Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 53

Sponsored Links

PAGE* 5⃣3⃣

Sumayya hawaye ne suka fara zuba daga idonta cikin muryar kuka tace please yarima kafahimceni wlh ba abinda kake tunani bane, sharrin shaid’anne kawai.

Wata uwar harara yabanka mata yace na tambayeki?……wlh Sumayya kin ban mamaki daman pills kikesha dan kar kisamu ciki? Inaso kisani duk abinda kika aikata kanki kikayi mawa kuma kanki kika zalunta, na gode ma Allah da bake kad’ai gareniba, kuma idan ke bakyason had’a zuri’a da ni toh wata tanaso, cikin ikon Allah sai gashi Allah yaba zarah ciki har kina ik’irarin cewa tana miki gorin ciki, ashe nan kekad’ai kikasan abinda kike shukawa tsawon dad’ewar da mukayi.
Ammah fa zarah ta burgeni.

Sumayya cikin sauri tad’ago kai takallesa hawaye sha6e-sha6e a fuskarta.

murmushin tskaici yayi sannan yace eh Sumayya,,,sannan inaso kisani kanki kika cuta ba ni ba kuma bazakiga illan hakanba sai nan gaba, a duk lokacin da kika 6ata mahaifarki kar kiyi kuka da kowa sai kanki.

Sumayya rusgar kukanta take kamar wanda aka aiko ma da sak’on mutuwa,girgiza kai tashiga yi dak’yar ta iya bud’e baki tace dan Allah yarima kayi hak’uri wlh sharrin shaid’anne.

Murmushi yarima yayi cikin rashin damuwa yace Sumayya kidaina cewa Sharrin shaid’anne, duk abinda kikayi daidai dake ne bazan yi komai akaiba dan da hankalinki saidai ina gargad’inki da kiguji lokacin da zaki kaini k’arshe dan wlh had’uwarmu bazatayi miki kyau ba….fuskarsa a d’aure kamar wanda bai ta6a dariyaba yace ina kika ajemin files d’ina?

Hannunta yana rawa tayi mai nuni da chan saman wani d’an k’aramim table.

Yarima zuwa yayi yad’auka batare da ya k’ara kallon inda takeba yawuce zai fita daga d’akin, cikin sauri Sumayya tabiyosa tace please yarima kasau…..hannu yad’aga mata sannan yaficce yabar d’akin.

Sumayya na ganin fitarsa nan taduk’e k’asa tashiga rusa sabon kuka cike da bak’in ciki da danasi, ita ba pills d’in da yarima yakamata da su bane yafi tayar mata da hankali, kawai tana tsoron labarin yaje ma su dada dan idan labari yakai musu ta san kashinta ya bushe, cikin sauri tamik’e tajanyo wayanta talalubo number d’in mahaifiyarta takira, sultana sadiya tana yin picking taji kukan sumayya ya cika wayan, a rud’e tace lafiya sumayya? Me yake faruwa?

Sumayya duk yadda taso tayi magana kasawa tayi kuka kawai take,,,sultana sadiya ta yi tambayar ammah ba amsa sai kuka, k’ulewa tayi tadakama sumayya tsawa tace ke ni kinutsu kiyi min bayani!

Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace ummah yau nashiga ukku asirina ya tonu wajen yarima kuma nasan sai su memartaba sunji.

a chan 6angaren sultana sadiya da take tsaye zama tayi tace sumayya me kika aikata?

Sumayya k’ara fashewa tayi da kuka tace ummah ya shigo ya kamani da pills.

Zaro ido sultana tayi cikin fad’a tace sumayya anya kina da hankali? Ban gargad’ekiba akan yin family planning? Ke wace irin kidahumace, wlh kije na gama shiga subgarki tunda ke bakida wayau, toh yanzu ga kishiyarki chan da ciki k’ila idan tahaihu zaki dawo cikin hayacinki.

Sumayya k’ara rushewa tayi da kuka tace ummah dan Allah kitaimaka min wlh na daina daga yau,

Sultana tsaki taja cikin 6acin rai tace kar ma Allah yasa kidaina inma wani yake zugaki kina wannan iskancin toh ba abu bane mai kyau, kin barni ina ta fama wajen ganin na taimakeki anzubar da cikin wata ashe ke kina nan kina d’irkan maganin hana haihuwa, kije kawai kiyi yadda kikeso ni na zare hannuna ga lamurranki….sultana sadiya tana fad’in haka takashe wayanta.

 

Sumayya tana jin sultana sadiya ta kashe wayan, dafe kanta tayi tacigaba da rusa wani irin kuka, tunowa tayi da zinat cikin sauri tanemo number d’inta tayi dialing.

 

Har tatsinke zinat batayi picking ba, tana shirin k’ara kira saiga kiran zinat ya shigo, cikin sauri sumayya tayi picking.

Zinat cikin muryar bacci tace ya dai baby,

Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat na shiga ukku.

Zinat cikin tashin hankali tace sumayya me yake faruwa? Wanine yarasu?

Sumayya cikin kuka tace zinat asirina ya tonu wajen yarima ya gano ina amfani da pills.

Tsaki zinat tayi tace toh sai me dan ya gane?

Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace sumayya kinsan abinda kike cewane? Ko bakiji abinda nace mikiba.

Zinat murmushi tayi tace haba sumayya ni wlh kunya kike bani yanzu saboda Allah saboda d’an wannan abun kike 6arnan hawayenki?

Sumayya shuru tayi tana saurarenta fuskarta d’auke da mamaki.

Zinat jin batayi maganaba yasa tace baby kikwantar da hankalinki kimori rayuwa kar ki saki kiyarda kifara haihuwa yanzu dan wlh zakiyi saurin tsufa kuma daga inda kika fara haihuwa yara duk sai sun rikitaki bakida lokacin kanki, kuma mijinki zaiyi baya da ke.

Sai a lokacin sumayya tayi magana tace zinat kifahimceni wlh yarima yana son haihuwa.

Tsaki zinat tayi tace kefa matsalata dake kenan baki ganewa, kinsan daga inda kika fara aje ‘ya’ya komai zaibi ya jagule miki mijinkima zai fara tunanin k’ara aure dan gaba d’aya zaki gunduresa, kibari kawai sai shekara mai zuwa lokacin kin tara abinda kika tara na dukiya a lokacin mijinki yana muradin ‘ya’yan sosai toh zakiga rawan kai wajensa dan bazai k’ara yarda yayi nisa da ke da babynkiba, indai kuma kina tunanin cikin wannan bagidajiyar yarinyar ne toh kidaina tunani kikwantar da hankalinki dan da nazo zai tashi aiki.

Sumayya cike da gamsuwa da maganar zinat tace hakane saidai yanzu ummah ta yi fushi da ni bansan ya zanyiba.

Dariya zinat tayi tace kar kidamu zan fad’a miki yadda zaki shawo kan yarima da ummah.

Sumayya murmushin jin dad’i tayi tace nagode sosai zinat saisa nake k’ara sonki.

Dariya zinat tayi tace bakomai baby nima kinsan ina sonki sosai insha Allahu nan da upper week zan shigo garin, Sumayya wani irin farin ciki taji ta dabaibayeta tace kai baby ammah wlh naji dad’i kuma nayi murna, ji nake kamar injawo lokacin yayi.

Dariya zinat tayi tace kai baby gaskiya naga alama kinyi missing d’ina sosai, yanzu dai bari inje bank zan yi miki depositing d’in wasu kud’i idan nagama komai zan kiraki muyi magana.

Sumayya ciki jin dad’i tace ohk dear sai najiki.

 

Yarima koda yakoma part d’insa tisa files d’in yayi gaba yana kallo ya kasa cigaba da aiwatar da komai, tausayin zarah ne da nadamar abinda yayi mata suka kamasa, dan tabbas ya san zarah ta cika mace ta gari tunda tana d’auke masa buk’atunsa kuma har ta amince tayi renon cikinsa abinda ‘yar uwarsa ta jini takasa, tunowa yayi da wulak’ancin da yakeyi mata tsaki yaja tare da dafe kansa yace ya akayi hakan ya kasance? Tabbas nasan zarah fushi take da ni, ji yayi duk ba dad’i dan haka yamik’e yafito yanufi part d’inta.

 

Yarima ahankali yatura k’ofa yashiga ganin babu kowa parlour yasa direct yanufi bedroom d’inta.

Zaune yahangota saman gadonta ta buga tagumi, zarah juyowa tayi takallesa wani irin dad’i taji a ranta sannan tajanye idonta daga kallonsa,

Yarima tsaye yayi yana k’are mata kallo ta d’an rame, duk sai yaji ba dad’i,,,ahankali yataka yanufi inda take daga gefen gadon yazauna,

Kallon zarah yayi da tad’auke kanta tak’i kallonsa tabbas ba k’aramin fushi take da shiba, hannu yakai yarik’o nata gabad’ayansu wani irin shock sukaji a jikinsu yarima runtse idonsa yayi ahankali yafurta zarah….shuru yayi maganar ta lak’afe a mak’ogoronsa dan baisan ta inda zai faraba.

Har a lokacin fuskar zarah a d’aure take kuma bata juyo takallesaba tana dai saurare taji abinda zai ce mata,

Chan k’asan mak’oshinsa kamar wanda akayi ma dole yace please kiyi hak’uri.

Ba zarah ba hatta shi kansa yarima da yayi maganar saida yaji wani iri dan a karo na biyu da zarah taciri tuta yaimata abinda bai ta6a yi ma waniba bayan iyayensa shine kalman hak’uri,

Zarah fizge hannunta tayi tamik’e cikin sauri tanufi toilet, yarima kiran sunanta yashigayi ammah ina tuni ta shige nan tamaida tarufe,

Cike da takaici yarima yadafe kansa da hannuwansa biyu shi kansa ya san tabbas ba k’aramin 6atama zarah rai yayiba a karo na farko da yaji haushin kansa ya kamasa dan gaba d’aya zuciyansa zafi take masa.

Ya dad’e zaune saida yayi kusan 30minutes ganin batada niyan fitowa yasa yamik’e jiki babu k’wari yafita yabar d’akin.

Zarah tunda tashiga toilet d’in kuka tashiga rerawa ita kanta batasan tak’amaiman dalilin da yasa take kukanba, saida taji fitar yarima sannan tawanke fuskarta tabud’e k’ofan tafito tahaye saman gadonta takwanta tana sheshek’ar kuka.

Shi kansa yarima duk ji yayi ba dad’i dan gaba d’aya ji yake komai ya kwancemasa duk wanda yakallesa sai yasan yana cikin damuwa, koda yakoma part d’insa key d’in motansa yad’auka yafita yabar gidan yaje gidan gona.

A saman 3 seater d’in da take parlourn yakwanta gabad’aya shi kansa ya rasa gane tak’amaiman abinda yasa duk yacanza dan wani iri yakejinsa daga k’arshe kallo yakunna nan yazauna yana kallon wrestling.

 

A nan yayi sallar isha’i sannan yakama hanyan gida.

 

Koda yakoma gida, part d’in zarah yakallah har zai wuce nasa sai kuma yaji baya iya wucewa dan haka yafasa yanufi part d’inta, a parlour yasamu kuyanginta zaune baibi ta gaisuwar da sukeyi masaba yawuce yanufi bedroom d’inta.

Lokacin zarah tana kwance saman darduma tana tasbihi, k’amshin turarensane da taji yasa tagane ya shigo d’akin, cikin sauri tamaida idanunta tarufe kamar mai bacci,

Yarima tsaye yayi yana kallonta dan duk atunaninsa baccin takeyi, ahankali yatako ya iso inda take duk’awa yayi yad’auketa yanufi gado da ita.

Koda yakwantar da ita zama yayi gefenta ahankali yazare mata hijab d’in da take jikinta sannan yazuba ma fuskarta ido ganin yadda tayi fayau da ita.

Zarah ahankali take safke numfashi kamar irin na masu bacci, tana jinsa yakai hannu yad’age mata rigar da take jikinta nan yashiga shafa cikinta, duk’ar da kansa yayi yai kissing d’in cikin sannan yagyara mata rigarta yajanyo blanket yalullu6eta.

Mik’ewa yayi yanufi k’ofa koda yabud’e saida yajuyo yakalleta sannan yafita tare da rufe mata k’ofan.

Zarah tana jin fitansa tabud’e idonta, yaye blanket d’in tayi tamik’e taje tamurza ma k’ofanta key sannan taje tayi wanka tayi shirin baccinta takwanta.

Yarima ma koda yakoma part d’insa wanka yayi yashirya sannan yahau saman gadonsa yakwanta, ina nan bacci yace baisan batunba, haka yaita juyi, nan zarah tacigaba da fad’o mai a rai ko ya runtse idonsa ita kad’ai yake gani duk yadda yaso yajanye tunaninta a ransa kasawa yayi, yarima ya ja tsoki ya fi sau goma a lokacin, sai daga baya yasamu bacci yad’aukesa.

____________

Dasafe bayan yarima ya gama shirinsa yana shirin fita sai ga sumayya ta shigo d’akin, kallo d’aya yayi mata yad’auke idonsa nan gabad’aya fara’ar da take a fuskansa tagushe.

Sumayya bata damu da yanayin da tagansaba zuwa tayi tazauna gefensa cikin kwantar da murya tace please yarima kayi hak’uri kayafemin abinda na aikata insha Allahu bazan k’araba na daina.

Ko inda take bai kallaba yashareta,
Sumayya marairaicewa tayi tace dan Allah kayafemin na yi maka alk’awali wlh bazan k’araba.

Wani irin kallo yarima yawurgamata sannan yace sumayya duk abinda kika za6a ma kanki daidai da ke ne, bana bak’in cikin hakan,

Shuru yad’anyi na lokaci kad’an sannan yace a tunaninki mata nawa suke bibiyata, mata nawa duk’awa suna rok’ona sukeso in auresu? Ke kin samu dama saisa kike yadda kikeso, hanya yanuna mata yace tun kan mutuncinki ya ida zubewa a idona tashi kifita kiban waje.

Sumayya kallonsa tayi taga babu alamun wasa a fuskansa dan haka tayi sauri tamik’e, tsayawa tayi gabansa tace please yarima ka…..wani irin kallo yawatsa mata cikin sauri tajuya tafita tabar d’akin.

Binta yayi da kallo cike sa takaici dan gani yake duk ita taja zarah take fushi da shi, tsaki yaja sannan yamik’e yad’auki wayansa da key d’in mota yafito.

Part d’in zarah yawuce dan yadubata saboda baya jin dad’in fushin da take da shi.
yana shiga zaune yatarar da ita a parlour saman cushin ta ci kwalliyanta tana sanye cikin english wears riga da skirt ta tufke gashin kanta, gabanta cup d’in coffee ne aka d’aura saman table.

Yarima tsaye yayi yana kallonta dan gabad’aya taso tarikitasa da yaganta, zarah d’ago kai tayi suka had’a ido saida gabanta yafad’i cikin sauri tajanye idonta daga kallonsa dan ita kanta saida tasamu tasaita nutsuwanta.

Takowa yayi yazo inda take zaune daga gefenta yazauna gab da ita nan yazuba mata ido, sharesa zarah tayi tad’auke kanta gefe kamar batasan da zamansaba.

Yarima ma janye idonsa yayi daga kallonta nan sukayi shuru gabad’ayansu, ganin batada niyar yin magana yasa yarima yace ke baki iya gaisuwaba?

Zarah d’aure fuska tayi kamar ba zatayi maganaba sai kuma chan tace ina kwana?

Shuru yarima yayi kamar bai jitaba saida yayi kusan minti d’aya sannan yace ya kike?

Ta6e baki zarah tayi sannan tace lafiya,,,,,tana fad’in haka tamik’e zatabar wajen.
Cikin sauri yarima yajanyota tafad’o jikinsa, ido suka zuba ma junansu zarah cikin sauri taruntse idanunta, yarima cigaba yayi da kallonta sai chan yakai hannunsa yashafi k’ashin wuyanta, ahankali kamar mai rad’a yace baby bakison cin abinci duk kin rame.

Zarah shuru tayi tak’yalesa tana ji yatura hannunsa cikin rigarta yana shafa cikinta tare da kwantar da kansa saman k’irjinta, su dukansu cikin wani irin yanayi suka shiga

Zarah ce tafara dawowa cikin hayyacinta dan haka tabud’e idanunta tanemi taturesa ganin ta kasa yasa tafashe mashi da kuka,

Cikin sauri yarima yad’ago yakalleta yace lafiya?..

Cikin kuka tace ni kakyaleni.

Yarima batare da ya yi maganaba yasaketa nan cikin sauri tamik’e tashige bedroom d’inta.

Yarima binta yayi da kallo har tashige nan yamaida kansa yajingine da kujera haushi da takaicin kansane yakamasa, daga k’arshe mik’ewa yayi jiki ba k’wari yawuce yabar part d’inta.

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

Back to top button