Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 7

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*7* free page

*Thanks for patronizing love you all irin na hajjo wash..kash.. Kibiyar sonku ya sokeni*

Hajjo sai wani zumudi take saboda tana son Isar da wasikan soyayya ga masoyin nata ta shirya da wuri after school ta kasa jiran maman Nana ta tafi kadai, bayan la’asar tayi ta xuba ido tana Neman Aman amma shiru ta kira yaron jiya ta mika masa letter tare da kudi tace masa ya jira koda bayan magrib ne ya tabbatar ya mikawa aman hannu da hannu yaron ya karba ya nemi waje ya xauna zaman jira har ta gama siyar da ruwa abincin maman nana ya kare bata hango motar Aman ba duk tabi ta damu tana tunani meyasa baizo ba kuma bai bata amsar wasikar tata ba dama Habiba ta fada mata cewa idan yana sonta zai rubuta Mata amsa amma gashi shiru, har lokacin tafiyarsu gida yayi suka wuce.
Al’amarin Aman kuwa a ranar ya shirya xuwan school saboda ya fara aiwatar da mission nasa akan hajjo tare suka fita as usual kowa ya wuce wajen lectures nasa sai da yamma suka kama hanyar komawa, yau hold up yayi yawa basu iso maraba da wuri ba har goshin magrib yana dube dube bai hango hajjo ba haushi ya kamashi suna nan yaron jiya ya leka ya mikawa Ayman letter yasa hannu ya karba smiling at d boy ya cire 1k ya mika masa yana xuba godiya har suka tafi. Aman ya cika yayi fam kamar zai fashe suna xuwa gida yayi saurin ficewa daga cikin motar ya kira wani driver yace ” ka shirya daga gobe zai zaka driver na na school ” ya wuce bai jira amsa ba, Ayman kuwa har wani zumudi yake na son karanta letter din ya kwanta a gado ya bude ” bayan dubun gaisuwa mai yawa Habibi masoyina ina sonka dafatan kana sona I love you me you me too me miss ” dariya ne ya kubce masa ya sake karantawa yafi sau biyar kafin ya nade ya ajiye inda ya ajiye na jiya, murmushi yake ya tashi zai shiga wanka wayarsa tayi ruri yana dubawa sabreena ce tsaki yaja yayi shigewarsa toilet ya wAtsa ruwa yana fitowa yaci karo da Aman hararinsa yayi babu Wanda yayiwa Dan uwansa magana ya bude wardrobe ya dauki kayan da zai saka, yana shirin fita Aman yace ” Umma ta kira tace meyasa baka daga calls din wata sabreen ne ko sabran waye oho, tace ka kirata back ” tabe baki Ayman yayi yace ” mayya kawai bana kusa ma bzata kyaleni na huta ba mtsww..” Murmushi Aman yayi ” mai farin jinin yan mata harda almajirai naga ana baka love letter koh” da gudu ya fice don Ayman yayo kansa , yana dariya yana sauka a staircase Ayman na biye dashi Ammi na waya kawai ya makale mata a baya yana buya Ayman kuwa yana kokrin fisgosa Ammi ta katse kiran ” me haka din anya lafiyanku kuwa,yara babu shiri kamar y’ay’an kaji ” ” Ammi ki gaya masa bana son abunda yake min ” Ammi kawai don nace yana da farin jini don naga wata almajira tana sonsa shine..”. What? Almajira kanka d’aya kuwa ayman , are you serious ko wasa kuke toh koda wasane kada na sake jin kana hulda da y’ay’an masiyata bana so Sam sam kana jina koh, both of you bana son kuna shiga harkar talakawa OK ” OK suka amsa cikin sanyin murya saboda Ammi bata boye bacin ranta ba ko kadan ta nuna kiyayyar da takewa talakawa a fili ta fara tafiya sai kuma ta tsaya tace ” Dady na hanya anjima zai sauko, kar kuyi nisa idan yashigo ku gaisa “sama ta wuce ta cigaba da amsa wayar da take . Ayman yace ” did u see that,ka gane me nake nufi idan nace baka da wayo right, surutunka yayi yawa sai ka rage” ya tashi ya tafi wajen cin abinci Aman ya sauke numfashi ya nemi waje ya xauna yana tunanin hanyar da zai bi don ganin ya jawo hankalin hajjo she is small but gara ya fara shiryata da wuri tun kafin ta kara wayo ko wani ya rigasa zuwa.

_________ ______________

Karfe 9 na dare daya daga cikin motocin Adamawa sunshine ta shigo birnin tarayya driver yace ” ina masu sauka a mararaba gara Ku sakko daga nan bazan kara tsayawa ba sai jabi park ” wani yace ” driver bazaka tsaya a nyanyan ba ?” ” bazan tsaya ba sai jabi ” haba wannan wane irin wulakanci ne zaku wuce ta Nyanyan amma kace bazaka tsaya ba ” nan hayani ta tashi driver ya ja birki yace ” fasinjan maraba da Nyanya sun sakko daga nan ” nan mutane suka fara fitowa ana ta zage zage driver da wani fasinja suka fara daga muryoyinsu nan Sule ya fara ba driver hakuri suna buga pidgin English dakyar aka kashe magana kowa ya Debi kayansa yayi gaba ya rage mutane kalilan dama population na maraba yafi yawa. Bayan dogon tafiya suka iso jabi kowa na sauka mala Sule ya fito ya tsaya yana kallon hasken wuta ga benaye da manyan gidaje da plaza da sauransu sai raba ido yake ta ina zai fara Neman Amina da hajjo cikin wannan babban birni haka, wani mai sha’i ya hango dama yunwa yake ji nan ya wuce aka dafa masa indomie ya xauna jira yana kallon mutane yadda suke kaiwa da komowa kamar ba dare ba, an xuba masa indomie yaci yasha tea yayi hamdala ya nemi ruwa yayi alwala ya gabatar da sallolin dake kansa na magrib da isha dama sunyi zuhr da la’asar a can Alkalerin Bauchi yayi aduan samun nasara kan abunda ya kawosa birnin Abuja Allah ya sadashi da iyalinsa. Wata black hummer jeep sai daukar ido take daga gani kasan na masu garin ne, yana sanye da manyan kaya ga qamshin turare dake tashi tana kwance a kafadarsa yana rungume da ita da hannu d’aya dayan hannun kuwa yana rike da cup na juice yana Dan sipping ” thanks wife nasan kina matukar qaunata da y’a’ya na nagode , Allah barmu tare I love you so much ” murmushi tayi irin na kasaitattun mata tace ” haba Oga nah me abin godiya a ciki nike da godiya don ka bani komai na rayuwa ” ” is OK you deserved it, ya yaran ya Dan gatan naki hope ya fara hankali yanxu ” ” toh alhamdulillahi muna fama amma da sauki since ya daina xuwa night clubs da tara yan mata ” ” good news ya favourite naki Prince hope yana enjoying garin namu babu matsala ” ” dama kinsan Ayman bashi da matsala kawai karatune baya so but yanxu da sauki yana concentrating ” ” daz good sai me kuma ” saitin kunnensa takai bakinta ta masa rada nan ya kwashe da dariya irinta manya driver sai sharar gudu yake , suna hiransu mai ban sha’awa ya ajiye cup din kenan driver ya taka wani wawan birki , Ammi tace ” wane irin iskanci ne haka ” salatin da driver yake ne yasa suka fito gaba d’aya mutumin na kwance a kashe jina jina kamar babu rai nan driver ya rike kai yana salati Ammi na zare ido cike da tsoro dady ya kalli gabas da yamma babu wata mota mai zuwa yacewa driver ” dauko shi kasa a bayan mota ” zare ido tayi tace ” a bayan mota kuma dady, idan police suka taremu kuma fa da alama fa ya mutu gara mu tafi kawai Ku barshi a nan ” dady yayi wani murmushi yace ” haba Amina baki da imani ne, ki duba halinda yake ciki ai gara mu tafi dashi gida sai a kira doctor a gida koh ” nan driver ya kinkimoshi dakyar ya saka a mota.

*pay your 300 n read peacefully, bazan ja Allah ya isa ba since you r all matured kunsan hakkin amana idan kikayi forwarding ya rage naki, tuntubi 07030077024 for payment details thank you*

Back to top button