Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 16

Sponsored Links

*talented writers forum*

*16*

*GLOW SQUAD Kuna Ina ku fito ku fito ku gyara jiki mata iyayen gyara Ummu Dalil tazo muku da zafafan kayan gyaran fata akwai organic skincare products akwai Kuma Oriflame products gyara shine mace tested and trusted Siyan nagari… Ku tuntubi 07030077024 domin Karin bayani*

Ammi tana xaune a falo tana duba wyar hannunta Ayman ya shigo da sallama a gajiye, gaisheta yayi yazo zai wuce ta dakatar dashi ” Ina ka samo sabuwar mota?” Cike da mmki ya d’aga Kai Yana kallonta ” yes! Kalleni da kyau jiya da yau ance min kana yawo da wata sabuwar mota Kuma ba motar gidan nan bane Ina jiran amsa ynxun nan banson Bata lokaci” kiyi hakuri Ammi motar abokina ne tare muke fita ” tsaki taja ” wato so kake ka tsiro da wasu halayen koh, ynxu duk motocin gidan nan Basu isheka ba sai kabi Wani Yana Maka lift salon a raina arxikin gidan nan koh” sunkuyar da Kai yYi ” kiyi hakuri insha Allah bazan Kara ba” da dai yafi Maka wllhi don banason rainin wayo ” a hnkli ya juya ya tafi Kai tsaye bagarensu ya wuce, karar TV yaji nan ya tabbatar Aman na falon donhaka ya shigo da sallama , Yana kwance bisa resting chair hannunsa rike da waya da Kuma remote ” man how far jiya naga fitowarka snake farm kodai ka fara buga solo love ne ” hararinsa yayi yace ” wato Ido ka fara sakamin kana bibiyata da inda nake zuwa ” ” Allah ya kiyaye mezan samu idan nayi hakan, kawai dai zan wuce skul ne na hangoka by mistake ” ” da dai yafi Maka” yasa Kai ya wuce, tsaki Aman yaja tare da cewa ” miskilin banza kawai…mtsww” wayarsa tayi Kara ya Duba zee ce tsaki ya ja ya kashe wayar gaba daya ya rufe Ido bayason matsalarta ta fiye naci gashi har ta fara masa zancen aure, Ayman na shiga daki ya zauna bisa gado ya sauke numfashi fauzan ya shigo da sallama ya ajiye school bag nasa tare da Kai hannu Yana cire masa safa , Bai Musa ba saboda ya gaji sosai Yana bukatar kwanciya. Ya cire safan tare da takalman cover shoe Dake makale a kafafun nasa ” a hada Maka ruwan wanka ne my prince ” Kai ya gyada alamar ehh.. nan fauzan ya wuce toilet ya hada masa ruwan ya fito, suit na jikinsa ya taimaka masa ya cire sannan ya juya zai bar d’akin sa Kuma ya tsaya, Ayman ya d’aga Ido Yana kallonsa ya Gane me yake nufi donhaka ya fara magana ” Allah ya taimakeka akwai Wani babban lamari dangane da mahaifiyar yarinyar nan,” kura masa idanu yayi Yana jiran Karin bayani fauzan ya cigaba da cewa ” is like she is educated Kuma at the same time she is civilized, ni Ina ganin wannan rayuwar da suke ciki Bai kamace su ba dole akwai wata magana a kasa idan har ka bani dama zan bincika asalin tarihinsu ” lumshe Ido yayi ya gyada Kai daga haka fauzan ya juya ya fice don a duniya idan akwai Wanda yasan Halin yarima Ayman toh fauzan ne saboda tun suna yara suke tare yasan halayensa cki da waje ya gama fahimtarsa yasan abunda yake so da Wanda baya so. Toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya Haye gado ya kwanta Bai nemi abinci ba Yana bukatar nazari akan abubuwa dayawa at least matsalolin nasa sun ragu don ya samu ya kawar da matsalar Hajjo yanxu saura matsalar aurensa Dake gabatowa, Yana son sanin menene next step da ya kamata ya dauka akan Hajjo ynxu dai ya gama yarda da cewa ya fada trkon sonta Babu yadda ya iya toh Amma shin zata so shi? da alama hankalinta yafi karkata kan Aman ynxu menene mafita? Yaya zai tunkareta Kuma wane lokaci yakamata ta Yaya zai tunkari inna da wannan maganar? Tabbas ita din macece Mai kaifin basira zata iya hango cin amana ckn wannan lamarin amma Babu ynda ya iya da zuciyarsa musamman Kuma idan yYi la’akari da auren da ake Shirin yuwa Aman din, iska ya furzar Yana kallon rufin d’akin Wanda pop ne ya mamayeshi da farin fenti.

************
Har yamma inna tana nan jugum ckn zuciyarta Babu dadi ga Wani tsananin kewar Hajjo Dake addabarta har Wani zuciyar na Bata shawarar ta koma gobe ta dauki abinta, Wani bangaren zuciyarta na nuna mata rashin dacewar Hakan Duba da yanayin Ayman da irin shawarwarin da ya Bata da Kuma makudan kudaden da ya kashe, idan tayi hakan Bata kyauta masa ba Amma abunda ta kasa ganewa shine meyasa Ayman yake Basu tallafi irin haka Anya kuwa saboda Aman ne? domin ita ta hango Wani abu daban ckn idanunsa toh amma ai dashi da Aman uwa Daya suke ta Yaya Hakan zai faru? mmn Nana ta shigo ta zauna kusa da ita ” Kai malama ashe dai ke y’ar binni ce, Kinga yadda kika hau wannan abin ( escalator) ai ni saura kadan na Suma wajen, irin wanga Abu suu…kawai ya fisge mutum, Kai rayuwa lallai habuja babban binni ce kuwa, Kinga gidaje lallai Hajjo zata zama y’ar binni ita ko irin wannan kyaun ginin makarantar” murmushi inna tayi tare da cewa ” don Allah mmn Nana kibar wannan zancen kinsan mutanen unguwar nan da kananun maganganu ynxu duk Wanda ya tmbaya zamu ce na maidata gida karatu shikenan” ” hakane Kam Allah dai ya Bada sa’a ynxu Kinga zakiyi sana’a ckn kwanciyar hnkli sai ki kara dagewa kina samun kudin ana Kai mata koh” ” hakane dole na tashi da kaina ba sai na Jira Wani ba Allah ya shige mana gaba, gobe zamuje kasuwa na hada kayan turaren wuta da na sabulu insha Allah” Allah ya kaimu gobe” daga nan suka cigaba da hirar duniya inna dai tana boye damuwarta ne Amma ckn zuciyarta tunanin Hajjo ne fal.

______
Haka rayuwa ta cigaba da guda ta kowane bangare, inna ta tashi tsaye tana sana’oin ckn gida ga Kuma almajirai da ta dauka suna Saida mata da pure water da zobo da kunun Aya kullum safe da yamma Allah ya Buda mata ckn kankanin lokaci ta sayi karamar fridge ga Kuma turaren wuta da humra da sabulu da dilka na gyaran jiki abin sai sambarka ynxu duk fadin Aso ansanta malama Mai kayan qamshi Ake kiranta ga Kuma karatun da take Bata daina ba, sukan Yi waya da Hajjo ynxh hnklin inna ya kwanta sosai har ta fara dan murjewa daga nan Kuma mazan unguwa suka kyalla Ido sukayi caa kanta suna zuwa ne na zancen aure ita Kuma Babu Wanda ta bawa fuska har mmn Nana takanji haushin meyasa bazata amince ta daura aure ba, dariya zatayi tace ” haba mmn Nana Ina aka taba yin haka sai kace bani da ilimin addini” da haka take rufe mata Baki , Ayman kuwa ba laifi yakan kirata su gaisa har sun dan fara sabawa duk da cewa ba Wani hira suke ba daga gaisuwa sai gaisuwa Amma Babu laifi inna tana bashi kulawa domin kuwa idan Bai kirata ba na Yan kwanaki zata kira taji lafiyarsa , ana ckn haka Hajjo tayi wata 2 a makaranta donhaka inna ta shirya zuwa dubota ta mata girki da stew dayawa Wanda zai mata sati tana ci ta hado mata abubuwan da tasan zata bukata ta shirya ita kadai ta tafi saboda mmn Nana zata kula mata da kasuwancin ta, Hajjo tayi murna sosai sun Sha hirarsu daga karshe suka rabu suna Mai kewar juna har ckn zuciyar inna taji dadin yadda ta samu hajjon tayi kyau ta Dan murmure adua ta mata da fatan nasara a rayuwa.
da yamma ta iso gida saboda hold up tana zaune a farfadan gidan ita kadai mmn Nana taje cefane , wayarta yYi ringing Ayman ne Dake ba tare sukaje ba tasan ya kirane yaji ko ta dawo gida murmushi ya bayyana a fuskarta ta amsa sallamar tasa ” Dan gidan inna Gani na dawo ban Bata bah” murmushi Mai sauti yYi yace ” dama nasan bazaki Bata ba innarmu saboda ke din jaruma ce” ya gida ya karatu” lfy alhmdllh ya sanyin idaniya ” dariya tayi duk lokacin da ya kira wannan sunan tasan tsokanarta yake Ji ” tana nan lfy kalau har wata y’ar kiba tayi” Masha Allah ynxu dai Ina fatan hankalin innarmu ya kwanta ” alhmdllh godiya ta tabbata ga Allah nagode sosai Allah ya biyaka da mafififcin alheri a rayuwarka ” Ameen ya rabbi” Yana Jin dadin aduo’in da take masa shiyasa yake son kiranta a waya Yana jinta a rai tamkar ummarsa ce saboda halinsu iri Daya na saukin Kai da Ganin girman Dan Adam ba irinsu Amminsa me wulakanta mutane ba ko jiya sai da ya sameta tana cin mutuncin wannan sabon maigadin…” Ya akayi akwai Wani abu ne naji kayi shiru” adua nake bukata innarmu Ina ckn mawuyacin Hali ki sakani ckn sallolinki Allah ya yaye min ya saukaka min ” subhanallah…meke faruwa” murmushi Mai ciwo yYi duk duniya Babu Wanda ya taba goyon bayansa akan auren nan har ummansa tana son auren Amma karo na farko yaji a ransa cewa zai samu Mai goyon bayansa duk da cewa Babu abunda zata iya masa akai, ” kayi shiru Dan gidan inna” inna jarabawarmu saura sati 2 Kuma ana son a min auren gida bayan na gama jarabawar ” murmushi tayi ” ynxu saboda aure kk Bata rai haka Ayman, shin kana da dalilin dayasa baka son auren?” Akwai inna ina da babban dalili”
“Fadamin Ina ji” inna bana son wacce zaa auramin Kuma …, ” Kuma me? Shiru yYi ya kasa magana da zai ce mata bayason sarauta sai Kuma ya tuna batasan waye shi din ba, ” Ayman!
“Inna kedai ki min adua”
“Naji zan Maka adua Amma Ina son ka kwantar da hankalnka ka rubuta jarabawa idan ka gama sai mu tattauna Allah ya baka nasara” “Ameen nagode innarmu sai anjima ” ya Katse Kiran, inna tayi jugum tana Jin tausayin Ayman su kuwa iyayensa meyasa zasu masa aure da yaranta a tattare dashi saurin me suke haka, Allah ya zaba masa Mafi alheri haka nan ta Bude wajen text message ta fara rubuta masa aduan istikhara har ta gama ta tura masa sai ga kiransa ya shigo ” inna ynxu naga sakonki nagode” “ka karanta aduar da niyya kullum ka Fadi bukatarka ka barwa Allah zabi insha Allah zaka ga haske ckn lamarin ” nagode innarmu ashe zan fara zuwa daukan karatu ” murmushi tayi tace” Allah ya kaimu ” nan ta Katse Kiran tana murmushi mmn Nana ta shigo da sallama tana kokarin zama ” Hala ke da y’ar d’akin nawane Ake waya naga sai faman murmushi kk” ” Kai mmn Nana..toh ba ita bace Ayman ne”
“Ah..toh kice dayan Dan gaban goshin naki ne don naga ynxu ya samu matsuguni ckn zuciyarki malama tunda har kiransa kk ” murmushi tayi tare da cewa ” ba dole ba mmn Nana ai yaron ne akwai kirki da sanin ya kamata Kuma gashi nan da nitsuwa bashi da rawan kan matasan ynxu Sam wllhi ” aifah ga Kuma rashin son magana ni nayi mamaki da naga ynxu Kuna Dan dadewa a waya dashi ,” haka suka cigaba da Yan hirarrakinsu har aka kira magariba suka tashi don gabatar da sallah.
Da dare Wani yaro ya shigo yace ana sallama da Hajjo a waje, inna tace Bata nan sai ga yaron ya dawo yace ana son magana da inna ckn mamaki tace toh wanene haka a ce ya shigo, tabarma ta shimfida masa nan akayi sallama qamshin turare ya mamaye gidan duk da bbu haske sosai inna ta ganeshi Aman ne nan ya zauna aka kawo masa ruwan sanyi da zobo Yana karewa gidan kallo ckn zuciyarsa Yana tunanin ta Ina zai fara, sun gaisa ckn girmamawa nan yake tambayar Ina Hajjo inna tayi shiru tana tuna gargadin Ayman akan cewa bayason kowa yasan inda Hajjo take toh Amma ai wannan Dan uwansane, ” inna bakice komai ba” ya tambaya ckn kaguwan Jin amsa ” ehh toh Hajjo ta koma Adamawa tana…” Haba inna meyasa zakumin haka, shine ko a sanar dani bayan na fada Miki Ina son aurenta ” murmushi inna tayi” kayi hakuri bamu nemi shawarar ka ba Aman ” cike da Jin kunya ya gane abunda ya fada Bai dace ba” am..am.. bahaka bane Ina nufin da an nemeni ko sallama mayi da ita ” Babu komai ya wuce ynxu dai tana can” Kuma Bata da waya koh inna?” Ah ah Bata dashi ai tana makaranta ne Basu rike waya” shiru yayi can yace ” kuyi hakuri da rashin xuwana wllhi mahaifiyata ce ta kafamin dokoki ta hanani xuwa saboda ankai mata labarin Ina xuwa wajena Hajjo shiyasa ta hanani xuwa, Kuma ynzu suna Shirin Yi min aure ni Kuma na fada musu Ina da wacce nake so, don Allah inna kada ki hanani Hajjo wllhi Ina sonta sosai ” “Allah yasa Hakan shiyafi alkairi ” amen Amma don Allah yaushe Hajjo zata zo ?” Sai anyi hutu ” toh shikenan nagode zan tafi, ya saka hannu ckn aljihu ya cire bandir na kudi ta ajiye mata furr..inna taki karba haka ya dauka ya Maida aljihu ya fita Yana musu sallama kan cewa zai Kara zuwa, numfashi inna ta sauke ynxu ne na Gane dalilin dayasa Ayman ya Bada shawarar cewa Hajjo tayi Nisa da gida wato mahaifiyarsu Bata son wannan alakar lallai dole ta raba Aman da Hajjo, hamdala ta sake Yi tana Jin dadin rashin samun Hajjo a gida da Aman yYi gashi da alama Ayman yafi Aman girmama na gaba dashi.

Back to top button