsaye inda su Hajjo suke ya nufa, hannu ya saka a aljihu ya zaro kudi ya karasa kusa da Hajjo ” ke, gashi ” ya Mika mata Bata karba ba sai kafesa da idanu kallonta yake suna kallon juna mmn Nana ta tashi ta wuce gun inna ” karba mana kin tsaya kallona ko don nafi saurayinki Kyau ne ” turo Baki tayi” ni yaushe na kalleka Kuma ai aboki yafi ka hasken fata” murmushi yYi Wanda ya Kara fitar da kyaunsa ” na sani, Amma ai ke farace Kinga perfect match kenan black n white” Yana gama fadin haka ya jawo hannunta ya damka mata kudin a hnkli yace ” take care cutie ” nan ya juya ya tafi ta Bude Baki tana kallonsa tana son harhada kalmomin da ya gaya mata

Back to top button